← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 82

Sashe 12

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Cikin Rashin Fahimta Mu"azzam yace"Banga ne ba"Shureim yace"Muna hanyar komawa Abuja hajiya tace mu juya kawai"Rike baki Mu"azzam yayi kafin yace"Abuja kuma i think sai gobe"Dariya Shureim yayi yana fadin"To miye ai babu komai Tunda kwalliya tabiya kudin Sabulu angon Wani sati"Yafada yana sheka dariya Bata rai Mu"azzam yayi yana fadin"kaidai dan iska ne wlh,nidai bama Hajiyata waya namata godiya.

Shureim na dariya ya mikama hajiya wacce itama ke dariya tana fadin"Wlh nan da ko wani satin mtsayinshi zai kamo naka,yaro"Mu"azzam dake jinsu yayi dariya yace"yauwa hajiyata Proud of  u Barrister mu"Yafada yana dariya,Dakuwa tamai kamar yana ganinta tace" kaniyarka nan,dan nema kawai wato karfi da yaji kaida Shureim kun maidani kakanku ko"? tafada tana dariya.

  Mu"azzam yace"yo hajiyarmu ai dole kiyi hakuri babu kakannin dole kece zaki cigaba da jan ragamar kujerar"Yakareshe fada yana dariya Itama dariyan tayi kafin tafara mai nasiha dacewa"Naji dadi da Suhaima taji mganata,, duk da nasan bazata watsamin kasa a ido ba,to ammh kaima ina so in fadamaka sai kayi taka tsantsan ma"ana duk abunda yashafi Auren nan kada kadinga yawan Tuna mata,domin wlh ina tabbas din bata yafe bafa,tana Rike dashi yardarta baya Nufin yafiyarta bane..So kabi komai asannu,munanan muna mata Addu"a Allah cire Abun aranta tunda yanzu zuru"ace za"a hada mai girma"Har tagama mganarta Mu'azzam naji yana jinjina kai sai da tagama ya Numfasa yace"Naji hajiyarmu kuma insha Allahu zaki sameni mai biyayyah da Bin Umarnin Ummi bazaki ji sabanin Tunaninki ba..,Allah ya shigemana gaba"hajiya ta karba Da Amin Amin kamin suyi sallama ya datse kiran jikinsa asanyaye jin dadinsa daya Amincewan Ummi shi aganinshi indai akayi auren zama yahada guri daya to za"a samu sauki (Tab lalle mu"azzam bakasan Ummi ba har yanzu..Zama yahada ko? zaka ganinma idonka in kafara amsa gwale gwale😂)

    Dama yana farfajiyan gidan ne sanda yake wayar da hannu kawai ya yafito Ushe wanda ke gun su sani maigadi suna hira,Da hanzari ya kariso yana fadin"Yallabai ina muka Nufa"Kallonsa Mu"azzam yayi kafin yace"Ina su Lami? suna chan ko ka maidosu gida ne? Cikin girmamawa Ushe yace cikin Gurbatattaciyan Hausansa'" A"a nadawo dasu tuni ma yallabai"Gyada kai kawai yayi, budemasa motan Ushe yayi yafada yana fadin"Ka hanxarta Ummi ke jirana"cikin rawan jiki Ushe yafada bangaren Direba yaja mota suka Fice bayan Sani maigadi yabude musu get suka Fice suna daga musu hannu.

Basu wani dade ba suka iso asibitin cikin Taku sa na kasaita ya fito ya nufi jikin asibitin dakin da Ummi ke ciki ya tura tare da sallama,Tana zaune agefen gado kamar mai jiran wani abu tana jin sallamansa tadago tana amsawa da hanzari ya isa gareta ya rumgomata yana fadin"Ki yafemin Ummi na don Girman Allah"Yafada yana kwantar da kanshi bisa kafadanta.

  Cije baki tayi tanajin wani takaichin na yadda Shettima ya dana mata bomb kuma yatashi da ita,hannu tasaka bisa kansa tana shafa gashin kansa tana Fadin"Shiiiiiii...Karka ce komai son..Ya wuce aguna Allah ya sanya alheri  a aurenka"Tafada kamar ta kurma ihu dagowa Mu"azzam yayi yana kallonta kafin yace"Da gaske Ummi kin amince"? yafada yana kallon,kwayan idonta daya ciko da hawaye.

Kauda kai tayi kafin tace"In ma ban amince ba son,zaka fasa ne bayan kaje kafad'amasa ka amince harma an sanya rana, biki yazo"Tafada cikin sanyi ammh kuma ranta abace.

