← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 82

Sashe 4

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   _Inna Tarasu da sunanka abakinta moodu,Tunda katafi daidai da rana daya inna bata taba fashin ambatonka ba,tunbayan Tafiyanka da shekara uku muka daina jin labarinka mallamin naku na mkrantar wanda da taimakonsa ka tafi ance yakoma garinsu da zama wato ghana saboda damuwa nida Baffa har ghana mukaje ammh sai muka tarar Da Allah yamai rasuwa kuma kasani shikadai ne yasan inda kake har ake samun labarinka agunshi..Wannan lbrin shi yadada tayarmana da hankali  tunda inna taji lbri shikenan bata kara lafiya ba tun baffa na bata hakuri kan zaka dawo insha Allahu har shima yagaza  saboda shuru  baka ba lbarinka gashi muna cikin halin rayuwa balle aje chan abincika mana kai,inna sai da ta shekara tana jinya hawan jini ya kwantar da ita kafin Allah ya mata rasuwa..Tabar duniya da begen ganinka ..Hakika munji mutuwan inna mussamman Baffa da fadi ,wacce tarame ta lalace tafita hayyacinta ashe mutuwan inna tadaki baffa duka duka kwana bakwai da rasuwarta shima yafita sai daukosa akayi yafadi abubuwa sukamana yawa kiwon damuke komai yafara karewa halin rayuwa yafara tsannata agaremu_

    _awannan Halin ne nayi Aure itakuwa Fadi tana gidan mijinta Allah bai taba bata haihuwa ba..Gwanin irin shekarun da kadiba baka dawo ba  yasa muka fara cire rai da kai ammh baffa kullum zencenka yake Mukuma mu ganin kana chan lafiyanka kalau kadai samu Abun duniya ne ka manta damu mukuma muna iya bakin kokari akanshi ammh baya gani ganin mun damu shiyasa baffa yarage ambatonka ammh mu munsani aransa bazai taba mantawa dakai ba..Shekarun baffa biyu kenan cikin halin ciwo Agidan munshafe shafinka munbarka amtsayin matacce ne Ashe kana  nan da Ranka moodu cikin koshin lafiya da wadatan arziki ka manta da tushenka da Asalinka ballatana iyayanka_

Shettima yakarishe hawaye suna kwaranya bisa kuncinsa harda shessheka Baffa ma dake kwance kukan yake..Moodu dayayi zaman yan bori akasa yadora hannu akai yasaki wani irin kuka mai ban tsausayi yana girgixa kaI..Hawaye shettima ya share kan ya waigo yace "Ka fice kakoma inda ka fito moodu munsaba rayuwar baka yanzu ma zamu kareshe rayuwar mu baka..Bamu bukatar ka moodu kafice mana daga gida"Yafada cikin tsawa yana nuna masa kofa.

Khamis Da suhaima dake tsaye gefe tsausayi ya cikasu suka kalli juna lokaci daya Da suhaima wacce tsoro ya shigeta duk da ba jin me ake cewa tayi ba..Ganin haka yasa khamis karisa ya dafa shettima yana fadin"Kar kayi haka dan"uwa ka saurareshi kaji dalilinsa mana"Khamis yafada cikin hausan sa daya koya gun moodu wacce bata fita da kyau..Dagowa shettima yayi yana kallon khamis sai alokacin ma ya gansa ya budi baki zaiyi mgana idonsa ya sauka kan Suhaima wacce taketa wiki wiki da ido..Cikin dakewa Shettima yace'"Moodu wayan nan Fa daga ina'"Yafada yana mai wani kallo.."Moodu yadago kansa idanunsa sunkoma jawur yakalli baffa dake kwance yana kallonsa kafin ya juya ya kalli shettima daya tsareshi da ido yace cikin shakakkiyan murya"Khamis abokina ne tare mukayi karatunmu dashi amadina.."sai yayi shuru Nuna Suhaima Shettima yayi kafin yace"Ita wannan fa"Kallonta Moodu yaga yadda ta tsorata taja baya idonta ya ciko dakwallah..Dauke kai yayi kafin yace" *MATATACE*....! dai dai lokacin Da"akA bude labule Fadi ta bayyana cikin dakin tana kuka tace"Matarka moodu..Au harma Aure kayi achan kafin kadawo ko..Mu muna nan muna rayuwa cikin kunci saboda rashinka..To wlh baka isa ba sai dai kabarmana gidan mun barma duniya kai hade da wa"inda suka maka walicci auren"Tafada tana fashewa da kuka.

