← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 82

Sashe 31

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fita direct dakin zahirah ya nufa bata afalo,cikin bedroom din ya shiga ya isketa kwance kan sallaya tayi barci harda abayan data gama sallah,tsausayinta ya kamashi ya isa gareta ya ciccibota ya maidata bisa gado ya kuma zare mata hijabin jikinta,sai asanan ya lura yadda lebenta ya kumbura daga sama da hannu yasa yana shafa gun,ko kaffara bazai yi ba aikin Ummi ne,lokaci na farko dayaji tsanar wani shashe na halin Ummi haurowa gadon yayi yakara ciccibota ya azata bisa jikinsa bakinsa ya sanya bisa leben nata yana zagayo harshensa akai yana mata wasa dashi,cikin barcinta taji kamshin Turarensa,tana bude ido taci karo da Fuskarsa dab datata,yana xagaye harshensa wajen daya dan kumbura,karaf suka hada ido,cikin fitan hayyaci tayo rimi ta afkamishi tana sakin marayan kuka,rikota yayi yana kara kamkameta lokaci daya yana shafa bayanta alamar lallashi.

Ajiyar zuciya tafara saukewa kafin yadagota yana kallon kwayar idonta yace"Am srry kinji...Allah ya baki ikom cinye wannan jarabawan my hirah.."Yafada yana share mata hawaye,dan murmusawa tayi kafin tace"Amin tare dani kai ya mu"azzam domin duk abunda ya sameni ya sameka ne..'"Kara rikota yayi yana fadin"Sosaima my Hirah duka hakurin namu ne wlh,tunda Ummi dolenmu ce dukkanmu.."Yafada yana zarcewa wata tashar,tuni ta sakarmai jiki suka fara ya mutsa juna,cikin lokaci kadan suka fita hayyacinsu ganin Mu"azzam na kokarim cire mata zanin dake jikinta ne yasa tayi saurin dakatar dashi tana fadin"Ya mu"azzam...U..Ummi.Fa na nan"Tafada cikin sarkewan Numfashi,kara rikota yayi kafin yace cikin sarkewan Numfashi.."Um..mi..Ta riga data kw..anta.."yafada bayan ya zare mata zanin lokaci daya ya mirginata tadawo kasansa,kafin cikin hanzari ya fara raba kansa da kayan jikinsa,fadi yake"Tallabeni Hirata wlh ina cike da Bukatar ki.."Jin haka yasa ta rikesa gam ta hau bashi hadin kai kafin kace me, komai yacigaba d Kamkama cikin Farinciki da Annushuwa,ita kuma Ummi tana chan tana barci harda minshari.

..Washegari daya dawo sallar asuba dakinsa yakoma don ya kimtsa saboda baya son ma Ummi tafara fahimtar wani abu,Ummi kuwa dama da wuri ta tashi bakwai nayi ta isa ga shashen Mu"azzam wanda yayi daidai da shiga zahirah dakin nasa kenan,zata wuce mkranta shine wai bazata iya wucewa ba sai ta gansa,ta shiga kenan yana tsaye yana kokarin daura tie dinsa,da hanzari ta ijiye School bag dinta ta isa garesa ta amsa tana fadin"Gud mrning.."mrning how are u? yafada yana kallonta mirmishi tayi kafin ta rausayar dakai tace"am Fine ZUMANA.."Kur yayi mata da ido lokacin datake dage tana kokarin daura masa tie din yace cikin kasala"mekikace hirah,plz sake fada naji.."Sunne kanta zatayi yayi saurin taranta da cewa"No plz kisake fada indai kina son farin cikina.."ganin yadda ya marairaice,yasa tasake maimata masa ahankali ,rumgumeta yayi yana fadin"Da gaske ni zumanki ne,da gaske ina baki zuma?yafada yana kokarin su hada ido taki yarda suna cikin wannan yanayin ne,sukaji sallaman Ummi daga falo cikin Rudewa zahirah ta kwace kanta tana fadin"Ummi.."Tafada tana zaro ido.

Shima cikin rudewan yake shiyasa yakasa mata mgana jin takowar Ummi zuwa bedroom din ne,yasa yayi saurin Fizgan hannu Zahirah ya turata tiolet ya rufe kenan Ummi na shigowa ganin yadda yake zufa alamar ba gaskiya yasa tayi tsam da rai tana binsa da kallo,kakaro murmishi yayi yana bin kansa da kallo yana so ya mazaye saboda sanin halin Ummi na gani har hanji,yace"Gud mrning Ummu Ibrahim.."Yafada cikin son nuna bakomai.

