← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 82

Sashe 42

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Tuni yara Sukaci sunayensu *SUHAIMA IBRAHIM MOHAMMED MOODU* Da *MUHAMMED IBRAHIM MUHAMEED MOODU* Sai fatan Allah ya rayasu cikin tafarkin addinin isalama,da kuma fatan Allah ba maijego lafiya mai dorewa Amin,yan group din janaf novella sun hallarta dasu da yan Uwar mijina fans1,2and3 ammh basu wani samu tarba mai dadi ba jin daga tawagar Ummi ce sukazo babu wanda yayi musu kallon arziki ba don ma bukar ya kwaba ba yasin cikin gidan nan da ansamu mai chanza wasu daga cikinsu halitta saboda Yadda suka Fusata da wulakacin da akama yarsu,jagoran Tafiyan my Sisi ce Aisha Alto da sahibata hafsat hafnan,ai jiki ba kwari suka dafafo hanya fuskar ba Annuri saboda haushi biyawa gaida mu"azzam din dasukace zasuyi ma ba wacce tabada fuska,kowacce gidanta aka sauketa jiki a sanyaye😂😛😝😜

______________

  Su hajiya kuwa koda suka dawo achan asibiti suka tarar da Ummi duk da sau uku arana ake barinta shiga,tunda yau da safe yafara cin abinci,to tea kadai ma yasha,shima bada yawa ba,saboda yadda bai iya jin dadin komai abakinsa,Ummi kuwa sai jidashi take tana wani riritasa shiko kallonta yakeyi yana jin haushi abunda takemai,ta riga tagama kashemai rayuwa kuma lallabansa metakeyi ai data barshi ya karisa mutuwa yahuta itama tahuta.

  Abunda ya dauremai kai zama tayi tana lallabansa da yayi hakuri ya kwantar da hankalinsa yana warkewa tayimai alqawarin auramai mace,wacce tafi zahirah sau dubu ,wacce zata dace dashi,kawai yabata lokaci sai ta sanyasa farinciki fiye da yadda baya tsammani,da toh kawai ya bita,ammh aransa yana fadin Ummi bata kaunarsa ya yarda to Wlh sai dai ta aurama kanta Auren ammh badai shi,shi in ba hiransa ba to yayi alqawarin dauwama haka har abada,domin duka sauran mata maza yake kallonsu Hiransa ce kadai ta fita dabam,komai nata dabam ne dana sauran mata,zuciyarsa tana cigaba da suya shiyasa cikin ransa ya yankema kansa mafita ya gwammace ko zai Mutu to yayi nisa da Garin ila ma da Kasar gabadaya ,don dai ya cigaba da zama anan har ya tsinci lbrin hiransa zatayi aure da wani to ya tabbata adaren zuciyarsa zata,buga ya mace.

   Kwana daya su hajiya suka kara suka wuce,batare da sunfadama mu"azzam yadda bukar yadau zafi ba,hajiya dai tayita lbrin yan biyu da gayyah saboda Ummi,wanda ko ajikinta don ko a mafarki ma bata kaunar ganin ya"yan duk da mu"azzam ya haifesu ammh batajin zata sosu domin tsanar uwarsu ta shafesu,shiyasa ma batama bi takansu ba balle ma hartaji harda sunanta akasa da hajiya tafara zata fice ta basu waje,tana wani cin mgani abunta,Sunkoma saboda aikin shuriem yana ta samun waya daga wajen aiki ga gida kuma ambar Zulaika ita kadai,daga ita sa yara,dole tasa suka tafi,bayan hajiya tayima Ummi fadan kiyayen harshenta,gadai da'n nata nan data ke Tunkaho kwance ba lafiya in ta gyara rayuwarsa ta gyaru ita kara batamawa itace zata sha wuya tadai amsa da taji kawai,ammh har aran Ummi wani kudiran ne ke ranta na dabam.

