Sashe 20
Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ummi tayi kwafa tace"To saurareni da kyau babu bawanki acikin gidan nan,Daga yau sai yau,gari na wayewa ke karime ki nunamata komai,daga yau ita nake bukatar ta tsaftace falon nan da dakina,kuma ki tafi da ita kichen ku nuna mata komai,su wanke wanke da yanke yanke,duk ku bata kan ku gama nuna mata kan girkin gidan,Nan gidan ba gidan da zaki zo ki kwanta bane don nima uwarki bata barni na kwanta ba"Ta kareshe cikin Tsawa..
Jikin Zahirah na rawa ta mike,karime ma ta mike tana fadin"muje ran..."Sauran mganar ta makale ne da suka hada ido da Ummi Sum Sum ta wuce zahirah tabi bayanta kafafunta na hardewa,Ummi tabita wulakantattacen kallon Aranta tana ma Tunanin anya yarinyarnan Lafiyayyane,kuwa domin koda yaushe in tana Tafiya kamar ta lauye ta fadi.
Suna shiga kichen din Su lami da Uwani dake aiki suna ganin zahirah suka zube suna gaisheta,tare da mata barka da Fitowa,cikin mamaki Zahirah ke kallonsu ganinsu manya dasu ammh suna duka mata,hawayen daya zubomata tasaka gefen hannu ta share lokaci daya tana musu mirmishu,kallon junansu sukayi kafin karime tace"Hajiya tace nazo da ita mu nuna mata komai,gyaran Falon ma tace wai na barmata"hada baki sukayi lokaci daya sukace"Ki barma wa..."Suka fada suna gwalalo ido
Karime ta kalli Zahirah tace"Eh haka hajiya tace,nifa wlh kaina ya daure,matar yallabai guda ammh Hajiya tana wani abu wanda hankali ya gaza ya dauka"Tafada ckin nuna damuwa,lami tace"Iko sai Allah Ke karime wai kinji da kyau kuwa? tafada tana nuna mamakinta,mirmishi karime tayi kafin tace"Wlh lami nima Abun yabani mamaki,kuma fa hajiyar zaria tafadama cewa yar"uwansa ce fa.
Uwani dake gefe tayi tagumi tace'Oh nifa duk kunsani ackin Rudi,wai ita hajiyan da kanta tace,haka kada fa yallabai yazo ya ganta Muyima kanmu sanadiyar Hanyar cin abincin mu fa'"Karime tace"To ya zamuyi Umarnin hajiya ne fa,ko yallabai bai isa ya tsallake Umarninta ba.
kallonta Sukayi dukkansu tana tsaye tana kallonsu ammh hankalinta bashi agunta ta lula tunanin gida da kewar yan"uwanta,Karime tace"Nifa gaskiya bazan iya sakata wani aiki ba,mu kyaleta dai ta zauna tana kallonmu gudun karta koma ciki hajiya ta ganta ko ya kuka ce'"Uwani batayi mgana ba tajawo wata kujeran Roba ta sakama zahirah tana fadin"Don Allah matar yallabai Zauna kina tsaye Tun dazu"kallonta zahirah tayi kawai sai ta sakarmata mirmishi batace komai ba.
