← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 82

Sashe 79

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu samu Fita ba sai washegari inda suka fara zuwa gidan Marayun da Ummi ta rayu nan Ummi take bukatar Tafara kai ziyara,illai kuwa duka wa"inda tasani abaya duk basu yanzu wasu sun rasu,wasu kuma ba"a san isalinsu ba,da farko datake bayani ma ba wanda yaganeta sai da aka dauko Tsohon report kana aka binciko sunanta da shekaran data bar gidan sai ko ga fayel dinta,Harda na yarjejeniyar Aurenta da moodu,Ummi tayi kuka kamar yanzu komai na rayuwarta agidan yake dawomata harta dakin dasukayi rayuwa abaya sai da Aka kai Ummi ta shiga tana kallo tana hawaye,tana kallon Fuskokin kawayenta ko tace yan"uwanta wanda sukayi rayuwa tare,ammh yanzu babu su,sai da wasu bakin Fuskokin,ma"ikatan gidan sukatara yaran gidan da kowa da kowa suka gabatar da Ummi amtsayin daya daga cikin wacce aka rike anan gidan har suka aurar da ita gashi yau bayan Tsawon wasu shekaru tazo gaishesu tare da alahalinta,sunji dadi haka ta dinga gaisawa dasu daya bayan daya,bayan tayi musu nasihan su zauna lafiya da juna,Tunda basu da wanda sukafi su,domin sune yan"uwansu,da zasu tafi Ummi tabasu Cheek na milayan3 kyauta asiyama Marayu Abun bukata haka sukayi ta godiya har bakin mota suka rakosu suna daga musu hannu tana daga musu tana hawaye,bama itakadai kowa dake wajen sai da ya tsausayama Ummi da duk mahalukin dake rayuwa agida, A ranar ko mu"azzam bai iya lallasa Ummi ba,domin kuka tayi tayi,domin hakikanin gaskiya mikin bayane aka tado mata.

  Sati daya cur suka kwashe asudan kafin su dawo kasarsu Nageria,aka bar yan kasan,tare da Amarya Asma"u da angonta wacce tazama yar sudan Abunta,kafin dawowarsu sun yawata kasar kamar zasu ga karshenta,hatta asibitin da Lubna take aiki sai da sukaje,nan ta hadu da Dr,sultan yayi Aure ya aura wata yar pakistan ammu musulmace Salima sunanta,itama likitace irinsa,harda cikinta,Sun amshi lamban juna ida da Lubna,domin kai tsaye Dr,Sultan yace"Itace Lubna wacce ta yaudareshi.."Duk da cikin zolaya ya fada,ammh zaka fahimci duk sanda ya tuna yanajin dacin Abun,daganan har inda suka fara haduwa da mu"azzam sai da sukaje,yau dai mu"azzam da kansa ya Umarci ma"aikatan wajen da suka kawo kayan sanyi,duk da basu ganesa ba,ammh zuwa wajen ya tunamai da abubuwa dadama,lalle rayuwa kenan,dagana Hotel din ya sauka yakaisu suka gani kowa sai mamakinsa yake,na yadda ya iya zuwa ya rayu agarin da baisan kowa ba shiko,yafada musu yanaji ajikinsa yasan wasu,domin duk sanda yaji kadaici yana Tunawa da Ummi anan garin aka haifeta haka zakali anan Auren Ummi da Abbansa ya kulli,shiyasa baijin yazo inda baisan kowa ba.Suna dawowa kwana daya sukayi a abuja Su Hajiya suka koma zaria,su Mahgana ma da,dasu Alhaji da matarsa hajara da Ya"yansu yan gata Ummi da moodu wanda dazasu tafi harda yimasu Ummi dasu zahirah bye bye,yara ko ajikinsu domin gatan da suke samu achan Abun sai wanda yagani,tuni gida ya watse aka bar masu gida da Abunsu,sai fatan Allah ba ma"aurata zaman lafiya.

*After 3 Month*

Da gudu mu"azzam ya fito daga mota dauke da zahirah wacce keta mukurkusu ga cikinta yayi wani girma yayi kasa alaman yakusa fitowa duniya,Ummi da yakura da Lubna na biye dasu cikin tashin hankali,itama ga cikinta nan ya girma da alamu shima ya tsufa,suna shiga cikin asibitin Nurses suka amshi zahirah suka gungurata zuwa labor Room,tana ta mukurkusu tana zuba salati,Sukaja suka tsaya suna salallami tare da Fatan Allah ya raba lafiya,Lubna ko na jinkine gefen kafadan mu"azzam hannunta na cikin nasa ta Jimke,tana tsiyayan kwallah,tana tsausayama kanta kuma tana tsausayama kanta da mijinsu,wanda ko ciwon kai sukayi bashi da sauran sukuni sai sun Warke,Rumgumota yayi yana bata baki,tare da tabbartama da cewa insha Allahu zahirah zata haihu lafiya.

