← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 45

Sashe 45

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

zamanin.
Karar mota taji tare da bude gate din da maigadi yayi,jikinta ne ya dauki rawa ta nufi window dakinta da sauri ta leka wai ko zata ga kowanene,giccin motar kawai ta gani ya shige,amma bazata iya cewa taga na cikin motar ba,dan tsaki tayi ta koma bakin gadonta ta zauna ranta ya dan sosu tare da tunanin yanda zata yi da mutumin da bata sani.
Zamewa tayi tayi kwanciyarta akan gadon ta afka tunanin rayuwar data wuce da kuma wadda ke shirin haye mata anan gaba.
Wasu hawaye neh suka taru acikin idanuwanta,ahankali ta mayar dasu ta rufe tana mayar da numfashinta sama sama.
Wayar dakinta ce ta haw ringing har sai da ta dan tsorata saboda tunda tazo bata taba jin tayi ringing ba,mi kewa tayi jikinta duk kerma yakeyi ta nufi wayar,tana gaf da katsewa tayi sauri ta dauka.
Muryar msi aikinta taji mai kula da kitchen tace,"anty sannu da hutawa."
Sodangi ta mayar da numfashi tace,"yawwa Ramatu."
Ramatu tayi kasa da murya cikin girmamawa tace,"dama boss ne yakeson ganinki a babban falonshi."tana gama fadar haka tayi kasa da wayar ta ajiye,ita kuma sodangi kasa ajiye wayar tayi saboda fargabar data shigeta.
Cikin kasala tayi kasa da wayar ta kalli hanyar fita daga dakinta taji duk tsoro ya kamata,amma tunda tasan bata da yanda zatayi dole ta zira flat Shoes ta bi hanyar zuwa falon cikin sanyin jiki.
Kamshin daya ziyarci hancinta ne yasa tadan firgita tare da karayin sauri, zuciyarta cike da son ganin kowa nene wannan ma abocin kamshin mai yanayi dana masoyinta abin kaunarta.
Juyawa yayi ya bata baya yana kallon window dake cikin falon,zubawa flowers din da yake hagge yayi amma akasan xuciyarshi kuwa sakata kawai Yake yana kwancewa ta yanda zai iya zama da wannan amaryar tashi.
Sodangi zuba mashi idanuwa tayi,saboda gani take kamar idanuwanta ne keson yi mata gizo,saboda safwan kawai take gani cikin shigar three quarter da yar amless.
Tsaye tayi cak taci gaba da son tantanceshi,kodai angon kama yake da safwan ne,shi dai aikin kurbar lemunshi kawai yakeyi cikin takaici da bakin ciki.
Gama tantance shi tayi ta kuwa nufeshi da gudu fuskarnan tata cike da farin ciki,ga wasu hawaye da suka fara tunkudowa.
Sam bayyi aune ba sai kawai yaji ta bayanshi an rungumeshi da karfi ga kuma sheshshekar kuka anayi
Ada mutuwar tsaye yayi yanda kasan ya mutu haka ya kame,amma sautin voice din dayaji yana fita yasashi sakin cup din dake hannunshi da sauri ya kama hanunta ya juyo duk idanuwanshi awaje,aikuwa tunaninshi ya zama dai dai,saboda ganin sodangi agabanshi kuma agidanshi yasa duk ya rude ya dago fuskarta data dukun kune ajikinshi tana kuka,hada idanuwa sukayi yayi dariya tare da sakin wani ihun jin dadi ya jawota ya rungume yana cewa,"wayyo Allah sodangita,waye ya kawo mani ke don yaga karshen farin cikina?"
Sodangi tana kuka mai hade da dariya tace,"nice matarka safwan,da aka daura mana aure kusan sati biyu da suka wuce."
aikuwa yanajin haka ya dukacya sungumeta ya rungumata ajikinshi ya nufi dakinshi da ita yana cewa,"bazan iya ba sodangi,sam bazan iya jurewa ba har sai naji dumin jikinki matata rayuwata."

Sam kasa bin bayansu nayi saboda yanda safwan yasa matakan tsaro abakin kofar dakin nashi,shi yasa kawai naga ya kamata nima in hakura hakanan,amma inason readers dasuyi nazari da kansu akan abinda zai faru awannan yammaci tsakanin safwan da sodangi.

My next Novel is KARSHEN MASOYA,till we meet again my fans 😘😘😘😘😍

ALHAMDULILLAHI WABIHAMDIHI ALAKULLIHALIN
Chapter 45 · 0% Book details