← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 82

Sashe 37

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da tayi dan gaba kadan kana ta waiga tayima gidan Kallon karshe don bata fatan ta sake dawowa cikinsa tayi tafiya mai nisa don harta fita daga anguwan kafin tasamu mai,Keken napep,da da farko da ta tsaidashi kin tsayawa yayi don shi azatonshima mahaukaciya sai da yadan lura dakyau,kafin ya dawo baya,rikonsa tahauyi kan ya taimakamata yakaita tasha inda zata hau motan maiduguri,kallonta yayi ada baiyi niyyar taimakonta ba,ammh ganin halin data ke ciiki ne yasa yace ta shiga suje,da hanzari ko tafada tana danne maranta cikin fitan hayyaci take kiran Sunan Allah.

Gabadaya Tunaninta ya chuse tanajin wani yanayi atare da ita,yanzu maiduguri ta nufa awannan daren,kodai taje gidansu Asma"u ne? to in tama je,gun wa zata,ta daura ma Asma"u Nauyi,to ita bama zata iya gane gidan ba,kai ko ma zan gane gwara na koma mahaifata domin Sune kadai gatana ayanzu,tana wannan Tunanin suka shigo tashan,ganin halin datake ciki ne,mai napep din da kansa ya fita ya sama mata mota inda Allah ya taimaketa mutum biyu suka rage Sharon din ta cika,zuwa yayi yace ta fito ga mota jikinta na rawa ta fito ta warwaro dubu daya akudin ta bashi,cikin tsausayinta ya girgixa kai yana bin tulelen cikinta da kallo yace"a"a ki barshi ni don Allah na taimaka miki.."yana fadin haka yayi gaba yana fadin ta biyoshi,cikin sagewar gwiwa tabishi tana daga kafa dakyar har motan ya kaita dakyar ta iya shiga saboda yadda ko"ina na jikinta ya saki,kallonsa tayi bakinta duk ya bushe tace"Nagode.."gyadama ta kai yayi yana fadin"Allah ya rabaku lafiya yakuma tsare hanya...'"Yafada yana wucewa.

Hawayenta ta share da haban dankwalinta,Mutum daya aka kara kafin Sutashi,sai da aka hada kudaden mota kana Direba ya shiga suka dau hanya..Suna tashi matar dake kusa da ita ta duba agogon wayarta 9:00pm na dare.

Runtse ido tayi tana kara takure jikinta ga maranta yadda yake kartamata cikin gwiwanta ta saka kanta tana ZUBAR KWALLAH,lokaci daya tana addu"a Aranta Allah yasa tana da rabon ganawa da iyayaanta,dakuma fatan ta rabu da cikin jikinta lafiya....

*Comment,share and vote*

#Intelligent writer"s#
#Janafi#
#Uwar mijina..!# 
*UWAR MIJINA...!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_

       *Mallakar:JANAF*
       *Wattpad:Janafnancy12*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*Intelligent writer's Asso*✏

_Hakika jiya naga Tarin masoya wanda ni MAMI JANAF Bantaba tsammanin haka UWAR MIJINA YA SAMU KARBUWA BA..bansan dawani kalma zanyi Amfani da ita ba wajen godiyata ga Allah(SWA) ba Ammh duk da haka ina mika godiyata garesa taredaku gabadaya, Allah ya saka da alkhairi yabar kuma so da kauna na har abada_

_*Attention:zan danyi tsokacine, gameda masu cewa wai sakin da mu"azzam yayi ma Zahirah wai bata saku ba,who told u ehe?to malamanmu sun fadama mana ko acikin maye ,mutum ya saki matarsa ta saku,balle wanda yayi cikin hankalinsa,mahaukaci ne kadai akace inda ya saki matarsa to bata saku ba,kuma masu cewa saki ukun dayayi mata amtsayin guda daya ne? waya fada muku,malamai sunce indai akayi saki uku lokaci daya to abarshi a Saki daya ne,ammh duk sakin da"akayishi A rarrabe ma"ana mutum yace ya saki matarsa saki daya,na sakeki saki biyu,na sakeki saki uku,to Aurensu ya haramta har sai in Wani ya doramata idda,to da hakan nakeso na fadamuku Auren Hirah Da mu"azzam ya haramta harsai wani ya doramata idda,Allah shiyafi kowa sanin Daidai*_

          *NO 24*

        ""Gaskiya direban wanda yasan hanya ne,sosai don Karfe Hudu na Asuba suka shiga babbar tashar na maiduguri,lokacin wasu duk sunyi barci saboda gajiyan mota ammh banda zahirah wacce ciwo yake mukurkusa,taci kuka kamar ba gobe,ga maranta dayake kartamata lokaci bayan lokaci,idanunta biyu ko alamar barci babu har suka iso cikin tashan ta maiduguri.

