← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 82

Sashe 71

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Suna Shiga wajen yadau sowa da ihu da tafi lokaci daya wata waka tana tashi ahankali na U ARE MY LIFE.."Sukuma suna taku cikin isa da Shauki hannunsu rike da juna,gefe daya kuma,suna damke da yan"diyansu duk wanda yagansu indan akace ya"yansu ne, sai sunyi mamaki matuka,Abun ya burge kowa fa,sun isa wajen dazasu zauna suka zauna suka sanya ya"yan nasu atsakiya kowanne ya rike hannu daya cikin burgewa,nan da nan waje yadau Sowa,kafin mc ya fito yafara gabatar da Abunda ya tara mutane,nan da nan aka zagaye kowani tebur da abinci bayan anci ansha aka sanya kida mata Suka shiga fili Sunata rawa cikin harda Ashe da mahgana,Su Shureim da Dr Abduljabar suma sun shiga fili sun chase sosai mu"azzam dai ko da akace su taso ki yaki,yakuma hana zahirah tasowa Asma"u ne tazo ta dauki su little ta shiga fili  tadan taka rawa mooh ya fito yana mata barin yan dubu na liki,su Shureim namai tsiya suna bazasu basu ba,Saboda shi balarabe ne,dariya kawai yake musu baya mgana saboda murna,sai wajen la"asar aka tashi bayan anyi hotuna da Sauransu,kafin kowa ya watse amaida amarya akafara Shirin Tafiya Abuja da ita don mu"azzam yace yau zasu wuce babu tsayawa,suna dawowa aka shiryamata kayanta da nata dana yaran sai akwatunanta aka fita dasu aka sanya amota,Wanka aka sakata ta sakeyi ta sanya wata atamfa da Farin hijabi kafin akaita wajen bahna dinta,albarka kadai yaketa sakamata domin yace in da zata ba bakonta bane kuma ita ba yarinya bace yanzu ta san Abunda ya kamaceta,Hardashi mu"azzam ya aika yazo ya hadasu yayi musu nasiha,daganan gidan Famfari suka nufa da ita wajen baffa da Yakura suma sukayi musu nasiha tareda fatan alheri,Wannan karon tafiyan babu yakura saboda ba mai kula da da Shettima shiyasa ta zauna Ashe ce da mahgana da wacce Ashe ke bima wa,Wacce suke cema yafindo,Sai mami mahaifiyar Asma"u,Wacce dama da direbanta Tazo shi ya dauketa,Shureim Shiya dauki amarya da yan"uwanta ayayinda Dr.Abduljabar ya dauki Mooh da Asma"u da mu"azzam wadanda Su little ke hannunsa,sun makalemai Ushe,kuma motar daya tuko ta dauko kayan abinci ne na gara,da kayan toye toye na al"ada,shikuma direban Shureim kayan sawan zahirah ya dauko da akwatunanta da kayan bukatuwanta danata dana yara,Sai mami ita kadai ita da direbanta karfe 5:30pm na yammah Suka bar garin suka dau hanyar maiduguri zuwa Abuja..

_________________

Basu isa Abuja ba,sai after 9 na dare kana motocin suka shiga maitama,abakin get din suka tsaya suka fara malamala hon da gudu sani mai gadi yazo ya budemusu motocin suka fara Sulalawa zuwa cikin gidan,Ummi da hajiya da mom sune ke falon sanda motocin suka shigo gidan,Lubna da zulaika ko ciki,suna hira.

