← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 82

Sashe 25

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Amkranta sunyi kamar yadda suka saba Da Asma"u har aka tashi gida,tare suka fito har bakin get kowacce na tsimarin jiran mai daukanta,shuru shuru babu wanda yazo sai chan sai ga direban Asma"u yazo tafiya da ita,tayi tayi Zahirah tazo sufara kaita gida taki yarda tace tabari itama yanzu za"a zo daukan nata,saboda haka yasa Asma"u taki tafiya ta tsaya jiran Wanda zai dauki Zahirah ammh fiye da minti talatin babu omo babu labari,dole tasa Zahirah bin Asma"u duk da ranta baimata, dadi ba,ammh bataso Asma"u ta zargi wani abu ne,Suna mikawa Asma"u tacema zahirah"Tunda dai yau gaki besty Allah sai kin karisa gida kingaida Mami.."Jin haka yasa Zahirah ta rude taso tayi gaddama Ammh Asma"u ta bata Fuska dole tayarda,ammah akasan Ranta duk zuciyarta babu dadi,ga gabanta dake faduwa.

A asoko road Gidansu Asma"u yake,wanda Sai Da zahirah ta saki baki da hanci tana kallon aljannar duniya domin gidansu mu'azzam ba gida bane,akan tsaruwa da haduwa na gidansu Asma"u,Zahirah bataso zama ba ammh Asma"u ta matsa harsai sukaji abinci sukayi sallah,mami kuwa taji dadin zuwan zahirah ta rumgumota tana sakamata albarka,dazata tafi Mami ta cikamata leda da kayan kwalliya na kamfanin MAKARI harda Atamfanta Super wax,da farko Zahirah kin amsa tayi,Asma"u ce ta amshi kayan tana Hararan zahirah,wacce taketa zubama mami,godiya tana amsawa da Amin.

  Tare da Asma"un suka koma zata rakata gida,wanda ko amotan Asma"u keta zencenta ammh ita zuciyanta na gida,illai suna zuwa Suka zuba hon Sani maigadi na wangale get sukafara cin karo da mu"azzam yana kai da kawo hannunsa goye abayansa,yana sanye da riga da wando na kamfanin Armani black and white,jin hon din mota yasa ya zurama get din ido azatonshima Ushe ne,sai yaga wata bakar accord tasawo kai cikin gida Abunda ya dauremai kai ganin zahirah ta fito daga motan ita da wata yarinya,daure fuska yayi yana jifanta dawani kallo wanda sai da zahirah taji kafafunta sun kasa daukanta,lura da yadda zahirah ta rude ne yasa Asma"u ta riko hannunta tana fadin"Shine broda dinki din nan.."?gyada mata kai kawai Zahirah tayi kanta nakasa.

    karisawa,sukayi Dan dukawa Asma"u tayi tana fadin"Ina wuni.."Amsawa yayi idonshi na kan zahirah kafin yace"Wacece ke? kuma daga ina kuke.."Yafada cikin bacin rai,Cikin dakiya Asma"u tashiga koramai jawabin abunda yafaru ta kareshe da cewa"Kayi hakuri wlh ba da gangan nadauketa mukaje gidanmu ba,naga ba"azo daukanta bane."Tafada tana mtse hannun zahirah wacce kanta ke duke taki ko dagowa.

Ajiyar zuciya ya sauke,kafin yace"it ok,ammh karku sake irin wannan,saboda kun tadamana da hankali,tunda ita ba ko"ina tasani ba"Yafada fushinsa na sauka ,Asma"u tace"Insha Allahu bazamu sake ba..."gyada kai yayi kafin yace"Madallah babu komai.."zahirah dai kanta na kasa duk kokarin mu"azzam nasu hada ido bai samu dama ba har suka shige ciki,Zahirah ta godema Allah da bata tarar da Ummi afalo ba,har suka shiga cikin dakinta,Asma"u bata wani zauna ba,illah zahirah tafita takiramata su karime tana nunamusu Asma"unta suka gaisa cikin sakin Fuska,da Asma"u ta tambayeta ina goggonta take,karya Zahirah tayimata da cewa bata nan,Asma"u bata kawo komai ba tace"In takara dawowa sa gaisa da ita..,Bata wani jima ba tayima Zahirah sallama wacce ta rakota har gun mota kafin takoma ciki,bata dai kara saka mu"azzam a ido ba har dare.

