← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 82

Sashe 8

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

......Bukar ne ke zaune yana cin abinci a yayinda Mahgana ke gefensa Daga barayin gun zaman Dining din Falon, daga cikinn Falon kuwa Zahirah ce ke wasa da kannenta su Alee wanda sune keta damunta da hayaniyarsu itakuma tana binsu da mirmishi kamar wata comedy..,Bahgana yakalli Zahirah kafin yakada kai yace"Baffa na nemana kuma am Sure kan Auren Yahna ne"Tagumi Mahgana ta zabga kan tace"wai yanzu Abban Alee da gaske Yahna aure zaku mata? tafada cikin Karaya kada kai yayi yana kallonta kan yace"eh Abunda Baffa yace kenan,kuma kinsan ban tsallake Umarninsa ko? kuma infact ma Bata isa zama gidan mijin bane kokuwa menene naga keda Yakura kundamu kanku"Yafada yana Tsareta da ido jaye idonta Tayi kafin Ta maida kan Zahirah Shima sai yabita da kallo Alee ne yaketa hawa jikinta suna Fada da Idirs Tama kasa rabasu kwatakwata jikinta suka fado sunayi kawai sai tafara hawaye saboda bata son hayaniya ko kadan,Tsam kawai tatashi ta shige daki ta barsu nan,kauda kanta mahgana tayi kan tace"Ka kalli fa wacce zakuma Aure kukaita wata uwa Duniya..Yahna macece mai sanyin Hali wanda halitarta ne batason kwaramniya ko kadan Wlh matukar batayi dacen gidan Miji ba irinsu hawan jini ke kashewa ba"a Sani ba, saboda Rashin maganansu"Tafada idonta yaciko da kwallah.

  Bukar yayi Tsam duk da yadade da wannan Tunani ammh kuma yazaiyi Baffa ne fa da kansa..Bazai iya bijirema Umarninsa ba gaskiya,ammh azahirin gaskiya koshi yana Tsausayama Zahirah matuka baya da yarda zaiyi ne Tunda ga Abunda baffa ya tsara.

Mikewa kawai yayi kan yace'"Karki damu chan dinma, gidane karki manta dan"uwanta fa zata Aura da mahaifinsa da Mahaifiyarta Nono daya suka sha"Yafada yana Wucewa batare da yabari taga kwallan data cika masa ido ba..

Mahgana tamike tana Fadi cikin Ranta"Hmmm.Baffa dai baiyi Hasashe ba,Domin wani gagarumin aiki yake kara taroma kanshi don ayadda Tasamu labrin komai Suhaima bazata taba Kaunar Jinin Fadi ba har abada,balle har yarta ta Auri danta..Bala"i "Tafada Afili tana Rike baki kan tace afili"babu matsausaya Sai marainiyar Allah wacce batason komai Na rayuwa ba.

  Koda Bukar ya isa gun Baffa mganar kenan yana fadamai yakamata atsaida lokacin bikin saboda baison adau lokaci,kallonsa bahgana yayi kafin yace"Ban Tari Numfashinka ba Baffa ammh inga shi yaron zai Fadi lokacin dayake son ayi sha"anin ko? don kar mushiga hakkinshi'"Shuru baffa yayi kafin yace"A"a In aka tsaida sai akirashi a shaidamai shikenan"Rausayar dakai bahgana yayi kan yayi mgana Baffa ya rigasa da cewa"kaje kuyi shirye shirye daya kamata,nan da Sati hudu nake so Ayi komai agama fatan ban Takura kaba'"

  Wani Gugun Bukar yaji zence nan da Sati hudu kuma? meke damun Baffa ne shurun dayayine yasa Baffa yin gyaran murya yace"Namaka katsalandan ko Bukar? Mirmishi yayi kafin yace"Kuskuren da mukayi afarko ne nakeson gyarasa tunkan Allah ya dau Raina,kayi hakuri kacikaman Burina don Allah Bukar"Yafada Muryansa Tafara Rawa da Sauri Bukar yace"A'a Baffa ka isa dani ma balle Abunda na mallaka,Allah ya nunamana lokacin"Yafada yana dukar dakai da haka sukayi sallama da Baffa yakoma gida.

  Koda yakoma mahgana talura dayana cikin damuwa data tambayeshi sai yacemata bakomai shiyasa ta kyalesa ammh itama Tasani mganar Zahirah ce ke damunsa Shima,shuru yayi bai gayama kowa ba sai yan"uwansa wanda suma sukayi tafada da son nuna baffa yacika son kai dayawa,aure kamar wata auren yar tsana,shidai bukar hakuri yayi tabasu domin bayason watsama baffa kasa a ido, yacigaba da shirye shiryensa Saida Abun yarage 2weeks kana Bukar yafadama mahgana biki fa yamatso Abun har yaso yadan taba zamansu Tace Saboda yaga ba itace ta haifi Zahirah ba..Hakuri kawai yaita bata baidatacewa,itakanta yakura kuka takama  ma baffa na Tsausayin Zahirah ammh ina bakin alkalamin ya rigaya daya bushe,Dole yakura ta hakura tafara shirin yadda zata gyara yarta.Wacce batason wainar da"ake toyawa ba.

