← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 45

Sashe 7

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ardo ya juyo da sauri yace,"a ina ka ganta,saboda ni bukatar ganinta kawai nake."sadah ya sunkuyar da kansa kasa yace,"tana cikin dakin molasa,saboda alokacin dana dawo tare muka shigo."ardo yayi ajiyar zuciya tare da dan guntun murmushi yace,"alhamdulillahi, ni dama tunani nah ko tayi wani wajen."kamo hannun sadah yayi ya mikar dashi tsaye yaci gaba da cewa,muje muyi shirin sallar magriba."

Sadah cikin ladabi da biyayya ya mike tsaye,dayaji abinda ardo ya fada sai yaga ai da sauran lokacin magriba din,don haka sai ya dubi mahaifin nasu yace,"ardo ko kamin lokacin ya ida inje in nemo dabbobin don kada subi wata hanyar da ban."Ardo ya dafa kafadarshi yace,"ko kaje sadah bazaka gansu ba,saboda ni kaina naje jejin sau biyu,amma ban gansu ba,sai dai zuciyata tana bani sun taho sun bace hanya,na kuma san komai dare zasu dawo."don haka butoci suka dauka suka nufi kofar gida don su gabatar da alwallah,ita kuma molasa ta nufi daki da sauri wajen sodangi.

Love you sis😘
08033481518
[4/8, 10:25 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

10

I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all😘😘

Idanuwanta abude ta shiga dakin,sbd sodangi kawai takeso ta gani,amma sai taga wayam.
Mamaki ne ya kamata saboda tuni ta riga tasan halin danta sadah sam ba yaro bane mai karya,don haka sai ta yanke shawarar ta bincike dakin lungu da sako,karkashin dan karamin gadonsu ta fara lekawa,wayam ta gani,don hatta da tulin kayan data san ta ajiye suma bata gansu ba,cikin sauri ta dago tana kara karewa dakin kallo sai idanuwanta suka dira akan kayan datake nema awata kusurwa an jibgesu.
Cikin daurewar kai ta nufesu tana jawowa sai sukayi ido biyu da sodangi tana ta zare idanuwa (Masha Allahu) sai mazurai take,sannan fuskarta dauke take da tsoro da firgicin abinda zai faru da ita.

Molasa abin yaso ya bata dariya,amma sai ta gimtse fuska,dama kuma sodangi tafi tsoron molasa akan mahaifinta,saboda yafi sakar mata fuska fiye da ita,don yanzu abinda yasa har takejin tsoron haduwa dashi saboda ganin hukuncin da yakeyiwa sauran yara idan har aka kawo mashi kararsu,gashi kuma tana tsananin tsoron duka.

Molasa fuska adaure tace,"miye haka sodangi? Wane irin abu ne kikaje kikayo har yasaki tsuma haka?"sodangi haba na rawa ta fito daga cikin kayan data boye tanq cewa,"don Allah molasa kada ki tona ni,idan ardo ya yambayeki kice mashi baki ganni ba."molasa tayi murmushi tare da shinfida abinda zatayi sallah akanshi tace,"kinsan abinda ba zaiyiwu kenan ba,watau kina son inyiwa ardo karya kenan?"dan tsaki taja sannan taci gaba da cewa maza kije kiyo alwallah kamin ardon ya dawo inji abinda kikayi tunda kinki ki fada mani."tana gama fadar haka ta kabbara sallarta,ita kuma sodangi ta mike cikin sanda ta nufi waje,alwallah takeyi amma idanuwanta duka biyun sunyiwa kofar gida zuru saboda kada ardo yazo ya sameta.

Sallar tayi amma duk ba a cikin natsuwa ba saboda muryar ardo dataji atsakar gida.molasa tana gama sallar tayi addu o inta ta nufi tsakar gidan wajensu ardo,gefe ta koma tare da tsugunnawa ta gaishe da ardon sannan shi kuma sadah ya gaisheta,wannan itace dabi arsu gaba daya gidan.

Ardo yayi gyaran murya yace,"molasa ina sodangin,ko baki ganshi ba?"molasa cikin damuwa tace,"na ganshi ardo,amma kuma taki ta fada mani abinda tayi maka."