*Comment*
*Share*
*Vote*

*#intelligent writer's#*
*#Uwar mijina..!!#*
*#JANAFI#*

 _*INTELLIGENT WRITERS ASSO*_✏

    🌺 *UWAR MIJINAH..*🌺
          _(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri tareda biyayyah mai tsanani)_

      *ALKALAMIN:JANAF*💖
      *WATTPAD:JANAFNANCY*

*Dedicated to my BLOOD Sisters JANAF*

*NO.4*

_*Kasani cewa himma da hakuri da dogaro ga Allah,Sune ginshikin samun Nasara A rayuwa..Assalamu Alaikum janaf*_✌

*NOT EDITED*⚒

""""""Moodu bai damu da yarda suke cemai yafice yabasu guri ba..,Illa fara labarta musu lbrin Abunda yafaru Tunbayan Barinsa gida da Aurensa da Suhaima har zuwa yau dinan yakareshe da cewa"Ku yarda dani Wlh ko da kwana daya bantaba mancewa daku ba kuna raina..Aurena da Suhaima kuma haka Allah ya kaddaramin bani da yarda zanyi,kuyiwa girman Allah kuyafeman dan"uwanku"Yafada lokaci daya shima ya kice da kuka.

Ammh ina Shettima da Fadi basu tsaya sauraransa ba illa ma suna kara Umartansa daya bar musu gida basu bukatarsa ahalin yanzu.

    ""moodu kukan yake kuka maicin rai da shesshekan zuciya Shettima kuwa Da fadi mganganu suketa jefan dan"uwansu dashi kamar basusan daga inda yafito suna kuma cewa yafita yabarmusu gida..

  Tuni Suhaima ta rude duk da batajin yaren dasuke fadi ammh ganin yadda moodu ke kuka kuma shikanshi khamis din talura da yadda hankalinsa ke tashe cikin harshen larabci take tambayanshi meke faruwa? kan yasamu zarafin bata amsa Fadi ta bankamata harara lokaci daya dacewa"Shegiya mara Asali"Wanda sai da moodu ya tsaigata da kukan dayake yadago yana kallonta..Khamis kuwa yaji kalman ammah bai fahimci ma"anarta ba tukun tunda hausan daya iya gurin moodu bata da wani yawa.

  Suhaima bata saba ganin tashin hankali ba balle dataga yadda fadi ke hararanta sai ta rude tanufi moodu cikin tashin hankali tana jansa tana mgana cikin harshen larabci wai yatashi yatafi..Shi yakara bakantama Shettima da fadi rai suka umarci moodu yayi gaggawan barin musu gida basu bukatarsa..Khamis yana ta kokarin basu hakuri ammh sunki sauraransa..Yakura kuwa na kofar dakin tana sharan hawaye domin suhaima ce da moodu ke bata tsausayi.

  Zannah moodu ne ya tsawatar yana daga kwance cikin wani hali da karfi hali yace"Haba shettima Dan"uwanku ne fa moodu wanda kuka fito ciki daya...Nasani moodu bazai barmu haka kurum ba ku yarda da dalilinsa kubarsa yazauna cikin yan"uwansa na rokeku"Yafada tari ya sarkeshi moodu ne yayi saurin isa kusa dashi ya tarairayosa ya aza kansa bisa cinyarsa shettima ya dauko ruwa yana basa.

  Mganar da zannah yayi shiya dakatar da Shettima da Fadi basu da yarda zasuyi ammh fadi ita tunda tadora ido kan Suhaima taji ta tsaneta saboda itafa harga Allah kanwar mijinta tayima alqawarin yayan nata( Kiji karfin hali)da sun hada ido sai ta bankamata harara.

   Tuni labarin dawowar Moodu tacika gari yan"uwa da abbakan arziki sai tururuwan zuwa ganinsa ake..Anata lbrin yazo da mata balarabiya kowa sai zuwa ganinsa ake shida suhaima masu zuwa don Allah da masu zuwa don gulma..Tuni labari ya yahadu agari ashe moodu ba bacewa yayi ba yana chan yana hutawanshi harda ma balarabiya yazo..Chaichai..Abu yacika gari..kowa da Abunda yake fadi.

   Wuni sukayi da baki shiyasa basu kara wani tattaunawa ba,dare nayi kunyar shettima yasa yabar Suhaima gun yakura shikuma yatafi yakama ma khamis otel yakwana yaso yadawo ammh damuwar dayake ciki tahanasq dawowa kuka reras yayita ma khamis yana bashi hakuri..Koda gari ya waye suka dawo ko mgana shettima baimai ba saboda yatafi ya kwana da khamis..Itakuwa suhaima taga rayuwa domin bayan Tafiyan moodu haka Fadi ta sakata gaba da zagi da cin mutumci duk da batajin metake cewa ammh tasan cewa komeye bamai Dadi bane.

