← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 82

Sashe 34

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki Ummi taja kan tace"mtseww..Kuma tacr muku nan ne gidansu.."Asma"u ta gyada kai tana fadin"Kwarai harma mun taba zuwa da ita..'kallonsu Ummi tayi kan tace"To ni bansan wata mai irin sunan da kika ambata ba,nan gidan dagani sai dana,sai ma"aikatana,kila kunyi batan hayan ne"tana gama fadar haka takoma ta zauna kafa daya kan daya tana musu sakaran kallo.

mami jikinta yayi sanyi aranta tana fadin"wannan mata akwai jaraba.."Asma"u ko mamaki ne ya cikata domin in bata manta ba dama zahirah tafadamata hannun goggonta take,kenan wannan ne goggon nata, mara mutumci ce ashe lalle zahirah na hakuri,suna kokarin tashi ne sai ga Karime ta fito ganin Asma"u yasa ta ganeta ta washe mata baki tana fadin"a'"a maraban ku da zuwa,muje ai zahirah tana ciki...'mikewa sukayi kamar akan kaya suke ammh sai da Asma"u tajuya tama Ummi wani kallo na cikin ido ko tsoro babu aranta,wanda abun mamaki har suka shige dakin zahirah Ummi takasa tashi balle tayi mgana kallon da yarinyar tayi mata ne yabata mamaki,tunda take ba wanda yataba mata wani banzan kallo irin na yarinyar ta kyale sai yau,kamar wacce tama asiri sai da suka wuce ta rakasu da tsaki tana wani gyara zama,niko nace aikin banxa.

Sai dai Zahirah taga Asma"u da Mami kwatsam wanda saboda murna sai da ta tashi ta rumgumeta kan ta duka tana gaida mami amsa mata tayi tana dagota tana tambayanta jikinta amsa mata tayi da jiki yayi sauki,zama sukayi suna gaisawa da Asma"u wanda keta kallonta yadda tacika gawani fari datayi fatarta tayi fresh da ita,ga Boobs dinta sunciko kamar zasu fasa riga,Mami ma kallonta take zuciyarta na saka mata wani abu ammh tayi saurin kauda tunanin hakan aranta,ganin Zahirah ai budurwace sai ta danganta hakan da ciwo da zaman Wuri daya.

Asma"u ko sai data ta bugama Zahirah zencen Ummi da cewa"Ke besty wai waccan matar da muka gani afalo itace goggon taki.."Gyada mata kai zahirah tayi gabanta na faduwa kada suce Ummi ta musu wulakanci tabe baki Asma"u tayi tana fadin"Tab ammh matar nan bata da mutumci kiinsan metacemana nida mami.."zaro ido zahirah tayi kan ta girgiza kai Asma"u ta cigaba da cewa"Cewa fa tayi wai munyi batan kai ne,bata ma san wata mai irin sunanki ba,kiji fa.."dan yake zahirah tayi kan tace"Uhm Ai Ummi haka take nima hakuri nake da ita..."Daga haka ta tsuke bakinta,lura da hakan da Asma"u tayi sai ta kyaleta,basu wani jima ba suka mata sallama bayan Asma"u tabata school bag dinta mami kuma tabata Leda cike da kayan Fruit harda kudi 5k amsa tayi tana musu godiya har bakin shashen ta ta rakosu kafin takoma abunta don mu"azzam ya gargadeta karta sake fita,ko fitan yakamata to ta sanya dogon Hijabinta,Su Asma"u na fitowa sukaga Ummi ko kallonta Asma"u batayi ba saboda matar sam bata kwanta mata ba,tacika wulakanci mami ce ma tace mata sai anjuma,in kun taka ku da kuke karatu ta tanka haka suka fice mami na mamakin wasu matan wa"inda suka dauiki duniya da zafi haka.

Aiko zuwansu Asma"u ranar mu"azzam yaga tashin hankali don Ummi tayi tsiya kamar ta ari baki,kan wlh kada wata tsagerar yarinya ta dawo mata gida itabatason rashin kunya hakuri shidai yayi ta bata dakyar ta hakura,achan daki kuwa da mu"azzam ya tsare zahirah da ya akayi Asma'u kawarta tazo tayima Ummi rashin kunya alhalin tafi kowa sanin halin Ummi,abunda Asma"un ta fadamata shi ta fadamai takara da cewa"kuma nasan harga Allah bazata ma ummi rashin kunya ba..""Tafada kamar zatayi kuka,rumgumeta yayi kawai yanajin takaicin halin Ummi na yarda take kokarin tona abunda suke kokarin Rufewa.

