← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 82

Sashe 49

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   tafada bayan ta sulale kasa tana kuka yakura tasharbe hawaye tana jijjiga little Ummi datake kananun kuka,tace"Abun ba dadin ji zahirah,Wlh ance duk mai imani yaga halin da Suhaima ke ciki sai ya zubarmata da hawaye,ina amfanin muguwar gaba,wacce batada tushe ballatana makana,yau duk inda tayi hakuri, wlh da duk haka bata faru ba,an bata goma ko daya bata gyaru ba.."dagowa Zahirah tayi cikin hawaye tace"yanzu babu wandan yasan lbrin inda yake,baya da lafiya yakura inajin Tsoro,inajin tsoro kada wani abu ya sameshi,wlh ina sonshi bani son Rashashi gabadaya yakura.."Tafada tana dafe kanta dataji ya sara mata,lallashinta yakura tahauyi da cewa"hakuri zakiyi kinga ko mahaifinki baisan na fadamiki ba nakasa hakuri ne nafada miki ammh ko baffanki ai dalilin ciwonsa kenan,rashin sanin takamamman inda mu"azzam din yake,shikanshi abokin nasa yace ya bincika ko"ina ammh babu lbrinsa yaface yayi nisa da garin ne gabadaya.

  Dafe kumatu Zahirah tayi tana fadin"Hasbunallahu wani'imal wakil,Allah mun godemaka daga wannan Sai wannan"Tafada tana share kwallah kan tamika hannu ta amshi littae Ummi ta ciro nono tafara bata,tana kallonta yadda take tsotsonta da zafi zafi,alamar yunwa takeji Runtse ido,Zahirah tayi wasu hawaye suka zubomata ta furta cikin karayan zuciya"Allah ya bayyanaka ya mu"azzam,duk inda kake ka tuna dani da ya"yanka muna kewaraka bayan mutuwar sonka zai sama abincinmu son ganinka kuma zai zama abun Fata agaremu har karshen Rayuwarmu,Allah ya karemun kai ya mu"azzam aduk inda kake.."Tafada hawayenta na diga bisa Fuskar little Ummi,kamar wacce ko kamar tasan me uwar ke cewa,tasaki nono ta zuramata ido,ana haka sai moodu ya farka shida da kuka,Yakura ne tamiko mata shi tahadasu Ta rumgume tana kuka.

  Yakura dake tsaye tana kallon ikon Allah tace"Kibasu abincinsu,kibar kukanan zahirah.."idanunta na kulle tana hawaye tace"Ba Nono sukema Kuka ba yakura,suma sun ji ajikinsu sunyi maraici,maraicin uba nagartattace,basu da masaniyar samun wani makwafinsa suma suna kukan Rashin mahaifine,nikuma ina kuka RASHIN MASOYI NE.."Tafada cikin wani yanayi..

  Yakura dole tasakai tafice daga dakin saboda yadda tsausayin zahirah ya cikamata ciki,falo takoma suna mgana da mahghana akan tarewar zahirah jibi,wanda take fadamata irin dagan datakeyi da zahirah kan kin cin komai aka bata na gyara jiki,ko na jegon ma bayan tagama kin yi tayi,mahgana tace"Da an mtsamata sai tasaka kuka,wai wazatama gyara,babu ya mu"azzam dinta,ita wlh babu wanda zatama gyara.."Ki jimin yarinya to Ai hakuri zatayi da mu"azzam din yamata nisa,in ma zata saki jiko ta gyara toh,ta gyara don gidan kishiyata zata,wannan karon bata uwar miji bace,ta kishiyace.

  Hakuri kawai yakura ke bata,ko ita haushin ma mahgana taji,to miye nawani bata kayan gyara,Takaicima yahanata zama dole tayi mata sallama ko dakin zahirah bata koma ba, ta fice daga gidan Aranta tana jin kishin Auren nan,duk da saki uku ne,ammh tanajin babu dadi,ko don mu"azzam dayake mutuwar son yarinyar,ammh yazasuyi wannan karon basu da tacewa,don iya alkunya bukar yayi musu shi,wannan karan kuma kiri kiri yake nuna shi ke iko kan yarsa.

    Ana gobe tarewan sai ga dangin Alhaji kabirun wa"inda suka zo daga kano sunzo kawo kayan Akwatu,guda biyar shake da kayan arziki,ankarbesu hannu bibbiyu cikin mutumci da karramawa,sunci sunsha dakuma zasu tafi suka wuce da abun arziki niki niki,suka tafi suna fadin kabiru yagama sa"a duk da sun so ganin amaryan ammh zahirah ta rufe kofar dakinta,tana ciki tana rafzan kuka,tana auna yadda zata rayu dawani Namiji ba ya mu"azzam dinta ba, gaskiya da wuya ta iya yimai biyayyah tsakani har ga Allah, babu wani da Namijin dake burgeta kamar ya mu"azzam shine na farko kuma na karshe,so zata yarda da Auren ne,kawai don bahna dinta ammh har abada zuciyarta yana ga Shi din dai IBRAHIM MU"AZZAM.

