← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 82

Sashe 65

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Kallo daya zakamata ka fahimci ta rame,saboda yadda idanunta suka zurma sosai,Tunanin makomar rayuwarta take ammh haryanzu takasa samun mafita,Tuni ta fawwalama Allah dukan Lamarinta ta rumgumi Alhaji amtsayin miji,kamar yadda yagana ta raba musu kwana,hakan ta kasance yana kwana bibbiyu ako wani daki,duka duka ne,Sau biyu ne ranar girkinta ya zagayo Alhaji ya kwana adakinta,ammh yau tsawon kwana goma sha biyu baya shigowa dakinta ranar girkinta,baya cin abinta kuma baya mata mgana,boyewa ganinta ma yakeyi,ko sun hadu afalo sai yayi Saurin shigewa daki ya rufe kofa,ko Abinci tayimai inyadawo kafin ta fito daga daki ya saka Yagana takaimai daki,duk da ba son Alhaji takeyi ba Shariyarsa gareta tamata ciwo,ko Su moodo sai dai ya aiko a karbesu tun abu bai bata mamaki haryakoma yanzu yana bata,intace bata damu ba tayi karya domin har Damuwar ta bayyana afuskarta.

  Yau din ta kuduri niyyar mai mgana taji wani laifi ta aikatamai da zafi haka,kuma in Alissafinta daidai ne,yau din ita kedashi,bata wani tsaya bata lokaci ba,ta mike ta sungumi little Ummi dayan hannun ta riko moodu tana nishi saboda yaran ba laifi sunada girma,falo ta fita ta kwalama Zulai kira,bayan ta zo ta mikamata little tace ta goyamata ita zata goya moodu,zasu shiga kichen ne,amsa tayi ta goyamata ita kuma ta goya moodu suka fada kichen Tuwan Shinkafai tayimai miyar zogale,lokacin dasuka kammalla komai ake kiran sallar mangariba,Zulai tabarma Daukan Wammers din zuwa saman Diining,itakuma ta karbi Little ta shiga dasu daki zata yi musu wanka.

  Agurguje tayi musu wanka itama tayi,ko shirin nasu agurguje,tayi musu itama ta shirya cikin wata doguwar rigan da mu"azzam ya aikomata dashi,Sallah tayi kafin ta dauki little Ummi ta goya ta riko moodu ahannunta tafito daga dakin dukkansu suna baza kamshi cikin sha"awa..

   Abunda tagani ne afalon yasata jan burki ta tsaya,yagana ce Zaune gaban Alhaji sun baje abinci atsakiyar falon sunaci suna dariya Ranta yayi mummunar baci batasan sanda ta karisa cikin falon ba tana fadin"ammh Allah ya hana zalunci baiwar Allah,meye naki namin katsaladan ranar girki na,naga dai ni na girka abu na,ko ba"a jira ni nazo munci tare ba,ajira nazo nabawa mijina Tunda yau hakkina ne.."Tafada tana huci wanda nikaina bansan cewa haka Zahirah take Intayi Fushi ba.

    Dawani salon rainin wayau Yagana ta dago tana kallon zahirah kan tasaki wata siririyar dariya tace"Hmm su miji manya,yo ai mijin naki da kansa yakirani ya Umarceni dana zubamai abinci,kuma na tsaya kusa dashi harsai ya koshi,shiyakamata kima wannan tambayan bani ba hajiya.."Tafada da rainin wayau,tuni idanun zahirah suka kawo ruwa cikin bakin ciki ta juya kan Alhaji tana fadin"Alhaji menayi maka,baka cin abincina,kadaina kulani? baka shiga dakina?in wani laifi nayi maka bazaka iya samu na kafadamun na baka hakuri ba.."tafada hawaye suna kwaranyomata.

  Alhaji da jikinsa yayi Sanyi ya dago yana kallon zahirah yace"Ko daya Zahirah babu abunda kika tabamin na sabawa duk iya zama dake.."yafada yana kallonta cikin kuka zahirah tace"To menene,ban maka laifi ba,duk meya jawo wulakancin..?tafada tana ratseshi da ido,kallonta yayi kafin yace"Ki koma daki zan zo na sameki muyi  mgana.."yafada cikin kulawa.

   Yagana ko dariya take kasa kasa daga,gani abun nayimata dadi matuka,zahirah takara gyara tsayuwa tana fadin"wlh babu inda zani sai ka fadamin dalilinka na yankemin wannan danyen hukuncin alhalin kace ban maka komai ba.."Alhaji ya dago yana kallonta yadda ta kafeshi da ido tana kallonsa cikin zubar kwallah,ajiyar zuciya ya sauke kan yace.

