← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 45

Sashe 37

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari around 10:00am safwan ya nufi wurin aikin sodangi,kai tsaye wurin Alhaji yunus ya nufa Mahaifin sameer,bayan sun gaisa Alhaji yunus sai rawar jiki yake saboda ziyarar da safwan ya kawo masu ta unexpected,shi kuwa kamewa yayi ya dora kafarshi daya bisa daya yana kadata.
Bayan ya fahimci Alhaji yunus ya samu natsuwa sai yace,"nazo ne don in daukarwa sarat Abubakar permission, saboda zatayi wata tafiya ta kwana biyu,kuma bayan nan inason kuyi transfer dinta ku mayar da ita kamfanin kasa da kasa."
Alhaji yunus jin maganar yayi kamar daga sama,saboda bai taba tunanin sodangi zata rabu da companing su ba a dan wannan lokacin,don haka sai ya dan rusuna yace,"yallabai kayi mana uzuri don Allah,ka bar mana sodangi saboda munajin dadin zama da ita kuma akwai ci gaba da muka samu adalilinta."
Safwan yadan hade ranshi yace,"just do what I say,please I dont want any complain."
Alhaji yunus yayi maza yace,"toh shikenan, yanda kace haka za ayi,kuma yaushe neh kakeso transfer din tata ta fito?"
Sameer ya mike tsaye yana wata ginshira yace,"any way,"yadan shafi kanshi sannan yaci gaba da cewa,"tun daga yau ku fara shirya ta,har zuwa ranar da zata dawo daga wannan tafiyar."
Yana gama fadar haka ya mika mashi hannu yayi mashi ban kwana,sannan ya nufi hanyar fita.
Yana fita babban yaro da sukazo tare yabi bayanshi,akan street din suka hadu da sameer shima yana shirin zuwa office din mahaifinshi.
Safwan tsayawa yayi cak inda yake har sameer ya iso inda yake,cikin rainin wayau safwan ya mika mashi hannu don su gaisa,sannan yace,"sannu da babban ma aikaci mai adalci,tunda yake daukar ma aikatanshi ya kaisu har gida don gatantasu."
Zuba mashi ido kawai sameer yayi saboda bayyi tsammanin jin haka ba Daga bakin safwan.
Shi kuwa safwan ci gaba da cewa yayi,"ina gayyatarka nan da yan kwanaki zan mayar da matata sodangi gidana,don haka muna jiranka cikin yan tayamu murna."
Shima yana gama yaba mashi maganar da yakeso ya kauce yayi tafiyarshi.
Duk abinda ya faru agaban Alhaji yunus ya akayi shi,saboda ya fito da niyyar yayiwa safwan rakiya sai ya jiyo irin zantuttukan da safwan
[4/28, 12:18 AM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

53

I dedicated this love story to my Hausa Novel group & my fans,thanks and love you all 😘😘

Yake fadawa danshi,don haka sameer yana shigowa wajenshi sai ya fahimci yanda yake ta fushi kamar afusace yake.