**************

Sati biyu cur Zahirah ta kwashe agida kafin takoma mkranta sai da ta warke sumul sai abunda ba"a rasa ba,yanzu ko agida duk inda zata da katon hijabi take yawo acikin gida dokar mu"azzam kenan saboda kaunda idon Ummu,duk da bawani fitowa take ba,ammh duk sanda hakan takama,sai tasanya hijabi ta rufe Jikinta,saboda cikin nata yafara turowa ta cikin rigarta abun masha Allah.

Itako Ummi ko aranta bata kawo wai in taga yarinyar da hijabi ta zargi wani abu ba,illa da sun hadu tayi tsaki tace"Munafuka irin uwarta.."In ba"ayi sa"a ba tasha rankwashi,ammh bata taba lura da yadda zahiran ta dawo ba hidimar gabanta kawai takeyi.

kwantashi tashi babu wuya awajen Allah gashi har cikin zahirah ya shiga wata na bakwai ajikinta babu wanda yasan dashi sai wa"inda suka san dashi dama,a mkranta kuwa ta dinga muku muku dashi kenan ko Asma"u bata taba lura ba saboda bazama takawo Tunanin hakan ba.

Ranar Friday suna cikin class bayan an tashi break Asma"u ne rike da wani littafi na Text messgs data gani ajakar zahirah tana dubawa zahirah na gefe tana rokonta tabata abunta rugawa Asma"u tayi tana fadin"report zan kai ki kina yarinyar ki dake kin san Siyan littafin text din soyayyah ko" tafada tana mata dariya ganin da gaske take zuwan zatayi sai Zahirah ta mike ta biyota da dan gudunta sai Asma"u tafara zagaya ajin,tana dariya,dan gudun da zahirah tayi sai taji ta gaji sai ta duka tana Numfashi dagowan nan da zatayi sai hijabinta ya daga cikinta ya bayyana awaje wanda gayanan har ya girma,Asma"u dake tsaye gabanta ta zaro ido lokaci daya ta dafe kirji tana nuna cikin Zahirah take fadi cikin Rawar murya"Me...ye...Wa.Nan..Besty.."Tafada tana matsowa ganin haka yasa zahirah tabi inda Asma"u ke nunawa taga cikinta waje sai tayi saurin jan hijabinta ta rufe jikinta na dan rawa.

Asma"u zata sake mgana zahirah ta rufe mata baki saboda an dawo break an ajinsu sun soma dawowa hannunta kawai takama suka fice daga ajin batare data mata mgana ba.

_wayyo Allahna mura plz manage dis one oooo...Bani jindadin jikina ur pryers iz nedeed_

1luv janaf fans,iya wuya muna tare😘

*Intelligent writer"s*
[18/08, 14:18] 80k: *🌺UWAR MIJINA..!*🌺
_(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tare da biyayyah mai tsanani)_

*Alkalamin:JANAF*
*wattpad:Janafnancy*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*Intelligent writer's Asso*✏

_*Dedicated to Zumunta Novella,Taskar littafan Hausa,Janaf Novella,Uwar mijina Fans1,2 and 3,Beneficial Writers,Auren Fari fans,Aisha Alto Novel meeragee Fans club..Kuna da yawa gaskiya wanda baki bazai iya Furtawa,ba Ngd sosai da kaunarku gareni Allah yasaka da alheri*_

*NO 22*

Tafiya sukayi har zuwa bayan wasu empty clasess,wanda sabbi ne ba"a fara karatu aciki ba.

Wani dan Dutse dake kafe ta bayan wajen Zahirah ta zauna kafin taja hannun Asma"u tazaauna kusa da ita,wacce tazama mutum mutum.

Kallonta tayi kafin ta sanya hannu ta dage hijabinta cikinta ya bayyana tasaka hannu tana shafawa,kafin tadago tana kallon Asma"u wacce ta sandare tana bin katon cikin Zahirah da kallo mamaki ya sandarar da ita.

"Wannan kike tambaya besty.."?Zahirah tafada tana kallonta kai tsaye Gyada kai Asma"u tayi don bakinta babu alamar zai bude balle tayi mgana,mirmishin Zahirah tayi mata kafin ta dauki Hannunta ta dora bisa cikin tana fadin"Ciki ne besty ciki na haihuwa.."Tafada tana saka idonta anata.

Zabura Asma'u tayi hannunta dafe da kirji tace"Ciki zahirah,wannan wani irin bala"i ne besty waya yi miki ciki besty wayeshi,?"Tafada ranta na kuna lokaci daya hawaye ya wanke mata ido.

