← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 82

Sashe 36

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonta ta dawo kan mu"azzam wanda ke tsaye kamar wani tsohon munafuki,Mirmshi tayi mai ciwo kafin tace"Ni Suhaima,ni Suhaima,ni Mu"azzam kaci amanata ka sabama alqawari, kayi ma diyar wa"inda sukayi sanadiyar rugujewar Farinciki cikina,ka na so dole sai na hada zuru"a dasu ko.."? tafada tana kallonsa Rausayar dakai yayi ya bude baki zaiyi magana ta katseshi da cewa'Karka kuskura kayi min mgana Ibrahim kagama min komai naga sakayyar daukan cikinka danayi har na tsawon wattani tara,nazo na haifeka nasha wahalan Shayar dakai nasha wahalan Rainonka saboda kai nasha kwana da yunwa nayi fadi tashi na rayuwa don duk kai kasamu rayuwa mai inganci,yau burina ya cika kazama wani abu ibrahim ashe da abunda zaka sakamin kenan..."Tafada hawaye suna mata ambaliya.

Jikin mu"azzam na rawa ya durkushe bisa gwiwowinsa agaban Ummi idanunsa sunkada sunyi jawur shima jijiyoyinsa kansa sun mike radau kamar wanda wani cuta ta kama,gabadaya miyan bakinsa ya kafe yarasa mafita lokaci daya abubuwa sun taru sun mai yawa ya bude baki zaiyi mgana kenan karime tace"yallabai,hajiya ku taimaka akai zahirah Asibiti wlh Nakuda ce,kuma haihuwar Fari kada Asamu mtsala.."Wani sakaran kallo Ummi ta jefa karime dashi kafim ta daka musu tsawa tana fadin"Ku saketa munafukai,ko zata haihu billahil azim baza haifanmin wannan dan iskan cikin acikin gidanan ba,sai dai ta haifeshi cikin gidan Shettima..,kuficemin daga gani banzaye kawai.."Tafada cikin bacin rai tana wuci kamar mahaukaciya.

Gaban mu"azzam yafadu Ras lokaci daya yana kallon Ummi wacce tafara taku zuwa gabanshi daidai lokacin dasu karime suka fice hankalinsu atashe,jikinsu a matukar sanyaye,ga Tsausayin yar baiwar Allah zahirah,ga kuma mamakin Rashin Imanin Ummi,haba ko bata taba haihuwa ba,ita macece balle ma ta haihu tasan zafin Nakuda ammh dayake zuciyarta babu imani ko ajikinta.

Tana takowa zuwa gabansa tace cikin kakkausan murya.." *IBRAHIM..."* Takirasa cikin dakewa da bacin rai jin kiran nata tuni zuciyarsa ta tsinke don baitabajin muryan Ummi cikin zafi haka ba,baisamu zarafin mgana ba zahirah ta karade falon da Salati tana fadin"innalillahi..Hasbunallahu..Subhannallahu..Ya mu"azzam ka yafemin wlh mutuwa zanyi,ka fadama bahna na ya yafemin,shiko baffa ka fadamai na kasa cikamai burinshi na wanke laifinsu wajen Ummi wanda nayi iya bakin kokarina ammh abu ya ci tura,don Allah ka isar da sakona gun yakura kace itama ta yafemin Allah yayi bazamu gana ba,wayyo bayana zan mutu....."Tafada cikin muryan kuka tana dafe bayanta,mu"azzam ya kalleta hawaye ya cikomai ido yanason zuwa gunta ammh yana tsoron Ummi wacce take kallon zahirah tana fadin"Ko zaki mutu ba " anan ba yarinya sai kin koma gaban shettima da sakona bayan ya amsa,in ma zaki mutu ne to alokacin sai nace sai munzo..."Tafada Fuskarta babu ko digon Tsausayi.

Kan Mu"azzam ta maida idonta tana fadin"Yau zan Nuna maka kai ba kowan kowa bane mu"azzam don bakai ka haifi kanka ba,yanzu ba sai anjuma ka saketa yanzu yanzunan..."Tafada cikin bada Umarni

Arazane yadago yana kallonta kamar yadda duk azaban dake addaban zahirah sai da tadago tana kallon Ummi wacce ke tsaye ta rike kugu tana hararan Mu"azzam wanda jikinsa ke mazari ayayinda zuciyarsa ke luguden Tsoro, ya kalli Ummi yana fadi cikin Rawar murya.."Ummi don..Alllah..Ki..yi..hakuri wlh bazan iya sakin..Zahi.."Tas!Tas!ji kake karan mari ta wanke mu"azzam dashi tana huci tace"Wlh ko zaka mutu sai ka saketa ko yanzu na daga maka Nono don ubanka.."Tafada lokaci daya tana watsama mai wani banzan kallo.

