← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 82

Sashe 50

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Suna shiga dakin Baffa na zaune bisa katifarsa wacce aka Shimfidamai Atsakar daki dayake jikin yafara sauki,yakan iyama zama a jinginamai da Filulluka,Da murna da Farinciki yakura ke fadin"Mallam tashi yau addu"arka ta cika ga Suhaima tazo gidanka yau"

  Tafada tana jawo Ummi zuwa gaban katifar, jin Abunda Yakura kefadane,yasa Baffa dan zaro ido bakinsa na rawa yake Furta'Su..hai..Ma..Ki yafemun don Allah,wlh hakiinki ke bibiyana haryanzu'ya kareshe hawaye suna bin kuncinsa.

   Ummi ta durkushe gaban Shettima tana fadin"a"a bakai zaka nemi yafiyata ba,nixan nema,yafi kuwa saunawa zaka roka baffa,kullum ciikin aikomin da sakon na yafemaka kakeyi,nikuma na hau dogin zuciya da turban shedan,wanda bai kai ni da komai ba Sai Nadama,Alhalin na manta Allah kadai ke tsara abu kuma yatafi ayyada yaso,Yau dai gani Durkushe agabanka ina mai neman Afuwarka,don Allah kayiman aikin gafara"Tafada tana fashewa da kuka.

  Baffa na hawaye yake fadin"Wlh bakimana komai ba Suhaima,dukkanmu masu laifine,Allah ya yafemana gabadayanmu,yarabamu da aikin danasani..'Yafada cikin Farinciki gabadaya dakin suka amsa da Amin,kafin kuma ashiga gaisawa,lokacin kuma ushe ya shigo da kayan abinci godiya sosai yakura da baffa ke jeramai shureim da addu"an Allah yakara budi.

   Baffa ya kalli Shureim yace"Shikenan kuma babu lbrin mu"azzam haryanzu ko"Baffa yafada cikin jimami,shureim yasaki ajiyar zuciya,kafin yace"wlh baffa bawani lbrin duk inda nake tunanin samun dan"uwa,wlh babu shi babu lbrinsa,sai dai mucigaba da addu"an duk inda yake Allah ya karkato da hankalinsa gida"Dukkansu suka amsa da Amin Ummi ko dukar dakai tayi tana share kwallar idonta,Hajiya da yagana suka kalleta cike da tsausayawa domin itace abun Tsausayi ayanzu.

  Sai gashi nan suka zauna anata maida zence ana jajantama juna,baffa ma dake kwance,bakinsa ya bude sai hira suke da Ummi,suna tuna da,suna takaichin,abunda suka aikata abaya suna fadin dama basuyi haka ba,to daman irin wannan Ranar ake gudu wato Ranar nadama,sallar kawai yatadasu,sukayi suka dawo su xauna Yakura ta dafamusu shinkafa da miya suka zauna sunaci,ana hira cikin farinciki da Annushuwa koba komai Ummi tasamu natsuwar zuciya saboda ta sauke wani nauyi daya tsayamata arai shekara da shakaru akirjinta dayaki wucemata sai yau,data roki gafaran Shettima takeji kamar an Saukemata wani Nauyi.

   La"asar nayi,Suka shirya dukkansu zuwa gidan Bukar,wanda yakura take shaida musu yau ne,ranar da Zahirah zata tare adakin mijinta,Ummi dataji mganar kamar saukan aradu,taji wani yamm,ajikinta ita tarigasu yin gaba saboda kukan daya tasomata,Shureim  kadai aka bari gun Baffa don yace bazai iya zuwa ba,Yaga zahirah za"a kaita gidan wani,koba komai yana taya dan"uwansa kishin zahirah,harga Allah yaji ba dadi,duk dai ko batayi auren ba,yasani ta haramta ga mu"azzam.

    Lokacin da suka isa gidan nasu zahirah ya kachame da yan"uwa da abokam arzuka anata hidima cikin daki kuwa Ashe ne ta takarkare tana ma Zahirah kwalliya tanayi tana masifa tana cewa"ke wai wata irin amaryace babu gyara,ballatanama kwalliya,haka zakijema mijin Fuska kozai kozai,dake, to in zaki mike ki mike wannan karan gidan KISHIYA zaki ba gidan UWAR MIJI BA..."

Tafada tana kokarin sakamata eye shadow runtse ido zahirah tayi Ashe tayi Saurin cewa"Wlh kika kuskura kika zubomin da hawayen banzan nan naki,alqur"an zan ci ubanki adakin nan,bar ganin kina da danyen jego.."tafada tana dugurinta akai,saurin shanye hawayenta tayi saboda tasan halin inna Ashe tsab zata aikata.

  Kamar amafarki takeji muryan wata kamar na Ummi Suna mgana da mutane Afalo,Saurin kwace kanta tayi daga hannu  Ashe ta fice da Sauri ta bar Ashe da masifan cewa"Ke kinyi haukane wai...?take fada,bayan ma tuni zahirah ta fice,wacce ke sanye da wani ubansu Swice less blue yana da ratsin milk colour ajiki,kayan sun amsheta matuka sun mata das dayake ruwan zafin ya amsheta matuka tayi kyau da ita.

