← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 82

Sashe 44

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Duka gidan suka tarraro harda zulaika da yaran,suka nufo Abuja cikin tashin hankali wanda baya misaltuwa,Koda suka isa asibitin suka wuce direct,sun ma tarar da Ummi harta farfado tana ta wasu sambatu tana kiran sunan mu"azzam tana so asaketa ta fita,dole Alluran barci aka garkama mata,dole duk wani mai imani yaga halin da Ummi take ciki sai yayi mata kwallah,agabansu hajiya komai ya faru,hajiya waje takoma tana sharen kwallah tare da fadin"Allah mun godema ka,daga wannan sai wannan,ya Allah kabamu karfin kirjin daukan wannan al"amari.."Taketa fada tana kuka,zulaika ma hawaye take sharewa tana matukar tsausayama wannan ahali mussamman Hajiya da Ummi ga kuma mijinta wanda baya da wani wanda zai lallashesa.

Shikan Dr.Shureim daga office din Dr.Abduljabar mota yadauka Ya fice zuciyarsa na kuna,domin abayanin da likita yake masa Ummi tasamu tsoracewa ne da Firgici shiyasa take wannan zaburan kuma adokar matukar ta kara farkawa cikin wannan halin tofa sai dai ayi hakuri domin kwakwalwarta tasamu mtsala sai kuma abunda Allah yayi,yana tuki yana sharan kwallah,Maitama ya isa,yayi hon sani maigadi ya bude masa get ya sulala ciki,koda ya fito Fuskarsa babu Annuri yayi cikin gidan su lami ne da Uwani xaune afalo suna ganinsa suka mike suna mai Sannu da zuwa,da hannu ya amsa musu kafin ya Nufi farar takardan daya gani bisa center table din dake tsakar dakin domin ko da baisani ba itace silar komai

Warwareta yayi yafara karantawa kafin ya gama hawaye sun jika takardan,rumgume takardan yayi yana kuka,kafin ya dunkuleta ya sanyata cikin aljihun,dakin mu"azzam yafada,komai na nan a muhallinsa,makullayen gidajen dayace ya gani da kudin daya barma ummi,kana ga keys din motocinsa da Katin nan bankisa masu muhimmancu,wanda yake tara kudi masu yawa ya barmata,kenan da guda daya ya tafi,kuma yana kyautata zaton wanda ya tafi dashi bashi da yawan kudin da wa"inda ya barma Ummi kedasu,ya duba kayansa sunan ko kala daya bai dauka ba,banda takardun mkarantarsa dana aikinsa masu mihimmanci su kadai ya tafi dasu,saboda tsausayin Mu"azzam Shureim baisan sadda ya fada bisa gadonsa ba yana rumgume blanket dinsa yana shakan kamshin Turarensa yanajin wasu hawaye na kwararamai yake fadin"where are u dan"uwa? plz come back home we miss u so much dan"uwa.."yafada sanda ya saki kuka da muryansa saboda yadda zuciyarsa ta tsinke lokaci daya daya Tuna halin da mu"azzam din ke ciki.

__________________

Koda Flight dinsu mu"azzam ya saukesu a babban Filin jirgin dake birnin na ikkon tashar taxi ya dauka zuwa wani babban Hotel dake garin na lagos yakama daki yayi kwanciyarsa,kafin zuciyarsa tagama shawaran inda kuma ya nufa,shima kamar yaji ajikinsa haka ya zauna yana ta kuka,acikin briefcase dinsa ya bude ya Fito da hotuna guda biyar,guda daya Na Ummi ne wanda suka dauka tare dashi Saudiya tasaka jallabiya baka,shima bakar jallabiyan ne ajikinsa yayo harami da farin yadi akansa,yana rumgume da Ummi suna dariya hoton yayi bala"in kyau an saka shi cikin Frem anyi babbam elegement dinshi.

  Sai guda daya wanda suka dauka da Shuriem ne Abuja sanda aka yimsu brr calling,Suma dukkansu suna sanye da American Suit na kamfanin Armani ne,ammh shi mu"azzam yana sanye da rigansu na lauyoyi da hula sun,daki kadafan juna suna mirmishi,hoton shima anyi babban Elagement dinshi an sakashi cikin Frem,sai guda daya na Zahirah ce tana sanye da kayan mkrantarta complete harda da safa da takalmi da jakarta sabe abayanta,tana dariya aka dauketa hoton da alamu kamar ma batasan sadda akayi mata hoton ba,Gabadaya beauty Point dinta ya bayyana Fuskarta tana bayyanar da Farincikin datake ciki,hoton mu"azzam ya dauketa ne ranar da zata fara zuwa mkranta.