*******

*BAYAN SATI DAYA*

  Zahirah da kanta ta kira Asma"u wacce kewaar zahirah ya isheta,tayi ihun murna sanda zahirah ke fadamata ta haihu da abunda aka samu,ammh tayi kukan jin sakin wulakancin da Ummi ta saka akama zahirah wanda har taci burin duk randa ta hadu da Ummi saitaci mata mutumci,Asma"u tazama so cool a mkranta ba zahirah gashi watanni kadan yarage su rubuta SSSE in ta tuna haka batasan sadda hawaye ke zubomata,Itakanta Mami ta tsausayama zahirah sosai tana fadin"Yarinya karama tahadu da jarabawa iri iri na rayuwa,mami da kanta tayi ma minista mgana zasu maiduguri,domin Kawance ai baice haka ba,nan da nan ya Amince suka tashi tundaga Abuja har maidguri da abun arziki niki niki Lalle yan maiduguri sunga kauna,don kwana biyu su mami suka musu kafin sukoma ,bukar yaji tsananin Farinciki ko bakomai zahiransa ba tazama wani abu,yau gashi ta dalilinta har diyar minista da matarsa suzo gidansa suyi kwanaki domin yarsa lalle Allah Abun godiyane,Zahirah ko taji dadin zuwan Asma"u ko bakomai tasamu wanda zasu tattauna matsalanta da ita,tayi kuka sosai Asma"u na bata hakuri,domin fa babu yarda suka iya kaddarace ta riga fata.

Suma da zasu koma sunga karramawan dangin Zahirah don suma sunhada musu komai iya karfinsu suka rabu suna godiya,sun cigaba da waya da Asma"un zumuncinsu ko saima yafi da karfi.

___________

Sati daya Mu'azzam yayi a asibiti kafin asallameshi ya dawo gida,bayan yasha dokokin likita,na cire damuwa aransa,kuma yadaina zurfafa tunani da yawan zama shuru,yakuma kiyaye duk abunda zai bata maasa rai ko na mutum kona Tunani,duk ya gujesu dakuma samun ishasahen hutu,dakuma shan mgani bisa ka"ida,Duk ya amsa da toh ne kawai ammh shi yanzu taya zai iya daina tunani ai har abada an gayyato Tunani,ckin rayuwarsa ne Tunda aka rabasa da hiransa.

    Kwana uku da dawowansa gida Ummi tana ta bare baren kula dashi ,karewartama dakinsa tatare ko tari yayi tadinga tambayan lafiya kenan,jama"a nata zuwa gaishesa expecially yan wajen aikinsu,gaskiya babu laifi ya samu sauki sosai tunda bai fara tsallake dokar likita ba,shima burinsa ya mike ga kansa,saboda ya aiwatar da kudirinsa domin babu gudu ba ja da baya.

Satinsa daya da dawowa gida ya tuburema Ummi shi zaikoma office,to ganin yadda take kan lallabasa tasamu ya manta da tsinanniyan yarinyarnan shiyasa ta yarda yakoma Aranar,wanda daman shima ba aiki zai kaishi ba letter ya rubuta musu na barin aiki na dan wani lokaci ma"ana Leave without pay kenan,matukar razana ma"aikatar ta razana da ganin sakon mu"azzam ko abokan aikinsa sunyi sunyi sun janyesa daga kudurinsa yaki,yace musu zai tafi karo karatu ne,to ammh abunda yabasu mamaki shine ita da kanta ma"aikatar in taga chanchantar mutum takan Turashi da kanta karo ilimi ammh shi farat daya kuma lokaci daya yace zai tafi abunda da mamaki,babu yarda suka iya illah binsa da fatan alheri.

*DON'T FORGET TO VOTE,COMMENT AND SHARE..It me Janafi*
*UWAR MIJINA...!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_

       *Mallakar:JANAF*
       *Wattpad:Janafnancy12*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*Intelligent writer's Asso*✏

_*Wannan Shafin kachokan mallakinku ne JANAF NOVELLA..mussaman masu sharhi,Fadila falalu maska(my Adila)😘,My Ummu kursoom(Abulkursoom)😍,my juwairiyyah Rogo❣,Mum khady(Kakata)💙,Malika masoyiyata❤,Suwaiba Husna,Aisha,Fatima,Abida mahamood(Anty momi)💖,Queen Aisha,Aysher,Safiyyah buhari*_
💕, _*Raliya mk,zainab Abdullahi,Anty khadija,..Kunada yawa wanda baki bazai iya furtaku duka ba,ammh duk wanda ke cikin group din Na janaf novella,ina mika godiyata garesa Allah yabar zumunci da soyayyar na har abada*_

*NOT EDITED*💥

                  *NO 27*

   Koda yadawo gida ko Afuska bai Nunama Ummi ba,illa ma biyemata dayayi sunata hira,ya warware kamar bashi ba,Ummi taji dadi rantayayi fari, tana fata Addu"artane taci na mu"azzam yafara manta da mayyar yarinyarnan data tafida kurwansa maiduguri.