'" *SABODA KE BA MATATA BACE YANZU..,YAU KIMANIN KWANA GOMA KENAN KINA CIKIN IDDARKI NE..*

      Da wani rawan jiki da firgici,Zahirah ta dafe kirji lokaci daya Tace" Ina..Ci..Ki..n..Idda..Ta ku..ma.. me k..a..Ke...Nu..fi.."? tafada bakinta da muryanta na rawa lokaci daya hawaye na wankemata fuska,kallonta yayi kafin yayi wani mirmishin yake yace"Ma"ana na SAKEKI KWANA GOMA DA SUKA WUCE,SAKI DAYA.."

      Saboda razana zahirah batasan sadda ta aza duka gwiwoyinta akasa ba tana fadin"ka sakeni Alhaji,na shiga uku menayi maka..? tafada tana zubar kwallah daidai lokacin da moodu dake hannunta ya subuce ya fadi akasa yana kuka,guda yagana ta saki kafin tace"gaskiya wannan karon kayi abunda ya dace,kama saki tunkan asaka ka,kai gaskiya aiki yayi kyau.."take fada tana shekewa da dariya.

Da kallo Alhaji ya bita yana dan mirmishi domin azahirin gaskiya yafara dawowa hayyacinsa da taimakon Mahaifiyarsa data sanya akemai Saukan qur"ani da Sadaka,dauke idonsa yayi akanta yamaida kan zahirah wacce ke kuka wurjanjan dakyar ya iya bude baki yana fadin"Ki yi hakuri.."dagowa kanta zahirah tayi idanunta sunkada sunyi jawur tana so tayi mgana ammh bakinta yamata nauyi,kawai sai ta yunkura tatashi,ta dauki moodu dake tsandara kuka,itama Tuni little dake bayanta ta fara nata kukan,ta shige daki da gudu tana kuka,tana shiga daga ita har yaran suka zube bisa gado suna kuka,zahirah fadi take"Shikenan nakara zama bazawara akaro na biyu.."take fada ranta na kuna,tasani batason Alhaji ammh sanda ya furta ya saketa sai da komai nata ya tsaya cak,dama haka Abun yake duk takamar mace,da izzarta kalmar saki na matukar girgiza ya"ya mata.

Alhaji baima yagana mgana ba,ya tashi yabi bayan Zahirah da kallo yagana tabishi tana maijin dadi aranta lalle aikin boka yayi,tashi tayi ta shige daki ta dauki wayarta ta kira kawarta zinatu,tana bata lbrin komai,itama ihu ta saka tana fadin"Dole sujema boka godiya domin aikinsa ba irin na sauran bane.."Sunata murna awaya,su azatonsu Asirinsu yaci Alhaji har ya saki zahirah basusan kwanan zencen ba.

Yana shigowa cikin daki zahirah tamike tana mai wani kallo,ajiyar zuciya ya sauke kafin yafara mgana"Zahirah ko alama ban sakeki don na bata miki ba""..To don ka maidani bazawara akaro na biyu ka aikata hakan..."Zahirah ta katseshi da cewa haka,Hannu ya daga mata kafin yace"Ba burina kenan ba zahirah,.."yafada yana juyamata baya kafin yacigaba da cewa"Nasani cewa koda na Aureki bawai don ina sonki bane,na aureki ne,domin kwadayin samun zuru"a daga gareki,kema kuma na san cewa ba sona kikeyi ba,biyayyah ce da kuma hakuri yasa kike zaune dani,na yanke shawaran Sakin ki ne saboda akwai wanda yafinin bukatarki wanda yake chan kwance cikin halin ciwo tunda ya rasaki,kema kuma nasani kullum cikin begenshi kike,domin gangar jikinki kawai ke tare dani ammh hakikanin gaskiya Ruhinki da zuciyarki tana tare dashi.."yafada cikin Raunin murya.

Daskarewa Zahirah tayi tana bin bayan Alhaji da kallo cikin mamaki da zubar hawaye tace"waya fa..da..Maka.."tafada tana rawar murya juyowa yayi yana fadin"kowaye ya fadamin ba sai kin ji ba,zaki rantse min da Allah cewa kullum baki cikin Tunani Tsohon mijinki kuma uban ya"yanki? zaki iya rantse cewa abunda na fada karya ne.."yafada yana kuramata ido.

Ja da baya zahirah tayi tana wani kuka,lokaci daya tana kamkame jiknta take fadin"a..a...."kiyi Shuru kawai Zahirah basai kince komai ba, narigaya dana yanke hukunci Nayi SADAUKARWA..,Zaki zauna anan gidan kici gaba da iddarki har zuwa jini uku,in inada rabon samun zuru"a Atsakani dake,zanyi murna da hakan,in kuma harkika gama jininki uku,ma"ana lokacin kingama iddarki zan maidake gaban iyayyanki,nayi musu godiya bisa hallarcin dasukayi min,kiyi Hakuri Zahirah nayi hakan ne,domin Farincikinki,farincikin kowa naki tare daFarincikin su Little Ummi,Allah yaga zuciyata,ammh inaji ajikina kila ban da rabon ganin kwai na aduniya ne..."yafada lokaci daya hawaye suna kwaranyomai kafin kawai yajuya yafice yana share kwallah.