Shiko Mu"azzam sam ya manta da zahirah ma saboda ya aiki Ushe kuma bai dawo da wuri ba,sai da lokaci yaja,kana yatuna da ita,koda ushe yaje mkrantan babu kowa,kuma ya tambaya sukace gaskiya basu da masaniya sukam,dole ya dawo yafadama Mu"azzam wanda jin haka yasa hankalinshi yatashi matuka tunaninsa kada yar mutane tazo ta bace ya shiga uku,ina tasani agarin Abuja,Kara tura ushe yayi kan ya dudduba kan hanya ko Tafara takowa akasa,to yatafin ne baidawo ba suka shigo,Ummi kuwa duk wainar da"aka toya tana dakinta bata sani ba,wardrope dinta take gyarawa tun safe shiyasa ba wanda ma yaji Duriyanta ko lunch dinta ma sama,aka hauramata dashi domin yau sarautarta ta motsa ne,Mu"azzam ya godema Allah da haka yafaru,domin bayason Tijaran Ummi sam.

******-

Yau kimamin kwana biyun da faruwan Haka,Ammah mu"azzam bai kara waiwayarta ba,taci karo dashi sau biyu tana gaisheshi yana amsawa adakile,kuma fuskarsa,babu Annuri ko kadan,Tuni zahirah tasha jinin jikinta,takuma fahimci Mu"azzam din Fushi yake da ita tun laifin Ranar nan,Tana so tabashi hakuri kuma bata samu dama ba,don akwanakin nan Ummi sai takai goma afalo bata haura ba sama,shiyasa babu halin zuwa bashi hakuri,tunda ba zuwa dakinta yakeyi ba yanzu yana Fushi da ita.

*MAFARIN KOMAI*

******

#*Soyayyah*

Ranar jumma"a gidan suka tashi da haihuwar zulaika matar Shureim wacce akama aiki a asibitin Chika dake zaria,ga hajiya jikin sai a hankali,dole Ummi ta shirya Aranar Ushe ya wuce da ita bayan yakai zahirah mkranta,wacce batason wainar da"ake toyawaba sai da tadawo kana su karime ke fadamata,Tsalle tayi itakadai adaki tana murna domin karime tace mata,kila Ummi ma tafi sati don ta debi kaya da yawa,Ran Zahirah fes,Ranar Wuni tayi walwalarta wanda ko malaminta dayazo yaga alama domin Karatun nasu ma na yau na dabam ne,haka take sakin kira"anta cikin Annushuwa,kamar babu abunda ke damunta.

   Karfe 8:00pm taji shigowar mota tasan kuma ya Mu"azzam ne,dama already tayi wanka cikin wasu riga da wando wanda cikin siyayyar da yayimata ne,red and black sai ta sanya mayafi R&S karami ta yane kanta dashi bayan tafeshe jikinta da Turare cikin wanda Mami ta bata ne,bayan kuma ta saka humranta wanda Su yakura suka zomata dashi,wani bakin flat shoe ta saka,ta fito tana Baza kamshi,abun mamaki shashen Mu"azzam kai tsaye ta nufa ranta babu ko fargaba.

  Kofar falon tana budene, tana turawa ta bude,falon babu kowa tsint ammh ko"ina sai tashin kamshi yake tsaf tsaf kamar ba dakin Namiji ba bedroom din ta nufa ta sanya hannu tayi knooking daga chan bangaren Mu"azzam da fitowarsa wanka kenan yace"yes come in.."da sallamarta ta shigo bayan ta turo kofan ahankali,tana dagowa karaf suka hada ido,tsuramata ido yayi yana kallonta sama da kasa,aransa yana fadin"Sarki ya tabbata ga Allah shugaban halittun duniya.

  Itako kunyane yakamata ganin yadda rigar wankan ya damesa har yana fitar da surar jikinsa,kirjinsa kuwa abude gargasa tayi kwance luf ruwa na diga ajikinsa,sunkuyar dakai tayi tanajin kamar ta juya,ganin haka yasa yayi Fuska kawai ya wuce gaban dressing mirror dinshi yana kokarin shafamai yayi kamar baisan da tsayuwarta agun ba.

*Comment and vote,share*

*One luv Janafty Fans*

[18/08, 14:18] 80k: *🌺UWAR MIJINA..!*🌺
   _(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tare da biyayyah mai tsanani)_

      *Alkalamin:JANAF*
      *Wattpad:Janafnancy*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*Intelligent writer's Asso*✏

_*I Dedicated dis page to u My Sisi of life...AISHA ALTO...,Soyayyarki gareni mai girmace,kaunarki gareni Allah ne kadai yasan iyakarta...Hakika kin zamo wani jigo na rayuwata,ina godiya da kulawanki agareni Janaf tafada kuma takara fada,AISHA ALTO KINA BURGENI*_💝

*NOT EDITED*⚒

             *NO 16*

     Kusa da sit din,wata yar budurwa aka ijiyeta wacce ashekaru bazata wuce sa"ar Zahirah ba,mirmishi ta sakarmata bayan Teacher nasu ya gabatar da ita amtsayin sabuwar Dalibarsu,itama zahirah mirmishin ta maida mata murna ya cikata na ganinta cikin sa"anninta da sunan daukan karatu,farincikinta yakasa boyuwa har ya bayyana akan Fuskarta,koda tazo Maths akeyi dayake double period ne,shiyasa ana kammallawa aka fita break.