   Ana zuwa kowa ya sauka,lokacin data saukane taji Tsausayin kanta ya dirarmata to yanzu ita ina Ta nufa,gidan Baffa ko gidan Bahna,agaskiyan batu bazata iya zuwa gida awannan Halin data ke ciiiki ba,saboda batason hakalin iyayanta ya tashi,ta inda aka hau dole ta nan za"a Sauka,batare da wani Tunani ba,ta tari mai Napep tace ya kaita Famfamari,dayake cikin tasha ne sai hada hada akeyi kamar rana kai bakace lokacin karfe hudu bane na Asuba.

   Suna tafiya ciwo ya dawo mata zanga zanga abun ba wasa tun tana dauka na yadda yake zuwa yabari ne,sai kuma taga abun ya girmema Tunaninta tun tana salati aboye har ya fito sarari,ganin yadda take juye juye yasa mai keken yakara gudu babu bata lokaci suka iso kofar gidan baffa shettima wanda dama yana bakin Titine.

  Zahirah dakyar ta sauko daga cikin keke saboda azaba ko takan mai keken bata bi ba, yana fadin Hajiya kudin fa,ina hankalinta baya jikinta cikin Fitan hayyaci ta karisa ga kofar gidan datake kulle ta shiga bugawa da karfin gaske hawaye na wankemata ido,ganin halin datake ciki ne yasa mai keken kada kai yayi gaba.

Shettima dake zaune afalo yana lazimi kamar amafarki yaji anata dukan kofa bana hankali ba,da hanzari ya mike ya dauki tocilarsa mai haske ya fice yana cema yakura,ana buga gida bari yaje ya gani,lokacin kuma yakura tashinta kenan,Ficewa yayi ya isa ga kofar yana fadin"Waye..? yafada cikin dan Tsoro kadan,zahirah data gama jigata ta furta cikin wata murya mai kama da na mutum na cikin mawuyacin hali'"Nine baffa,.."Tafada lokaci daya dataji wani abu yana binta akafa.

Gabansa ne yayanke yafadi cikin Rawan murya yace"Kece wa.."? tafara Fitama daga hayyacinta tace"Za..Hi..rah ce ...."Tafada tana jingina da kofan dajin zata fadi,Cikin wani irin Rudewa baffa yace"Zahirah wata zahirah kuma,innalillahi wa"ina Alaihirraju"un..'yafada yana zare sakatar gidan Rigigaf kawai yaji mutum yafadomai Cikin tashin hankali baffa ya riketa yana fadin"Ke dawaye kukazo da tsohon darenan,ina mu"azzam din.."? yafada cikin Tashin hankali.

  Zahirah tabata cikin hayyacinta fadi kawai take"ya Sakeni baffa,Baffa Ummi tasa ya mu"azzam ya sakeni,ku taimakeni zan mutu..."Lokaci daya tanajan wani dogon salati kan taja Numfashi ta sulale ajikinsa,Baffa cikin wani irin tashin hankali yahau kwalama yakura kira..."Yakura.!Yakura..!Yafada da karfi.

  Yakura dake daki ta fito asukwane tana fadin"Gani mallam lafiya kuwa wannan kiran.."? tafada tana karisowa ganinsa rike da mutum yana jiggawa yana kiran sunan zahirah yasa yakura karisawa da sauri tana haskata take fadin"Mallam yahna ce,ina kasamota ne,munbani mun lalace.."Tafada tana tallafota sai taji ta tallafi ciki ,cikin tashin hankali ta kalli kasanta kafin tace"Mallam ciki ne ma da ita,Nakuda ma takeyi,kuma har faya ta fashe,kamamin ita muje cikin gida.."

  cikin Tashin hankali Baffa yace"A"a kudai zamuje asibiti ne.."girgiza kai yakura tayi tana fadin'Ba lokaci mallam haihuwar tazo gadan gadan ne.."Tafada tana rikota shima yakama mata suka tallafeta domin jikinta gabadaya ya saki Numfashima dakyar takeyi saboda azaba cikin daki yakura ta shiga da ita tana salati,tsakar dakin ta kwantar da ita tana kwayemata doguwar rigar dake jikinta sama take fadi"Zahirah kiyi Nishi da karfi kan da ya fito,taimakeni don Allah..'Tafada tana waremata kafa cikin azaba Zahirah ke sakin Nishi da karfi Yakura na fadin ta kara kamkameta tayi tanaa salati da karfi hawaye na zubomata,baffa kuwa yana falo yana safa da marwa duk addu"ar datazo bakinsa yake karantawa cikin tashin hankali.