Dama Tun tasowarsu Mu"azzam yakira Ummi ya fadamata gasu bisa,hanya shiyasa duk wani abu daza"ayi na tararsu an kammallahshi kama daga kan girke girke zuwa kan kayan lashe baki,suna jin Diran mota suka mike,Ummi dake sanye da wani Ubansu less,Doguwar riga less din daga kallon Farko zaka gane bakaramin dukiya aka mikaba kafin a daukosa ba,Kunnanta da hannuwanta Zinarene, ke kyal kyali yana haskawa,da hanzari suka fice Ummi ce kan gaba,ita ta bude motar da zahirah take ta fito da ita babu kunya Ummi ta rike hanci ta rangada kuda akunnan zahirah aifa sai waje yadau sowa,mahgana da Ashe ma suka soma guda,harda juyawa da rawa,Mu"azzam dayaji Ummi na guda sai dayayi mamaki,dama haka Ummi take,ita ta riko zahirah da kanta harzuwa cikin gida,itakuma hajiya da mom suma ma sauran jama"a sannu da zuwa,haka aka sassauke kaya su karime na jida suna kaiwa cikin gida,gabadaya suka dumguma zuwa falon hardasu mu"azzam din,Wanda yayansa ke makale dashi sunki yarda da kowa sai shi,jin guda daga falo shi ya fito da zulaika da lubna daga saman Ummi itama Lubnan tayi shigarta ta alfarma cikin Shaddart Navy blue,riga da zani tayi kyau sosai abunka da farar mace,da hanzari suka sauko suma masu sannu da zuwa,ita ta kariso ga Ummi tana riko zahirah tana fadin"oyoyo Antyna barka da zuwa..."Zahirah bata amsa ba domin tana cikin mayafi ne,daganan dakinta nada wanda ta barshi aka nufa da ita da kafar dama Ummi ta umarce zahirah ta shiga saiga Ummi har kan makeken gadon zahirah tayima mata masauki tana sakin guda da kanta,su ashe na tayata,lubna ce ta zauna agefenta tana rike da hannuwanta nan da nan Ummi ta fice tabada umarnin kawo kololin abinci kafin kice kwabo ancika gabansu da Nau"ikan Abunci kala kala da drinks suma su mu"azzam an kai musu shashensu Abun sai wanda yagani,Lubna bata nuna kishi ba ko kadan ita ta samo pilet ta zuboma Zahirah sinasir da miyar alayyahu,tazo har kan gado tayaye mayafin nata ta mikamata abincin,zahirah batayi musu ba,ta karba da mirmishi tana fadin"Ta gode.."

Batawani ci dayawaba ta ture Lubna ta dauke bayan ta tsiyayamata ruwa okofi,tasha ta koshi,yanmatan ne kadai a bedroom din Su ashe da mahgana da Sauran suna falo suma Sun baje suna diban arziki,Lubna ce aciki da Zulaika sai zahirah da kawarta Asma"u,maminta tana falo wajen su hajiya Suna hira,Sai da suka kusa raba dare kana kowa ya kwanta saboda gajiyan hanya,zulaika da Lubna dakinta suka koma suka kwana,Su little ko wajen Ummi suka kwana Abunsu suma murna suke kamar sunsan sun dawo gida ne.

Washegari da hadahadar walimar dasu Ummi suka hada aka tashi ko kafin karfe goma tuni an kayata haraban gidan da kujeru farare da tanti,Karfe shadaya na safe aka fara gudanar da walima,Ummi ta gayyaci wata malama takanas daga zaria wato MALAMA SAFIYYA MUHD BA"ARE.,Ita tazo ta dagargaji wa"azin zama da miji da kwatanta adalci awajen maigida,dama ko awajen zama zahirah da Lubna suna sawun gaba hannunsu sarke da juna,hakikanin gaskiya wa"azin ya tsuma musu jiki matuka mussaman ma zahirah wacce taji duk kishin lubnar ya ficemata aka,in tayi duba da yadda bata kishi da ita,duk inda take tana tare da ita,tana nuna mata kauna mai tsanani,haka kurum taji ta burgeta,kuma itama tayi alkawarin taimakama mijinta wajen sauke nauyun dake wuyansa ko ya rabauta ranar gobe kiyama,Sai wajen uku na yammah aka tashi daga walimar bayan anci ansha,kuma anyi rabe raben su karamin alqur"ani da casbaha,da azakar da dabino,dauke cikin wata karamar jaka da"aka rubuta sunanye su Zahirah da mu"azzam din bayan ansaka Cut cee,Childreen SUHAIMA AND MUHMMED MOODU,abun sai wanda yagani,antashi cikin Farinciki da Annushuwa,bayan an cikama malama kayan arziki direbanta ya dauketa suka koma zaria.

