← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 82

Sashe 58

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Dafe kirji mu"azzam yayi yana rike bango saboda yadda kalaman Abbie suka kusa sakawa ya zube kasa bai shiryaba,cikin,bin bango ya kariso falon yana fadin"my Hirah ce..Ta..yi..Au..re.."? yafada yana karisowa falon hannunsa dafe da kirjinsa lokaci daya hawaye na kwaranyomai.

  Atare mom da Abbie suka kallesa domin basusan da karisowar gun ba cikin Tashin hankali Abbie yace"Shikenan Final..'"yafada yana karisawa kusa da mu"azzam yana fadin"cool down Son,waya cemaka tayi aure,? yafada yana rikosa fizge kansa mu"azzam yayi yana fadin"kai kafadama Abbie,kai naji kana fada,plz and plz tell me d truth,da gaske Zahirahta tayi aure,kuma tatafi mun ya"ya gidan mijin."?yafada cikin tswa idanunsa Sunyi jawur jijiyoyin kansa sun tashi har lokacin yana rike da kirjinsa.

  Abbie ya bude baki zaiyi mgana mu"azzam ya dagamai hannu yana fadin"plz Abbie..Juz want to know.."yafada yana tsiyayar hawaye,runtse ido Abbi yayi yana fadin"eh da gaske ne Son but.."No.."Mu"azzam yafada yana buga kansa da garu yake fadin"No..No...No..My hirah iz my alone.."yake fada yana buga kansa da garu wanda har kansa ya fashe yafara zubar da jini

Hankalin Abbie atashe ya nufesa yana fadin"Son..plz stop it.."yake fada yana nufar mu"azzam din,mom kuwa kuka ta saka,Matswa mu"azzam yayi yana kallon Abbie yana fadin"No Abbie Stay where u are.."yake fada yanaja da baya yana kuka kamar wani tababbe.

Daidai lokacin Lubna da tashigo falon ganin halin da mu"azzam yake ciki ne,yasa tayarda jakar hannunta ta isa garesa da gudu tana fadin"ya mu"azzam..."tafada da karfi dagowa yayi yana kallonta kafin ya saka hannu ya tare hancinsa dayake zubar da jini baiyi mgana ba kawai ya juya yana tangadi yake fadin"don"t come closer juz leave me,leave i want to die.."yake fada jini na zubomai ta baki.

    Da gudu Lubna ta karisa kusa dashi tafada jikinsa ta rumgumsa ta baya tana fadin"bazaka mutu ba,bazaka mutu ba,domin kana da muhimmanci wajen wasu rayukan dadama,don Allah ya mu"azzam kabari na duba ka plz.."tafada tana kamkamesa cikin kuka.

cak ya tsaya yana bin hannunta data zagayo dashi cikinsa da kallo kafin ya bambare hannun ya juyo da ita yana kallonta Itama shi take kallo tana tsiyayyar hawaye bakinsa na zubar jini lokaci daya da hancinsa,yace cikin wata murya "Do u luv me? do u want to stay wit me lubna,zaki rayu da wanda zuciyarsa zata dauwama ason Zahirah,zaki zauna da wanda zai dauwama akunci na har abada,zaki zauna da wanda baya kallon ko wace mace da sunan so sai hirah,shin zaki iyazama dashi kuma kicigaba da sonshi.."yafada ciikin ihu yana jijjigata yace"Yes naji nakuma yarda rayuwata yanzu bata dawani Sauran amfani ta mutu Tunda zahirah tabarni juz tell me zaki soni ahaka kuma ki zauna dani,answer me.."?! yafada cikin tsawa.

   "Yes i do..."!lubna ta fada bayan Ta sulale akasa ta zauna tana fadin"yes i do.."i love u ya mu"azzam frm buttom of my hrt tun ranar dana fara ganinka i swear i die for u,zan rayu dakai na bautakama koda bazaka taba daga ido ka kalleni ba yes i accepted nima tawa kaddaran kenan.."tafada kuka nacin karfinta,shima mu"azzam Sulalewa yayi yana kallon Abbie da mom harda mooh daya shigo ba dadewa da suka zura musu ido kamar suna watching Film.

  Yace"plz Abbie..Ka..Au..ra..Min..Lubna...gobe.."yafada yana dafe kirji,yana tari kuma Abbie kuwa hawayen dayake boyewane, suka kwaranyomai yamakasa mgana Mu"azzam yasake cewa"kar...Ka..ce...a..a.."yafada tari nakara sarkeshi lokaci daya da zubowar wani gudan jini daga bakinsa,da Sauri lubna ta rikosa tana fadin"Abbie ..." da karfi.