   Sai da yakura tamata mgana itama din bata ragama mata sai da dai tabar gidan aka samu sa"ida..Duk da yakura batajin larabci da hannu taita bawa suhaima hakuri wacce ta kwana kuka sai yanzu taji nadamar yarda da Auren moodu har ta yarda ta biyoshi nigeria ammh ta yanke shawarar khamis zata bi takoma kasarta ta haihu..Yakura ita taita dawainiya Da suhaima taneman mata makwanci takawomata abinci duk da bata mgana sai dai ta kalleta kawai tamata murmishi alamun tagode sosai.

**********

Satin su daya dawowa ammh shikanshi moodun zaman hakuri yake yi da yan"uwan nashi mussaman Fadi wacce bata da hakuri ko kadan gata masifaffa ko agidan Aurenta darajan zannah take ci,Suhaima cikin satin datayi ta fuskanci wani Abu haushi sauyin rayuwa tayi kuka kamar idonta zai fadi saboda takuran fadi..Wacce ke wuni agidan sai dare take komawa,shikanshi moodu baisamu ya kebe da ita saboda shima bai zauna ba suna ta cukun cukun chanjin kudinsa zuwa na nageria,sai da komai ya kamkama ya ciro kudin duka yazo ya zubesu gaban Baffa da Shettima da Fadi ammh sai me sai suka juya baya kan basu bukatar komai da dabayanan wake basu kiri kiri suka ki yarda Yakai Baffa Asibiti Abun Takaichi kuma Shettima ke biyema Fadi yana yarda da shirmenta.

  Lokacin Da khamis yayi shirin komawa Nanfa Suhaima tasaka Danja ita gida zata koma kuka take kamar zata shide,Dakyar khamis ya lallabata ta yarda zata zauna ammh da sharadin zai dawo yadauketa,khamis yayi tabawa moodu baki ganin yadda duk ya shiga tashin hankali kafin tafiyarsa sunyi mganan Da Baffa kuma ya Fahimce sa Shettima kamar wanka akama Asiri.

Sunrabu cikin kewa da kaunar juna..Akan sai wani lokaci,wanda lokacin da har yanzu baiyi ba kenan Domunn  Rabuwar moodu Da khamis Ta har Abada kenan.

Saboda gudun mgana yasa Moodu ya yanki barayi nan cikin gidansu yaja sasa nashi shida Suhaima wanda sai da yaja cucekuce kamar basusan inda yafito yarasa wannan Tsana da yan"uwansa suka masa ba,Suhaima tashiga halin Rayuwa gun Yakura ne kadai take samun Dama Dama ammh Fadi tayi mata mugun Tsana wanda ko a idanunta bai boyu ba

  Cikin lokacin moodu yanemi lecturer a Universty of maiduguri kuma suka daukesa ba laifi yasamu Abun Duniya wanda sai dai ya ijiye ko yakaimasu Shettima ba amsa zasuyi ba..Shiko baffa Jiki yayi Nauyi ko mgana bai iyayi..Tun Abun nabawa moodu mamaki haryazo yafara Damunshi Uwa uba ga amanar marainiyar Allah wacce Tarame ta lalace saboda zullumi Tuni Shima yafara ramewa Damuwa suka taru suka sanyamai hawan jini wanda ba wanda yasani sau shi Sai Allah sai Amininsa khamis.

   Ana haka kwatsam Aka wayi gari Da Rasuwar Zannah bukar,wanda mutuwar data girgiza jama"a Dadama,ciki harda moodu wanda sai da kwanta asibiti babban Tashin hankali Shine wajen karban gaisuwan haka Fadi ke kuka tana birgima tana fadar Sunanshi dana matarsa akan susuka kashe musu uba..Abun nan yayi Sanadiyar haifar dawani Nauyi akirjin moodu wanda bai wuce ba har Ranar dayakoma ga Allah

  mutuwar Zannah itace mafarin komai Domin lokacin kuncin Rayuwa tabude musu Suhaima wacce kullum kuka take tamadaina zencen komawa gida domin ganin Shikan Shi zannah baida kwanciyar hankali,Suhaima macece dabata manta alheri komai kankantarsa balle wanda yabatamata lokaci Daya taji ta tsani Fadi Da Shettima wanda bata fatan ko mutuwa tayi su sallaci gawanta..Dafari bata fahimtar bakaken kalaman Da Fadi ke jifanta dashi ammh yau da gobe yasa tafara Fahimtar wasu daga cikin Hausa hartakecin wani Abu daga ciki.
Chapter 4 · 0% Book details