Dare nayi aka fara shirin zuwa Dinner,wanda dukkansu matan ne Wato Lubna da zahirah wanda kowacce ta dau ado,kaya iri daya suka sa wani blue din material ne mai Stones fari suka sanya matukar kyau sunyi daya baka daya fara,ba"ayi african Time ba,Karfe 8:00pm aka fara dinner saboda ana so atashi da wuri,Guri ya cika da al"ummah Tundaga kan likitoci da lauyoyi domin kunsan yau ranar tasu ce,wannan karon hatta da Ummi da hajiya ba"a barsu abaya ba,sun hallarci wajen dinner din yan janaf novellah 1,2,hafnan novellah,Uwar mijina fans1,23 Zumunta novellah Taskar littafan hausa Aisha Alto Novels,Taskar marubuta da Sauransu suma sun sha anko sun hallarcin wajen dinner nan,sahibata kuwa barayin abinci ta nufa kowani kala sai taci dakuma ta fakaici indon mutane da diba ta zuba cikin wata burgamar jakarta,😂😛hakama Sisinah Aisha Alto ita tebura ta dinga bi duk wanda ya rage nama,sai tayi sauri ta dauke tana waige waige data ga ba"aganinta sai ta bude wani buhu da tazo dashi ta zuba aciiki...😂😂😜, mu"azzam na tsakiyar matansa,wanda suka sha kyau Suka koshi,anci ansha anyi rawa,kuma anyi barin naira,koda za"a yanka cake,mu"azzam sai da yafara bama Zahirah kana ya juya yabama Lubna,ita kuma Lubna ta yanka tafara bawa zahirah kana ta juya tabama mu"azzam,haka itama Zahirah tayi Tako sha  harara wajen Mu"azzam din wanda daga karshe suka bawa ya"yansu dukansu su ukun,Asma"u ko tana tare da Saurayinta wanda yagama sacemata zuciya mooh,suna chan suna zencensu na soyayyay,karfe 11:00pm aka tashi daga wajen dinner,kowa yakoma gidansa ya kwanta saboda gajiya yan maidugurima da Wuri Suka kwanta saboda gobe sammako zasuyi na tafiya gida.

Gari na wayewa Su Ashe suka fara shirin komawa gida karfe takwas na safe Ushe ya daukesu zuwa maiduguru cike da kayan alheri daga mu"azzam da Ummi,hajiya da zulaika da shureim ma sha biyu nayi suma suka dau hanya bayan Hajiya tatarasu tana musu nasiha,Su Asma"u ne karshen Tafiya domin maminta tabi zuwa gida,domin sai an kwana biyu kozata koma mkranta,bayan sun karbi nombar juna ita da mooh,wanda ya jaddadamata kafin yakoma sudan zaizo suyi mgana,to haka dai aka rabu cikin kewa Dr.Abduljabar ma aranar yakoma gida,gida ya rage daga Ummi sai mom,sai Lubna da zahirah da mu"azzam da ya"yansu little Ummi da moodu wadanda suka samu sabon waje sai guje guje suke,antafi da cikinsu an dawo dasu da kafarsu Allah kenan..

*Kai yasin nagaji*

janafty

*UWAR MIJINA...!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_

       *Mallakar:JANAF*
       *Wattpad:Janafnancy12*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*GIFT TO:Hussain80k*

*Intelligent writer's Asso*✏

*NOT EDITED*💥

          *NO 45*

    """Sai da baki suka tafi kana Ummi tatarasu Zahirah da mu"azzam da lubna da mom da mooh tayi musu nasiha mai ratsa jiki nan take takira Abbie ta waya shima yayi ma mu"azzam nashi nasihan duk dai fadan na su zauna lafiya ne,kuma ya kwatanta adalci.

Ummi ta taso har inda take takama Hannun Zahirah tana fadin"Don Allah zahirah kiyiman alfarma taimakama mu"azzam wajen kwatantanta adalci a tsakaninki da lubna ki kuma yimin alfarmar zaki kalleta ne amtsayin yar"uwa ba kishiya ba don Allah kiyiman wannan alfarmar.."Rike hannunta zahirah tayi tana fadin"Nayi miki Ummi wlh bazan Rike Lubna dawani mgunta ba,mganar adalci kuma insha Allahu yaya mu"azzam zai kwatanta atsakaninmu domin in knga gida yana zaune lafiya to hadin kan Matansa,nikuma na tabbata yadda bani da mtsala haka itama kanwata bata dashi ko ba haka ba kanwata? tafada tana kallon Lubna.

  Mirmishi tayi kafin tace"Hakane Ummi insha Allahu bazaki samu wata baraka daga barayina ba nayi miki alqawarin rike ki,amtsayin uwata zahirah kuma amatsayin yayata kana yaya mu"azzam amtsayin yayana,kuma adalin miji gareni bazan taba Fushi don ya nuna gazawarsa akaina ba,zanyi kokarin naga nayi mai biyayyah har zuwa karshen numfashina.."Tafada tana sunkuyar dakai gyada kai Ummi ta hauyi tana share kwallah kan tace"Naji dadi kuma na gode muku,indai kukamin haka kun gamamin komai,Allah ya zaunar daku lafiya ya kauda duk wata fitina Atsakaninku."Dukkansu suka amsa da Amin.
Chapter 71 · 0% Book details