← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 82

Sashe 53

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

  Mom tabisu da kallo sha"awa aranta jin dadin ganin zaratan mazan masu kwarjini da tsari,sannu da aiki mu"azzam ya mata,ta amsa tana kallonsa tana washe baki alamar tana cikin Farinciki,Abbie ne shima ya fito ganinsu haka shima yasashi Farinciki sosai,Rumgumesu yayi dukkansu yana ma Allah godiya,yana dagowa yaci karo da lubna tana tsaye tana kallonsu cike da burgewa waremata hannu yayi yana fadin"oya come and join us Dota.." 

Da Sauri ta kariso ta gefen mooh ta tsaya bayan ta sanya hannu inda Abbie yadafa bayan mu"azzam,tana kuma kallon bayan mu"azzam din,sakin su Abbie yayi yana fadin"welcome to happy Family my Son.."yafada cikin murna mu"azzam yace"Tanque Abbie..Nagode ma Allah da yasa ina da rabon haduwa daku,haduwa da Family dina wanda sukamin nisa"jinjina kai Abbie yayi yana fadin"kadaina godemin Son iz my Duty so muje muci abinci ko?

yafada yana kallonsu kada kai sukayi suna mirmishi gaba yayi suna binsa abaya,lubna kuwa duk motsin Mu"azzam a idonta,kamar ya sani ya waiwayo karaf ko suka hada ido mirmishi ya sakarmata for d First time,sandarewa lubna tayi saboda yadda mirmishin ya daketa lokaci daya wucewa yayi yabarta itako dakyar ta karisa taja kujera ta zauna jikinta amace.

  Kowa nacin abinci ammh gabadaya attention din lubna naga Mu"azzam,wanda ko shi baima san wainar datake toyaba,bai wani ci abincin dayawa ba ya tashi,mooh yabisa suka koma falo suna hira,sai tamaida kunnanta kansu,tanaji yana fadama mooh shi lauya ne yana aiki a hight Supreme court Abuja,a inda shi mooh din kefadamai Shi Quantity Suver,yakaranta A jam'ar Malesia ayanzu haka yana aiki da gwannatin kasar sudan wajen shimfida kwalta,sunata dai hiransu mu"azzam ya saki jiki yana ba mooh lbrin yanayin aikinsu A Nigeria shima yana bashi nashi,ahaka Abbie yazo ya samesu wanda shima sama sama yaci abinci hankalinshi na gunsu tsakiyarsu ya zauna,shima aka shiga hiran dashi.

  Tagumi lubna ta buga tanajin yadda zuciyanta ke bugawa duk bayan kowani dakika matukar ta kalli mu"azzam,mom dake gefe ta kura mata ido tana mamakin meya same Lubna yau,ganin bata da wannan amsan ya sata ta mata banza taciga da cin abincinta.

_________________

*NAGERIA*

  Motar su Zahirah na tashi Ummi tayi Wuf ta fito,tana fitowa ba wanda ya ganta Waje ta fito ta iske ushe cikin mota batai wata wata ba,ta bude baya ta shiga tana fadin"Ushe mu koma Famfari.."jin mganarta kawai yayi asama kamar zaiyi mgana  sai dai ya fasa yaja motar suka Fice daga unguwar.

   Hon Suka zuba abakin makeken gidan da hanzari megadi yazo ya bude musu get motocin suka sulala ciki,Ashe ce kan gaban Fitowa tana sakin guda,itama mahgana ba"a barta abaya ba,tuni suka rikita gidan,chan wata yar yayan bukar ta fito da Turaren Wuta tana hurama Amarya wacce Yakura ta fito daga ita daga mota.

Gaba su Ashe sukayi suna sakin guda da tafi lokacin da suka nufi kofar da zata sadasu da babbar tagamemom falon Zahirah dake rike hannun yakura jitake kamar ana janta gudan ko da su Ashe suke kamar ta mutu takeji banda Tsiyayar hawaye bata komai cikin katon lifayan da aka nadeta dashi.

