← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 82

Sashe 81

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

  _Lubna ce ta fito daga daki,tana sanye da wata shadda doguwa dark blue medicated glass a idonta tana fadin"Anty wai yau lafiyan,Daddy kuwa,bai fa tashi ba tun bayan dawowarsa daga sallar asuba.."Hannu Zahirah ta yarfa tana fadin"bari kedai yanzu nashiga na taya Amina hada breakfast din,na fito da niyyar zuwa tasosa,Sai baffa ya fito da kuka babbam kwabo yaci zalinsa.."Dariya lubna tayi tana kallon moodu da little da suka wani hade rai suna mgana kasa kasa,karisawa tayi tana fadin"wlh gwanda ya dinga dukansu yara saboda rashin jin kamar masu amfani da inji.."Tafada tana zama kusa da moodu ta rumgomosa tana fadin"Srry momy ce ko? ku kyaleta kunji.."Dora kansa yayi kan kafadanta kafin yace"Dat my mami..l love u buh mu gobe zamu koma gida mungaji.."yafada yana kallon Little gyadai tayi kafin tataso itama ta zauna kusa da lubna sun sata atsakiya kowanne yadora kansa bisa kafadanta,fuskarsu take shafawa tana fadin"ku kyaleta zamu kai karanta wajen Daddy in ya fito zai hukuntata.."Tura baki little tayi tana fadin"Umh mami tab,ai gwanda kifadama namecy na,Daddy dabayaso  laifin momy ko kadan.."dariya Lubna tayi tana kara rumgumesu tana fadin"Nikuma banison laifin ku ya"yana so ku kwantar da hankalinku babu mai kara mtsama muku acikin gidanan_..

_tsaki zahirah Taja kan tace"Mtseeww..,Kike biye musu Allah raka taki gona in banda fin karfin in akataba zaluntar dan gida kuna baki,wlh mun gaji kuzo ku koma gidanku ya"yana suma su samu sakewa.."Waye ake kora haka..? Sukaji anfada daga bayansu dukkansu suka waiwaya jin muryan Daddynsu Koda na waiga mu"azzam nagani yazama Dattijo dan kimanim shekara hamsin da Duriya Abun mamaki kansa haryafara Farin gashi,yana sanye da bakar jallabiya da wani Siririn Farin glssa,wanda yakarama Fuskarsa kyau,yakara fari da manyanta,ammh fa kwarjin nan nashi na nan da cikar zatinsa_.

  _Da hanzari baffa ya karisa yana fadin"Daddy..."Shabesa mu"azzam yayi yana fadin"Na'am Baffa na,how far..'Kwabe fuska yayi kan yace"yaya ya dukeni.."yafada yana nuna moodu wanda ke zabgamai harara,Kallonsa Mu"azzam yayi kafin yace"ok dakai Mommynku ke fada ko,meyasa kacika saurin hannu ne,Abbana..? Lubna tace"Laifinsa zaka gani,bazaka tambayi meyayi mai ba.."Harara ya sakarmata kan yace"Bazan tambaya ba,uwar son kai bakison laifin yaran nan, sam mamin yara,komiye yayimai Aishi babbane sai ya kyaleshi yaci girma ko.."Little ce ta mike tana fadiin"Wlh Daddy akomai sai ka nuna sonkai kan duk Abunda momy tace akai,kusha kuruminku goben nan zamu barmuku gidanku ko bruh.."gyada kai yayi alamar hakane_.

_Rike baki mu"azzam yayi yana fadin"yau naga yaran zamani,nima ido kukasamin ashe.."Dariya lubna tayi bata ankaraba mu"azzam ya sakarmata rankwashi akai yana fadin"ke kike daure musu gindi suke wannan Abun,to muma bamu bukatarku Ayashe ta gaida ayyah.."Dafe kai lubna tayi kafin tace ashagwabe'"Kai Daddy gaban ya"yana zaka rankwashe ni.."Dariya zahirah tayi kan tace"Wlh kau,ankusa yin Abun kunya.."Mu"azzam yace"bakijin mgana ne,dat why na miki dukan shari"a ko yan biyuna.."Kallon juna sukayi moodu da little kan su hada ido suce"Hmmm..Daddy kenan.."Suka fada harda hada kafada,Kallonsu yayi kan yace"Daddy mene Eye.."Dariya sukayi kan suce"Daddy da momy da mami..hmmm sai Allah.."Suka fada harda tafawa,Dariya iyayan suka kwashe kan mu"azzam yace"Kunga yan biyunan akwaisu da gulma."Little ce tace"Bawani gulma Daddy kullum bakwa tsufa,Rayuwarku tana burgeni sosai Daddy Allah yabani miji wanda zai soni kamar yadda kakeson mommy da mami.."Baki zahirah ta rike kan tace"la'ila ha'illahi..."Mu"azzam yace"Eye Ummina To Amin"ya fada yana dariya sunne kai tayi tana dariya kan taruga zata shiga shashen Ummi sai gata da buyagin yara suka ci karo da little tace"Ke lafyan ki,kike Gudu haka?_.."