Kallonta karime tayi tace"ki zauna Ranki ya dade..."Girgiza kai tayi kan tace"Ina aikin da zan muku, nafara.."Tafada cikin Nuna Sanyinta kallonta sukayi lokaci daya sukaji kaunarta ta mamayesu atare suka hada baki suka ce'a'a babu wani aiki ranki ya dade ki zauna ki huta abinki"
Duk da haka taki zama sai da sukayi da gaske kana ta zauna a tsorace tana kallon Kofa,karime ta gyada kai kan tace"Ki zauna da kyau hajiya bata shigowa kichen din nan"Jin haka yasa hankalinta kwanciya,haka ta zauna tana kallonsu suna aiki,suna hiransu wani waje ta murmusa wani waje tadanyi dariya ganin haka yasa suke dan Tsomota cikin hiran nasu,duk bata tsoma musu baki ammh takanyi musu mirmishi basu damu ba,domin Sun Fahimce halitarta ce rashin son mgana,tare da ita suka karishe girkin Tuwon Semo ne sukayi musu da miyar danyen kubewa,sai Farfesun kan sa,da alalan hanta da sukayi ma yallabai,lemon abarba Uwani tahada shima duk na yallabai ne,gudun Fadan hajiya yasa,suka bawa zahirah wasu kololin ta dauko suka zo Dinning suna jerawa Ummi dake zaune Ranta fes Aranta tana fadin"Kadan kika gani yar banza,sai kin barmin gidan dana da kafarki"
Sai da suka kamallah komai suka goge kichen din Kana suka Nufi dakinsu koda suka Fito falon Ummi ta hau sama,abun mamaki zahirah dakinsu karime ta bisu basu hanata ba,abincima cewa tayi tare dasu zata ci,tuwon sukaci daman shi ne yafi, burgeta taji tana sha"awanci,kafin dare Tuni Zahirah taji ta saba dasu karime saboda yadda suke girmamata gasu babu Ruwansu,duk da,bata mgana sosai ammh sun lura ta saki jikinta dasu,suko fahimtar haka yasa suka kara janta ajiki suna mata hira tana dariya Uwani na bada lbrin Yanmatancinsu akauyensu Haka xahirah ke dariya harda kyakyatawa,suko murna ta cikasu don sosai Yarinyar ke basu Tsausayi mussamman Karime wacce take kallonta kamar yarta Asma"u data haifa da cikinta,Sai da aka kira mangariba,kana suka rakata dakinta,basu wani jima ba suka mata sallama suka fito,sanin Yanzu yallabai zai Shigo.
Aiko Illai bayan mangariban ya shigo da yake yana Tsaya masallaci yin sallah,barayinsa ya zarce direct bayan yayi wanka ya sauya kayan cikin riga da wando na jc,Fitowa yayi ya haura Saman,Ummi domin harga Allah ya ma manta da zahirah ma arayuwarsa balle yayi Tunani Dubata,tare suka sauko Da Ummi sukaci abinci kafin su zauna Afalo suna hira,Issha"i aka kira ya mike ya fice ,yana dawowa sallama yayi Ummi ya wuce sashensa domin yau din nan yagaji matuka shiyasa yana zuwa brush kawai yayi ya kwanta Sai barci.
********
Yan Kawo amarya kuwa yakura da Maghana sun iso gida lafiya cikin koshin lafiya,ammh Kuma tun suna hanya Yakura ta roki alfarman Mahgana Ta boyo abunda yafaru Tsakaninsu da Ummi don Allah kada tafada ta tadama Bukar da hankali,suyi shuru da bakinsu sudai nasu addu'ane Allah ya yayyafama abun Ruwan sanyi.
Mahgana ta ji mganar don da suka koma banda saka albarka basu ce komai ba,sun bada lbrin yahna ta shiga jin dadin rayuwa kam,tagama dacewa duniya sai dai kuma lahira ake mata fata,Jin wannan lbri ya sanyayama Bukar rai,wanda zullumin dake ransa sai da ya ragu,Mahgana kuwa kallonsa take tsausayinshi na ratsa Aranta tace"Bazan ko taba, fadamaka wani hali yahna ke ciiki ba,kodon kaima ka kasance cikin Farinciki.
Shiko Shettima Koda yakura tace haka yajitace ne kawai ammh bawai don ya yarda ba,domin yafi kowa sanin wacece Suhaima shiyasa kai tsaye yace"Lamarin zai daidaita ammh ba yanzu ba yakura kamar yadda kika fada ba:"jin yace haka sai ta kallesa tace"Ah to ashe kanama son komai shine kake tambayana ai bai kamata kanemi karin bayani ba,Cutane dai kam acucu yahna sai dai Fatan Allah yabata ikon cin jarabawa,tana gama fadar haka ta shige daki tana kuka,shiko Shettima tasbihi yake tayi cikin Ransa yana jin a jikinsa komai zai daidaita lokaci kawai yake jira.
_______________
Hakama Washegari Tunsafe Zahirah tatashi bata koma ba,dama Tunda tazo gidan bata taba barcin Safe ba,Tunkan Hajiya ta sauko Karime ta tatayata suka gyara falon Tas,karime tayi mopping dinshi ta kunna Turaren Wuta,dakin Hajiya ne sai ta sauko daman dokarta kenan ba"a Tashinta in tana barci.
