← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 45

Sashe 9

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kur tayi mashi da idanuwan ta tace don Allah inason in ga safwan yayanah👏.dafa kanta yayi yana murmushi yace "kiyi hakuri kanwata saboda shima safwan din kusan kullum abinda nake fama dashi kenan,wai yana
son ya ganki,idan ba don ardo ba ni da tuni na kaiki gareshi,shi yasa nake ta baki hakuri.

Love you sis 😘
08033481518
[4/8, 10:25 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

13

I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all 😘😘

Sodangi tayi kasa da idanuwanta,sauran hawayen dake ciki suka ida zubowa ta rufe idanun.

Yar karamar ajiyar zuciya tayi ta sake bude idanuwan ta kalli dan uwanta sadah tace,"ban san irin yanda nakejinsa ba araina,saboda idan ina tare dashi nakanji ni acikin farin ciki da walwala,kuma rashinshi yana sa inji gaba daya wani irin ciwo ya kamani wanda baida magani har sai na ganshi,don ko yanzu irin abinda nakeji kenan yaya sadah shi yasa kaji nace maka inason in ganshi."

Sadah yayi shiru saboda gaba daya sodangi tasa jikin shi ya mutu da tunanin halin daya ganta aciki,don haka numfasawa yayi yace mata,"toh kiyi shiru ki daina zubar da hawayenki,insha Allahu zanyi bakin kokari inga kinganshi gobe da maraice,"bude idanuwanshi yayi sosai ya kalleta yaci gaba da cewa,"amma da sharadi guda sodangi."

Goge hawayen dake fuskarta tayi tana murmushi tace,"minene shi yayanah? Ka fada mani ni kuma zan zamo mai bin umurninka."sadah ya kalleta yayi murmushi, saboda yanda yaga duk ta rude acikin dan kankanen lokaci yace,"zan kaiki ki ganshi amma kuma bazakiyi magana dashi ba."

Dan jim tayi saboda ba haka taso ba,amma tunda bata da wani zabi daya wuce tabi umurnin yayanta dole tasa ta amince ta jinjina kanta tace,"toh na amince yayanah."murmushi yayi yace,"tunda kin amince sai sharadi na biyu,ki saki jikinki kici gaba da walwalah kamar kowa,kuma abinci ma daga yanzu ki daina barin har sai ance kici,ni kuma idan har naga wannan sauyin zan cika maki nawa alkawarin."

Dariya sodangi tayi ta kalleshi fuska a sake tace,"nima zanyi duk abinda ka umurceni da inyi insha Allahu.
Tundaga lokacin sodangi ta saki jikinta da sauran danginta taci gaba da hidimarta kamar yanda ta daukarwa yayanta alkawari.washe gari kuwa da safe komai ya kara canzawa daga walwalarta,domin har yan biki suka fara mamakin canzawar da tayi cikin dan kankanin lokaci.

Ayau sadah bai dauki wani lokaci mai tsawo ba a wajen kiwo ya dawo gida,wanka yayi ya canza sannan suka fakaici idanun yan biki shi da sodangi suka bar gidan.

Gidan da safwan yake ginawa ko acikin birni sai haka,saboda idan ka ga yanda aka tsarashi dole abin ya burgeka,domin babu abinda babu na more rayuwa da jin dadi.

Wani wuri suka samu ya nunawa sodangi yace ta tsaya nan saboda zata iya haggen shi,sannan shi kuma ya nufi gidan kanshi tsaye,bai shiga ba amma sai yace ma wani cikin ma aikatan yayi mashi magana dashi.

Jim kadan yana nan atsaye safwan ya iso fuska asake ya mika masa hannu suka gaisa.
Daga inda sodangi take labe ta hango safwan,ai kuwa wani dadi ne ya kamata taji kamar ta ida isa wajen shi,amma sam bata da wannan damar,ganinshi tayi yayi kiba ya kara haske acikin 'yan kwanakin da bata ganshi ba.
Da sauri ta kalli jikinta taga yanda ta rame duk ta ya mutse,sai taji duk ta tsani yanda ta koma, saboda idan da safwan zai ganta da wannan ramar wata kila bazai kara son ganin ta ba,kara makalewa tayi a inda take ta buye sosai ta zuba masu ido.

