← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 82

Sashe 57

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Tana goye da Moodu,little tayi barci,kamar wasa taji kururuwan kamar ta mace,ana ihun na shiga uku na lalace, tsayawa tayi ta saka kunni,dakyau sai taji acikin falon gidan ne,ihun ke fitowa,kuma ma harda muryan Alhji takeji yana fadin"Haba yagana,kibar kiran kin shiga uku,mama tatafi,ita data tafi batayi Sauri ba,muda muke nan bamuyi jinkiri ba,addu"anki take bukata ba kuka ba" yafada cikin damuwa.

  Da Sauri Zahirah ta bude kofa ta fito tana bin yagana da kallo wacce ke birgima akasa tana ihu,ga Alhaji sai faman Riketa yakeyi yana bata hakuri,ga zulai ma agefe tayi tagumi cikin mamaki zahirah ta karisa tana fadin"Subhannallah..Lafiya kuwa?

  Alhaji ya dago yana kallon zahirah kafin yace"wlh Allah ne yayima mahaifiyar yagana rasuwa,yanzu aka kirata ake fadamata.."yafada cikin nuna alhini,fuskar zahirah na bayyanar da damuwa tace"ashSh..Allah sarki Allah yajikanta da Rahama,ai ba kuka zatayi ba tashi zata yi ku hanzarta tafiya ko? Tafada tana kallon yagana kan tace"Allah yajikanta Da rahama.."

  Ko amsa mata yagana batayi ba,ta mike tana fadi cikin kuka"Alhaji muje,wayyo mamata.."take fada kamar wata zararriya,Alhajin ya amsa da Amin,daki yakoma da Sauri ya daukomata mayafinta ya bita waje,domin Tuni harta fice zuwa haraban gidan tana,kuka,da kallo zahirah ta bisu daidai lokacin da Alhajin ke fadin"bari na kaita zan tsaya nasamu jana"iza" yafada yana kurama zahirah ido

  ganin kallon dayake mata ne,yasa tayi saurin cewa"Toh adawo lafiya.'tare da zama kan kujeran tana kokarin sauko moodu daya fara kuka,zulai tayi saurin zuwa ta karbesa tana chabesa sama,dama tana yawan zuwa daukansu,saboda tana son yaran,karo na farko da zahirah tazauna Afalon hartakai tsawon wani lokaci,koda little Ummi tatashi zulai taje ta daukota ta goyata ita kuma ta goya moodu,suka fada kichen suna aiki tana taya zulai saboda yau ta samu sake ba Alhaji ba yagana don Tunda ya fita bai dawo ba har yanzu.

     Misalin karfe 5:00pm na yammah Alhaji kabiru ya shigo agajiye,lokacin har sun kammallah girkin zahirah tasake yin wanka,ita da yaranta,tana sanye cikin riga da sikat na wani material dinki Fitted ne yakamata sosai matuka,tasanya dankwalinta tayi Daurin nan na Maryam babangida,ta tura gashinta cikin ribbom duk da ba,kwalliya tayi ba tayi kyau sosai cikin kayan kamar ba ita ba,suna zaune afalo suna hira da zulai yayi sallama ya shigo.

  Zulai ce ta mike tanamai Sannu da zuwa amsa yayi yana karban little Ummi dake hannunta,daganan ciki ta shige ta barsunan,shiko tunda ya shigo yake kallon zahirah yadda tatafi dashi,itako lura da kallon dayakemata ne,yasa ta zargu ta kasa tashi,kanta na sunkuye taji sanda yazauna kusa da ita yana fadin"Srry amarya yau an barki ke kadai.."yafada kafadansa na gogan nata.

  Tuni jikinta yafara rawa tadan mtsa tana fadin"ayyah babu komai,ya hakuri? Allah yajikanta"kallonta yayi yana fadin"Hakuri da godiya matata,ai ni Rasuwar nan,bazan ce komai ba,ammh nikam tayiman dadi.."gabanta na faduwa tadago tana kallonsa kafin tace bakinta na rawa.."sabo.da me..ne..? tafada bakinta na rawa.

Mirmishi yayi yana fadin"Dalili kikeson ji? yafada yana kafeta da ido.."gyada kai tayi gabanta na fadi,ba zato kawai taji bakinsa daidai kunnanta yana fadin"saboda yau zan samu kebewa da amaryata,kilama har nasamu nasaran bata ajiyan yan hudu wannan karan"yafada yana sakarmata hucin mganarsa bisa dogin wuyanta,Tuni jikinta ya dau rawa tayi Saurn matsawa,wanda yayi sanadiyar Tashin moodu take barcin kwance agefenta,da kallo yabita yana dariya yake fadin"meye haka,sai kace wannan Shine farkon ki.."yafada yana wani kallonta kasa kasa.

