← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 82

Sashe 15

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Suna zuwa kofar shiga babban falon hajiya tayi ma zahirah rada akunni tana fadin"Ki shiga da kafar dama,zahirah bayan kinyi addu'an fatan zaman lafiya agareki"Jin haka yasa tafara karanto addu"a tana kuka kafin su shiga falon wanda daman babban falo ne mai girma da tsari wanda yake dauke da kujerun royal chair har seti biyu,golden colour wanda sukayi ma falon kwanya bayanshi sai wani kafet mai kama da auduga wanda da kasanya kafa zakaji kafarka Ta, lume aciki,sai wani tafkeken Tibin bango daya kusa cinye rabin falon daga yamma kuma wani babban dining area ne wanda yaji wani ubansu Dining table wanda akallah mutane fin goma zasu kammallu agun.

      Daga gefe kuma wani korido ne wanda da ka shiga zaka ci karo da wani babban daki ciki da falo wanda cikin nan store,duk wani nau"in abinci yana ciki,sai falon inda nan ne madafi ma'ana wajen dafa abinci wanda yaji kayan wuta na amfanin yau da kullum,inka fito kuma dakuna uku ne ajere,na su karime ne duka.

  in mutum yadaga kai sama kuma mattakalan bene zai ci karo dashi,kana hawa zaka tarar da dakuna biyu kachal wanda nan ne shashen Ummi mai gayyah mai aiki..Daki daya bedroom ne,kawai da tiolet daki dayan kuwa babban falo ne mai dauke bedroom da tiolet harda kichen,Ummi tana zaune ne cikin one bedroom ne mai babban falon tabarshi ne in tayi baki kamar hajiya wanda ko wannan zuwan nan ta sauka.

    In ka kara saukowa kuwa akwai wani korido dayake kallon saman Ummi,dakabi nan sai sashen mu'azzam dauke da babban falo da bedroom da tiolet,indan ka fito kuma daga gefe ne sai ga wani daki shima dauke yake da falo mai 2 bedroom aciki harda kichen.

  Shi Naga hajiya tanufa tasaka makulli tabude, tana fadin"To amarya ga dakinki ki shiga da kafar dama"Yakura ta rikota tana tayata addu"an kafin su sanya kai cikin dakin wanda ke tashin kamshi ko"ina agyare yake falo ne,dan madaidaici mai dauke da wasu arnan kujeru royal chairs purple ne masu kyau sai wani capert daya mamaye duka dakin wanda taushinsa ya wuce misali,wani mamaken talabijin ne ke ta aiki shi kadai sai center table wanda ke tsakiyar dakin,Yakura da mahgana sakin baki sukayi suna bin,ko"ina da kallo,basu gama kallo ba sai suka dangana da cikin bedroom din wanda shima komai na ciki purple ne, shima ya kawatu da Royal bed da wani makeken wardrope da  madubi wanda ke shake da kayan ado na mata  dama, kowani daki agidan agyare yake da kayan more rayuwa.

  Kan gadon dayaji lafiyayyan zanin gadon aka ijiye zahirah wanda kanta ke dunkule cikin lifayanta ammh kallo daya zakamata kasan yarinyace karama ,haka suka karime ke fada bayan sun Fito daga dakin,nan fa suka shiga jera musu abinci kala kala wanda sukayi musu hajiya keta rawan jiki dasu,sallah suka farayi kafin su zauna suna cin abinci bayan hajiya tabasu wuri,Yakura da mahgana suna ta fadi zahirah tagama sa"a ammh *UWAR MIJINTA* itace babban mtsalanta.

    mu'azzam kuwa,da Shureim bangarensa suka fada sukayi wanka gado suka hau suka kwanta domin sun gaji jiki na bukatar hutu,shima kafin kace me dukkansu barci ya kwashesu,shiko mu"azzam da ,zullumi yayi barci saboda rashin ganin giftawan Ummi,kuma baisamu kebewa da hajiya ba balle yayi mata mgana.