_Ummi na kallah sai da nayi Kabbara Allahu akabar Ummi ce da kaganta fuskarta bata chanzaba,ammh ta tsufa don akallah zatabama 70 baya gashin kanta yakoma fari,hartama dan duka,Furkarta yadan chanza,ammh hutu da jin dadi yasa hasken fatanta na nan,tafe take da yaran kai da kai,kowane yana rike da ita yana fadin"Ummi kaza,Ummi kaza.."Allah sarki Ummi dama Abunda takeso kenan,to yau ga mu"azzam yataramata ya"ya kiriniya da hayaniya kuwa sai wanda yagani_.

  _Zahirah ce tatarota tana fadin"Takwaranki keson Aure Ummi..."Ummi ta kalli little tace"Yo miye aciki,inace kema kina kamanta aka miki auren ko.."Sunne kai zahirah tayi akafadan mu"azzam suko sauran yaran suka saka dariya,Ummi ta riko hannu little tana fadin"Zo muje dakina kifadamin wakikeso takwara,ni dakaina zani gidansu na tambayan miki izini wajen iyayansa.."Dariya su zahirah suka saka ,zaro ido little tayi kan tace"kai Ummi.."eh mana.."Ummi ta katseta tana jan hannunta yaran sukayi duu zasu biyosu moodu ya daka musu tsawa mu"azzam ya harareshi kafin yace"Kai karka firgitamin ya",yana kuzonan kunji ya"yan Daddy baisan darajan haihuwa bane sai ya haifa.."Bata rai yayi kafin zahirah tace"Bi bayansu daman Ummi ai ta iya biyema shirmenku kaida yar"uwantaka.."Bai ko kallesu ba ya wuce yana fadin"Ko muntafi Ummi kawai da mami za muyi missing sauran ko..Hmm.."yafada harda daga kafa,Zahirh tace"muma mun yafe wlh Allah raka taki gona.."yana kunkuni ya shige shashen Ummi,wanda daman chan suke wuni in hayaniyar ya"yan momy ya damesu,wani lokacin kuma dakin Ummi aketarewa duka yaran suna kiriniya,aiko yaya moodu yayi jam ido in anki yakai hannu,sakamakom su ita little Ummi babu ruwanta tana da sanyi sosai dayake gabadaya yaran Hutu suke_.

  _Muntaz ne tafito daga daki tana fadin"Mommy ina biccuit dina dana ijiye adaki ban gani ba.."hajiya karama tayi karan tace"Yaya muntaz nadauka na cinye.."Zaro ido muntaz tayi kafin tace"Kut nace ki daukane da zaki daukanmin Abu,bakuna da naku biccuit din ba.."da Sauri zahirah tace"a"a uwata ta kaina rabu da ita,muje daki na baki wani banason kina shiga shirgin yaran nan,kinsan ke uwace.."Dariya lubna tayi kantace"bawani Sonkai dai ake nunamana kiri kiri.."mu"azzam yace"Kema kya fada,dai.."zahirah taja hannu muntaz tana fadin"Eh din mutum da mamansa kuma sai abun yazama saka ido muje mama ki karba rabu da Daddy da mami yan adawane.."Washe baki tayi tana fadin"Dat my mommy..I love u.."Da haka suka shige cikin hannunsu sarke da juna,muntaz kenan,zahirah tana matukar kaunarta babu mai tabata ya zauna lafiya koda mu"azzam ne_.

_Bata jima ba,tafito daga ciki tana fadin"to bagashi ba har na bata wani tana ciki tana cin Abunta,na kashe rigiman.."Kyabe baki mu"azzam yayi kafin yace"next week zasu tafi zaria gabafayansu yaran,domin inason nima na sake da matana gaskiya.."Dukkansu dariya sukayi kafin yamike yana fadin"ku matanan zaku illatani da yunwa fa,almost pass 11 bamuyi breakfast ba.."Lubna tace'Kai ne kejin yunwa ammh Tuni yaran sun sha complex tun safe,oya kumuje kuyi breakfast kafin zo ayi wanka mufita mu buga basket ball.."Ihu suka saka suna fadin"ehyyyyee...Maminmu we love u so much.."Suke fada dukkansu dariya take tana fadin"I love u too my Childreen_.."