  Ai da hanzari Zahirah ta mike zata bar wajen,ammh me,hannunsa taji cikin nata yasaka ya rikota tadawo da baya tafada gefensa kadan,ya rage tafadama kan Little dake hannunsa,saurin kallonsa tayi zatayi mgana yayi Saurin cemata"Abinci fa?yau Tunda yagana batanan bazan samu mai bani abincin ba.."yafada yana sauke kanshi bisa dogin wuyanta yana shinshinawa.

  Jikinta na rawa tafara kokarin Tashi tana fadin"Armmm..Bari akawo maka.."tafada bakinta na hadewa ganin yadda ta rudene yasashi sakinta yana fadn"plz ki kawonin nan,kar ki jera bisa dinning din nan.." yafada yana binta da kallo yadda ta saurin fadawa kichen jikinta narawa,mirmishi yayi yana kokarin daukan moodu wanda yafara kokarin yin kuka yana mamakin wayon yaran watanninsu biyar ne,ammh sunyi wayau kiu dasu,yana musu wasa suna bangala dariya,jikinta na rawa ta kawoso warmmers din abinci ta hau jeramai bayan ta shimfidamai babbar darduma tanayi tana tura baki aranta tana fadin"lalle nema mutumin nan,ko ya mu"azzam bantaba jerama abinci bisa darduma ba,sai kai.."take fada aranta gefe daya kuma tsoro ya mamayeta.

   Bayan tagama zata gudu yayi saurin dakatar da ita da Fadin"dawo ki zauna ,ban sallameki ba"babu yarda ta iya illa dawowa datayi ta zauna tana tura baki,duk yana lura da ita,kasa ya sauko bayan ya jiyemata moodu dayayi barci,little ce idonta biyu da ita ya zuba abincin tunda baisamu an zuba masa,farar shinkaface da miyar kifi,yaci abincin ammh bada yawa ba yana goge bakinsa da Tissue yace"kira zulai ta kwashe kayanan,tunda naga kin gaji da aikin"yafada yana mikewa sabe da little lokaci daya yana fadin"bari naje nayi wanka,zan dawo miki da ita" yafadi yana wucewa dakinsa.

  Da harara tabisa kan ta mike ta hau jiddan kayan tana maidwa kichen,ciikin sauri takammallah takoma dakinta bayan ta dauki moodu dayayi barci,ta kwantar dashi tafada tiolet tayi wanka ta dauro alwala tazo ta kabarta sallah,ta idar da Shafa"i da wuturi kenan,tana hanzarin mikewa tasakama kofar makullin,tayi alqawarin sai dai little Ummi ta kwana wajensa,ammh bazata bari abunda ya gudurta yafaru ba, sai da me,tamike kenan tana linke sallaya ya sawo kai dakin da sallama,yasauya kaya zuwa bakar doguwar jallabiya,little tana sabe bisa kafadansa tayi barci da kallo ta bisa lokaci daya taji gwiwanta yayi Sanyi,bai kalleta ba,yawuce ya kwantar da ita kusa da dan"uwanta,ya dawo yana kallonta kai tsaye yace"kina da alwala.,?."yafada yana kallonta.

  Cikin rawan jiki tace"eh.."gaba kawai ya wuce yana fadin"shimfida sallayan.."haka kurum yace,tsaye tayi tana kallonsa,kafin tayi mgana ya kabarta sallah,dole ta shimfida sallayan tabisa sukayi raka"a hudu kafin ya sallame yana kwararo addu"oinsa cikin ilimi,aran Zahirah tace tabdijam ashe kana da ilimi ammh kana zaune mace ta asirce ka,yadade yana addu"a kafin ya shafa,juyowa yayi yana kallonta itako tayi Saurin sadda kai jikinta na rawa.

  Bai mata mgana ba,ya mike yaje yasakama kofar makulli,kafin yakoma kan gadon ya dauko yaran daya bayan daya ya jerasu bisa wata kujeran cussinon,tana da fadi da tswo kamar gado take,kwanatar dasu yayi ya tofa musu addu"an kafin yakoma bisa gadon yazauna yana kallonta,cikin dakewa yace"Zo nan Zahirah.."yafada cikin kakkausan murya.

Kadan yarage zahirah bata saki Fitsari ba,savoda tsoro jikinta na rawa ta mike ta isa garesa tana fadin"ga..ni.."kanta na kasa,sama da kasa ya kalleta kan yace"ki cire hijabinki kizo nan nace" yafada cikin bada Umarni,jikinta na rawa tadago tana kallonsa kafin idanunta su ciko da kwallah girgiza kai tayi tana fadin"bazan iya ba.."tafada tana sharbe majina alamar kiris yarage bata saka kuka ba.