•••   ••••••       

     Mu"azzam Tunda Sukayi mgana Da Shureim ya manta da mganar nan..Saboda baison Tashin hankalin Umminsa shima Shureim din baisamu zuwa ba saboda yanayin aikisa, kuma ko awaya basu kara tattaunawa ba,Kwatsam Ranar yana office sai ga kiran Bukar wanda yana gani sai da gabansa ya amsa saboda yasani Baffa ne,zufane ta ko"ina ketomai take cikin Rawan jiki yadaga kiran bayan Sungaisa Da Bukar sai yabawa Baffa wayar yana Fadamai cewa shikeson mgana dashi.

   Mu"azzam Hankalinsa ne yatashi lokacin da Baffa Shettima ke gayamai sun Tsaida lokaci nan da Sati biyu yazo adaura Aure..Kuma kada yadamu tunda shima din na gidane basai yatakura kanshi ba bayan andaura Aure yazo yatafi da matarsa..Turkashi..Shidai har suka gama wayar bai cikin hayyacinsa Innalillahi wa"inna Alaihirraju"un..Tabbas yashiga tsaka mai wuya Yazaiyi da Ummi wani kalamai zai Fadama Ummi ta yarda dashi.

  Baigama Abunda zaiyi ba ya kira Ushe yace sukoma gida..Har suka iso gidan bai sani ba, sai dayaji Ushe na fadin Yallabai mun iso" Dole ya fito jikinsa a matukar Sanyaye fitowarsa keda Wuya ya hango Ummi na Fitowa idonta akanshi, ta kuramai ido lokaci daya ya daburce,Itakuwa tun Fitowarsa daga mota, ta lura bai cikin Natsuwarsa shiyasa itama Hankalinta ya tashi ta karisa gareshi da, hanzari cikinn Tashin hankali tace"Son..Wht hpped naganka wani iri,hop dai bawani Abu bane yasameka ba ko?, tafada Tana Riko hannunsa.

*Don"t Forget to*
*Comment*
*Share*
*Vote*

*JANAFI*💕

_*INTELLIGENT WRITERS ASSO*🖊_

🌺 *UWAR MIJINAH..!*🌺
        _(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)_

       *ALKALAMIN:JANAF*💕
        *WATTPAD:JANAFNANCY*

*DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF*

_I DEDICATED dis page to u ANTY FATIMA(In low)...Hakika kirkin gareni sai dai nace ALHAMDULILLAH..Kulawanki akaina sai dai nace MASHA ALLAH,..Alherinki gareni kuma Sai dai nace ALLAH YAYI MIKI SAKAYYAH..,Bayan ya iya miki Abunda kika gaza..Tanque So much Janaf Relli Appriciate_🌹

*NO 7*

........Saurin kakaro mirmishi yayi yana kara riko hannun Ummi yake Fadin"Normal Ummi kaina ne yadameni da ciwo dat why nadawo gida"Yana Fadin Haka Ummi ta rude tafara taba wuyansa tana fadin"Ayyah shiyasa naga kayi wani iri oya muje kaci abinci na baka magani banison zama da ciwo kasani son"Tafada tana jawosa suka Nufi hanyar Falon ushe na binsu abaya dauke da yar jakarsa.

  Suna shiga falon tashiga kwalama lami kira wacce ke kichen tafito Arude tana Fadin"Hajiya lafiya kuwa naji kiran ne daga Sama" Ummi takalleta daidai lokacin da Mu"azzam ke zama kan kujera hannuwansa duka biyu dafe dakai tace"Ina lafiya son ne yadawo gida ba lafiya"Dafe kirji lami tayi tana Fadin"Munshiga uku hajiya yallaban? Tafada duka idanunta waje.

   Ni tara na shiga bama uku ba, lami,abinci zaki Taimakon dashi yaci na bashi mgani"Tafada kamar zatayi kuka da sauri lami takoma da baya tana Fadin"Yanzu kuwa hajiya..Yallabai sannu,Allah kenan yanzu yanzu da lafiyanka anjuma kuma ta kubcemaka"Tana wannan mganar tafada kichen din karime da Uwani na tambayanta lafiya takwashe komai tafada musu suma din dafe kirji sukayi idanuwa waje kafin su cikin rawan jiki su fice zuwa falon.

