← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 82

Sashe 60

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana gobe tahowarsu ya saka Abbie yakaisa,har gidan marayun da Umminsa tayi rayuwa,gidan ya chanza sosai ansamu cigaba ta fannoni da dama,Kuka wurjanjan mu"azzam yakeyi na tsausayin Ummanshi,lokaci daya yaji kewa tare da kosawa ya saka idanunsa ana Ummi,wlh tallahi yayi kewarta so ba adadi,Abbie ya basu kyautar kudi sosai har na miliyan biyar kafin su baro wajen duk da basu ganesa ba,domin an chanza masu kula da wajen,yana kyautata zaton kilama basa raye,shiko mu"azzam ya gudurta aransa yana komawa zai kawo Ummi tazo taga inda ta rayuwa,domin tunda ta fita gidan bata kara komawa ba.

Washegari jirgin karfe 10:00am na safe ya daga dasu mu"azzam da Abbie da mooh da mom,da lubna zuwa kasar Nageria suna fisrt class ne,ayayin da Mooh da mu"azzam ke zaune kusa da juna,Lubna suna gefe ita da mom,sai Abbie dake kujeran gabansu shi dawani bakin mutum dan Africa ne daga ganinshi,tunda jirgin yadaga yafara tafiya asararin samaniya abubuwa dama dama,suka shiga dawoma mu"azzam kamar yanzu suke faruwa,nan da nan jikinsa yafara rawa idanuwansa sun kala sunyi jawur jijiyoyin kansa sun mike,Da kallo Lubna tabishi ta girgizamai kai cikin tsausayawa,ita kadai ne ta lura da halin dayake ciki,saboda daman duk motsinshi na kantane,ko rayuwarta bata mata kaffa kaffa kamar yadda take da tashi,kauda kai yayi kafin yamaida kanshi ya jingina jikin kujera yana lumshe ido.

*Godiya ta mussaman,gareku Janaf Novell Fans 1&2 tare da Uwar mijina Fans 1,2&3 hakika jiya naga soyayya wacce ta tsayamin rai ,bantaba tsammanin haka uwarmiji ,yasamu karbuwa awajen ku ba naga sharhi masu tsuma zuciya,akwai wa"inda sukayi sharhi tamkar suna rubutu Novel,godiyata agareku bazata fadu ba,ammh kusani cewa wlh tallahi ni Jamilajanafty ina mayen sonku har cikin raina,ina rokon Allah yabarni da ku,har karshen rayuwa,nagd ngd....Allah yabar zumunci Ameen*

*Comment,share and vote*

*Janaftyjamila*

*UWAR MIJINA...!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_

       *Mallakar:JANAF*
       *Wattpad:Janafnancy12*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*GIFT TO:Hussain80k*

*Intelligent writer's Asso*✏

_Shatu🌹Shatu🌹Shatu🌹,where are u? come Closer,cuz shafin gabadayansa mallakinki ne,kin chanchanta,kuma kinkai dukkan mtsayi,Karamcinki gareni maigirma ne,haka kirkinki gareni sai dai nace Masha Allah,ina matukar godiya da Allah yahadani dake amtsayin masoyiyata ta hakika,Na yaba kuma ngd,Allah ya iya miki Abunda kika gaza,Nagode da kulawanki gareni Rabbi ya saka miki da gidan Aljannah mafi Soyuwa FIRDAUSI_😘🙏

*YASIN NAYI EDITING*😎

            *NO 37*

        ""Awa6 suka shafe asama kafin jirgin daya,kwasosu daga Sudan yayi dirar mikiya, dasu Ababban Filin jirgin na Abuja.

   Daganan Tashan Tasi suka dauka harzuwa maitama District,kofar gidan mu"azzam mai motar ya taka birki,da wani rin yanayi mu"azzam ya fito daga cikin motan yana bin gidansa da kallo,wanda ya barsa tsawon watannin Shidda da wani abu,idanunsa suka kawo kwallah yayi Saurin maidasu,Mooh shiya sallami mai tasin bayan ya sauke musu jakukkunansu,Abbie ne ya karisa ga get din yana kwankwasawa.

  Sani da Falalu sai Ushe dake zaune kan wani benci,sun tsuge da lbrai basu ma ji Buga kofar ba,sai da Abbie yasake bugawa kana sukaji da hanzari Sani ya mike ya isa ga get din ya bude bayan ya leko da kansa,ganin Abbie khamis tare da baki ya sashi washe baki yana fadin"Yallabai yanzu kuke tafe? yafada yana bude musu kofan sam bai lura da mu"azzam ba,don shine na karshen Shigowa bayan Abbie da mooh sai mom sai lubna sai shi na karshe.