  Kowa yafice sai Zahirah kadai ke zaune tana raba,ido yarinyar data mata mirmishi ita tatashi tazo har sit dinta tana fadin"Assalamu Alaiki yar"uwa.."Tafada tana zama kusa da ita,Zahirah tadago tana kallonta lokaci daya take amsa sallaman nata"Amin wa"alaikas salam.."Ta amsa cikin sakin Fuska hannu ta mika mata tana fadin"My Name is *ASMA"U GADDAFI NURA* daya daga cikin daliba ta Nurul bayyah"Tafada tana mata mirmishi cikin Farinciki zahirah ta mikamata hannu suka sarke tana fadin"My Name is *ZAHIIRAH ABUBAKAR BAHGANA* Naji dadin haduwa dake Asma"u"

   Hannunsu rike da juna suna mirmishi Asma"u tace"Nima haka Zahirah..."Atare suka kalli juna suka murmusa daganan kowacce tayi shuru sai chan Asma"u ta kalleta tana fadin'"Bazaki Fita break bane.."Gyada mata kai kawai zahirah tayi Ok kawai Asma"u tace tana tashi,sit dinta taje ta bude jakanta ta dauko wani katon biccuit da Madarar holladian tazo ta kawoma Zahirah tana fadin"Nima bancika fita break ba,komai nake bukata nakan zo dashi daga gidane,so muci wannan.."Kallonta zahirah tayi tana ayyana kirkinta mirmishi tayi zatayi mgana Asma"u ta marairaice tana fadin"Plz Besty karki ce A"a don Allah.."Ganin yadda tayi yasa zahirah takasa mata musu,nan sukaci biccuit din suna korawa da madarar holandian din,har suka koshi,hira suka cigaba dayi Duk da Asma"u ce keta hiranta,ita daga Umh sai A"a.

  Suna zaune aka dawo aji sai Asma"u takoma gun zamanta,koda english Teacher ya shigo maida hankalinsu sukayi kansu harda zahirah wacce taga bambamci sosai ta fanni da dama da mkrantar garinsu,dayake tana son Abun aranta Tuni ta cire komai ta maida hankalinta kan Abunda ake koya musu,ahaka har aka tashesu,koda aka tashi tare suka fito aji ita Da Asma"u wacce ke rike da hannunta kam,har bakin get din school inda Direban Asma"un ke jiranta,Haduwar farko Asma"u tayima Zahirah tayin shiga motarsu su kaita gida ammh Zahirah tace itama za"a zo daukanta ba yadda ta iya illa ta shiga motar direba yaja tana dagama Zahirah hannu itama tana dagamata,basu dade da Tafiya ba sai ga Ushe,wanda daman Mu"azzam yafadamata shi zai dunga zuwa daukanta in an tashesu.

   Cike da Murna Zahirah ta shigo falon tana kwalama karime kira da"Mama..Na daw..."Kalamanta sun makale ne lokacin dataci karo Da Ummi,zaune tana kallonta,,tuni jikinta yafara rawa saboda tsoro durkushewa tayi bakinta na rawa,tace"Ina..Y..Ni Ummi.."Tafada tana kafta ido.

    Wani dirty look Ummi ta watsa mata tana mamakin yadda yarinyar tayi wani kyau da ita,wato tasamu hutu ko,tabe baki tayi kafin ta kauda kai ko mgana,ganin haka yasa  zahirah mikewa jiki asanyaye ta karisa dakinta,Da kallo Ummi tabita tana tsinema Shettima da Fadi,domin su suka cuceta.

     Tana shiga daki,ta cire Uniform din nata tafada tiolet tayi wanka tazo tayi sallah,tana nan zaune Sai ga karime ta shigomata da kulan abinci tana mata barka da dawowa,cikin farinciki zahirah ta rumgume Karime tana murna nan fa ta zauna tana ta bata lbrin mkranta,harda lbrin Asma"u Karime taji dadi aranta ganin yadda zahirah take cikin farinciki mara misaltuwa Ai su karime sunsha Hiran mkranta kamar ba gobe...
Chapter 25 · 0% Book details