  Koda sukaje sun iske Sani maigadi da Falalu durkushe sunatama yallabai sannu wanda ke kwance kan cinyar Ummi tana shafa kansa tana jeramai addu"o"i tana tofamai bisa kai,kamar zatai kuka kokuma ciwon yadawo jikinta nan su karime ma sukabi ayari suka zube suna jeramai sannu wanda ke amsamusu dakai kawai ammh a zahirin gaskiya jiyake dama shine su domin su basu da wata damuwar kamar yadda yake ciki,lafiyansa kalau kawai yarasa mezaicema Ummi ne, wanda hankalinta zai kwanta,to gashi bai tsiraba shiya manta yadda in yana ciwo Ummi haka zata sakashi gaba tana kuka bata sukuni sai ya samu lafiya..To yaudin ma hakane yafaru ita tadinga bashi abinci abaki Wanda yakeji kamar yana cin madaci ammh hakanan yaita Turawa yana gama ci dama tama Family doctor dinsu waya Dr Abduljabbar wanda yace yana hanya.

Koda Dr Abduljabar yazo yaduba mu'azzam kawai yace Rashin Samun hutu ne alluran barci yamai yace ya kwanta yasamu barci na good 5 hours yana tashi komai zai koma Normal,ai Ummi ta dakanta ta rikeshi har dakinta ta ciremai,takalmi da Socks taciremai caot din,ta kwantar dashi bisa gadonta tana Fadin"Oya sleep kaji dai Abunda Dr yace ko'"Yagyada mata kai yayi, sai tacigaba da cewa'Bani son katashi sai na tasheka da kaina so Rest kaji son"Tafada tana shafa kanshi.

Kallonta yakeyi kafin yariko hannunta yace"Nagode Ummi na Nagode"Yafada idanunsa sun kawo kwallah kafin yayima hannun kiss mirmishi tayi tamaidamai kiss din bisa goshi tana Fadin"Iz my duty son..Love u so much"Tafada tana kara kissing dinsa bisa goshinsa shikuma lokacin alluran tafara aiki idanunsa na lumshewa blanket tarufamai zuwa kwankwasonsa kafin ta fice bayan Ta rufomai kofa..Ajiyar zuciya ya sauke yanajin kamar ya fashe da kuka..Yazaiyi Baffa shettima zai watsama kasa a ido ko Ummi wacce ta sadaukar da fatincikinta akansh,ta sadaukar da dukkan jin dadin Rayuwarta zuwa gareshi,yasan cewa Ummi bazatataba fahimtarsa ba kilama tayi Fushi dashi Fushi na har abada..Da wannan Tunanin barci yayi awon gaba dashi.

   """"Saida yashafe wajen awa shidda yana barci kafin yatashi shima din kiran sallar mangarib ne yataadashi wanda daman haka yake komai Nauyin barci wlh ana fara kiran sallah Allah ke tayar dashi..daidai lokacin daya mike Ummi ta shigo dakin Ganinsa zaune yasa Takarisa tana Fadin" Nasan daman yanzu zaka tashi shiyasa na shigo"Tafada tana zama kusa dashi wuyansa tataba zuwa kansa tana Fadin"Ya jikin hop u feel better Now, son?"Tafada murya cikin Damuwa lumshe ido yayi kafin ya bude cikin sansanyar murya yace"Naji Sauki Ummi daman Ciwon kai ne,fa kawai"Yafada yana kallonta.

   Shiiiiiii.."Tace hannunta bisa bakinshi kafin tace"Ciwon kanka son Awurina ba kawai bane,bakasan tashin hankalin dana ke shiga bane duk sa"ilin dana ganka ba cikin walwalwarka ba"Tafada tana shafa fuskarsa riko hannuwanta yayi yana Fadin"Duk wanda yasamu Uwa kamar tawa Uwar hakika shi mai Sa"a ne kamar yadda nasan Nimai Sa"ane Nasamun ki Amtsayin mahaifiyata Ummi na"Yafada yana kwantar da kansa bisa kafadanta,Hannu tasanya tana shafa kanshi mirmishi take kawai ammh takasa furta komai sai shine keta maimata "ina sonki Ummi na".

Har dare yayi haka Ummi keta hidima da mu"azzam ko abinci takasaci wayyo baiwar Allah gabadaya tsausayinta yacika Mu"azzam shiyasa yafaramata barcin karya donta kyalesa yaje dakinsa ya kwanta..Ammh ina Ummi bata yarda ba Dakinta takara maidashi ta, kwantar dashi kamar wani jariri bayan ta Tofeshi da addu"a Kallonta kawai Mu"azzam keyi baida tacewa gashikuma soyake ya kebe yakira Shureim yafadamai komai ke faruwa domin kanshi fa ya kulle ya Rasa mafita.

****   *****  *******
Chapter 8 · 0% Book details