  Illai kuwa ba"ayi awa daya da Shiga da ita ba Dr,Farha ta fito bakinta har kunne ta nufi su mu"azzam tana fadin"Congratulatin Brr,mu"azzam matarka ta sauka ansamu diya mace,sai kuje ku zo da kayan haihuwa da Sauri don Allah..."Dukawa kawai mu"azzam yayi yanama Allah godiya da kirari,Haka su Ummi ma,sun tasomata suna hamdala afili atare,Mu"azzam ne yace"To Dr ya matata take? hop dai itama tana lafiya.."Mirmishi tayi kafin tace"Alhamdulillah tana cikin koshin lafiya,ana gyarata ne,ita da babbyn,yanzu za"a kawota dakin hutu,ku hanzarta kawo kayan haihuwa don Allah.."Tafada kafin ta wuce abinta,Lubna kamar ta zuba ruwa kasa tasha saboda murna kallonta yayi tsausayinta na kamasa saboda yadda Cikin yayimata nauyi yace"Kema Allah saukeki lafiya."yafada yana riko kafadanta,Sadda kai tayi kafin ta amsa da Amin su Ummi natayata,Zaunar da ita yayi yana fadin"bari naje nazo da kayan da suka bukata Ummi,sai na dawo,"yafada yana hucewa,suka bisa da adawo lafiya,saboda rudewa dama ko adazun shiya Tuka motan,to yanzunma Shi ya tukata yafice daga Asibitin Fuskarsa na bayyanar da Farincikin dayake ciki.

*Comment,share and Vote*

  *Jamilajanafty*

*UWAR MIJINA...!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_

       *Mallakar:JANAF*
       *Wattpad:Janafnancy12*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*GIFT TO:Hussain80k*

*Intelligent writer's Asso*✏

_*Alhamdulillahi ya Allahu...Before i close d last chapter of diz Novel UWAR MIJINA...,i want to use dis Oppurtunity to Thanks to Someone1 So special to me,He is my Daddy✌,He is my Uncle🤘,He is my Teacher,He is my mentor,He is my Heart💝,He is my Luv💘and He is my Dream🌙,He luvs me💕,He Support me👍,He care For me😘,He Trust me👌,He guide me👫,Infact He iz my Life💖,UNCLE ME❤,The Person of UMAR BELLO SADIQ💘🔐,Tanque for d True luv Daddy,Tanque for Been Their For me,Tanque Daddy...,Tanque Uncle....,Tanque....,Tanque So much I love so u much may God bless u Amin...*_🙏👄💅💑

_*END*_🖐

        *N0 50*

     ""Cikin Farinciki da Annushuwa ya karisa gida koda yaje su karime hankalinsu yaki kwanciya nan yake shaida musu zahirah ta sauka an samu diya mace,murna ba"a mgana Karime harda guda da juyi dariya kawai yayi ya Shiga cikin bedroom din zahirah akwati gudane na kayan baby yadauko bayan ya bude wardrope ya daukoma zahirah dogayen Riguna guda biyu,dakinsa yakoma ya dauki kudi yasaka a Aljihu ya fito,yace baba karime tazo Suje asibitin tare,su lami su zauna zai kira waya ushe ya kawosu haka ko akayi karime ta shirya suka koma asibitin.

Koda sukaje har ankawo Zahirah daki na musssaman,ita da jaririyan yana mika kayan Nurses suka sanya mata bayan sun nadeta cikin kayan sanyi,ita kuma zahirah ammh mata alluran barci,tana hutawa,Ummi aka fara mikama jinjirar kafin lubna da yakura Mu"azzam ne na karshe daukan Tsurama yarinyar ido yayi yana kallon kamar an tsaga kara da zahirah hatta yatsun hannunta dana kafanta irin daya dana zahirah ne, Farinciki ya lullube Mu"azzam yau ga mai kama da hiransa ahannunsa,rumgume yarinyar yayi yanajin wani sonta da kaunarta mai tsanani yana tsirgamai addu"a yayi mata cikin kunni kafin yamikama baba karime ita ya fita zuwa office din Dr Abduljabar