   Hajiya kuwa falo suka dawo ita da zulaika,suna hiransu ammh ranta abace yake saboda abunda suhaima tayi mata,tun jiya tafita batunta saboda tun tafiyar su Mu'azzam take bata baki ammh suhaima takiji wuni tayi adaki,bata fito ba shiyasa yau din hajiya ko mgana bata mata ko dakin ma bata shiga ba,aranta tana fadin"Sai dai ki kashe kanki don ko ga amarya nan tazo"

  Kamshin Turaren da sukaji ne yasa suka kalli saman Ummi ce ke saukowa cikin takun isa sanye take da wata shadda gezner, doguwar rigar golden colour,wacce taji aiki sama da kasa,ta daura dankwalin bisa kanta bayan ta tamke gashinta,wuyanta sanye da sarka zinare da kunnenta harda hannuwanta kafafunta kuwa sanye da wani Vine ne mai dan Tudu sai mayafi data yafo mai dan girma.

  Fuskarta babu fara'a ko kadan duk da ba wani kwalliya tayi ba ammh kyau xalla ya bayyana,saukowa take cikin takunta na isa,hajiya da zulaika suka bita da kallon burgewa don sun shaida Ummi fa macece ta nunawa ako"ina.

  Ta iso falon lokaci daya tadan saki Fuska tana fadin"Sannu da gida yaya" mirmishi Hajiya tayi kan tace"Hoho..Hajiya suhaimar shagali kin gama fushin naki kin fito'"Dariya kawai tayi tanazama Zulaika dake gefe tana gaisheta ta amsa tana fadin"Lafiya kalau zulaika ya hidima kuma,Allah ya saka da alheri"Zulaika ta amsa da Amin.

  Hajiya ta kalleta tace""yan maiduguri fa sun iso dazu, mun barsu suna cin abinci ne"Tafada tana kallon Fuskanta Yamutsa fuska Ummi tayi kafin tace"uhm.."Kawai kauda kai Hajiya tayi kafin tace"Zulaika dan bamu wuri don Allah"Tashi zulaika tayi tanufi barayin su lami dake chan kichen suna shirye shiryen dora dinner.

   Hajiya takalli Ummi tace"Karki sake ki fara ma Suhaima wannan ba girman ki bane, Rama cuta ga wanda baiji ba baigani ba'"Ummi takauda kai kafin ta kago mirmishin dole tace"Allah bakomai yaya..Kawai nakasa kauda abun araina ne balle har na manta" hajiya tace"Hakuri zakiyi ki kuma tuna Allah ma muna masa laifi ya yafemana to kema kiyi koyi da musulman kwarai ki yafe suhaima don Allah"

Kuri tayima hajiya da ido kafin ta muskuta tace"Shikenan yaya zan duba komai zai wuce"Jin haka yasa hajiya washe baki tace"Yauwa diyar albarka kokefa,maza tashi kije tundazu yakura keta tambayanki" da mamaki tace"Kina nufin da yakura aka zo"Hajiya tace'Eh ita da matar baban yarinyar"jin haka yasa Ummi mikewa tana fadin'bari na leka "Har ta wuce ta dawo tana fadin"af nace su mu"azzam basu dawo bane banji duriyansu ba.

  Hajiya tace"Inafa tare suka iso,suna ciki kila suna watsatsake gajiya ne kinfa san maiduguri ba kusa ba"batayi mgana kawai takada kai tawuce kowani taku intayi kamar ta kurma ihu takeji yau matar shettima da diyan Fadi sune zaune cikin gidan danta kai shettima yagama cutarta ta ko'ina.

.

    Da sallama tashiga falon,mahgana ne zaune afalon,tana ganin Ummi ta shigo ta mike da sauri kallonta kawai tayi ta fahimci itace suhaimar data dade tana jin lbrinta daga bakuna da dama,kwarjininta yasa mahgana saurin sadda kai tana fadin"Sa..nn..u ha..Ji.Ya"Cikin rawan murya Ummi tajuyo ta kalleta akaikace tana wani kyabe baki ko tankata batayi ba, tafara taku zuwa cikin bedroom din bayan ta sakarmata dogon tsaki,bayanta mahgana tabi da kallo aranta tana fadin'"Baki ba mara da kunya ba,bala"i yanzu ina zahirah zata iya da wannan jaraban"Tafada aranta tana kuma kama baki kamar tana jinta.