Kichen suka koma suna aikinsu suna hiransu yau dai ta dake,tare sukayi wanke wanke ita da lami,kuma ita ta goge kichen din duk tanayi kamar bata da jini ajiki ammh haka take kokarin yin komai cikin hanzari,cikin lokaci suka kammallah breakfast din suka jera koma bisa Table suka koma daki,yau din cikinsu ta karya domin hakan ya fimata dadi,don yana sawa ta Tuna da gida kuma hakan yana sakata cikin nishadi.
Suna jin Sanda Hajiya ta sauko Ta nufi dakin dan lelenta,suka Fito tare takaishi Dinning Suka karya har Fitansu ma sunaji sanda ta rakashi,aransu suna mamakin wannan karfin hali mace da mijinta ammh ki maidata boyu boyu ackin gida,wlh basu zata Ummi da wannan Mugun halin ba.
Ganin Ummi ta dade da Saukowa yasa Karime tace Zahirah tatashi suje su gyaramata dakin nata,suna ko Fitowa sukaci karo da ita Falo,bisa daya daga kujerun Falon anci ado,kafa daya kan daya,akwai jikin Zahirah na rawa ta durkushe tana gaisheta ko amsawa batayi ba illa dagama hannu datayi tana fadin"bani bukatar gausuwarki malama,karime haura da ita,ki nunamata yadda kikeyi,don bani son akin amaja"Tafada tana wani yamutsa Fuska da Toh karime ta bita suka haura sama tare.
Karime ta gwada mata komai,ita ta gyara bedroom din,itakuma ta shiga Tiolet ta wanke wanda sai da karimen tazo ta amsa don harta gama gyaran nan ammh ita zahirah ko Rabin wanke bayin batayi ba,Karime ko tsausayinta ke kamata domin Tasan tabbas zasu samu mtsala da hajiya,don Tatsani mutum mara karkashi gashi ko ita ko Zahirah haka Allah yayi ta,komai cikin hanzari take yinsa ammh kuma sai ta dau lokaci tanayi bata gama ba.
*After one week*
Zuwa wannan lokacin duk wani ukuba da wahalan Rayuwa zahirah ta gansa muraranta domin Gyaran dakin Ummi kullum sai ta mareta sabida yadda take bata lokaci bata gama ba,tunda kuma ta fahimci in sunje da karime na kamamata ne,yasa tace karimen ta daina zuwa,kullum haka zata gyara falon ta kuma yi mopping dinshi kafin taje dakin Ummi kan kace me tayi baki ta lalace duk ta bushe dama ba auki ba,duk da wai basu fara bata girki ba sai abunda ba'a rasa ba aboye don Ummi bata sani ba,Zahirah yanzu tama daina kuka domin ta gane a wahala zata dauwana har ta mutu,don akwai Ranar data wankema,Ummi Bayi ta manta batayi ma Ummi mopping din kasan bayin ba,ta zo shiga tsantsin Ruwa ya dibeta ta kusa fadi,wlh Ranar sai ta gunmaci mutuwarta don Ummi a fusace ta fito falo takwala mata kira tana zuwa,bata yi wata wata ba ta saka hannu ta wanketa da kyawawan maruka har guda biyu bayan ta saka kafa ta kwasheta ta fadi warwars bisa kafet,Wanda sai da bayanta ya amsa da kafanta wanda sai da tayi targade,Ummi tayi ta bala"i wai da gangan Tayi saboda tana son kasheta,haka ta tasata gaba sai da taje takara wanke mata bayin ta goge,Koda ta koma daki taci kuka kamar ranta zai Fita kafin dare Kafa ta kumbura tayi Sumtum koda su karime suka gani,sukaje suka Fadama Ummi cewa tayi"Ba kumbura ba tama Rube ita ina ruwanta,jin haka yasa Uwani duba kafar nan tagano Targade ne,ai ko Zahirah taji kuka lami da karime suka riketa taja mata,dayake ta iya babanta yakoyamata tun a kauye,Su kansu sun tsausayamata matuka man zafi suka Shafemata kafan dashi kafin sumata sallama su fice.