  Jikin Abbie da mooh na rawa suka karisa Suka rikesa Abbie na fadin"Don"t go Son,wakeup nabaka auren Lubna gobe sai adaura muku aure.."yafada yana jijjigasa,lumshe ido mu"azzam yayi yana sakin mirmishi kafin ya damke hannun Abbie yana fadin"Tanque Abbie..."yafada kafin jinin yafara zubowa ta hancinsa lokaci daya jikinsa na saki,kafin kuma idanunsa suka fara rufewa

Da wani irin Ihu da firgici lubna take Furta.."No...."lokaci daya tana tare jinin da duka hannuwanta.

_*Wowowo Janaf fans ya kukaga page din yau? very interresting ko? Tarihi ne zai maimata kansa,domin haka Moodu yayi daga zuwa sudan yadawo da Ummi Suhaima,tabbas hakan yana cikin kaddaransa ne,ga mu"azzam ma zai dawo da lubna,shima yana cikin kaddaransa,ga zahirah Alhaji kabiru yafara moran sadakinsa,bata da yarda zatayi shima yana cikin kaddaranta,bakomai kake so Arayuwa kake samu ba,ba kuma koda yaushe ake Farinciki,yau ayi Farinciki gobe akasani haka,so tari muna mallakan abu ne batare da munsan abun zaimana wani amfani ba,sai don kawai bamu da yarda zamuyi ne,sau tari zamu hadu dawasu mutune,mu so su koda son bazai mana amfani ba,to lubna tana son mu"azzam koda soyayyar bazata amfaneta ba,Shima zai aureta koda Auren bazai amfaneshi ba,Allah kadai ke iya tsarama bawa Rayuwarsa yadda yake so kodon yabamu wata aya dazai zama izini garemu,am srry duk wanda page dinnan bai masa ba,ya yafemin haka Salon lbrin yake,Ngd sosai Allah ya sadamu da kaddaran da zamu iya dauka Amin*_🙏

*Sharhi nakeso yau sosai bani son wannan godiyar yau,kufito ku tattauna saboda Karfin gwiwata plz*

*comment, share and vote*

    *Janafty*   
*UWAR MIJINA...!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_

*Mallakar:JANAF*
*Wattpad:Janafnancy12*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*GIFT TO:Hussain80k*

*Intelligent writer's Asso*✏

_*I Dedicated dis page to u guyzs ZUMUNTA NOVELLA.,.Special thanks,to u Maman sayeed and Noor,Aisha Aliyu,Yar Fulani,Nusiba gidado(wish u quick recovery dear),Ummu sudess,and u Ummu husna,and all members of d group,..Thank you once again,Janafty relli appreciated*_😘✌

*NOT EDITED*💥

*NO 36*

Cikin azama Mooh ya mike yana fadin"Abbie kamosa muje asibiti kamar fa ya suma ne? yafada yana rikosa da hanzari lubna ta mtsa baya Abbie ya tallabo Mu"azzam mooh ma yatallafo gefensa suka fice dashi zuwa haraban gidan,lokacin tuni ya suma jikinsa ya saki,bayansu lubna tabi tana rafzan kuka,mota mooh suka sanyasa,kafin Abbie yazauna baya tare dashi shikuma mooh ya shiga bangaren direba yaja suka fice da hanzari.

Lubna ta nufi motarta tana fadin"mubi bayansu mom.."tafada cikin kuka,komawa mom tayi ta yafo gyale kan doguwar rigar dake jikinta tafada motan Lubna suka mara su Mooh baya.

Asibitin da lubna take aiki Suka kaisa suna isa cikin,gaggawa likoci suka amshesa sukayi cikin emergency dashi suna kokarin ceto Numfashinsa,ciki harda Dr Sultan ,lubna ko tana waje takasa shiga, kuka kawai takeyi kamar ranta zai fita mom ce ke rumgume da ita tana faman lallashinta mooh ko da Abbie suna tsaye suna safa da marwa,fuskokinsu babu Annuri ko kadan hankalinsu amatukar tashe.

Likitocin sunyi matukar wahala akan Mu"azzam domin condtion din dayake ciki yayi over gaskiya wannan karan ma,ya rasa jini da yawa,koda akazo cikin gaggawa ana bukatar jinin Lubna ta mike zata bada Dr Sultan ya dakatar da ita domin yace ko tamanta ne,bafa tayi wata da bada jininta ba,bazai yuyu yanzu asake diba ba,sai alokacin su Abbie kejin Lubna tabawa mu"azzam jininta tun farko,tundaga lokacin Abbie ya yarda ya Amince yarsa tafada kaddaran son mu"azzam wanda shikuma yake kwance yana fama da jinyar soyayyar watanta.