  Yagana dake Cikin bedroom dinta ita da kawarta Zinatu tayi wuf tatashi jin guda ya mamaye gidan,dafe kirji tayi tana kwalalo ido take fadin"Zinatu ya tabbata ga amarya an kawo,wlh ji nake kamar naje na burmata wuka agaban iyayan nata.."

Tsaki zinatu taja tana fadin"mtsewww...Sai kije ki bankamata ana miki fadan kikiyayi kiwon awaki kina zencen kyallah ta haihu,miye na damuwa keda kikasan nan da Sati daya zata koma inda ta fito.."

*Comment share and vote*

       *Jamilajanafty*
*UWAR MIJINA...!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_

       *Mallakar:JANAF*
       *Wattpad:Janafnancy12*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*GIFT TO:Hussain80k*

*Intelligent writer's Asso*✏

*NOT EDITED*💥

            *NO 33*

   "Kallonta yagana tayi kan tace"Allah Qawata.."wani killer smile Zinatu tayi kafin tace"indai da mallam da boko sai fita ta barmiki gidanki da mijinki nasha ruwan walh Qawata.."

  Tafada cikin gadara da wani yatsina hannu yagana ta bata suka kashe tafadin"Shegiya qawata ko shedan na tsoron hada hanya dake'"dariya tana fadin"don uban mutun shidin shedan na hada hanya dashi,ne yo duk karatun dayane,Karatun dare dukkanmu mukayi Shiyasa har tafaru ta kare bamu Fahimci komai ba"dariya suka sheke dashi suka kara tafawa daidai lokacin dasukaji shigowarsu falon yan"uwan Alhaji da sukazo daga kano suna musu lale marhaba.

   Cikin mutumci da kararramawa yan"uwan kabiru suka amshesu akasa suka zaunar da zahirah,wata diyar goggon kabirun wacce,ake kira da uwani tayi karaf ta karbe Little Ummi dake hannun Hajiya tana fadin"Allahu akbar kaga inda akeyi don Allah,irin haihuwa jikar akbarka,Allah yasa wata shekara ki haifoma yan hudu ne ma ba yan biyu ba"tafada tana shilla little ummi wacce ke bangala dariya,nan wata ma ta karbi moodu suna tayabawa suna saka albarka.

  Hajiya ne tayi gyara murya tana fadin"To masha Allahu yaudai ga amaryanku mun kawo muku,munji dadin yadda kuka karbemu ga zahirah nan ta shigo cikinku fatan zaku riketa tamkar yarku ta cikinku domin yanzu taku ce sai,kuma kunyi hakuri dan tana da danyen jego"Uwani ce ta karbe da cewa'"Mu karba wlh Allah yabada zaman lafiya mai dorewa da hakuri da juna,yara kuma muna so inda karima akawo wlh kawu bai ki ba,shida ya kwashi Shekaru kullum ya shigo gida sai haushi wata karya kullum jiya iyau babu cigaba"tafada tana hararan dakin yagana wacce ke ciki sunajin duk maganganun da uwani ke watsawa.

Cikin Zafin rai,yagana ta mike zinatu ta rikota kallonta tayi tana huci tace"sakeni na fita naci mai cin uwar wanchan ballagazan karuwar kauyen"Tafada tana huci,sakinta Zinatu tayi tana fadin"easy madam,barta keda kikeda takamar nasu hannu yo wani burga za"ayi miki barta tayi lokacinta ne,gobe bazata yi ba ko,?"tafada tana kallonta ajiyar zuciya yagana ta sauke kafin takoma gefe ta zauna tana huci zinatu na mata dariyan shakiyanci.