  Ko kafin yammah tayi haihuwar na zahirah yagama karade dangi kaf,hatta mutan sudan lbri ya ishesu,mutan maid ma haka,mutan zazzau ma lbrin haihuwan ya ishesu sai kira suke suna ma maijego barka da angon karni tare da fatan Allah ya sauki Lubna itama lafiya,kwana daya jal Zahirah tayi asibiti aka sallameta takoma gida,tacigaba da samun kulawa wajen Tsofaffun hannu Ummi da yakura,lubna ma da cikinta yayi girma itama ba"a barta abaya tana bakin kokarinta akan kula da zahirah da yar jinjiranta,abangaren angon karni ko abun ba"a mgana hidima yake da lafiyansa hade da Aljihunsa,Yarinya da uwarta sunga gatan Duniya domin akwatu biyar yayima zahirah na kayan Fitan Suna,uku nata biyu na bby,bai fadi Sunan daya sakama yarinyar ba sai Ranar da sati ya zagayo wato Ranar Suna kenan,jinjirar Zahirah taci sunan mahaifiyarta FADI ammh zasu dinga kirata MUNTAZ,Ummi ce kadai tasan da sunan,lokacin da mu"azzam ke fadama su hajiya da safe sunan jinjirar Zahirah zuru tamai da ido tana jin sanda hawaye suka cikamata ido saboda murna,bata san kalan Fuskar mahaifiyarta ba,bata taba sanin dalin uwa ba,Batasan ya akejin shauki na dumin jikin mahaifiya ba, tatashine ita cikin maraici,akullum intaga yadda iyaye suke so da tattalin ya"yansu sai kadaichin nata uwar ya bijiromata,baranar da zata zo bata tuna da mamanta ba,duk da bata taba ganinta ba sai ahoto,yau gashi mijinta kuma yaya gareta,ya sharemata hawaye ya sanyamata sunan mahaifiyarta mafi soyuwa aranta,lalle bata da bakin da zata godema Mu"azzam.

Hawayentane suke kokarin zubowa shiyasa tatashi da sauri ta shige tiolet tayi kukanta ma"ishi kafin ta fito,ashe mu"azzam na lura da ita tana fitowa yakirata awaya yace tazo shashensa ta sameshi bata kawo komai ta rumgume muntaz data sha gayunta ta Nufi turakan megida,yana zaune bisa gado ta shigo da sallamanta tana sanye da wani Swice lesss,blue and Pick yayi mata kyau sosai Fuskarta an mata make up tayi kyau sosai.

  Da Sauri ya tashi ya isa gareta yana fadin"Ko kunya bakiji sai wani daukan ya"kikeyi.."yafada yana amsata,kallonsa tayi kawai tayi mirmishi ganin haka yasa,ya ijiye muntaz bisa gado yazo yakama kafadun zahirah yace yana kallon kwanyan idonta"Meya saki kuka,ko sunan dana samata ne bai miki ba,kifadamin my hirah sai achanza,dama na dauka zaki fi kowa murna ne da hakan dat why na yanke hukunci ban gayamiki ba.."yafada yana kuramata ido.

Saurin Rike hannunsa tayi tana girgiza kai tace"a"a ba haka bane,tayaya zaka saka sunan mahaifiyata mafi daraja aguna nace bani so.."tafada idonta sunciko da hawaye,rage girman idonsa yayi yana fadin"to meya saki kuka,uhm..Tell me.."?yafada yana Shafa wuyanta,hannunsa ta damko kafin ta runtse ido hawayen idonta suka zubo tace"Kukan Farinciki ne,yaya wlh narasa yadda zan fasssra kaina,ayau ammh abu daya nasani ina cikin Farinciki da wannan sunan yaya mu"azzam,tare da godema Allah,daya bani gwarzon miji mai sona da kaunata,nagode yaya mu"azzam Allah ya...."Shiiiiii...."yace yana dora hannunsa bisa bakinta kafin lokaci daya yajata ya rumgume kamkam,rikesa tayi tana kara sakin jikinta,lokaci daya ta saki kukan datake rikewa,Bubbuga bayanta yake alaman lallashi,yake fadin"is ok umh..,Miye namin godiya,ai inna fadi Nima uwatace koda bata haifan mata ba balle ta barmin ke gaki kin girma kin aureni,kin bani Farinciki kin haifamin yara,to miya fi wannan soyuwa,wlh hirah yadda nakejinki araina zanyi iya baki raina matukar ke zaki rayu ki zauna aduniya ni kuma na tafi.."yafada shima muryansa ya chanzawa.
Chapter 79 · 0% Book details