    Washegari duk wani shiri nasa ya kammallah sa,kaya ko kala daya bai dauka ba,daga shi sai briefcase dinsa ya fito cikin shigansa na American Suit masu ruwan toka,ya mtse wuyansa da tie kafafunsa sanye cikin Rufaffun takalmana na fatar damusa,hannunsa kuma sanye da agogo na kamfanin Rado,fuskarsa babu Annuri ga idanunsa da suka kumbura saboda kukan daya sha jiya da daddare,har Ga Alla ba"a son ranshi zai yankema Ummi wannan Hukuncinba,domin tunda ya girma yayi wayau baitaba nesa da itaba,Tare suka rayu,akwai shakuwa da soyayyah ta uwa a tsakaninsu mai girma,wacce dalilin hakan yakeji kamar bai kyautama Ummi ba,ammh kuma zuciyarsa tana bukatar hutu,zaman agarin nan Tamkar dawo da hannun agogo bayane,zai Nesa da Ummi da kasar gabadaya ko zuciyarsa zata dawo da aiki daidai kamar yadda takeyi ada.

    Lokacin Da Ummi tayi Tozali da mu"azzam sai da gabanta yafadi ganin yadda idanunsa suka zurma,kallonsa tayi kafin tace,"Son meya sameka a ido ne?,naga sun chanza kalane..?"shafa sumar kansa yayi kafin yace"Babu komai Ummi,wani abu ne yafadamin a ido,dazu da zan dawo sallar Asuba.."yafada yana kallon kasa baiso ya kalli Ummi taga kwallar data taru a idanunsa.

  Bata dai yarda ba, sai ta rausayar dakai tace"Ayyah Srry muje kayi breakfast kafin kawuce kasan bansan zama da yunwa.."tafada tana riko hannunsa,dojewa yayi yaki binta waigowa tayi tana kallonsa kan tayi mgana ya rigata da cewa"Allah Ummi banajin saka komai abakina yanzu,but i promise u da na isa office zan sha tea.."Kuramai ido tayi ita duk sai taga yau ya chanzamata,bayason kallon kwayan idonta batasan dalili ba ,sai ta gyadamai kai tana fadin"Karka zauna da yunwa don Allah son u know ur condition ko.?."

gyada mata kai yayi yana damke hannunta kafin yace"ki yafemin Ummi na..."yafada idanunsa sun kawo kwallah,matse hannunsa tayi kafin tace"Nayafemaka Duniya da lahira ibrahim,da laifin daka aikatamin da gangan da wanda ka aikatamin cikin rashin sani duk na yafemaka su har abada.."jin abunda tafada yasashi fadawa jikinta kuka na neman kwacemai Rumgunesa tayi tana fadin"Shiii..insha Allahu kukan ka ya kare son kaji.."Tafada tana shafa bayanshi,kokarin dannen kukansa yake,ammh hakan ya gagarara sai da ya sakarma Ummi wacce ta razana da yadda ya kamkameta yana kuka,ammh sai tayi la"akari da abunda yafaru,ta hau lallashinsa da bashi baki,har yayi shuru,ita da kanta ta rakasa har bakin mota ta budemai ya shiga kafin Tarufe tana mai addu'an adawo lafiya har motarsu ta fice daga gidan.

Suna Fita mu"azzam ya Runtse ido yana fadin"Ki yafemin Ummina..."yafada wasu zafafan hawaye na zubomasa kafin ya sanya hannu ya share basuyi wani nisa ba ya umarci Ushe daya paka motar cikin mamaki ya samu waje yayi parking fitowa mu"azzam yayi tare da briefcase din dake hannunsa ya mikama ushe wata marar takarda yana fadin"gida zaka koma,ka kaima Ummi wannan takardan, na manta ban bata ba kafin mu Fito,kada kadamu dani zan hau Taxi na karisa.."yafada cikin bada Umarni.

   Ushe da mamaki ya sandarar dashi don tunda yake tuka yallabai haka bata taba Faruwa ba, ko mantuwa yayi sai dai ya maidosa ya dauko,ammh yau gabadaya yallabai ya chanza kamar wani bakon al"amari keson Faruwa dashi,Jikinsa a sanyaye ya karba yana fadin"Ammh yallabai daka bari na dawo sai mu karisa tare.."hannu mu"azzam yadagamai da cewa"Karka damu zan karisa,kai dai kayi hanzarin kaima Ummi sakon dana baka.."
Chapter 42 · 0% Book details