Shi kanshi sadah ayanda yaga safwan ayau sai da gabanshi ya fadi,saboda kamalarshi da kimarsa da kwarjininsa duk sun bayyana,sannan ga wani tsananin kyau da yayi tamkar wani balarabe.

Safwan ya kauda kai daga kallon da yakeyi mashi,shi kuma safwan yayi murmushi yace,"yaya sadah,"watau sunan dayaji sodangi na kiranshi dashi kenan,saboda agirme yasan ya girmeshi.
Safwan yaci gaba da cewa,"ko ardo ya aiko ka awajena neh?"sadah ya furzar da iskar dake cikin bakinshi yace,ardo bai aiko ni ba,wannan zuwan kai na neh,saboda inason muyi wata mgn mai muhimmanci."
Safwan ya gyara tsayuwarshi yace,"toh ko sai mun shiga daga ciki neh?"sadah ya girgiza kanshi yace,"ba sai mun shiga ba,saboda maganar bazata dauke mu wani dogon lokaci ba."gyara tsayuwarshi yayi shima yaci gaba da cewa,"ina wani nazari akanka,shin wanne irin so kakeyiwa sodangi"?

Jin tambayar yayi tamkar saukar aradu abisa kansa,amma da yake wayayyene dan zamani sai yayi dariya yace,"yaya sadah wannan tambayar taka ta bani tsoro sosai,saboda sai naji acikin raina kamar baka yarda dani bane."
Sadah yayi dan murmushi yace,"ba ban yarda dakai bane,amma ina ganin kamar kai da ita baku dace bane,saboda kai mai kudi ne na bammaki,ita kuma talaka ce wadda bata da komai sai rufin asirin Allah."safwan yayi kasa da murya yace,"duk wannan dalilin ba zai hana in auri sodangi ba,saboda ina sonta da yawa,son da bazan iya kiyasta maka adadinshi ba.

Love you sis 😘
08033481518
[4/8, 10:25 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba Saleh daudawa

14

I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all😘😘

Safwan yayi kasa da murya yace,"duk wannan ba zai hana in auri sodangi ba,saboda ina sonta da yawa,son da bazan iya kiyasta maka adadinshi ba."sannan ya dago idanuwanshi ya kalli sadah yaci gaba da cewa,"ina so ka yarda dani yaya sadah,ni da sodangi mutuwa zata raba mu."

Sadah yayi murmushin jin dadi ya jinjina kanshi alamar yarda da abinda safwan yace ya dafa kafadarshi yace,"na yarda da kai safwan 100%but duk da haka zan kara tunasar da kai cewar,duk duniya bani da kamar sodangi,itace jini nice anta,don haka ka kula mani da ita kamar yanda ya kamata,please 👏 kada ka bari tayi kuka ta dalilinka,domin sodangi tana sonka da yawa,yawan ma bazan iya kiyasta maka shi ba don she Love's you so much.

Safwan yayi dariyar jin dadi,saboda tuni ya riga yasan da cewar sodangi tana sonshi,hannu yasa ya shafi sumarshi yana murmushi yace," kada kaji komai sadah saboda sodangi tawa ce har abadah."

Sadah ya mika mashi hannu suka kara gaisawa saboda farin cikin abinda yaji daga safwan din,sannan yayi ban kwana dashi ya juya ya fara tafiya.safwan dake tsaye yana kallonshi ya sake kiranshi dadan karfi.
Da sauri sadah ya juyo yana murmushi, sai safwan din ya matsa kusa dashi yana cewa,"mancewa nayi in tambayeka,wai miyasa ardo ya hana akawo lefen sodangi gida?"sadah yayi dan murmushi yace,"kasan mutanen mu,baka da bashin maganarsu amma su suna da taka,kuma ko yanzu wannan gidan da kake ginawa cewa sukeyi wai mun saida sodangi wajenka ne,toh bare kuma suga tulin kaya tunda mu nan ba haka mukeyi ba,kaga karshe bamu san kuma abinda zasu fada ba."