Ashe Tun kwana biyu da suka wuce  inna Ashe da mahgana sukaje sukamata jere agidan Alhajin,wanda ko da sukaje yaganar batanan an tafi yawon bin bokaye ba zama,su kadai sukayi jerensu suna yaba tsarin gidan nata,suna fadin Nan ma zahirah tayi sa"a Ammh Allah yasa kada tafadama mtsalar kishiya bayan ta baro ta UWAR MIJI.

  Kaya sabbi Bukar yakara yima zahirah komai sabo,don ya nuna bajintarsa,Tabbas yana bala"in sonta komai ya samu wa ita yake karewa,babban burinsa yaga yawanke duk damuwar dake ranta,yazama tazauna cikinn Farinciki kamar yadda take ada,itako zahirah ko daya ba"a burgeta ba,kallon kowa kawai take,ita ta kanta kawai take da ya"yanta da kuma kwana sallar datakeyi na Allah ya tsare mata mijinta aduk inda yake,..Kiji karfin hali irin na zahirah,ga mijin ki chan,,Alhaji kabiru Nepa😂😂😂

Ko mganar shan kayan gyara mahgana da Innarta Ashe ta hadata, aiko ta sameta tayita mata fada kamar ta daketa,takuma kasa ta tsare sai da cinye kazan da"aka yimata na jego wacce ba"ayi mata ba,sai Fefesun yan shilla,da Hadin gumba wacce ake sha da madara,halin na yan Maiduguri ne domin mahgana tayi su da kanta hakanan don babu yarda zahirah ta iya take sha tana kuka,tana gamawa aka kawo turaren tsugunnne,shima Ashe ta karbe yaran tana fadin"Maza tsugunna,ana nuna miki hanya kina wani kukan iskaci,yo Shi mu"azzam din dakikema kwakwa,bafa zaki koma gidansa ba yarinya tun wuri ki dainama kuka,don gidan Alhaji nan ne gidan zamanki na har abada,ke ko Zuciya baki dashi,uwarsa tasaka yayi miki sakin wulakanci,ammh don jaraba da sakarci kina nan kina kulafuncinsa,kina ta halaka kanshi da yaransa."

  Tafada harda dungurin zahirah akai suko yaran da harara ta bisu tana dungurar dasu bisa gado tace"Ku koyi zama ku kadai don uwartaku gidan mijinta zata,taje itama tasamu ladan Aure,bawai a iya renonku zata kare ba,Shegun ya"ya masu kama da tsinanniyar kakarsu,ni yaya yakin mun ne,tuni nace ya kawo munsu na dinga dirkamusu madara Allah ke rayawa,ke kuma abarki kici amarcinki "
kona sati uku ne..

Zumbura baki Zahirah tana kuka tace"Ni.wlh bamai rabani da ya"yana,tunda bawani ya haifamin ba,kuma aure ai bance ina so ba,Takurani akayi,kuma wlh tallahi ni babu amarcin da zanci ba zan ci Amanar ya mu"azzam ba.."tafada tana rufzan kuka wiwi..

baki Ashe ta rike kan tayi shewa tace"Ayyiriri Ayyiriri nanaye..Ohni Aishatu yau naga duniya,yo kada Allah yasa kici amanarsa don ubanki,ke in bakici nashi ba yaci naki ai,ke Soyayyah ko?to Soyayyar taci kazan kazanta,sakarya kawai,kinji in kinje ki hanasa kanki,yako turmusheki ya amsa abunsa,tunda kudi ya biya,kuma karki zauna kiyi abunda yadace ni dake shege ka fasa.."Ashe tafadi haka kan Tafice tana masifa ita kadai,Itako zahirah tana tsuguuno kan kaskon Tana hawaye ita kadai,Su little Ummi ko sunyi tsit suna raba ido sukansu sunsan Ashe ba dama.

_________________

   Wanan Zuwan da Shettima yayi da shirin zuwa maiduguri yayi, kara zuwa duba jikin Baffa,dakuma duka yan biyu,domin shine makwafin ubansu,dole Ya kula dasu,hajiya najin haka tace itama zata tunda baxai kwana ba sai su dawo,Ummi dake zaune tana jinsu ta daga ido tana kallon hajiya.Wacce ta waigo ta kalleta kan tace"Suhaima ya akayi ne?tafada tana karisawa kusa da ita,dom yau kwana uku kenan Ummi batayi ma kowa mgana ba,ko mgana kake mata sai dai kallo tana tsiyayyan hawaye.

  muskutawa tayi tana fadin"Za..Zan..zani yaya..."Tafada murya na rawa..Shureim da Hajiya suka zaro ido suka ce"ina..? atare cikin mamaki,sadda kai tayi kan tace "inda zaku.."gyara tsayuwa hajiya tayi tana hamdala aranta kan tace" *MAIDUGURI ZAMU FA..*"

Ummi tadago kanta hawaye suna gangarowa tace"eh cham zani nima yaya,na Sauke nima Nauyin dake kaina,ko abunda ya tsayamin shekara da Shekaru ya wucemun na huta nima..."Tafada tana mai Fashewa da kuka.