Takowa Ummo tayi zuwa gabanshi tana kallonsa kan tace"Lafiyanka kalau kuwa.."? tafada idonta akanshi,mirmishi yayi mata yana fadin"Lafiya mekika gani hala Ummi? yafada kanshi tsaye shima yana kallonta kur tamai da ido kafin tafara bin ko"ina na bedroom din da kallo,shima ganin haka yasa yabi iinda takebi da kallo,karaf idanunsa suka sauka kan jakan mkrantan Zahirah gabansa ya buga dam..Yafadi yasan in Ummi taga wannan jakar wlh yau sai yagayama aya zaginta..Saurin shan gaban Ummi yayi tare da riko hannunta yana fadin"Oya Ummi muje muyi taking breakfast zan,mkra"Yafada lokaci daya yana jan hannunta,bata da yadda zatayi illa bin bayansa ammh zuciyarta bata bata ba.

Ko a Dinning din ma tana lura dashi duk hankalinsa ba"a kwance yake ba,ta tambayeshi yace babu komai,dole ta sakamai ido,sama,sama yakarya yayi mata sallama ya fice,agaban idonta suka fice daga gidan shida ushe,shiyasa takoma cikin falon saboda rashin yardan da batayi ba yasa takara komawa dakin Mu"azzam din,takara duddubawa bata ga komai zuciyarta dai duk da haka bai bata ba,harda su bude buden wardrope tayi ammh bata ga komai ba dole ta fice.

Itako Zahirah tana cikin tiolet ko"ina na jikinta na rawa tana jin Fitansu shine ta sababo ta fito ta dauki jakarta kenan takarajin motsin dawowar Ummi Shine takara rumtuma tiolet din aguje,tana jin sanda Ummi ta shigo tana bude buden wardrope,fitsari sai daya cikamata mata mara dataji,takunta akusa da bayin,kamkame jikinta tayi tana toshe bakinta da hannunta saboda kada kukan datake boyewa ya bayyana,cikin ikon Allah tafice bata duba bayin ba,ajiyar zuciya ta sauke kafin tahau share hawayenta.

Shiko Mu"azzam suna fita yasa ushe pakawa,sai da yadan bata lokaci kana ya fito daga motan yadawo gidan,sai da yaleka falon yaga ba Ummi kana yayi zuruf ya shige dakinshi,sauri sauri ya shiga ciki ya burma tiolet din wanda zahirah sai da taja baya ta zata ummi ce,sai taga mu"azzam,hannun ya sanya abakinshi yana fadin"Shiii..." da hannu ya yafitota ta kariso garesa yakamo hannunta suna tafiya suna sanda,kamar wasu marasa gaskiya sai da yaleko falo baiga Ummi ba,kuma ya duba samanta bata kana suka fito suna sanda,suna gabda ficewa ne sukaji takun Ummi tana kiran Uwani,ai daga mu"azzam din har zahirah a tamanin suka fice waje,basu tsaya ko"ina ba sai da suka danganta da waje,Allah yasa bakowa aharaban gidan harta sani,kila ya zagaya ne,da sunyi abun kunya.

Sai da suka shiga mota ushe yaja suka wuce kana suka kalli juna suna sakin ajiyar zuciya atare lokaci daya suna kuma kwashe da dariya harda tafawa,ushe dake gaba sai da yadan waiwayo yana mamakin oga da kansa harda kashewa,lalle duniya tama yallabai Dadi.

_*Kuyi hakuri da yadda kuke samu ba yawa,am mana haihuwa ne,ASMA"U M YUSUF( Janaf A2) ta sauka tasamu bby girl Halimatus sa"adiya(Ihsin bby)Muna bukatar addu"arku daga bakunan ku masu albarka*_

*Comment*
*Share*
*Vote*

*#Intelligent writer"s#*
*#Uwar mijina..#*
*#JANAF FANS#*❤❤
[18/08, 14:18] 80k: *🌺UWAR MIJINA..!*🌺
_(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tare da biyayyah mai tsanani)_

*Alkalamin:JANAF*
*Wattpad:Janafnancy*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*Intelligent writer's Asso*✏

*NOT EDITED*⚒

*NO 20*

Har suka kai mkrantar su zahirah suna ta dariyan gudun da suka kwasa sai sun tuna sukara tintsire da dariya,mu"azzam yace"Ya"yan zamani kenan,tabbas ko taga yayan zamani wa"inda suka fita wayau da dubara.