Siyan jinin akayi leda biyu aka sanyamai bayan anyi nasaran Tsaida jinin dakuma daidatuwar Numfashinsa,ammh ta taimakon Na"urorin dasuke jawo Numfashinsa,likitocin sunyi ta masu Abbie fada suna fadin"Tayaya za"a dinga barin masu wannan problem suna zama cikin damuwa yakamata duk abunda suke bukata ayi musu shi cikin gaggawa,ba"a son su dinga zama su kadai balle su yawaita tunani mara kyau,yanzu gashinan yakai mataki na biyu domin gefen zuciyarsa hartafara kumbura sakamakon mtsamata dayake da tunani hade da damuwa,sunce agaggauta yimai duk abunda yake so kafin ya farka matukar suna son da"nsu araye domin akara Faruwan haka daidai ne yake,da Rasa rayuwarsa domin zuciyarsa tana gabda kaiwa stage din karshe.

Iya tashin hankali Abbie ya shiga dafe kansa kadai yayi yana kiran Sunan Allah mooh dake gefensa ya dafa kafadansa yana fadin"plz Abbie ka cikama Mu"azzam alqawari ka daura masa Aure da lubna,saboda gudun kada mu rashashi,haka Allah ya nufa lubna ce matarsa bawa bai isa ya gujema kaddaransa ba.."yafada idanunsa sun kada.

Juyowa Abbie yayi yana fadin"Taya zan daura Auren mu"azzam da lubna alhalin zuciyarsa,bata tare da ita,tana tare da tsohuwar matarsane,anya baka ganin hakan cutuwane garesu duka biyun damu kanmu gabadaya.."Abbie yafada yana kallon mooh,girgixa kai mooh yayi yana fadin"Kaddaran Allah kenan,ada muna da masaniyar zuwansa garin nan ,har lubna ta hadu dashi ta taimakamai? harta kawo shi gidanmu kaganshi a mtsayin wanda ka dade kana nema shekara da shekaru? bamu da masaniyar komai Abbie,to kadauka duka komai Allah ya tsarashi ne,kuma baka tunanin ita lubna na tsananin sonshi? wlh nadade da gane lubna na son mu"azzam Abbie,kuma rasashi tamkar itama takamu da irin ciwonsa ne,kenan kana so ayi biyu babu ne,? yafada hawaye na kwaranyomai.

Tsuru da ido Abbie yayimai kafin yace"u are great son..,tabbas mganarka haka take komai da Allah ya tsara daki daki yake zuwa,na yarda na Amince zan daura musu aure ammh sai in da yardan ita lubna taji tagani zata iya auransa,to ni bani da mtsala dole ne bazan musu ba dukkansu.."yafada yana kallon mom da lubna wa"inda suke gefe suna jin duk abunda suke fadi...

Takowa yayi har gabanta kafin ya kira sunanta "Lubna."yafada yana dukawa bisa gwiwowinsa dagowa tayi tana fadn"Na"am Abbie.."tafada lokaci daya hawaye na kwaranyomata,kallonta yayi cikin ido kafin yace"Ki fadamin gaskiya bawai don zakiyi taimako ba,da gaske kina son mu"azzam? kuma kin yarda zaki zauna dashi ahaka? yafada yana kafeta da ido..

Dagowa tayi tana kallon Abbie kafin ta sunkuyar dakai hawaye suna zubomata tace"ya zanyi Abbie? juz tell me ya zanyi? wlh nayi kokarin yakice son mu"azzam tun lokacin danaji lbrinsa ammh ina Allah baya shawara da mutum lokacin dazai Umarci mala"ika daya diga soyayyar dayanmu a zukatanmu ba,bani da zabi Abbie,i Swear zan iya rayuwa da mu"azzam ahakan Abbie,shikuma yacigaba da rayuwa da son wata,i accept na yarda it my destiny.."tafada tana dora fuskarta bisa kan hannun Abbie tana kuka mai cin rai.

Mom dake gefenta ta rumgumeta tana fadin"a"a karkiyi haka dota,baki tunanin ki rayu cikin kuncin rayuwa,tunda baya sonki."Tafada tana rumgumeta,kamkameta lubna tayi tana fadin"Wlh zan iya mom,indai zan dinga kallonsa amtsayin mijina koda bazai taba kallona amtsayin matar aurensa ba,naji nagani kuma zanyi mai biyayyah tamkar baiwa agaresa"Tafada tana tsiyayan hawaye.
Chapter 58 · 0% Book details