← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 82

Sashe 13

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Fuskarsa tana Fitar da wani Annuri na dabam,anko sukayi domin shima Shureim irin shigan dake jikinsa kenan, domin shiya yimusu Ankon., Ummi na ganin suna takowa gareta tayi maza,ta maida kanta cikin blanket saboda kukan daya taho mata..Tanaji aranta shettima yagama da ita duk abunda zatayi daga baya ne..Tana ji tana gani mu"azzam yadau kwalliya zashi daurin aure..kawai sai tafashe da kuka harda shessheka wanda har ya fito sunajin sautin kukan nata.

Da mamaki suka bita da kallo kan suyi mgana Hajiya ta musu nuni da kofa da  suFita kawai,mu"azzam baida zabi illa juyawa yana fadin"Ummi na ina bukatar addu"anki zamu dau hanya'Banza tayi dashi dole jiki asanyaye yabi Shureim wanda yaja hannunsa suka Fice.

Babu yarda ya iya..Yanaji yana gani ushe yakaisu Airport suna zuwa sanarwan Sunaye yafara gudana lokaci kadan aka kirasu suka shiga jirgin kafin a kammallah komai yahau sararin Samaniya ya fara lulawa MAIDUGURI.

*Comment*
*Share*
*vote*

*#Intelligent writer's#*
*#Uwar mijina...!#*
*#Janafnancy#*
_*INTELLIGENT WRITERS ASSO*🖊_

🌺 *UWAR MIJINAH..!*🌺
        _(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)_

       *ALKALAMIN:JANAF*💕
        *WATTPAD:JANAFNANCY*

*DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF*

*NOT EDITED*⚒

                  *NO 10*

     """Awa uku suka shafe a sama,kafin jirgin ya saukesu a babban Filin jirgin dake birnin na maiduguri,Mu"azzam da kansa yakira Bukar yafada masa isowarsu wanda dama tun suna gida yafada masa zasu biyo jirgi In sun kariso azo a daukesu.

  Bukar da kansa yazo filin jirgin ya daukesu zuwa chan gidan nashi, daya kachame da al"umma mata da maza wa"inda suka zo daurin aure,babban Falon Na gidan Bukar nan aka saukesu wanda sukansu yan"uwan Bukar din da sukayi tozali Da mu"azzam din sai da suka raina kansu domin sunga tsantsan  kyau,ilimi da kamala tareda tsantsan kwarjini da dattako.,Ba shakka zahirah ta dace da samun gwarzon Namiji haka suke fadi duk wanda ya fito daga falon bayan sun gaisa,Bukar daganshi ya shiga cikin gida inda mata ke gudanar da sha"aninsu yayi ma mahgana mgana kan akawo masu Mu"azzam abinci kafin su wuce daurin auren,Jin isowar ango yasa gidan yadau guda lokaci daya.

    Kafin kace kwabo an cika gaban su mu"azzam da abinci Nau"i na dabam dabam sai wanda suka zaba,Shureim ya kalli Mu"azzam yace"Ango fa kasha kamshi,to ya ne zaka taba ne kafin mu wuce"yafada yana dagamai gira.

  Tsaki Mu"azzam yayi kafin yace"Sai dai kai,domin naga kamar kafini bukata"Yafada yana Cigaba da dannan wayansa,Dariya su brr barau suka sheke dashi suna Fadin"Shima yana kukan aure so ba cin abinci"Kara darawa sukayi kafin Shureim yacire babban Rigansa yana fadin"To Ango ayi kuka lafiya,yan"uwa ku sauko muyi mu harraka kafin kuma na anjuma"Yafada yana zama lokaci daya da bubbude kulolin gabansa,Sinasir ce sai na biyu Tuwon shinkafa sai Farar shinkafa.

  Sinasir suka zuzzuba da miyar Alaiyyahu wacce taji nama da manshanu suna ci suna zolayansa suna dariya,Shiko yama gefe ko kallonsu bayayi yana ta latsa waya abinsa Shureim ya kallesa yana tura sinasir abaki"Wai nace ba"Yafada yana kallon Mu"azzam wanda ya dago yana kallonsu.

  Ganin haka yasa Shureim yace"Amaryan ba nan ne gidansu ba"eh sai akayi ya"mu"azzam yafada cikin dage kai,Dariya shureim yayi kafin yace"yo ko gilmawarta banji ba,balle kamshinta kasan ance yan maiduguri badai kamshi ba"Yafada yana tauna kashi Dariya Dr Abduljabar yace"Kwarai su daman, da kamshi aka sansu"Kauda kai Mu"azzam yayi kafin yace"Sai ku shiga ciki duk wacce kuka gani tana kamshi itace amaryar"Yafada yana wani hararansu dariyan shakiyanci suka shekemai dashi sunayi suna dibam garan abinci shiko yayi musu banza.