*Comment,share and vote*

Nice dai taku jamilaomar, ba Nagudu bace😂ba kuma kuma jut bace,JANAF NIKE. 
*UWAR MIJINA...!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_

       *Mallakar:JANAF*
       *Wattpad:Janafnancy12*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

_*GIFT TO:Hussain80k*_

*Intelligent writer's Asso*✏

_*Congratulation My Anty SIS NAJATEE..,4 ur completing ur Amarxing,special,adorable,fabulous,Fantastics and Educated Novel ZAB'IN RAINA...,Ina rokon Allah yayafemiki kurakuran dake ciki,mukuma yabamu ikon amfana da darussan dake ciki,Kisani ki kara sani UR'S KANWA Love u back and moon*_😘✌

*NOT EDITED*💥

            *NO 31*

   Tun da suka dau hanya Ummi ke rafzan kuka,tsakanin Hajiya da Shureim babu wanda yayi yunkurin lallashinta, domin ya chanchanta data kokan,Ushe ne ke tukasu yayinda Shureim ke muhallin gaba,sukuma hajiya da Ummi na gidan baya,gidan su karime kadai aka bari,bayan hajiya taja kunnansu duk da tasan cewa basu da wata mtsala.

    Dayake Sun taso da wuri wajejen la"asar suka isa maiduguri,Ummi dagowa tayi tana karema garin na maiduguri kallon rabonta da garin Shekaru ashirin da wani abu,duk da garin yadan chanzamata baisa takasa gane wasu wurareba,duk da ansamu chanje chanje dakuma cigaba daga gwamnatocin dasuka gabata.

   Tsayuwar motar kofar gidan Shettima shiyakara rikita Ummi,tacikin motan take karema gidan kallo,duk da gidan yasamu gyara,ba kamar yadda ta sanshi ba,bai hanata Tunawa da abubuwa dadama ba,ciki harda sanda mai taxi ya saukesu ita da moodu da khamis suna gaba tana binsu abaya lokaci daya tasanya hannu tana toshe bakinta saboda kukan daya tahomata kallonta hajiya tayi bayan tafito daga motar tace.

  "Ki Fito Suhaima,nasani zaki Tuna wasu abubuwan,ammh ya mutum zaiyi Rayuwar kenan dama,abunda yabaka dariya watarana shi zai saka kuka.."

  jin haka yasa Ummi yin karfin halin Fitowa tana gyara,Zaman vail din dake jikinta,Shureim dake tsaye yana jiransu shikanshi Ummi ta bashi Tsausayi matuka,ganin yadda Ummi ke bin gidan da kallo tana tsiyayyar hawaye yasa Hajiya zuwa takama hannuta kawai Ta nufi cikin gidan da ita,shiko Ushe umarni Shureim yabasa daya bude booth ya debo kayan abincinsa dake ciki ya shigo dasu.

Yakura tana kichen taji sallamar kamar ta hajiya baraka,Jug ne a hannunta ta diboma baffa ruwa zata bashi magani,ta fito tana fadin"Muryan wa nakeji kamar ta Hajiya bara..."kalamanta sun makalene sakamakom tozali datayi da Ummi wacce ke tsaye tana tsiyayyar hawaye,jug din dake hannun yakura ya subuce yafadi cikin mamaki da al"ajabi ta furta.

  "Su..hai..Ma.."Tafada cikin Rawan baki Da gudu Ummi tasaki hannun Hajiya ta ruga ta isa ga yakura tafada jikinta tana fadin"Nice yakura,kinganni ko,Don Allah ki yafeni Yakura,ba laifi na bane laifin Zuciyatace,dakuma shedan wanda yake tusamin akidar tsanarku wacce bata da tushe ballanta makana,ki yafeni don Allah"

  Yakura data ke ji kamar mafarki take da Sauri Ta rike Ummi tana fadin"Suhaima kece dakanki,kice kike fadin a yafemiki lalle Allah abun godiya..Allah mun gode maka Alhamdulillah.."Tafada hawaye suna zubomata kan takara rumgume Suhaimar suna kukan Tare.

Hajiya tace ganin koken nasu yaki karewa"To mu karisa daga ciki mana,kuka ai yakare,tunda Kin gane gaskiya kuma kinyi nadama.."yakura tace"Tabbas dama mu kullum Fatanmu da addu"anmu gareki kenan"Hannun Ummi taja tana cema su hajiya bismillanku,Shureim sannu da kokari.
Chapter 49 · 0% Book details