Numfasawa ardo yayi sannan ahankali yayi mata bayanin iyakar abinda ya gani,sannan yaci gaba da cewa,"yanzu abinda nake tsoro shine,ko wani dan cikin rugarnan yaga sodangi da wannan mutumin?idan har kuwa an gansu dole ne inyi mata hukunci kamar kowa"
Jin haka sadah ya dago idanuwanshi da sauri yana kallon ardo cikin firgici yace,"ardo sodangi bazata iya daukar wannan bulalar ba,kuma idan har kana tunanin ta aikata wannan laifin,to ni zan amsar mata hukuncin duk da ya hau kanta,amma yanzu inason ka bani izini inje in tambayeta iyakar abinda ta sani akan wannan mutumin."

Ardo ya zubawa sadah ido yana kallonshi cikin tausayi yace,sadah sai dai kayi hakuri,domin nima komai zanyi bada son raina zanyi shi ba,don dai banda yanda zanyi ne shiyasa,amma yanzu kaje wurinta kaji abinda zata fada maka."

Sadah yamike jiki asanyaye ya nufi dakin molasa,yana shiga sodangi ta taso jiki yana rawa,saboda duk tanajin abinda yake faruwa.

Hannunshi ta rike ta mau tana zubar da hawaye tare da girgiza kanta alamar batayi komai.ji yayi tausayinta ya kamashi,don haka shima kama hannun nata yayi ya zaunar da ita akan gadon molasa,sannan shima ya zauna gefenta yana kallonta.

Numfasawa yayi sannan ya kira sunanta,"sodangi."da sauri ta dago kanta ta kalleshi tare da amsawa.don haka sai yaci gaba da cewa,"a ina kika hadu da mutumin nan?"

Sodangi bata boye mashi ba duk ta fada mashi har abinda ta fada mashi a dazu.shiru kawai yayi yana kallonta har ta gama sannan ya kada kanshi yace,"ya taba cewa yana sonki neh?"

Sodangi tayi shiru tana tunani,can ta dago kanta tace,"eh ya taba cewa,don har yana cewa yana so muyi rayuwa tare." Sadah ya kara zuba mata ido,saboda yaro ne mai hankali da fahimta,don haka sai ya sake tambayarta,bayan kama hannunki da kikace yayi sai kuma mi?"
Sodangi tayi kuri tana kallon shi ta rasa abinda zata fada,amma dayake tasan tsakaninta da dan uwanta akwai shakuwa kuma babu abinda yake boye mata na rayuwarshi,don haka sai tayi kasa da idanuwan ta cikin jin kunya tace," yana rungumeni ajikinshi don har yana cewa turarenah yanayi mashi kamshi mai dadi....."
Bata karasa ba taji ya kama kunnenta da karfi ya murda cikin bacin rai yace,"kinji kunya sodangi, tunda har kin mance da Martabar gidanku kuma kinci amanar yarenki watau fullanci,domin duk inda bafullace yake yana da gadon kunya,amma ke na lura kin saki taki kare ya dauka."

Wani uban tsaki yaja sannan ya kara fisgo kunnen da karfi,ita kuma zani tasa ta toshe bakinta da karfi tana kuka amma bata son iyayenta suji,saboda kara dan uwanta ya hukunta ta da iyayenta suji abinda tayi.sai da ya gama punishing dinta ta hanyqr murdar mata kunne sannan ya saketa tare da mikewa yayi waje.

Kusa da ardo ya sake zama,amma baice komai ba har saida ardo ya zunguroshi yace,"ya mukaji kayi shiru sadah?kodai ta aikata abinda muke tunani?"sadah yayi wani dan guntun murmushi yace,"ardo bata aikata ba,amma shawarar da zan baka shine kayi gaggawar aurar da sodangi domin yaron dake zuwa wurinta ba irin ajinta bane,don haka idan har kun samu ganinshi ku tambayeshi idan aurenta zaiyi,idan yace a a toh ku nemi wani ku batashi."

Shiru ardo da molasa sukayi suna kallon sadah kawai sbd dukkansu zuciyarsu ta basu wani abu,amma sadah ya boye masune.don haka babu wani tunani da ardo yayi ya dauki shawarar dansu,dai dai zaiyi mgn sai yaji kukan shanunsu suna wucewa garkensu,gaba daya suka mike tsaye cikin farin ciki,sallama kuma sukaji abakin kofa,don haka sadah da sauri ya nufi wajen yana amsawa.