Jikinsa na rawa ya rarrafa yakama kafar Ummi yana fadin"Ummi na don Allah kiyiman aikin gafara,ki tsausayama baiwar Allah nan,kibari toh in munkaita asibiti ta haihu koma miye nayi miki daga baya.."jaye kafanta Ummi tayi tana fadin"Ban yarda ba sakarta yanzu.."Tafada cikin bada Umanarni..

Sulalewa yayi ya zauna yana kallon zahirah wacce itama ke kallonsa hawaye na wankemata ido,wani sonta da tsausayinta na tsirgamai Ummi ce tadakamai tsawa da cewa"au bazaka saketa ba,sai na daga maka nonon,kenan kashirya biyana kudin Nonon daka sha kenan.." cikin Sauri Mu"azzam yace"a"a Ummi zanyi zan saketa.."Yafada yana Rintse ido kafin ya furta cikin rawan murya"Na...Sa..Ke...Ki...Sa.Ki...Da..ya..Zahirah..."yafada lokaci daya yaji wani abu ya tsayamai a makogoro yakasa wucewa.

Zahirah dake jin jiki sai da numfashinta ya dauke na wani lokaci kafin ta fashe da kuka,kuka mai tsuma rai,ga Nakuda ga sakin Aure,kai wannan bala"in dame tayi kama,girgiza kai Ummi tayi kan tace"Ai kuma baka isa ba,duka zaka cika shemata mallam,ai daga wannan na bar kara baka dama yaro.."tafada tana gyara tsayuwarta.

Jiyayi duniyar tayi masa kunci Ummi tadakamai tsawa tana fadin"Kazabi ka biyani Nonon nawa Kenan?Tafada tana kallonsa girgixa kai yayi yana kallon zahirah yakara cewa.."Na..Sa..Ke..ki..Sa.Ki...Bi..yu..."Yafada yana durkushewa shima kamar ya saka ihu zahirah kuwa cikinta ne ya harbamata ta rarrafa ta isa ga mu"azzam tana fadin"A"a yaya mu"azzam...'"Tafada kamar zata shide.

Kara dakamai tsawa Ummi tayi tana fadin"Wlh zan kira maka tsinuwa yanzu mu'azzam matukar baka karishema shegiyar yarinyarnan sakinta ba.."Tafada tana hambarinta da kafa Zahirah duk da azaban datakeji haka ta dago tana tana kallon Ummi Kafin tace"kar..Ki..yi...Ha...Ka..Um..mi..."Tafada lokaci daya tana cije baki.

Juya baya Ummi tayi tana fadin.."Allah ya..."a"a Ummi don Allah karki soma don Allah.."yafada cikin karyewan Numfashi Tace "To karisa mata cikon Ukun ta yanzu.."Tafada cikin bada Umarni.

Yana kallon idanun zahirah wanda hawaye suke ambaliya ya bude baki zaiyi mgana Zahirah ta yunkurin ta fado jikinsa tana fadin"a"a..Karka Furta don Allah,karka furta ka haramtama zama na har abada.."Tafada tana kamkamesa Ummi ta daka tsaki zatayi mgana yayi Saurin cewa"Na sake ki saki uku Zahirah ammh wlh badon bani sonki ba,sai don bin Umarnin Mahaifiyata.."yafada yana kamkameta suna kuka dukkansu mai cinrai.

Mirmishi Ummi tayi kafin tace"Alhamdulillahi..Yanzu burina ya cika na tabbata in kika koma ma shettima da wannan sakon kadai ya isheshi yaji abunda suka saka naji alokacin.."tafada tana saka hannu ta fizge Zahirah tana fadin"Sakeshi tunda batare kukazo Duniya ba,yanzu sai abi wani sarkin ko,nidai na yarda kwallon mangwaro na huta da guda.."

hannunsu na sarke da juna suna kallon juna suna kuka,Ummi ta ja hannun ta raba tana fadin"Munga laila da majnun saketa don ubanka.."tafada cikin dakamai,tsawa,sakinta yayi yana dafe kansa kuka yake kamar karamin yaro,zahirah da cikinta yake hautsinawa kamar zai fito duniiya alokacin daya ta yi karfin Halin mikewa Ummi ta izata tana fadin"Toh sai ki ficemin daga gida wlh ko daki bazaki koma ba, mayyah Tafi kije ki fadama Shettima komai banison kirage komai so nake zuciyarsa ta buga kema nayi takaichin mutuwar uwarki don nasan da tana raye kilama zuciyarta ta buga ta mutu,.."tafada tana ingiza keyar Zahirah zuwa waje ko tsausayi bashi aranta.