Har cikin haraban mkrantar suka kaita kana Ushe yajuya da yallabai,kamar kullum Asma"u na kofar ajinsu tana jiranta Rumgume juna sukayi suna murnan ganin juna,wanda cikin kwanakin na Asma"u na mamakin kibar da zahirah ke mulkawa,ga haske datake karawa,sai ta danganta hakan,da hutune kawai tasamu da chajin manshafawa,ashe bata sani ba kawartata tajin abunda ita bata taba ji bane,ma"ana Da Namiji.

Tabbas Zahirah da mu"azzam sun zage sun Nuna ma Ummi in ita Uwar zamani ne to,suma ya"yan zamani ne masu amfani da kwakwalwarsu kansu wajen aikata abu,Tuni suke kife Ummi ta baibai Tunda dai tana takura musu da rana wani lokacin daga mkranta yake zuwa ya dauketa suwuce wani gidansa dake jabi wanda ko Ummi batasan da gidan ba,don bai dade da siyan gidan ba,suje sai la"asar kana ya maidota gida ya ijiyeta bakin get yakoma,su ushe suna ganin Abunda kefaruwa,suma dadi sukeji ganin yallabai cikin walwalarsa,wani lokacin kuma su karime ke musu gadin Ummi in ya shiga dakin Zahirah,kai ta ko"ina suna da masu lura da ita,tana cikin gidan suke kwana daki daya manne da juna ammh bata sani ba,kuma bata taba lura ba saboda da taku sukeyi,zahirah tuni itama mu"azzam yafara ciremata tsoron Ummi aranta,itama tasan hanyar layance ma Ummi sak wani lokacin Ummi na falo zata sababa ta shige dakin Mu"azzam duk bata lura ba,akwai kuma ranar data dako sammako ranar kuma zahirah adakin mu"azzam ta kwana jin shigowarta kawai sukayi lokacin zahirah na bakin madubi itada Mu"azzam sun fito wanka bayan sungama farantama juna rai,tana tsaye daga ita sai towel tana ma kansa cumbing suna hira sai shigowar Ummi sukaji aiko da hanzari Zahirah tashige cikin wardrope tana makyarkyata,Ummi data ga wulgawar mutum kamar amafarki tace ma mu"azzam waye taga kamar yayi wajen wardrope basarwa yayi yace mata shine fa,don babu kowa adakin data dage itafa taga kamar mutum ,mutum din kamar mace don taga bakin gashi bari ta duba tagani ganin da gaske take sai ta duba,kawai sai ya duke mata yana fadin wayyo cikinsa da rawan jiki tayo kansa tana masa sannu,to ranar da ciwo ya cecesa ammh fa zahirah ta zauni cikin wardrope din don sai da ummi tadade adakin na Mu"azzam kan takoma dakinta.

Aiko zahirah tasha dariya wajen mu"azzam sanda ta fito duk ta hada zufa,ita kanta dariyan take sunayi suna kyalkyatawa,suna hada jiki kamar wasu yara basu ma tunanin Ummi ta kara shigowa ta kamasu.

*After 4 month*

Abubuwa dadama sunfaru cikin wadannan watanin ciki harda Kamallah jarabawan su zahirah na Ss1 suka fada SS2,alokacin duk wanda yasan zahirah indan yaganta bazai taba shaidata ba saboda yadda tayi kiba ta cika sosai tazama mace shikanshi mu"azzam mamakin girmanta yake saboda sanin sadda aka kawota kamar kara,ba laifi yanzu takanyi waya da gida chan maiduguri ta wayar mu"azzam harta da baffa da yakura suna yawan mgana,kullum kuma yakura ta tambayeta game da zamansu da Ummi cewa take babu komai saboda mu"azzam bazata so ta karya alqawarin dake tsakaninsu ba,kuma ita bata da burin tadama iyayanta hankali,shiyasa kullum Zaman lafiya take shaida musu da alkahiri ya mu"azzam gareta,domin aboyen nan babu abunda baya mata baya tauyeta duk wani hakkinsa yana kokarin saukewa,Babu abunda zatacemai sai godiya tareda godema ma Allah daya mallakamata shi a matsayin miji gareta.
Chapter 31 · 0% Book details