Alhaji yunus yayi murmushi yace,"ka zauna mana,sai wani harare harare kakeyi."
Sameer ya samu kujera ya zauna ranshi abace yana fuskantar mahaifinshi yace,"mi ya kawo safwan awannan lokacin?"
Alhaji yunus ya kada kanshi yana dariya yace,"kaji wata tambaya awajen sameer,ko ka mance mu dashi mun zama hadin gwiwa neh?to ka saurare ni sosai kaji abinda zan fada maka da kunnuwan basira,duk da ban fahimci maganar da kukeyi ba,kuma ban san abinda ya hadaku ba,toh ka bashi abinda yake so,kodon tsira da martabar wannan kamfanin."
Sameer ya bude baki zaiyi magana,Alhaji yunus ya tsayar da shi da hannu yace,"ban son musu bare gardama,kaje kawai ka zartar da abinda nace."
Sukuku sameer ya mike jikinshi asanyaye yake tafiyar tamkar wanda kwai ya fashe mawa acikin ciki ya nufi office dinshi.
Yana budewa office din ysyi tozali da fa iza akan kujera tana zaman jiranshi,don haka tana ganin shi ta zabura ta Mike tsaye tana kallonshi.
Kauda idonshi yayi daga kallonta yaja kujera ya zauna tare da kifa kanshi akan table yana mayar da ajiyar zuciya.
Fa iza tayi kasa da murya tace,"kayi hakuri sameer saboda nasan matsalarka tunda naga oga safwan yau ya shigo cikin kamfanin nan.
Dago kai yayi da sauri ya kalleta irin kallon nan na mi kika sani akai?
Fa iza ta kada mashi kai tace,"na san komai sameer,kuma na daina jin haushinka dakai da sodangi tunda duk naji ayanda kake kallona,shi yasa na shiga na fita don in fidda kaina daga tunanin da kakeyi mani."
Wayarta ta zaro ta danna mashi recording din da tayi na firar da sukayi da Hajiya Maryam,a inda ta saki baki ta fada mata tsohon sirrinta data kashe Hajiya zainab mahaifiyyarshi,tare da fada mata kudirinta na nan gaba,watau idan ta samu sameer ya auri fa iza,sai ta kashe Alhaji yunus don ta samu damar mallake sauran dukiyar daya bari shi kuma sameer su rinka juyashi yanda suke so,shima daga baya idan sukaga zai kawao masu matsala shima sai a kaudashi ya bi bayan iyayenshi.
Duk wani bakin ciki dake kwance azuciyar sameer sai da ya wanke,saboda yana ganin karshen Hjy maryam yazo,saboda lokacin daya fada cewar ita ta kashe mashi uwa cewa akayi miye shaidar shi.
Mikewa yayi da sauri,bayan ya amshi wayar ya tura duka recording din acikin wayarshi ya nufi kofar fita.
Fa iza ta kira sunashi,ya waigo cikin zafin nama tace mashi,"kabi komai ahankali sameer."
Murmushin daya aiko mata da shine taji kamar ta narke don jin dadi,sannan kalmar data biyo bayan murmushin,"kada kiji komai fa iza,saboda ayau kin fanshi kanki da kanki.sai dai na dawo."
Komawa tayi kan kujerarta ta zauna cikin farin ciki,tare dayin addu a,ya Allah ka dubi al amarina,saboda ina tsananin son sameer har karshen raina,Allah kasa ya zamo miji agareni." Tana gama addu ar ta zauna zaman jiran dawowarshi.

Shi kuwa yana fita office din Abbanshi ya koma ya kunna madhi wannan recording din yaji,gaba daya yaji wata zufa ta karyo mashi, hankalinshi yayi matukar tashi don rasa abinda zaicewa sameer yayi sai dai hawaye saboda gaba daya hankalinshi ya dawo jikinshi,matarshi ya tuna da irin tsananin son da yake mata amma tunda ta mutu bai sake tunawa da ita ba sai yau.
Mikewa yayi da sauri ya dauki wayarshi ya kira abokinshi DPO Ya fada mashi tsaf abinda ake ciki,sannan kuma ya tabbatar mashi da akwai sheda mai karfi wadda zasuyi amfani da ita wajen kamata."
Koda Alhaji yunus ya gama wayar,da kyar sameer ya kamashi suka nufi motarsu,lokaci kusan daya suka isa da yan sanda,don haka kai tsaye suka shiga suka kama Hjy maryam tare da wasu yan koranta da aka samu acikin gidan.
Hjy maryam kuwa gaba daya ta saduda,saboda dama bokanta ya fada mata duk ranar da Alhaji yunusa yasan sirrin data boye to a ranar duk wani mugun kullinta zai kare,kuma daga ranar babu abinda zatayi ya kara tasiri arayuwarta.