  Tana fitowa falo abunda tagani yasata ta daskarewa a tsaye jikinta lokaci daya taji hawaye sun cikomata ido,UMMI ce durkushe gaban,bahna dinta tana,kuka mai cinrai fitowarta yasa falon yayi tsint kallon yadawo gunta,yan"uwan mahaifinta ne,sai hajiyar Shureim,da kuma yakura sai Ummi dake durkushe tana gunjin kuka,Jin shurun yayi yawa ne yasa Ummi kallon barayin da Zahirah take,Nan suka hada ido hudu ana juna,cikin wani yanayi zahirah tahau ja baya idanunta na zubar kwallah,lokaci daya jikinta na rawa juyawa tayi zata koma daki bayan ta saka hannu ta toshe bakinta da kukan dayakeson kubcemata.

  Da Hanzarin Ummi ta mike daga durkushen datayi tana fadin"ina zaki zahirah,kema gujemin zakiyi kamar yadda mu'azzam ya gujemin ya tafi ya barni.."Tafada muryanta ta sarke hawayenta na zuba ta cigaba da cewa"Don Allah don Annabi,kiyi hakuri zahirah,kimin aikin gafara karki gujemim ke kadaice nakeda da ita yanzu wacce zata san dafin dayake damuna azuciyata"Tafada tana durkusa bayan tahada hannuwanta tana kuka take fadin'Naji na yarda ni Suhaima na zama azzaluman Uwa ga mu"azzam,nakuma zama muguwa,mara imani gareki zahirah,kada kiyi duba da mugayen hallayanta,ki juyo ki kalleni kiyiman aikin gafara,wlh natuba nayi Nadama duka abubuwan dana aikata miki,Kiyi yafemi..Ki..Ya..fe..min.."Tafada tana kuka mai tsuma duk mai Sauraro kafin tari,ya sarketa ta duka tana rike kanta.

  Zahirah data ke tsaye hawaye sungama wankemata fuska,tawani juyo da wani irin gudu ta isa ga Ummi ta dagota tana fadin"Na yafemiki Ummi,wlh bantaba rike ki araina  daidai rana dayaba,duk abunda kikayimin bana ganin laifinki,kema batamiki akayi,Kullum burina kidawo ki yafemana mahaifiyata abunda ta aikata gareki,gashi yau burina dani da ya mu"azzam yacika,ammh kuma yau ta kasance babu shi,balle yaga wannan rana mai dimbin tarihi."Tafada tana kuka da Sauri Ummi ta Rumgumeta tana fadin"Babu Son Zahirah,son ya tafi ya barmu Alhalin ya manta cewa bazamu iya rayuwa babu shi ba, ammh komai yafaru ni najama kaina,Allah ne yake hukuntani da laifin dana aikata..,Allah na tuba ka yafemin.."tafada kuka na kecemata,kamkame juna sukayi suna kuka mai cinrai.

  Gabadaya jikin mutanen dake falon sai da yayi sanyi,yakura da hajiya kuwa kwallah suke sharewa,Shikanshi bahna juyawa yayi yana share kwallah,ita kanta Maghana kwallar take sharewa,Gyarab murya bukar yayi yana fadin"kubar kukan hakanan kada wani mtsalan ta sameku,ku zo muzauna duka a taru ayafema juna,an zama daya,abunda Allah kuma ya kaddara babu mahalukin daya isa ya hana"yafada cikin sanyin jik,hajiya ce ta isa ga Ummi ta kamo hannunta tana fadin"Muje ki zauna suhaima kinsan baki da cikkakiyar lafiya,ki rage wannan kukan don Allah.."Tafada tana riko hannunta,kam kuwa ummi ta riko hannu zahirah suka karisa cikin Falon suka zazzauna,umarni bukar yabama kowa akan azauna.

  gyara zama bukar yayi yana fadin"Alhamdulillah Allah shine abun godiya,dama abunda ake nema mutum yaringa yi kenan,yayi nadama Tunda Wuri tunkafin lokaci ya kuremasa,Babu komai hajiya Allah ya yafemana gabadaya.."yafada cikin kulawa.

  Muskatawa Ummi tayi hannunta na rike dana zahirah tace"Nagode sosai Allah ya kara girma.."Tafada bayan ta waiga bayanta itama mahgana tana rokonta gafara,nan tace ta yafemata nan Ummi tabi kowa afalon yan"uwan bukar tana cewa su yafemata,nan duka aka ayafi juna cikin mutumci da karamci,zahirah ta mike Ummi ta kalleta tace"Ina zaki Dota.."