Zahirah dataji wani karfi yazo mata ta daddake ta ture ummi,wacce sai tayi taga taga zata fadi dakyar ta iya tsayawa kan kafafunta,Kallonta zahirah takeyi cikin tsana da Bacin rai kafin tace da karfi..." _Kinji kunya wlh Tir da ke,mekikayi kenan,kinyi abun burgewa don kin saka danki yayi saki uku alokaci daya,sakin da Allah da kansa ya hana,wanda ko daya akayi sai al"arshin Allah ya girgiza,ammh ke uku kikasa akayiman aka sakeni da tsohon cikin jokinki ajikina,To kije duk Abunda kikayi Allah nagani,kuma da izinin lahi hakkin na, dana ya mu"azzam sai ya kamaki,sai ya kamaki barganin kina mtsayin ,mahaifiyarsa aike ba Allahnsa bane..._"Tafada cikin tsawa idanunta sun Firfito Da hanzari Ummi taja baya tana rike baki domin yarinyar tabata tsoro kan tasamu zarafin mgana zahirah ta cigaba da cewa"Ko baki ce natafi ba zama ne yakare acikin gidan,nan,kuma sakon dakikace na kaima baffa zan kaimai,ammh kisani Sakon zaije garesa,ammh kisani ki kara sani zai Tafi ammh kema zai dawo gareki zai dawo gareki ki rubutu ki ijiye sai kinfini kuka da shiga kunci.."Tana gama fadar haka ta fice tana jan jikinta cikin tsananin bakinciki da halin ciwo.

Ummi datayi mutuwar tsaye ta rakata da fadin"Oho dai nidai,gidane dai dole mutum ya barsa tunda ba da kudin mai dattin hula aka gina ba.."tafada tana tafa hannu..

mu"azzam dake kife dakai ya dago da Sauri yana kokarin mikewa Ummi ta dakamai tsawa da cewa"Kana motsawa wlh zan debama albarka maras mutumci kawai..."Tafada cikin tsananin Fusata,kallonta yayi idanunsa sunja launi wani kallo na Anya kekika haifeni ma,Ummi kuwa taji kallon ajikinta shiyasa tace'Kai don ubanka wani irin kallo kakeman,ni ne dai Suhaima,kuma nice nan Uwarka nina haifeka,in ma kana tamtama ne kadaina.."tafada tana zama kan kujera ta harde,maida kansa yayi ya cusa cikin gwiwa yana jin kansa na barazanar fashewa ga kirjinsa dake ruwan lugude yanaji kamar wani abu kamar dutse aka dora masa awajen.

Zahirah na fitowa kofar falon taci karo dasu karine durkushe suna kuka,alaman sunajin duk abunda ya faru,kallonsu zahirah tayi hawaye suna zubomata ta sanya hannu ta share tana fadin"Sai wata rananku,har abada bazan manta da alherinku gareni ba nagode muku sosai.."Tafada kuka nacin karfinta tajuya da Sauri tafara tafiya karime ta mike ta kwalamata kira."Diyata.."Tafada tana mai zubar kwallah.

Cak ta tsaya hartazo kusa da ita dankwalin kanta ta ciro ta yafamata kafin ta hau kunce haban zaninta ta warwaro kudi masu yawa yan dubu dubu ta mika ma zahirah tana fadin"Karbi wannan diyata kije dashi kiyi kudin mota nasan baki dashi..kije Allah ya saka miki .."Tafada tana juyawa da gudu,da kallon zahirah tabita,tanajin kwallah na taruwan mata,sharewa tayi tana kara damke kudin dake hannunta Allah sarki mama,dazu da safe yallabai ya biyasu kudin Albashinsu shine ta bata,Allahu ya sakama wannan matar ta fada aranta kafin tagyara dankwalin dake kanta kafarta ko takalmi babu tajuya tafara tafiya gayadda cikinta ke murdawa ammh hakanan ta daure.

Su uche da sani maigadi da falau suna gefe suma sunyi zugum tazo ta wuce ta isa get din kenan sani ya rugo ya budemata yana kallonta kada kai tayi tafice kafin ta waigo tana kallonsu suna share kwallah,mirmishin yake ta musu tana daga musu hannu take fadin"Sai watarananku..."Cikin siririyar murya kafin tajuya tafara tafiya cikin sauri duk da ciwon dake cinta gashi dare yayi don lokacin har anyi mangariba babu kowa atitin kowa ya shige gidanshi.
Chapter 36 · 0% Book details