Dariya zahirah tayi kan tace"Mijina ya mu"azzam shi yayi min ciki,besty cikina ba dan shege bane,dan Sunna ne wanda shedu suka taru suka daura shi.."Zuru Asma"u tamata da ido kafin tace 'bangane mekike Nufi ba,wani ya mu"azzam,din? "Tafada cikin mamaki da al"ajabi,Riko hannunta Zahirah tayi ta sake zaunar da ita,kafin ta shiga bata lbrin tarihin rayuwarta daga farko har karshe harta gaban dake tsakaninmu Ummi da iyayyanta tafadamata,kafin ta gangaro zuwa rayuwarta da Ummi da yadda yanzu take boyon wannan cikin ta kareshe da cewa"Na damu besty Wlh inajin tsoron Ranar da Ummi zata ganni da cikin nan kila sai ta kusa kasheni.."Tafada hawaye na zuraro mata.

Asma"u dake kallon zahirah tana kuka ta sanya hannu ta sharemata hawaye,itama zahirah sai ta sanya hannu tana sharemata atare suka sakarma juna mirmishi,Kafin Asma"u tace"lalle besty Rayuwarku tana cikin hadari a lbrin nan ,na lura kaf Ummi bata da imani aranta,ina matukar tsausaya miki kin taso cikin maraici,gashi kinyi dacen miji ammh Uwar miji ita zata dakushe kwanciyar hankali.."tafada cikin damuwa Rausayar dakai Zahirah tayi kafin tace"Nima fargabana kenan besty wlh dashi nake kwana nake,tashi,in bata gani yanzu ba,zata gani agaba,don zan haihu kuma dole taji.."tagumi Asma"u ta xuba tana fadin"wannan matar anyi yar kutumar uba,yo ba"a yafiya takema Allah laifi ya yafemata,sai ita tadauki wani mummunar akidar riko,kai wlh Allah waddai halinta "tafada kafin ta cigaba da cewa"Ke karki wani daga hankalinki,mijinki na sonki,duk ranar data gani sai kimata bayanin danta ne yayi cikin,sai tayi abunda zatayi,shegiyar tsohuwa mara imani.."rije baki zahirah tayi tana fadin"kirufamin Asiri bani da kowa agarinan,In ummi takamani da duka sai na daina Numfashi xata rabu dani.."Tamke Fuska Asma"u tayi tana fadin'Kina da ni,Besty ko duk duniya zasu juya miki baya ni ina tare dake,so kicire duk wani tsoro aranki Abunda take gudun ya rigaya da yafaru,kuma hakan yayimin daidai,hakan ne kadai zaisa tagane ba"a ma Allah dabara.

Jinjina kai kawai zahirah keyi Asma"u na bata shawaran cire tsoron Ummi aranta,takuma yarda ta gamsu,sun dade awajen kafin su tashi sukoma class har an Fita period daya basu nan,kowannensu wajen zamansa yaje ya zauna suka maida hankali wajen Chemistry teacher nasu domin shi suka tarar cikin ajin.

Da Zahirah takoma gida tafadama Mu"azzam yadda sukayi da Asma"u ammh bata gayamai shawaran da ita Asma"un ta bata ba,shuru kawai yayi,shikanshi kan ya kulle yama rasa mafita,harga Allah baida kuzari da karfin gwiwan taran Ummi da wannan zencen gwara ya bari in ta haihu sai taga mai gabadayan lokacin bata da yarda zata yi dole ta rumgume kaddara.

Asma'u ma datakoma gida take lbartama Ummi abunda ke faruwa Mami ta rike baki cike da mamaki tana fadin"ba shakka sanda mukaje gaisheta naga kamar alamar ciki tare da ita,to ganin ba aure tayi ba,shiyasa na kauda wannan Tunanin Araina,ikon Rabbi dama haryanzu akwai masu mugum riko kamar na kafuran farko"Mami tafada tana mamakin hallayar Ummi kamar wacce bata da sani akan addininta.

Zahirah tabi shawaran Asma"u tadan rage tsoro aranta,ammh duk da haka tana taka tsan tsan da rayuwarta gudun Faruwan komai,Ummi kuwa ita ko aranta bata kawo hakan zai iya faruwa ba,shiyasa bata sanya ido ba balle tagano wani abu,hankalinta kwance jira kawai take lokaci yayi ya saketa takama gabanta don har abada batajin zata iya hada zuru"a da diyar Fadi ba.
Chapter 34 · 0% Book details