      Zahirah ta kalleta kan tace"Ina zuwa ummi,yanzu zan dawo.."Sakin hannunta ummi tayi tana binta da kallon Tsausayi,ita bama kanta take tsausayama ba tafi tsausayama Zahirah don ita akafi cuta itace yarinya,daki zahirah takoma ta dauko yaran duka biyu ta rumgumesu ta nufo falon dasu,Ummi na ganin Fitowarta ta nufeta tana amsan littale Ummi take fadin"kai,kika iya daukansu lokaci daya,baki tsorom su kubce miki.."tafada tana kurama little Ummi dake hannunta ido.

  Mirmishi zahirah tayi tana fadin"Ai na saba ummi,banajin komai.."tafada bayan ta ijiyemata moodu gefen cinyarta inda ta dora Little ummi,Kura musu ido Ummi tayi cikin wani yanayi na fita hayyaci hawaye nabin idonta ta dago tana kallon zahirah kafin ta maida kanta gun hajiya,gyadamata kai hajiya tayi tana mirmishi,maida kallonta tayi kan zahirah kan tace"yanzu wadannan yaran ne,acikin ki sanda na koreki.."

  Tafada cikin wani yanayi,gyadamata kai zahirah tayi tana mata mirmishi tace"macen takwaranki ce ummi,namijin kuma sunan Abba,ya mu"azzam yace asamai.."Tafada bayan hawaye ya zubomata,Cikin kukan Fitan hayyacin Ummi ta rumgume jikokinta tanajin wani irin kaunarsu na ratsata,matuka cikin kuka take fadin"Ni wata irin azzaluman uwace,ni wata irin Uwar miji ce,mara rabo aduniya,nayi sanadiyar raba,uba da ya"yansa,bayan burin kowani uba yaga kwansa aduniya kaichona ni Suhaima Kaic....."Zahirah ce ta saka hannu ta rufema ummi baki tana fadin"a"a Ummi kibar fadin hakan,komai kika ga yafaru daga indallahine,ba laifinki bane Ummi dama chan rubuttacene daga rabbil izzati.

  Juyowa kawai Ummi tayi tahadata da ya"yan ta rumgumeta tana kuka take fadin"nagode zahirah..Nagode nayi takaichin raba Son da nagartacciyan mata kamarki,nayi takaichi har in na tuna kamar na kashe kaina nakeji.."Tafada cikin kuka itakanta zahirah kukan take,ganin kukan nasu yafara yawa ne,harsu little Ummi sun fara nasu kananun kuka,bukar yace don Allah subar kuka komai ya wuce,daki zahirah takoma chan ta basu little Ummi mama,tanayi tana kuka tana fadin"ya mu"azzzam kana ina? yau ga ranar daka ke mafarkin zuwanta,yau ga ranar da Ummi tayarda tayi nadaman Abunda ta aikata.."taketa fada tana kuka.

  Karfe shidda daidai aka Fito da zahirah bayan tasha tarin nasihohi,gun iyayyanta,itako Ummi hawayenta yaki tsaiduwa,tun lokacin da Ashe ta karbu su little ummi dayake suna hannun Ummi ta kwakwumesu tana kallonsu tana kuka,tunda aka Fito da zahirah Ummi tayi Wuf tafada tiolet tana gunjin kuka,kaichonta Yanzu ita da kanta ta jagoranci wani yaketa gonar danta,wayyo ta cucu kanta,tana ji tana gani aka saka zahirah awata bakar benza wacce mijinta ya aiko aka dauketa aciki,bayan Sauran motocin gudu uku,Su yakura ne kan gaba,Hajiyar shureim kuma taso ta doje Bukar yaroketa kan taraka zahirah to babu yarda zatayi,Ummi kuma an nemeta ba"a ganta ba,kowa yasan boyewa tayi,to ai babu dadi ne sai hakuri tunda aikin gama ya rigaya daya gama,zahirah tayi kuka kamar ranta zaifita har saida muryanta ya fara dishewa,bama zata iya fadan irin Tashin hankalin datake ciki bane,ammh lokacin data yada kanta bisa kafadan yakura tana kuka acikin mota babu wanda take tunawa sai mu"azzam ajirgi sanda take rumgume jikin Yakura tana kuka za"a kaita gidan mu"azzam ammh sai gashi Tarihi ya maimata kansa,ammh kash yau gidan wanin mu"azzam za'a kaita tafiyan tasha bambam da wanda sukayi na farko,Su little Ummi ko na hannun hajiya Suma sunsha kwalliyansu shar,suma zasu gidan sabon papane dole su chakare😜

_____________________

  *SUDAN*

  Tayi parking din motarta cikin haraban asibitin ta fito tana takunta d'ai d'ai,cikin shigar pakistan Riga da wando sai wani siririn gyale data saka bisa kanta,takalmin kafanta mai dudu ne sosai,tana gabda shiga mainpalour din asibitin sukaci karo da juna,da kallo tabisa yana dagowa suka hada ido,Daure Fuska yayi ya ratsa ta gefenta ya wuce yafara tafiya cikin takunsa na sanyi.
Chapter 50 · 0% Book details