  Cikin washe baki Abbie yace"wlh kuwa sani,yanzu muke tafe dani da iyalaina.."Cikin fara"a Sani yace"masha Allah,lalle hajiya zata ji dadin ganinku,sannunku da zuwa"Yafada yana kallonsu mom,Mu"azzam ko na bayan mooh ya labe Yana jin yadda jikinsa ke rawa kamar baitaba rayuwa agidan ba,kasa boye kansa yayi kawai sai ya fito daga bayan mooh din idonsa na kan sani dayake kokarin maida kofar ya rufe.

   Yana rufe get din ya waigo yana fadin"Sai ku..."Sauran mganar ta makalene sanda yayi arba da yallabai,cikin rawan jiki sani yaja baya bakinsa na rawa yake Nunashi yana fadin"ya...lla..bai..Ko ba shi bane.?."Yafada cikin tamtama,mirmishi Mu"azzam ya sakarmai yana fadin"Nine Sani...Na dawo gida"Yafada kwalla tana ziraromai ai da wani gudu sani ya kwasa wajen su Ushe yana fadin"aradu kuzo kugani,ga yallabai chan yadawo aradun Allah kuzo ku gani.."yafada yana jan hannun Falalu ,banzan kallo suka bisa dashi kafin Falalu yace"wani yallaban,kai kawai gane ganenku na kauye kafara gani anan,to ta inama zaka ga yallabai.."Ganin sunki yarda ne yasa Sani kara cewa"Aradun Allah ba karya nakeyi ba kuzo ku gani,don su kuresa suka mike suka karisa wajen dasu Abbie ke tsatstsaye cikin mamaki suna kallon yadda mu"azzam ke kallon ma"aikatan gidansa yana hawaye.

    Suna zuwa sani ya dinga nuna musu mu"azzam yana fadin"Ku kallesa,kunga ni ko aradun Allah yallabai ne"Da kallo Ushe da falalu suka bi Mu"azzam kafin su isa kusa dashi Ushe ne yace"Oga...Na u..? yafada cikin mamaki,dariya Mu"azzam ya saki lokaci daya da kuka kawai ya rumgume Ushe yana fadin"oga na u.? yafada yana kwaikwayonsa.

  Cikin wani murna Ushe ya rumgume yallabai yana fadin"yes na our oga,i Swear na yallabai.."yafada yana dariya lokaci daya da kuka,ai da hanzari sani da falalu suka rufama Ushe baya suka rumgume yallabai suna kukan Farinciki,Abbie ya kalli mooh shima ya kalleshi kafin su saki mirmishi lokaci daya itako lubna gefe taja ta harde hannu akirji,tana kallon mu"azzam wani sonshi yana kara shiganta,ashe haka yake da kyakyawan mu"amala da ma"aikatan dasuke karkashinsa lalle dole suyi kewa kuwa.

   Suna ta hayaniya da ihun murna sakinsu yayi yana musu alama da suyi shuru yana kallon Abbie yace"Abbie kufara shiga,ni sai shigo daga baya"haka ko akayi su Ushe suka kwashi kayansu sukayi cikin gida suna murna su Abbie suka rufamusu baya,shiko mu"azzam tafiya yafarayi ahankali yana bin ko"ina da kallo yadda fulawoyi suka bushe wasu ma sun mutu,komai na gidan ya chanzamai,gabadaya gidan ya yi kura,motocin hawansa kuwa duk sunyi kura alamun ba"a hawansu kenan,kwallah ta ziraromai yayi Saurin Sharewa.

   Da murna Su Ushe suka shiga falon,hajiya ce kadai ke zaune tana kallon Tashar Arewa24 anayin Shirin nan na akushi da rufi,suka shigo da mamaki take kallonsu kan tace"kai daga ina? wayan nan kayan fa.?."Sani yace"Hajiya bakin Sudan ne,kuma da.."Falalu ya bige masa hannu yana fadin"ba"ance ayi shuru ba tukunnah..."Kallonsu hajiya tayi kafin tayi mirmishi zatayi mgana kenan Abbie yayi sallama ya shigo falon bayan sai mooh kafin mom da lubna subiyo bayansa dauke da sallama abakinsu.

  Da hanzari hajiya ta mike tana fadin"La ba shakka kuwa,sannnunku da zuwa marabanku da bakin lrabawa"take fada tana washe baki cikin murna da farinciki kafin tahau kwalama Ummi kira tana fadin"Suhaima,maza ki fito ga khamis yazo shida iyalansa gabadaya.."

Ummi dake sama,taji mganar hajiya daga sama,ahanzarce ta sauko bakinta yaki rufuwa tana fadin"a"a maraba maraba masha Allah,.."Take fadi tana saukowa daga saman Stairs cikin Farinciki wanda rabon datayi tun kafin tafiyar mu"azzam.

  Tana Saukowa ta isa ga mom ta rumgumeta tana fadin",Lale marhababika yar"uwata.."Rumgumeta mom tayi tana amsamata cikin harshen labarci,kafin ta saketa ta isa ga lubna tana fadin"Ko ban tambaya ba,wannan diyata ce ko"kai tadagamata tana mirmishi kwallah ya cikamata ido Rumgumeta Ummi tayi tana yafito Mooh da hannu tana fadin"Kaima son taho nan na ji duminka,Allah sarki inama dan"uwanku na nan Da naga tsantsan Farincikin dazai shiga na ganinku.."