_Da kallo mu"azzam yabita har ta karisa dasu gaban makeken dining din tajama Kowa kujera tana kokarin Saving dinsu,Zahirah ce ta kwanto bisa jikinsa shiya dawo dashi cikin hankalinsa kafim tace"Kana kallon hidman mamin yarane.."Mirmishi yayi yana riketa yake fadin"Lubna ta kasance wata jigo ne na rayuwarmu ni dake zahirah,tabamu gudummuwa mai yawa,Duk tsawon zama da ita wlh batata batamin rai ko nuna wani damuwa da kishi kan irin son danake miki ba kuma koda rana daya batataba sabamin da gangan ba,kullim cikin min biyayya take,to in zuciyata bata girmama alherinta ta sakamata tabata waje acikin zuciya ta ba nakega kamar bata mata adalci ba_."

_Dagowa zahirah tayi ta kallesa tana mirmishi tace"Sosaima Ai im baka so mamin yara ba,yaya kayi butulci Allah kuwa.."Ya runtse yana fadin"Ina sonta sosai my hirah,Tunda na fahimci tanason abayyana mata so,nikuma nayi alqawarin bayyanamata shi akoda yaushe..Ina sonku dukkanku matana na duniya dana Aljannah..."Yafada yana rumgume zahirah ji yayi an Rumgumesa tabaya ana dariya Lubna Ce,tun dazu take tsaye tana jinsu tazo cewa suzo suyi breakfasat sai ta iskesu suna mganar Zahirah tamata in kiya da ido da tayi Shuru kartayi mgana sai yakai aya_..

  _Dukkansu suka hada baki wajen fadin"MUMA MUNA MATUKAR SONKA MIJINMI,GWARZONMU,BANGONMU KUMA ABUN ALFAHARINMU...,"Suka fada suna dariya Juyo da lubna yayi yana kallonsu Kafin yace"Kai gaskiya Allah nasona,duka matana kyawawane.."Suma sukace"muma Allah na sonmu don mijinmu daya tamkar da dubune cikin maza"dariya ya saki kan Shafa kansa yana fadin"To dukkanmu mu godema Allah daya mallakama juna.."Fadawa Jikinsa sukayi suna fadi atare su duka ukun.." *ALHAMDULILLAH...* Tafi sukaji daga bayansu suna waigawa suka ga duka yayansu ne, little da moodu ne gaba Harda Ummi tana tsaye kwallah sun cika mata ido moodu yace"Oya all of us Say ALHAMDULILLAH.."Aikuwa suka dauka gabadaya_" *ALHAMDULILLAH..*

*NIMA ANAN NAKE CEWA ALHAMDULILLAHI GODIYATA TA TABBATA GA ALLAH (SWA) WANDA DA IKONSA KOMAI YAKE FARUWA,KANA TSIRA DA AMINCI ALLAH SU TABBATA GA ANNABI MUHAMMED(SAW)TARE DA SAHABBANSA DA IYALANSA GABADAYA...KAMAR WASA NAFARA POSTING DIN UWAR MIJINA RANAR 7/7/2019 RANAR SUNDAY,MUKA FARA YAU NAYI GOBE BAZANYIBA,WATARANA MA HAR INA TSALLAKE KWANAKI,AMMH KUKAYITA HAKURI DA TSUMAYEN JIRANA GASHI AYAU 26/9/2019 RANAR THUESDAY MUN KAMMALLAH SHI,TO BADA KUDIRAN KOWA BANE SAI ALLAH DOMIN SHINE YABANI LAFIYAN YI MUKU TYPING GODIYATA GA ALLAH BAZATA TABA YANKEWA BA,INA ROKONSA YABANI LADAN ABUNDA NA RUBUTU DADAI,KUSKURE DANAYI ALLAH KA YAFEMIN DOMIN NOBODY ABOVE MISTAKE,KUMA DAN ADAM TARA YAKE BAI CIKA GOMA BA,KUKUMA ALLAH YABAKU IKON DAUKAN DARUSSAN DAKE CIKI*

_Kana zan mika sakon godiyata ga Kungiyata daya Tamkar da dubu wacce da hadinkanta hade da karfin gwiwanta Nake gudanar da wannan Rubutun nawa INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION DAYA TAMKAR DUBU...,Ina rokon Allah yabama our boss lafiya yasa zakkar jiki ne,mu kuma Allah yakara hada kanmu Ina matukar alfahari da kasancewata acikinku_
Chapter 81 · 0% Book details