  Saurin Riko hannunta yayi yana Fadin"wlh Tallahi Ummi Tunda bafffa yafadamin wannan mganar Auren nan,kullum cikin zullumi nake Ummi bansan,yadda zan misalta miki ba ammh Ko alama wannan Aure bai kwantamin ba"Yafada yana murza hannunta mirmishin yake tayi tana riko hannunshi tace"It ok..Kana son yarinya ai ko"? tafada kanta tsaye lokaci daya kuma ta tsareshi da ido.

Dariya ta kusa kamasa ganin yadda Ummi ta tsareshi da ido ,dan murmusawa yayi kafin yace"Ummi wani irin so kuma,?Ai SO DAYA NE Kuma ke na baiwa shi,infact ma ni yarinya Tunda nake banta dora idanuna akanta ba"Yafada cikin halin ko inkula.

Ran Ummi fes tace"Yauwa son..Bani son, ma ko ka ganta ma kasota, don bazan bari tazama abokiyar rayuwarKa ta har abada ba..Zan samo maka daidai dakai kaji ko"Gyada mai kai kawai aransa yana fadin"Wani so? miye ma wata aba soyayyah,ai don BIYAYYA NE,kawai zan Aureta.

Hannu Ummi tabashi irin na yara tace"alkawari Fa son.."Tafada tana mai dariya shima dariyan ya soma bayan ya mikamata hannu ya sarke nata yana fadin"Cikawa Ummi na"yafada yana jijjiga hannun alamar tabbatarwa..Rumgumesa tayi tana fadin"ina matuka sonka Dana"Shima hugging nata yayi back yana fadin"Nima haka Ummi na.

    _Wayyo Mu"azzam ka gama kashe kanka da kanka don kaniyarka kaga Zahiran ne,kokuwa kasan me gobe zata haifarwa..I swear kashiga list din Ummi don kasan bata mantuwa_😥

  Mu"azzam ne yaje har office yama Dr.Abduljabar mgana kan cewa yazo yayi discharging dinsu zasu wuce,zuwa yayi ya dubata kafin ya rubuta wasu magunguna yabasu tare da cema Ummi data takoma ta samu barci don Allah,godiya sukayi masa kafin su Fito Ummi da kafanta har mota Mu"azzam yacire Budadden Takalmin sa ya bata,tunda lokacin da"aka kawota hankali atashe ko ta takalmi ba"a bi,Dr.Abduljabar na biye dasu yana musu dariya,da hanzari ushe yataso ya karbi kwandon abincin dasu karime suka kawo yasaka abooth kafin ya bude musu mota suka shiga Dr.Na musu fatan Allah kara lafiya lokaci daya ya juya yakoma cikin asibitin.

   Hon Ushe ya danna abakin
get din,sani maigadi yazo da hanzari  ya bude musu suka sulala ciki,da gudunsa yazo ya bude musu murfin motan,Ummi tafara fitowa Fuskarta cikin Fara"a Ai sani na ganinta ya washe baki yana fadin"Barkanmu da arziki Hajiya,ya jikin kuma"Amsawa tayi da "Jiki da sauki Sani ya aiki"Amsawa yayi da "Alhamdulillah.

  Daga murya yayi yana kiran Falalu yana Fadin"Kazo ga hajiya tadawo"hayaniyar shiya fito dasu karime daga ciki suma cikin murna suka yamaimayeta suna mata sannu da jiki,har daki suka rakata su karime Mu"azzam ne ya Umarce su dasu dafamata wani abu taci,bayan tasha mgani tayi salollinta sai ta kwanta,cikin rawan jiki Suka fice suna matan fatan samu lafiya

Sai da Ummi ta rama sallolinta kana taci abimci Tasha mgani Awaya Mu"azzam yahadata da hajiya tana mata barka da sauka gaisawa sukayi sama sama kafin suyi sallama domin kowannensu na bukatar Hutu.

  Mu"azzam dakansa ya taimakama Ummi tayi brush yarikota har bisa gadonta ya kwantar da ita..Tare sukayi addu"ar kwanciya barcin kafin su shafa tare..dakinsa yatafi yayi shirin barcinsa cikin kayan barcinsa Pjm ash colour da blanket dinsa yazo nan kasa kan capet din dake dakin ya kwanta yana kallon Ummi wanda ya barci yayi awon gaba da ita..Mirmishi yayi yana Fadin"Ummi na kenan,Allah ya barminke"Shima dai cikin lokaci barcin yayi awon gaba dashi.

•°•°•°•°•°•°°•°•°•

*MAID*

   Shirye shirye fa na cigaba da kamkama A bagaren Su bukar da yakura kota kowani fanni an shirya ma Abun,bukar akwati guda yayi ma Zahirah na Fitar biki bayan uban kayan dakin dayayi mata yan Dubai.