  Yakura ne takatse su da yadda suke zubama zahirah kirari da kuma yabo,gefe daya kuma suna yadama yagana habaici,da fadin"amm,ina shashen uwargidan mu kaita mu damkamata amana bisa al"ada dare nayi.."Uwani ta mike tana fadin"ku taso ku biyoni kunsan matar gidan sai mai gidan"tafada cikin gatse taso zahirah sukayi suka bi Uwani inda Ta wuce kai tsaye cikin wani bedroom tana tura kofan lokaci daya da sallama.

Su Ashe na ganin haka suka hada baki suna sakin guda,masu yawo da kamshi Turare suna ta fama dashi,Suna shigowa yagana da zinatu suka kallesu shekesheke cike da mamaki har suka zazzauna bisa kafet din dake tsakar dakin,Uwani tace tana nuna yagana"ga uwar gida karfen gida,uwar gida ga amarya hasken gidan ta shigo an kawo miki amanar nan ne ta iyaye dasuke badawa tun al"adunmu na da.."

  Da gayyah tafadi maganar bayan ta wani juyamata ido,wani wulakattacen kallo yagana kebin uwanin dashi kafin tace"yo ai na aza uwani yar kanzaki ke zaki karbi amanar don naga kiris yarage ki kaso aurenki kuzo ki auri kawun naki muyi zaman kishi,dake"tafada kai tsaye lokaci daya tana balla masu Hajiya da sukayi tsuru tsuru harara

Baki Uwanu ta rike kan tace"Wane ni da kaddarar dole,ai Uwani tayi zaman kishi dake yagana watan tonon asirinki ne yazo,ai amaryar dai ita ta dace dake,domin daga kamun ludayin mutum ake gani beran masar ne,ba mutum takamar wani Namiji  mage ba"Tafada tana tura dankwalinta gaba.

zuciya ta ciko Yagana zatayi mgana Zinatu ta rigata da cewa"kai kai Qawata wannan wani turare ake busamana,kada ace dai Turaran mallakane ake turaremu dashi"Tafada tana toshe hanci yamutsa Fuska yagana tayi tana fadin"wa yasani Tunda dangin ASiri ne,in Atsaye suke to ni yagana A tafe na kwana,zencen amana plz and plz kutashi ku barmin daki,amana ban karba ba,bakuma zan karba kabiru ne tazo taji abunda nakeji inace jijiyace takawota tazo taja ta barta domin mallakin yagana ce ita kadai.."Tafada cikin izgili.

  Cikin mamaki suke binta da kallo barinma hajiya wacce ke bin yagana da kallon mamaki,itako zahirah tana cikin mayafi tana kuka,batasan sadda taji kukan ya tsaigaita ba,tadago kanta ta cikin shara sharan lifayanta tana karema yagana kallo wacce ke jifansu da mugun kallo,Ashe ne ta miki tana fadin"ikon Allah haba baiwar Allah ammh kodon ganin idonmu kya rage wani abun ko? muma saboda al"ada ne kada muki kawota kice ba"a darajaki ba,ammh kam amanarta ai mijintane kadai zamu damkamawa,keda ita kuwa kowa ya iya allonsa ya wanke,yadda za"a kirasa mijinki haka za"a kirashi mijinta,kinga duk abun daya ne"tafada tana ballamata harara kan tace"kutashi mu sada ta da dakinta dare nayi kar mu shiga lokacin ango.

Dariya suka sheke dashi atare kafin zinatu ta mike tana fadin"ke kuma asuwa,gayyah Arna a idi,jibi bakinki don Allah..."Tafada tana nunata kafin sukara tsintsirewa da dariya,Ashe kuwa ta waigo tace"Ni a ubanki da uwarki,Tambadaddiya mara kamun kai,yo gwanda kowa da kowan wanke ko banza ita kawar taki Allah ya rufamata Aure ya lullubeta kefa,banda yawan kan ta zubar ba abunda kekiyi Kasuwa duka ta kulle an rasa inda za"a sai yawon bin gidajen kawaye Ana neman kashe musu aure,kibari kiyi auren sai ki samu bakin mgana" Tafada tana huci tare da rike kugu.
Chapter 53 · 0% Book details