     Knooking tayi akofar bedroom din yakura dake ciki tana lallashin zahirah taci abinci tace"Waye shigomana,mahgana"Bata taba zaton Suhaima bace,da siririyar sallama ta shigo dakin lokaci daya suka hada ido da Yakura,da sauri yakura ta mike tana fadin"wai suhaima nake gani haka kodai idona gezo yakeman"Mirmishin kasaita Ummi tayi kafin ta tako cikin isa da takama tana fadin"Nice dai Suhaimar dakika sani yakura ba gizo idonki,
ke miki ba, kina gidan dana Mu"azzam ne"Tafada cikin izza lokaci daya tana sauke idonta kan zahirah wacce ke zaune kan gado ta cire lifayan daga ita sai doguwar rigar shaddan dake jikinta yarintarta tafito fili kirjin nan ma yanzu yafara tasawa kura mata ido Ummi tayi lokaci daya tagano kamarta da uwarta kamar an tsaga kara ankarya Tuni fuskar Ummi ya chanza tahade rai sosai tana binta da wani kallon na zaki ci ubanki ne.

  Zahirah kuwa da sauri ta sunkuyar dakai jikinta yahau rawa tuni idanunta suka ciko da kwallan tun sanda Ummi ta shigo kallon farko zahirah ta mata gabanta yafadi balle dataga yadda take kallonta Allah sarki tuni tafara hawaye da hannu tasaka tana sharewa jikinta kuwa bai bar rawa ba.

  Yakura dake tsaye tana kallon Abunda ke faruwa itama cike da tsausayi take kallon zahirah kan takoma ta kalli Ummi tayi karfin hali cewa"ai nasan muna gidan danki mu"azzam ne kawai mamakin ganinki nake shekaru fa dayawa"Tafada itama bakinta yafara rawa Ummi tayi mirmishin dayafi kama dana takaichi kan tace"eh hakane kam yakura ya kwana dubu kuma"Tafada ammh still idonta na kan zahiirah.

.Yakura tace"Sai alheri shikenan kin guji maiduguri ko'Tafada da sigar zolaya,hoho ai nan da nan Ran Ummi ya baci takankance ido tace"Yakura kika ce me? na guji maiduguri "Tafada bayan ta sakarmata idanunta wa"inda suka fara chanza launi Yakura ta kalleta sai yanzu ta tuna tayi fa baram barama, Kafin tayi mgana Ummi ta kariso kusa da ita tana fadin"Ai maiduguri itace garin da duk aduniya in aka ambaceta nakejin kaina cikin bakinciki wani lokacin ma har na koka,garin da tunda nasaka kafata cikinsa ban kara farinciki ba sai da na barsa,garin da aciki aka kasheman mijina wanda naso rayuwa dashi koda bamai yawa bane.! garin da nashiga kunci da takura da halin kakaniyan rayuwa duk acikinsa,kin manta yakura kece kike tallafamin da abunda zanci aboye dani da dana,? kin manta? nace kin manta ne? tafada tana zare mata ido kuma cikin tsawa.

  Yakura tayi kasake kawai tana binta da kallo Ummi ta damke hannu yakura tana fadin"Shine kuma kike tambayana na gujeku alhalin kuka fara gujeman,ku,kuka fara kyamatata,saboda mene, ni bazan nisanta kaina daku ba,kuma na nisan ta duk wani ahalina,daga rabarku ba"Tafada tana sakin hannunta lokaci daya tana sakin ajiyar zuciya kafin tajuya tana kallon zahirah wacce ta rabe jikin gado tana kuka tace.

    *YAKURA KINYI KUSKUREN BARIN SHETTIMA YA YA AURAMA MU'AZZAM DIYAR FADI,HAR ABADA ZAN CIGABA DA KALLONTA AMATSAYIN MUGUWAR UWARTACE, WACCE BABU IMAMI KO KADAN ARANTA,KUMA WLH TALLAHI SAI TA DANDANI KUDANTA FIYE DA WANDA UWARTA TA DANDANAMIN DAT IZ MY PROMISE*
Chapter 15 · 0% Book details