🍒🍒🍒🍒

Safwan kuwa tunda ya bar kamfanin su sameer dashi da babban yaro sai suka nufi unguwarsu surayya.
Kamar yanda sukayi alkawari da sodangi cewar zasuyi tafiya,ita haka ta tashi da wuri ta shirya afnan sannan ita ta shirya kanta sukayi tsaf gwanin ban sha awa,don haka su safwan suna isowa fitowa sukayi tare dayin ban kwana da ummah mahaifiyyar surayya,don ita surayyar ma bata kwana gida ba sai dai ta kira wayar sodangi tace ta fafawa ummah cewar ta wuce gidan Anty fati,koda dodangi taso ta tambayeta game da haduwar da sukayi da safwan sai tace kawai ta bari sai ta dawo zatayi mata bayani.

Fitowa tayi tana jaye da afnan,shi kuma yana ganinsu ya fito daga motar ya tarbesu,saba afnan yayi ajikinshi yana tsokanarta ita kuma tanayi mashi dariya.
Bude sit din gaba yayi kusa da babban yaro ya zaunar da afnan tare da sanya mata belt na jikin sit din motar,ita kuwa babu abinda take cewa sai,"daddy ka taho mani da ice cream dina."shi kuwa idan ta kirashi da daddy dinnan ba karamin dadi yakeji ba,don haka dama ledar tana anan gaban sit din,don haka yana budewa ya hadata da katuwar roba da dan spoon din da zata sha,shi kuma ya koma baya kusa da sodangi ya zauna,sai alokacin ya kalli sodangi ya numfasa yace,"sorry my dear,tunda kuka fito afnan ta dauki hankalina,gashi ni dake ko gaisawa bamuyi ba."
Rusunawa tayi cikin dan girmamawa ta gaisheshi,kin amsawa yayi sai hannunshi daya zira ya damko nata cikin dubara ba tare da babban yaro ya fahimci komai ba,saboda shi idan banda aikin driving babu abibda yakeyi sai dan lokaci lokaci idan afnan tayi mashi tambaya yana bata amsa.
Safwan tunda ya rike hannun sodangi bai saketa ba har saida suka kawo gidan da za su.
Sodangi ta daga idanuwanta ta kalli gidan,taga zubinshi tun awaje ma ya tsaru iyakar tsaruwa.
Safwan ne ya zuba mata ido kawai yana kallonta don yaga iyakar yabawarta akan gidan,aikuwa gaba daya hankalin sodangi ya dauku akan gidan,bama da suka shiga taga komai acikin tsari aka gina gidan,saboda kwata kwata ma gaza misalta yanda ginin gidan yake.
Safwan yana gaba shi da afnan ita kuma sodangi tana biye dasu har ya kaisu wani tankamemen falo hadadde irin wanda ya amsa sunanshi.
Wuri ya nuna masu suka zauna,shima gefen sodangin ya zauna,dago kai tayi ta kalleshi tace,"kazo nan ka zauna bazakaji kunya idan masu gidan sukazo suka samemu ahaka ba?"
Safwan yayi dariya yace,"this house is ours,ya kika ganshi?idan har bayyi ba yanzu insa azo acanza shi."
Sodangi ta kara juya idanuwanta acikin falon tayi murmushi, kuma sai ayanzu ne ta fahimci lallai gidan babu kowa sai masu aiki.
Safwan ne ya tabo kafadarta da tashi kafadar ya daga mata girar idonshi daya yace,"ya dai naji kinyi shiru,kodai bayyi ba nrh?"
Sodangi tayi murmushi gami da mikewa tsaye tace,"gida yayi kyau matuka,yanzu tunda na gani sai ka tashi ka mayar damu gida."
Bai kai ga bata amsa ba wayarshi tayi ringing yayi maza ya fiddota dama kamar kiran wayar yake jira,don haka ya dauka,daga can bangaren akayi mashi magana,amma shi baice komai ba har wayar ta tsinke.
Kallon sodangi yayi murmushi kamar wanda baida gaskiya yace,"kiyi hakuri sodangi,akwai wani abu kadan da zanyi sai inzo mu tafi,amma kamin time din afnan zoki rakani wani waje yanzun muje mu dawo kada mammy ta gaji da jiran mu.

Love you all sis😘
08033481518
[4/28, 7:13 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

54

I dedicated this love story to my Hausa Novel Group & my fans,thanks and love you all 😘😘
Chapter 37 · 0% Book details