Sai guda biyun kuma na ya"yansane wanda Shureim,yadauko masa su  ahoto ya kawo mai yagani shine ya turasu duka awayarsa yasaka aka wankemai su kowanne an mai babban kati anyi elagement dinsu cikin Frem,wanda suke sanye cikin kayan sanyi na alfarma fuskarsu tar suna fitar da Annurinsu na jariran dake cikin kwanciyar hankali da Ni"imar ubangiji,duka yahada hotunan ya kamkame yana wani kuka mai cinrai,tuni saitin zuciyarsa ya fara zafi,yana tangadi ya tashi ya bude fridge din dake dakin ya dauko ruwa yazo ya zubo da magungunansa dayazo dashi ya hausha cikin rashin hayyaci da kewar wanda sukama mutum nisa.

  Allah ya taimakama farkawan da Ummi tayi ta farka cikin hankalinta,tadaina fizge fizge takoma yin kuka,mai cinrai kamar ranta zai fita,shigowar hajiya shiya kara  tsinkema Ummi jiki tana so tatashi takasa cikin sauri Hajiya takarisa gareta tana fadin"Bari kokarin Tashi Suhaima,baki da lafiya.."Tafada tana kallonta yadda tadawo cikin wuni daya kawai,cikin kuka da wani irin tsoro Ummi ta kamkame hannun hajiya tana fadin"Hajiya mu"azzam yana gunku ko? tare dashi ma kukazo yanzu ko? don Allah karki ce da gaske ne mu"azzam yatafi ya barni don Allah karki cemin dagaskene,duk abunda ya faru.."Tafada cikin shidewar Numfashi cikin hawaye Hajiya tace"Da gaske ne Suhaima mu"azzam ya zabi yayi nisa damu saboda hallayanki da taurin kanki,dakuma rashin yafiyarki,abunda nayi ta guje miki kenan,nafada miki suhaima inbaki zubar da makamanki ba,to watarana ma Da'n naki dakike takama dashi zai zo ya kubcemiki,kika kiji,yanzu waya gari ya waya,kifadamin tsakanin keda Da shettima waye ya fadi,kuma waye keda riba.."Tafada kwallah suna zuraromata.

  Kife kanta Ummi tayi akafadan Ummi tana kuka take fadin"Hajiya zan mutu,wlh mutuwa zanyi,taba kirjina kiji,wlh zan mutu bazan zauna acikin duniyar daba mu"azzam ba,bazan iya ba.."tafada tana dora hannun hajiya bisa kirjinta taji yadda yake harbawa da Sauri da Sauri,rumgumeta
hajiya tayi tana fadin"Bazaki mutu ba Suhaima nafi so kiyi nadamar abunda kika aikata kafin lokaci ya kure miki.."Cikin kuka Suhaima tace"Nayi whl nayi hajiya Nayi Nadamar abubuwan danayita aikatama Mu"azzam hajiya dana sani ban saka ya saki matarsa ba..."

   ""Allah ya rabumu da aikin danasani Ummi ammh bakin alkalami ya rigaya daya bushe,mu"azzam yabarmu,kuma yayi nisa da mu domin na bincika duk inda nake da tsammaninsa babu shi babu dalilinsa.."yafada yana dafe kansa,Shureim kenan wanda shigowarsa kenan,daga hajiya har Ummi an rasa mai lallashin wani Ummi fadi take"Ni dazai dawo wlh zani har maiduguri na roki Shettima gafara Zahirah ma tadawo dakinta,indai zai fasa barina yadawo mu zauna tare ban saba da kowa ba sai shi Shureim shine uwata shine ubana,,shine da"na shine madadin yan"uwa na,wlh rashin mu"azzam tamkar rabani da duk wani jin dadin rayuwata ne.."tafada tana kamkame hajiya,shureim daya jingina da bango fadi yake"Ai shikenan Ummi,komai fa ya kwabe,.."yafada shima kamar yayi kukan.