Tsam ya mike ya isa gareta yasaka hannu ya zare hijabin jikinta yayi wurgi dashi yana fadin"meye kikeyi haka?kamar bakisan komai ba kefa ba yarinya bace,kamar yadda nima ba yaro bane,saboda haka dukkanmu munsan Abunda yakamata basai na tsaya ina miki dogon Turanci ba."yafada yana rumgumota kuka kawai Zahirah ta fashe dashi,saboda ganin yadda ta shiga hannun Alhaji ba hanyar tsira.

  Shafata yafarayi yana shinshinan wuyanta kafin ya zage mata zip din rigarta yayi cireta gabadaya bra dinta ma rabata yayi da ita,lokacin dayayi arba dana Shanunta,wanda suka cika fam dasu cikin rudewa yake lagudasu yaji abu atsaye cur,ba irin na yagana ba kamar silafas😂itadai zahirah dikim tayimai tana hawaye tanaji yajata kan gadon ya kwantar kafin ya cire jallabiyan jikinsa ,lokaci daya yana kashe fitilar dakin bayan ya kunna dumlight din dakin.

   Tanaji tana gani ya hayo kanta yana binta da sumba jikinta na gogan nasa,kukanta yakaru ne sanda taji yayi kasa da sikat dinta lokaci daya da pant dinta ganin yadda take kuka yasashi rumgumeta yana fadin"kiyi hakuri kibarni nasamu natsuwa dake,in kuma inada rabo har nayi nasarar baki ajiyar da"na ko ya"ta aciki mahaifanki don Allah" yafada yana shafa ta ta ko"ina.

  Cikin Ran zahirah tayi Saurin cewa"ba Amin ba.."tafada tana cije lip dinta tanajinsa yagama wassanin da ita ya nemi hanya yana karanto addu"ar saduwa da iyali idanu ta runtse daidai lokacin daya shigeta da karfi rikesa tayi lokacin dataji wani azaba ya ziyarce ta,bata san sadda ta furta" wayyo Allahna.." tafada cikin azaba da ZUBAR KWALLAH.

   Mirgina kanta tayi gefe tana kuka hawayenta na zuba masu zafi cikin wata murya take fadin"ka yafemin..."take fada tana kuka,saboda bata da yarda zatayi ta gujema kaddaranta tabbas wannan yana cikin abunda Allah ya tsara musu ita da ya mu"azzam basu da yarda zasuyi.

____________________

  *Sudan*

    ""Zuwa wannan lokaci tuni mu"azzam ya yanke ma kansa shawaran komawa nageria koda bayaso,domin akwanakin wani mafarki yake mai ban tsoro,sai ya dinga,ganinshi cikin wani daji bakikirin babu gida gaba babu baya,yana cikin waige waige sai ya hangosu wasu yan yara guda biyu suna tahowa inda yake,shima cikin azama zai nufesu ammh kafin ya karisa sai kasa ta rufta atskaninsu rami ya bayyana mai girma,hankalinsa ya tashi yaran suna mikamasa hannu shma yana mika musu hannu ammh hanunsu baya kaiwa saboda ramin daya raba tsakaninansu,suna cikin hakane sai gawata mata tazo gabadaya jikinta alullube ko Fuskarta ba"a gani tazo taja hannnun yaran da karfi tafara tafara tafiya dasu,suko suna kuka suna mika musa hannu,yana mika musu hannu,ammh kememe taki sakinsu saima kara jansu datakeyi suna kuka suna mikomasa hannu ahaka harsuka kusa bacemai kana matar ta waiwayo da Fuskarta daidai lokacin da haske ya bayyana kawai sai yaga Fuskar Ummi,ta bayyana Idanunta suna zubar kwallah.

  Cikin karaji ya Furta "*UMMI NA..*"yafada karfi daidai lokacin daya farka daga mafarkin duk yahada zufa,koda ya duba dakin babu kowa,yana tunanin mooh yatafi office,yadade zaune hannunsa dafe kai yana nazarin mafarkin dayayi,inbaiyi kuskure ba ya"yansa da mahaifiyarsa suna bukatarsa,tun yanzu kafin lokaci ya kuremai,hankalinsa tashe ya tashi ya fada tiolet yayi wanka yazo ya shirya cikin riga da wando black and white,sallolin dasuka kubcemai yayi domin yadade yana barcin.

  Fitowa yayi falon daidai lokacin da Mom ke cema Abbie "wai ya mganar matar tasa da yaran,naji bakace komai ba haryanzu.?"jin haka yasa mu"azzam dakatawa yaji mai Abbie zaice,ajiyar zuciya Abbie ya sauke kafin yace"Ina sane naki cewa komai Rumana,koda naje na nemi ganawa da itakanta,yarnyar,naga kuma jikokina dana ma mu"azzam alqawarin dubosu in naje,to na tarar da yarinyar tayi aure harta tare,kuma tatafi da yaran gidan mijin.."
Chapter 57 · 0% Book details