Cikin dan lokaci Zahirah tasaki wani nishi mai karfi sai ga da yafito yakura ta jawosa yana canyara kuka tana kokarin nadesa da zani taga alamar sabuwar nakudace takara tasoma zahirah cikin murna ta jiye yaron bisa gado tazo ta riketa tana cemata tayi nishi,cikin galabaita take Nishin karfinta duk yagama karewa cikin ikon Allah sai ga yarinya ta fado Yakura ta chabeta tana fadin"Alhamdulillah."

Baffa dake falo shima Alhamdulillah ya furta yana karama Allah godiya don ga kukan jarirai nan ya karade gidan saboda tsausayin zahirah baisan sadda hawaye suka zubomai ba,Allah sarki Allah yaga niyyarsa,hakan yatabbatar da cewa bawa bai isa ya gujema kaddararsa ba,wannan kaddaran zahirah ce, Allah bata ikon cinyewa.

Kafin gari ya waye yakura ta gyare mai jego tsaf ita da jariranta sun kame bisa gado suna barcin gajiya,tunda zahirah tashiga ruwan zafi,yakura ta gasa mata jiki tana dawowa daki barci ya dauketa saboda wahala,suko jariran Duka ruwan zamzam yakura ta basu kan ta daukesu takaima Shettima,wanda ya rikesu duka biyun yana kallonsu yakura yace"Me aka samu.? tana mirmishi tace"Mace da Namiji ne,ga Namijin nan kamar kayi kaki,itako macen,tamkar suhaima ce.."kallonsu Shettima yake yana mai Farinciki aransa koba komai yana mai Farinciki da wannan albarka da aka samu,wato rabon ya'yane yasa ka shi matsawa sai anyi auren kenan,hawayen dayake makalewa ne suka zubomai cikin mamaki yakura ke kallonsa tana fadin"Mallam yau ba ranar kuka bane ranar Farinciki ne,ina shi mu"azzam din ko ba tare suka zo ba?

Dukar dakai baffa yayi yana fadin"da tare suka zo da baki ganshi ba yakura,itakadai tazo nan kuma tafadamin cewa Suhaima ta saka danta ya saketa a daren jiya kuma takorota.."yafada cikin karaya dafe kirji yakura tayi tana fadin"Na shiga uku na lalace,da tsohon cikin tasa aka saketa,ashe Suhaima bata da imani koda ta saka yasaketa bazata iya mata lamunun kwana gobe da safe ta kamo hanya ba,ammh saboda rashin imani da tsausayi ki saka asaki yarinya da tsohon dare ga tsohon ciki,wlh abunda na guda kenan,nasani dole watarana haka zata Faru.."Takareshe fadan haka tana fashewa da kuka,bai hanata ba don shima hawayen yake saboda bai da hurumun hana kansa kuka,domin duk shine silan komai.

yakura taci kuka kamar mene bama kamar in takalli ya"yan sai taji tsausayinsu ya tsirgamata,zahirah bata dade da barci ba ta farka tunda tatashi take kuka,kamar ta zare ko yayan data haifa bata ko kallesu ba,yakura bata hanata ba ta barta ta koka domin dole ne,yaran sunata kuka yakura tayi tayi da itama ta karbesu taki kallonta tayi tace"Kibar kuka yahna Haka Allah yaso,in kikai hakuri sai kiga kinci ribar Abun,inkuma da rabon sake zama tsakaninku sai kiga kun sake komawa karkashin inuwa guda.."dagowa zahirah tana kallonta tace"Bazamu mu taba komawa guda ba yakura,saki uku Ummi tasa yayi min kuma duk a rarrabe..."Salatin da yakura ta yankane sai da baffa ya shigo dakin cikin rudewa yana tambayan lafiya,cikin kuka yakura kefadamai Abunda zahirah tace mata takara da cewa"Ammh ko Suhaima tacika babbar jahila mara takwwakali,kuma insha Allahu da sannu zata ga sakayyah..."Shettima bai iya mgana ba illa kadai kai dayayi ya fice yana jin zuciyarsa na kuna.

Dakyar Yakura talallabata tasha kunun kanwar data dama mata,sai dumamanman Tuwon data zubomata duka ta sharesu don ba laifi taji yunwa,yaran kuma zamzam aka cigaba da basu dayake basu da rigima kafin Ruwan Nonon yazo.

********
Chapter 37 · 0% Book details