Bay san mai sallamar ba,amma duk da haka sai ya bashi hannu suka gaisa yace,"nan ne gidan ardo?"ardon ne ya karaso dai dai sadah yana cewa,"eh nan neh."ardo yana karasowa shima ya mika mashi hannu don su gaisa,amma sai bakon yaki yayi sauri ya zube kasa yana gaisheshi.

Ardo yaji dadin yanda wannan matashin ya girmamashi don haka sai ya umurci sadah daya kawo masu tabarma.da sauri sadah ya juya cikin gida ya dauko tabarmar harda ruwan sha,shimfidata yayi ardo da bako suka zauna,shi kuma sadah ya koma gefensu ya tsugunnah

Ardo suka kara gaisawa da bako,sannan ya nemi sanin kowa neneshi?dan matashin nan ya gyara zamanshi yace,"ni sunana safwan."

Love you sis 😘😘
08033481518
[4/8, 10:25 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

11

I dedicated this love story to my Hausa Novels & my fans,love you all 😘😘

Jin sunanshi yasa sadah ya zabura ya mike tsaye rannan abace ya nuna shi da dan yatsa yace,"sake biyo ta kayi?to ta Allah ba taka ba,kuma idan har baka kama kanka ba duk abinda nayi maka kai kaja wllh."

Ardo ne ya dakawa sadah tsawa yace,"kai ni bana son shashancin banza,daga ganin mutum kawai sai ka haushi da masifa."sadah ya bude baki zaiyi magana sai kawai safwan yayi maza yace," ardo ni ne safwan wanda ka gani tare da sodangi dazu,kuma nazo don in sanar da kai cewa ina sonta kuma zan aure ta."ardo yayi murmushi yace,"alhamdulillahi yaro ai ka kyauta,saboda tun dazu tunani nah ina zan ganka kuma q ina kake da kai da iyayenka,amma tunda ka gajerce mani wahala ka kawo kanka ai abu yayi dadi, don haka sai kayi mani bayanin ko kai wanene?"

Safwan yayi kasa da kansa yayiwa ardo bayanin cewar shi dai mahaifinsa na abuja kuma babban dan kasuwa neh, amma asalinsu katsinawa ne,amma mahaifinsa bai faye zama ba,don haka zan turo maka kanin mahaifina sai ku ida jin komai daga gareshi.

Daga ardo har sadah sunji dadin wannan bayanin na safwan,domin bayanin nashi ya nuna masu bada wasa yazo masu ba,don haka anan take ardo ya nunawa safwan jin dadin shi,kuma yace," ina jiran zowarku goben kai da wakilinki domin ko bakazo ba dama nayi niyyar bayar da ita ga wanda nakeso."

Jin furucin ardo yasa safwan yayi wuf ya dago idanunshi yana kallon shi,watau ashe da tsoro ya hanashi karasowa da yayi asarar rasa sodangi arayuwarshi.

Sai da yayi sallar isha I sannan yayi ban kwana dasu tare dayiwa ardo alkawarin dawowa gobe kuma da wuri.

Abin yaro, sodangi jin ba wanda ya sakeyi mata mgn tun daga tambayoyin da sadah yayi mata yasa ta fito ta kama hidimarta kamar yanda ta saba.

Don haka yauma kamar kullum data gama yan ayyukan da take taya mahaifiyyarta sai ta shirya tsaf ta fito zata kada shanunsu ta tafi kiwo,sadah ta gani acikin shanun yana kwance waddanda aka daure, fuskarshi asake ya dago ya kalleta yace,"sodangi sai ina neh?"
Itama dariya take tace,"kiwo zani yaya sadah,kai yau bakaje makarantar ba?"

Tsaf ya kwanto shanun ya kadosu waje yana cewa,"kin mance ne,ai yau lahadi ba a zuwa makaranta."dafe kanta tayi tace,"wai ni,wallah na manta sam yaya sadah,toh baka zuwa katsina kenan?"

Sadah yayi dariya tare da amsar sandar hannuntq yana cewa,"yau bana zuwa ko ina sai kiwo,kinga na hutasheki kenan sai kije ki taya molasa aiki."
Chapter 7 · 0% Book details