  Dr.Abduljabar ya shigo shikanshi halin da wannan Family din dasuka zama tamkar yan"uwansa suka shiga ya tabasa,dakyar ya lallaba Ummi yayi mata alluran barci bayan ta rike masa hannu tana fadin"Dr nasan kasan inda mu"azzam yake,kacemai yadawo wlh na tuba nabi Allah,kace mai eh ya dawo zanje na dawo masa matarsa indai hakan shine zaisa ya zauna dani ,wlh kaji na rantse ko yanzu sai naje maiduguri,kai likita ko a kasa ne ma indai Mu"azzam zai dawo gareni zan tafi zani wlh ku tsausayamin ku memomin da'na"Take fada lokacin da alluran tafara aiki ajikinta ta sulale bisa gadon tana Fadin.."Da'na...!..."Da gudu hajiya ta fice tana gujin kuka shureim ko baya ya juya yana shesshekan kuka,Shikanshi Dr.Abduljabar hawayen ya share ta kasan medicated glass din dake idonsa yana gyarama Ummi kwanciyarta,kafin ya kariso kusa da Shuriem yana bubbuga bayansa alaman lallashi,juyowa kawai yayi yafada jikin Dr.Abdujabar yana fadin"I feel Alone Dr.Ya zanyi shikadai ne dan"uwa na,kalli halin da Ummi ke ciki,kalli halin da Hajiya ke ciki i swear to god Mu"azzam shine ginshikin farincikinmu rashashi kuma tamkar rasa walwarmu ce ta har abada..."yafada yana mai sakin kuka.

  Lallashinsa ya shiga yi yana fadin"Kabar kuka zai dawo very soon...Inaji ajikina shima duk inda yake yana cikin halin dakuke ciki,insha Allahu Soon brr zai dawo gida da zarar zuciyarsa tayi sanyi."Shureim ya dago yana kallonsa idanunsa jawur yace"Babbar illar Dr.Shine bazai kula da kansa ba,zama zaiyi cikin lalura karshe zuciyarsa ta buga ya mutu,inda,baya da kowa,mukuma yabar zukatanmu cikin zullumi da saka rai na har abada.."yafada yana buga kansa da garu saboda yadda zuciyarsa ke amsawa,dakyar Dr.Ya lallashesa suka fito daga dakin yakaisa office dinsa yana basa baki har ya samu natsuwa,koda ya fito ya iske hajiya zaune fuskarta ta kumbura saboda kuka,ga zulaika ma nata fama da yara, itama ta sha kuka,hajiya na ganinsa tace yazo ya tafi da zulaika gida tasamu tayi wanka taci abinci taba yaran nan,ita tana nan,Yayi na"am da batunta ya umarci zulaika data tashi su tafi harda karime hajiya tace su wuce wanda lokacin dare yayi,itakuma hajiya dole dama abarta ta kwana da ummi saboda yanayin yadda take farkawa,shi Ushe tundazu yakoma gida cikin alhini.

Koda Sukadawo gidan ba wanda ya runtsa su lami duk suna falo xaune jugum jugum,inda suka saba sauka nan zulaika tafada tayi wanka tayima yaranta kafin tayi  sallolin da'ake binta ko abinci dasu lami suka kawo mata kadan taci shureim kuwa shashen mu"azzam yashige yana ta kuka dakyar zulaika ta lallabasa tayimai wanka ta shiryasa,dakyar ya yarda yasha tea tabashi paracetamol yakoma ya kwanta domin ciwon kai ne da zazzabi suka rufesa,gefe itama ta kwanta rumgume da yaran tana share kwallah tsausayin mutanen da suka kasance jarumai ammh yau Ranuninsu ya bayyana.

_________________

   Wahegari Tun safe mu"azzzam ya fita neman ma kansa mtsaya koda yaje Airport na birnin ikko jirgi daya ne zai tashi da karfe 9:00am na safe kuma zai yada zangon A EGYPT,Cikin ransa yayi kasake yana ayyana Zuwansa garin da baitaba zuwa ba, kawai wani sashe na zuciyarsa ya sanar dashi Kayi rayuwa achan mana,ka manta Abbanka yaje chan,Umminka tayi rayuwa achan Tabbas nima Zan maimata Tarihi zai maimata kansa,Zan isa garin na SUDAN nima in taba rayuwata achan,koba komai garin da Ummi na da Abbana suka fara haduwa ne.

Tuna haka yasashi saurin yanka ma kansa tikiti da sauran chuku chuku abunga ga masu dashi nan da nan komai ya kammallah ko hotel din daya kama bai koma ba,daman daga shi sai yar jakarsa ya fito zama kawai yayi yana jiran tashinsu zuciyarsa ta matsu ya bar kasar Nageria kasar da babu komai cikinta sai kunci.

  9:00am din kuwa jirgin ya tashi ya lula dashi cikin sararin samaniya cikin wani yanayi Mu"azzam ke maimata inda zashi da karfi.. " *SUDAN*
Chapter 44 · 0% Book details