Yana fita Zahirah takoma bisa gado tafada tana kuka,lokaci daya taja moodu da little ta rumgume tana fadin"Zamu koma gidan Abbanku,zamu koma gidan Abbanku.."take fada tana kuka da dariya lokaci daya hawaye suna zubomata,kamar ko yaran sun sani sai sukayi tsit,suna kallonta kawai,rumgume tayi kamkam tana dariya hade da kuka lokaci daya,Tarasa kukan me takeyi,na mutuwar aurenta ko na murnar ta hallarta ga mu"azzam,tama rasa wani yanayi take ciki,jikinta na rawa ta rarumi wayarta talalubo nombar mahgana tadokamata kira.

Lokacin mahgana na falo tare da bukar suna cin abinci kiran zahirah ya shigo ta daga tana fadin"Zahirah ce,maman yan biyu.."Tafada tana kallon bukar daidai lokacin data dauka,sallama tayi ammh sai zahirah ta katseta da cewa.."Mahgana Alhaji ya sakeni.."Tafada hawaye na ziraromata,saurin mikewa mahgana tayi,hannunta na dafe da kirji tace"Alhaji ya sakeki? mekikayimai Zahirah..? tafada hankalinta tashe goge kwallah zahirah tayi kan tace"Babu abunda nayinai mahgana,da kanshi ya sakeni,sai yau yake fadamin kwana na goma ina cikin idda.."

Dafe kai mahgana tayi tana sallallami,Bukar dake zaune ya mike yana fadin"Ita wa aka saka.?.'Mahgana ta yanke wayar tana fadi asanyaye"Zahirah..."Zaro ido Bukar yayi kafin yace"Shi Alhaji kabirun ya sakarmin ya'.."Yafada yana bayyanar da bacin ransa kai mahgana ta daga tana fadin"eh..,Tama ce yace yau kimanin kwana goma duk tana cikin iddarta ne.."Hulan kansa ya cire yana fadin"Innalillahi wa"inna Alaihirraju"un..."Yake fada yana share zufan dake ketomai,Mahgana ko dakinta takoma farinciki ya isheta tarasa wazata kira tafadamawa bata da nombar Ummi,kawai sai ta kira yagana.

Yagana na zaune tana bama shettima Abinci abaki kiran mahgana ya shigo wayarta hartaji tsoro ta dauka tana fadin"mahgana lafiya kuwa..? naga kira da daddare..? Mahgana na dariya tace"Albishirinki..."Tafada tana dariya,gyara zama yagana tayi tana fadin"Goro fari kal dashi mahgana,domin daga jin dariyarnan taki abun Farinciki ne ya samu.."Da hanzari mahgana tace"kwarai ma kuwa,yanzu zahirah takirani tana fadamin Alhaji dai ya saketa tun kwana goma da suka wuce.."zaro ido yagana tayi tana fadin'Kibari don Allah.."Dariya mahgana ta sakamata tana fadin"wlh Tallahi da gaske nake fada miki.."

Ai yagana batasan sadda ta saki guda ba,tana fadin",Masha Allahu matarmu ta dawo.."take fada harda hawayen murna kashe wayar mahgana tayi aranta tana kara godema Allah dayaba Alhaji ikon sakin zahirah hankali kwance batare da an kaucema hanya ba.

Shettima dake zaune yabi yagana da kallo kafin yayi mgana ta rigashi da cewa"Allah yayi da rabon zama tsakanin masoyan guda biyu,mijin zahirah ne ya saketa,tun kwana goma dayawuce,kaga kenan ma yanzu haka tana cikin iddarta ne.."Tafada tana bayyanar da murnanta,Washe baki Shettima yayi yana fadin"Alhamdulillah..Allah yasa karshen wahalarsu kenan.."yafada yana jinjina kai.

Yagana ta amsa da Amin daidai lokacin datake kiran Ummi a waya,takira ta shiga ammh har ta yanke ba"a daga ba,sai takara kira,Lubna dake bedroom din Ummi tana shiryamata kaya awardrope taji wayar Ummi na ringing ta dauko ta kawomata kafin ta sauko kasa wayar ta yanke,Tamikama Ummi wayar kenan kiran ya sake shigowa Lubna tace"Yauwa gashi Ummi ana kiranki.."

Ummi dake zaune Afalo ta amsan wayan tana kallon Screen din wayar take fadin"Mutan maiduguri ne,Yagana ce,Allah yasa lafiya.."tafada tana daga kiran daga chan bangaren Yagana tace"Uwar ango akaro na biyu.."Dariya Ummi tayi tana fadin"yagana yau kuma sabon suna na samu,me aka samu ne,naji muryanki tayi chakwai ne,kamar wata yar budurwa yar sha takwas.."Tafada cikin zolaya.
Chapter 65 · 0% Book details