  Ahaka suka kammallah kafin duk su share hannayensu da bakinsu da Tissue,babu dadewa sai ga bukar yazo yace su fito su shiga ciki su gaisa da goggonin Zahirah kafin su rankaya ,zuwa gun daura auren lokaci ya kusa,Cikin jin dadi suka mike mu"azzam na baya baya,suka iza keyarsa gaba koda suka shiga nan suka ga dangi kowacce taci adonta ammh fa sun dane jikinsu cikin,lifaya wanda ya burgesu shureim sun gaisa da kowa da kowa don kowani daki sai da suka shiga,kanwar bukar itace autansu Aisha sunanta suna cemata, Ashe ta fito da gudu da wani kasko ahannunta wanda yake cike da Rushin wuta ga turare yana fitar da hayakin kamshi tafara zagaye Mu"azzam dashi tana sakin guda,nan da nan guri ya kaure da guda da wake wakensu na chan sai abun yakoma burgesu shureim tuni suka fitar da wayoyinsu suna daukan bidiyon yadda mata suka zagaye mu"azzam kowanne rike da kaskon Turare suna mai Feshi da hayaki,tare da guda,dakyar dai suka barsa ya isa gaban mahgana wacce keta faman saka mishi albarka bayan tasaka hannunta bisa kanshi"Allah ya albarkaci Aurenku moodu da zahirah,Allah yayi ma rayuwarku albarka,Allah ya baku zuru"a tagari,Allah ya zaunar daku lafiya,ya kauda dukkan Fitina akanku..Yaasaka ace gwara da akayi"Tagama fada hawaye suna zubomata gabadayan jama"an gun suna amsa mata da Amin.

  Shikanshi mu"azzam jikinsa yayi sanyi, shima din da Amin din yake amsawa su shureim na tayasa,To dakyar da mu"azzam yasamu ya fice daga gidan saboda yadda akamai cha mata suna ta kirarin Zahirah tagama dace da sun gwarzon mazaje.

    Suna Fitowa suka shisshiga motoci sai Famfari gidan Baffa Shettima inda za"a daura Auren,koda suka isa guri ya cika da al"ummah sai wanda yagani lokacin Da Mu"azzam ya fito daga mota wasu sun ma dauka Moodu ne saboda kamar da suke,sai daga baya suka fahimci shine angon,Baffa shettima yaci fararen kaya da Babban riga harda rawani bakinsa kuwa yaki rufuwa,wani masallaci dake kusa dasu anan aka shiga domin daura auren wani yaya ga bukar shiya, amshi auren zahirah a inda mai gayyah mai aiki baffa Shettima ya nema ma Dansa Mu'azzam,auren zahirah kan sadaki Naira dubu dari,shaidu sun hallara kuma an nema sun bada cikin lokaci Alkwarin Allah ya tabbata Tuni yan,sheda suka hau sanarwa.

   *ALKWARIN ALLAH YA CIKA AYAU MU"AZZAM MOODU YAZAMA MIJI GA ZAHIRATU LAKADAN BA AJALAN..."

Saboda Farinciki Baffa shettima Rumgume Mu"azzam yayi yana kuka kamar karamin yaro,kowa yadauka kukan murna ne ammh shi anashi barayin ba haka bane tunawa yayi da dan"uwansa Moodu uwa uba,Fadi wanda duk sun kwanta dama,rashinsu babban illa ne agareshi maraici ya lullubesa,haka yakoma ya Rumgume Bukar yana kuka yana mai godiya,shikuma yana mirmishi kawai domin yanajin sa wani iri duk da yacika ma Shettima Umarninsa,.

    Jama"a kuwa dadama zunde sukayi tayi suna cewa"Dole shettima ya makale yahada Aure,yaga yaro yazama mutum ga kudi,ga dukiya ga uwa uba kyau,bayan ya manta dimbin Muzgunawa da takuran Da Suhaima ta fuskanta sanda tazauna tare dasu,dayawan su sunso suji ya Suhaima zatayi in taji wannan al"amarin(Kusan mutane baka gadonsu ammh sana da gadon bakinka).