  Itakuwa Zahirah cikin lokaci tachanza fatarta tayi sulbi saboda yadda yakura ta dage babu wasa,fuskarta tayi fayau tana Fitar da Annuri,Ko"ina ta gifta wani kamshi ne mai tsaya azuciyar wanda yashakeshi ke binta duk inda tagifta..koda bikin ya rage saura kwana uku An rigaya an mata kitsonta na bare bari,yan kanakana yariyari 2step an zubomata shi har baya,dayake ba laifi tana da suma,Ga kunshinta an zubamata shima turbarkallah masha Allah.

  Zahirah tafara tsarguwa da wannan Abubuwan da"ake mata koda ta tambayi yakura sai dai tamata dariya tace'"Diyata kenan ki kwantar da hankali abun alheri ne zai sameki Matsayinki ne zai karu kinji karki damu"Ko kwalliyan ne baki so adaina miki"Jin haka yasa ta girgiza kai tana dariya.

  Baffa shettima yakasa boye jin dadinsa godiya kuwa yazubama Bukar ba adadi..game dako gayama zahirah yace sai an daura auren In mijinta yazo tafiya da ita,zai fadamata( Kai dai Shettima kacika son kanka da yawa yasin).

********

    Ranar alhamis Hajiya Baraka ta iso ita da matar Shureim Zulaika tare shi Shureim din,wanda agobe zasu bi jirgi zuwa Maiduguri daura Aure..Ummi babu wanda tafadamawa to dawa ma take hurda zuwan hajiya yasa tama su karime mgana kan Suyi shirye shiryen abinci gobe nasu dana bakin maiduguri..

Sunji mamaki da Hajiya baraka ke fada musu gobene yallabai zaiyi aure"Abunda basu taba ji ba Ummi kuwa kauda kai tayi ranta na mata kuna,hakuri hajiya ta basu tare da cewa abun yazo agurgujene,shiyasa basu ji ba.

Abangaren mu"azzam ko baida wani shiri Brr.Barau kawai yafadamawa,sai Dr.Abduljabar,Shureim kuwa yazo da abokin aikinsa Dr.Haruna kurfi,Su kadai ne zasu tafi maidugurin gobe in Allah ya kaimu.

   Ummi kuwa tayi bakan ko mganar bikin ake bata sanya baki,shima mu"azzam din koda wasa bai taba kwatanta hirar da ita ba,yana kiyayewa ammh duk wani motsinshi Tafin Hannunta yake kar take kallonsa aransa tana ayyana abubuwa dadama wanda nikaina ban sani ba.

*RANAR DAURIN AURE*

  Rana bata karya saida Uwar diya taji kunya takowani bangare shirye shirye,ne ke gudana tun ma bangaren su Zahirah su abun da gaske suke don kuwa gida tuni ya cika da yan"uwa da abokan arziki..Mahgana itama tana chan danata gayyah ga kuma yakura wacce itace gayyah komai.

    Zahirah tafara fahimtan wani abu domin Duk inda ta gifta amarya ake cema gashi Yakura ta shiryata cikin wani ubansu less bayan tanadeta da lifaya,.Ita kadai adaki tana tunani domin ita tunda take bata taba yin kawa arayuwarta ba ita kadai take rayuwarts..Duk wani shagali da sauri suka farashi domin Shettima yace Yakura su zama cikin shiri ana daura aure mu"azzam zai wuce da matarsa.

  Abangaren Su mu"azzam kuwa jirgin karfe goma zasu shiga zuwa maid,shiyasa da wuri suka kammallah shirunsu suma anasu barayin sun safe su karime suka tsabtace gida suka fada kichen  domin hada hadan abinci Hajiya kuwa na lura da ummi ko jiya batayi barci ba tarasa wannan bakar zuciya irin na suhaima,yanzu ma tana kwance ko tashi batayi ba gashi ita hartayi wanka zulaika ma ta cakare abunta tashige cikinsu su lami suna aiki dayake sun santa babu ruwanta.

  goma Saura kadan Mu"azzam da Shureim suka shigo dakin Ummi wacce ke kwance cikin bargo hajiya na gefenta tana mata fada kamshin daya bugi hancin tane yasata dagowa luuu..Tayi da ido na ganin yadda mu"azzam yaci ado wata ubansu gezner brown ammh light riga da wando yar ciki,harda malummalum kansa dauke da wular zannah bukar,kafafunsa kuma cikin booth suke bayan hannunsa daure,da agogon azurfa mai kyau da kyalkyali yana daukan ido.
Chapter 12 · 0% Book details