Safwan yayi dariya yace,"da ardo ya barni naso inyiwa sodangi abinda ba a tabayi wa wata yarinya ba a kauyen nan,amma ko yanzu ma ba matsala saboda na tanadar komai acikin gidanta."

Acikin farin ciki sadah ya rabu da safwan ya nufi inda sodangi take aboye ya sameta sai murmushi take.kallonta yayi shima yana murmushin yace,"hankalinki ya kwanta koh tunda kin ganshi?"sodangi ta daga mashi kai alamar eh tace," naji dadi yaya nah,amma naso ace ya ganni munyiwa juna magana."

Sadah yace,"kada ki damu,wata rana zakuyi maganar."daga kanshi yayi ya kalli yamma yaga yanda rana keta haramar yin kasa ta koma ga mahaliccinta yaci gaba da cewa,"ki tashi mu koma gida kamin a farga bamu nan su fara cigiyar mu."

Sodangi ta mike tsaye ta nufi hanyar da taga sun biyo amma zuciyarta cike da tunani kala kala,can ta gaza daurewa tace,"yaya sadah wai wannan wurin danaga safwan ya fito ina ne?"sadah yayi murmushi yace,"wata ma aikata ce ake ginawa."kada kanta kawai tayi sukaci gaba da tafiya.

Washe gari wurin karfe sha daya na safe safwan ya iso tare da kanin babanshi da wasu manyan abokanenshi,sai kuma abokanen safwan din.anyi duk yanda amusulunci ya ta nada an daura auren Sarah (sodangi) & safwan.sai alokacin sodangi tasan kowa nene mijinta,ai kuwa murna fal cike da zuciyarta,amma sai ta boye bata bayyanar da farin cikin ta ba saboda ta fahimci rashin kunyar da ake cewa tanayi,domin kwata kwata bata iya boye son da takeyiwa safwan a duk inda ta shiga shi yasa ake ganin rashin ta idonta.

Walima akayi sosai,saboda ardo ya yanka shanunsa har biyu,kuma duk abinda akeyiwa yar gata ardo sai da yayiwa sodangi,duk da safwan ya hana da yayi mata komai,amma sai da ardo yasa aka bashi wani bangare don zuba kayan sodangi daya sai mata.

Ance biki wan shagali kowar raina shi ba nashi ba,haka akayi ta kai da komowa har zuwa bayan isha I,safwan da abokananshi sukazo da motocinsu suka kwashi amarya da jama arta suka kai sabon gidan da ya gina.
Ganin cikin gidan yasa mutanen dan kauyen suka dasa surutun kyan da yayi da kuma yanda aka tsara shi.ita kuwa sodangi tunda aka kaita bata bude mayafinta ba bare taga abinda ake ta surutu akai.
Da yake taro daya sukeyi,don haka yan kai amarya da suka gama yan leke lekensu da kayancinsu aka kara kwaso su duk aka mayar dasu gidan ardo,toh anan ne labari ya kara yaduwa na irin kyan da gidan sodangi yake dashi,anan fa masoyan ardo sukayi ta Allah sam barka dayi masu addu ar zaman lafiya.

Gidan tsit yayi mata gashi duk an watse babu kowa acikinshi sai ita kadai saboda ko yar tsohuwar da ake bari ta kwana saboda washe gari da safe taje tayi masu tonon asiri safwan sai da yasa aka tafi da ita,don haka gidan babu abinda kakeji sai karar injin din daya ba dukkan gidan haske.

Tsoro ne ya fara kamata,sannan ga wani irin sanyi da dakin yayi kamar an sanya ta acikin kankara,don haka sai ta kama jikin ta kankane sai rawar dari take,domin gaba daya jikinta ke jijjiga saboda sanyi.

Safwan kuwa yana can cikin abokananshi suna tsara yanda zasu cashe adaren yau,saboda su da kansu suka hada mashi wata gaggarimar dinner da zasuyi a katsina motel,kuma zata iya daukarsu har zuwa karfe ukku na tsakar dare kamin agamata,don haka sai ya fara tunanin yanda zai zame masu ya gudu zuwa wurin matarshi ba tare da sun gane ba.
Chapter 9 · 0% Book details