Achan cikin gida kuwa,Lokacin da masu sheda suka sanar da an daura Aure,kannen yakura dake daki tare da Zahirrah wacce ke zaune kamar mutum mutum,tafara fahimtar meke faruwa da ita ammh abunda ya daure mata kai,in Aure za"ayi mata waza"a daura mata, ita da ko tadi da saurayi bata taba yi ba,bata gama mamaki taji sun rufeta da guda lokaci daya suna mata ambaliyan Turare mikar da ita sukayi suka Fito da ita Falo suna Fadin "Takawarki lafiya Yarinya mai babban mtsayi"Suke fada suna mata tafi da ihu gefe daya suna busa mata hayakin Turare.

Tuni zahirah taji tafara Rudewa kafafunta suna hardewa idanunta sun ciko da hawaye fahimtar haka da Yakura tayi ne ya sa ta isa garesu tana fadin"Don Allah ku dakata da wannan gudan kunsan fa yata batason hayaniya" Tafada tana rikoTa ai zahirah naji yakura ta rikota kawai sai ta fada jikinta lokaci daya ta fashe da kuka tana fadi cikin Rawan murya"Da gaske..Ne...Ni..Ni aka ma Au...Re"Tafada hawaye suna karanyomata..kallonta yakura tayi lokaci daya itama taji ruwan hawaye kawai sai taja hannunta suka fada kuryan dakin harda Rufo kofa.

   Zaunar da ita yakura tayi kafin tafara share mata hawaye tana fadin"Kibar kuka yata..Kinji!Farinnciki zakiyi da godiya Allah daya daga darajanki Ayau din kika zama matar aure mai Daraja"Tafada tana kallon kwanyan idonta,Naurau Naurau tayi da ido kafin tace""Taya za"a min Aure ban sani ba? kuma ma waye na aura? tafada kanta tsaye ammh cikin sigar yarinyata

  Mirmishi yakura tayi tana zama kusa da ita tace"Karki damu yanzu badadewa ba zaki ga angon ki,kuma na tabbatar in kika gansa sai kin godemana saboda zaben da mukayi miki"Tafada tana,dariya Abun mamaki itama zahirah dariyar tayi tana Rumgumota take fadin"Ammh anan gidan zan zauna ko"Tafada bayan tadago tana kallonta,shafa kanta yakura tahau yi aranta tana ayyana yarinta har yanzu na damun Zahirah

Bata bata amsa ba sukaji gida ya rude da guda ana ma ango kirari gaban zahirah ya yanke yafadi takara makalkale yakura lokaci daya jikinta na rawa..Dan kallonta yakura tayi cikin tsausayawa kafin tace"Kinji ko ga angon chan ya kariso maza tashi ki kiga wanka bari na turo yagana takara shiryaminke nasan kila shettima ya bukaci ganinki"Tana fadar haka tazame jikinta,tafice tana share kwallan data biyo mata.

      waje ta fito inda Su mu"azzam suke dangi sun yamaimai mayesa suna sakin guda dasa albarka duk inda ya gifta jinjina ne domin dai duk inda Mutum yake to mu"azzam yakai Cikin dakin yakura suka shiga suna gaisawa da baki,anata saka albarka da fatan zama lafiya yakura tayi tasaka albarka tana hawaye Lokaci daya tana kallon Mu"azzam batare da kowa yaji mai tace ba tadan sunkuyo tace"Suhaima ko ta amince"Kallonta mu"azzam yayi kafin yayi kayatattacen mirmishi yace"Ta amince domin da yarda ta nazo nan"Kallon ban yarda dakai ba yakura ta mai kamar zatayi mgana sai kuma tafasa.

   Har suka gama gaisawa da jama"a basu ga ko keyar amarya ba sukuma basu tambaya ba,itakuwa tana cikin daki yagana tagama shiryata cikin wata shadda green doguwar riga wacce taji aiki bayan ta yaneta da lifaya fuskarta tana ta kyalkyali da haske ga kunshinta wanda ya haskata sai zallar yarintarta ta fito fili..Koda Yagana ta jawota zuwa falo har su mu"azzam sun Fice daga gida,fitowarsa yasa suka kara sakin wani guda na ganin yadda amarya tayi kyau kamar ba ita ba.

Suko su Mu"azzam suna Fitowa shureim ya kallesa yace"Kai nifa wlh nagaji wai dangin naku basu karewa ne"Yafada yana daure Fuska,shiko Dr Abduljabar cewa yayi"Wlh ni kafafuna sunfara zafi fa..Kuma gashi bikin naga kamar ba yan mata sai matan aure"mu"azzam dake jinsu yayi musu banza don shima yagaji gaskiya yana bukatar hutu,shiyasa ya nemo bukar ta waya,Kan zasu je su dawo.
Chapter 13 · 0% Book details