Tafada kwallah na ziraromata,karisowa mooh yayi ta hadasu ta rumgume tana kwallah,kafin akoma afara gaisawa cikin Farinciki,Ummi da kanta ta shiga kichen ita dasu lami suka hau jido ma su Abbie kayan motsa baki,dana tande tande kafin adora musu girki,Yau din Ummi tana cikin Farinciki sosai wanda har yakasa boyuwa bisa fuskarta.

  Mu"azzam dake bakin kofar falon yakasa hakuri,bai san sadda ya fada falon ba,da Sallamansa cikim muryansa mai cike da zati Ummi dake duke tana zubama su Lubna lemo ta dago da Sauri domin ko amafarki taji muryan Mu"azzam zata shaidata,gabanta ne yayi mummunar faduwa lokacin da idanunta sukayi arba da mu"azzam tsaye kikam yana kallonta yana hawaye,sanye yake cikin american Suit dark blue and white,Fuskarsa tayi fayau yakara fari kuma ya rame sosai kamar ba shi ba,mirmishi yake yimata hawaye suna gudu bisa kuncinsa.

  Kofin glass din dake hannun,Ummi ya subuce ya fadi,tana hawaye take fadin',"Nasan gizo kakemin son..,kamar yadda kasabamin,'Take fada tana kuka tana ja da baya,inda take nunawa suka bi da kallo da hanzari hajiya ta mike tana fadi da karfi.."wanake gani kamar mu"azzam.."? Hajiya ta fada tana dafe kirji.

Abbie khamis yace"Ba kama bane hajiya shine.."yafada yanamata mirmishi ai da wani gudu hajiya ta karisa kusa dashi tana fadin"Ibrahim mu"azzamu..."Tafada hawaye suna zubomata,Mu"azzam dake tsaye baisan sanda ya fada jikin hajiya yana fadin"Na"am hajiyarmu nayi kewarki.."yake fada cikin kuka,Rumgumesa hajiya tayi kafin ta waigo tana fadin"Wlh Suhaima mu"azzam ne,shine .."Take fada tana dariya lokaci daya da hawaye

  Ummi data daskare atsaye tana bin mu"azzam da kallo ta nuna sa tana fadin"Mu"...az...zammmm....."Tafada cikin kyarman baki,da gudu ya saki hajiya ya isa gareta da wani irin Rumguma ya fada mata yana fadin"Ummi nah.."Yake fada yana kamkameta kawai sai ji yayi Ummi ta sulale daga jikinsa tasume,cikin tashin hankali yake jijjigata yana fadin"wayyo Ummi na,ki tashi gani na dawo bazan karayn nisa dake ba..'yake fada yana girgizata.

  Lubna ne,ta isa ga fridge ta bude ta dauko Ruwa mai sanyi tamika ma mu"azzam ya shekama Ummi yana shafa Fuskarta yana hawaye ajiyar zuciya Ummi ta sauke kanta ta bude ido tana bin mu"azzam da kallo hawaye na kwaranyomata,yasaka hannu ya sharemata yana fadin"Stop craying Ummina,bazan sake tafiya in barki ba..,"Yafada yana riko hannunta.

Damke hannunsa,tayi Tana fadin.."Son,why..? take fada tana kwaranyan hawaye Rumgumeta Mu"azzam yayi yana fadin"Ki yafemin Ummina,na tuba bazan kara ba"Rumgumesa Ummi tayi tana kukan tana fadin"Ka yafemin Son,namaka laifi na muzgunama rayuwarka daga karshe nayi sanadiyar rabaka da matarka uwar ya"yanka,wlh sai bayan tafiyarka nasan kaine rayuwata,bazan taba jin dadi rayuwa ba,in baka,ka yafemin don Allah.."Take fada tana kuka.

  Dago Fuskarta yana sharemata hawaye yana fadin"bantaba rikeki koda da rana daya ba Ummina,wlh Allah dayane banji ko digon bacin rai ba,game da hukunciki gareni,kawai wani abu ne da zuciyata ta kasa dauka,Ummi zahirah tana da wani gurbi azuciyata wanda rashinta agareni tamkar rasa wannan gurbin ne,ki yafemin tafiya danayi na barki Kinji Ummina,na dawo bazan kara barinki ba"kamkame juna sukayi Ummi na fadin"Bakamin laifi ba Son,nice nan nabatamaka,kuma nayi nadama na gyara kuskurena bazan kara ba,Allah yamaka albarka Ibrahim yajikan mahaifinka"Take fada tana kuka,shikuma yana sharemata kwallah yana fadin",Amin Amin Ummina."
Chapter 60 · 0% Book details