← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 45

Sashe 25

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin haka yasa sodangi ta debi hanya da sauri har tana tuntube tana kuma waigenshi tana murguda mashi baki tare da fadin wasu maganganu da bai fahimci abinda take cewa.

Dariya yayi ya shafi sumar kanshi ya zuba mata ido har ta nemi bacewa ganinshi.wayarshi ya fiddo a aljihunshi ya kira babban yaronshi yace,"ka tarbi sodangi gata nan zata fito ta bayan restaurant dina,kuma kayi bakin kokarinka ka dauketa,amma idan taki ka kyaleta kabi bayanta hat zuwa gidansu."
Rusunawa yayi yace,"yes boss angama."sannan ya kashe wayar.
Safwan ya samu wuri ya zauna yaci gaba da tunanin sodangi,watau bazai mance dadin dayaji ba lokacin daya rungumota ajikinshi,domin ji yayi komai na jikinta ya kara canzawa,can kuma daya tuna kissing dinta da yayi duk da batayi responding ba,sai da ya rasa yanda zai misalta dadin dayaji.

Lumshe idanuwanshi yayi ya fada ahankali,"sodangi ke tawa ce ni kadai,saboda you are different then others."

Wayar shi ce tayi ringing ya zura hannu ya daukota ya kanga akunne ba tare daya duba sunan mai kiran ba,muryar Tahir yaji yana kiran sunanshi.

Gyara zamanshi yayi yace,"yeah my friend ya akayi neh?"
Tahir yace,"ina ka shiga neh?kafa san jiranka muke don ya kamata kazo wajen sameer."
Murmushi yayi saboda shi sam ya mance da yasa a tsare mashi sameer don haka sai yace kasa su sakeshi kawai,sannan kuma yaci gaba da cewa,"Tahir ka turo a daukeni."
Tahir yayi dariya yace,"lover boy a ina zamu same ka?"kwatance yayi masu sannan yaci gaba da tunanin sodanginshi kamin su iso.

Kusan lokaci daya Tahir da babban yaronshi suka iso,cikin farin ciki safwan ya nufi motar da Tahir din yazo da ita zai shiga,sai kuma ya dakata ya yafito babban yaro yace,"zo nan ka fada mani aiken da nayi maka."
Tunda ya taho safwan yaso ya gane akwai wani abu,amma sai yasha jinin jikinshi ya natsu yace,"ya akayi neh?"
Babban yaro ya rusunar da kanshi yace,yallabai babu yanda banyi da madam ba akan ta shiga mota amma taki saurarenna,toh shine na hakura nabi bayanta kamar yanda kace.
Bayan mun iso sallari dai dai junction sai adaidaitar data shiga suka wuce ni kuma sai go slow ya rikeni har wannan adaidaitar ta fito, ni kuma dana samu na shiga sai ban...........
ai bai bari ya ida fadin abinda zai ida cewa ba,saboda har ya gama karantar abinda zai ce sai ya kashe shi da wasu irin kyawawan Mari kusan ukku kuma lokaci daya.

Kuyi hakuri gashi nan don kada ku jini shiru shiyasa nayi maku wadda ya sawwaka.

Love you sis 😘
08033481518
[4/9, 2:28 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

37

I dedicated this love story to my Hausa Novel and my fans,thanks and love you all 😘😘

Nan take babban yaro ya zube kasa yana tuba a gabansu safwan,shi kuwa gaba daya farin cikin dayake ciki ya gushe,rannan bace ya kalleshi yace,"kana so ne kace mani zan kara rasa sodangi?"
Wani huci yayi ya furzar da iskar dake bakinshi yaci gaba dacewa, "wallahi karya kakeyi,kuma idan har ka bari haka ta faru toh abakin aikinka kuma sai nasa an daure mani kai har igiya tayi rara."

Nan da nan babban yaro ya tsure saboda yasan halin oganshi muddun ya fadi magana toh bai dagawa akanta.
Anan suka barshi duk jiki asanyaye saboda tashin hankalin daya hango ya tunkaroshi.

Sodangi kuwa kusan adaddafe ta isa gidansu surayya,babbar sa ar da tayi surayyar bata nan sai mahaifiyyarta,don haka shigewa tayi dakinsu ta kwanta ta darji kuka iyakar son ranta,saboda ganin safwan da tayi ayau yasa ya tado mata tsohon ciwon daya dade acikin zuciyarta.

Sodangi tasan tana tsananin son safwan kamar ranta,amma abinda yayi mata ne take tunanin yanda zata iya yafe mashi ta ruwan sanyi kamar yanda yake tsammani,jikinta ne ya dauki dumi tamkar mai zazzabi saboda kukan data wuni tanayi,sannan ga tsananin tunani da ta matsawa kwalarta.

Son ganin afnan ya bijoro mata acikin zuciya har take ganin kasancewarta akusa da ita zai iya sawa ta samu relief akan abinda takeji.

Wayarta ta daga ta fara neman number sameer,amma gashi tana ringing ba a daga ba har wajen sau ukku,abinda bai tabayi mata ba tunda suka hadu,don haka sai taji ta damu,sake kiran da zatayi nrh taji ya rufe wayar gaba dayanta.
Dan mamaki ne ya kamata tayi shiru hsr zuwa wani lokaci,kasa hakura tayi saboda ta riga ta sanya wa ranta tafiya gida,don haka sai ta yanke shawarar ta kira Abban sameer.
Haka kuwa akayi tana kiranshi ringing daya tayi yayi karaf ya dauka yana dariya yace,"sarat Abubakar!"
Sodangi ta sunkuyar da kanta cikin girmamawa ta gaisheshi.
Amsawa yayi cikin fara arshi,domin dakaji yanayinshi kasan cikin farin aciki yake yace,"saratu nasa da kun gama kai tsaye waje na zaku nufo."
Sai alokacin sodangi ta tuna da abinda ya kaisu company su safwan,don haka sai tayi sauri tace,"ranka ya dade ai abinda mukaje nema an dace,kuma duk sauran bayanai awajen sameer zakaji su."

Numfasawa Alhaji yunus yayi yace mata,"ni da idanuwana har yanzu ban ga sameer ba sai dai ya bayar da sakonnin report din da yazo dasu wanda kukayi,toh nima anan naga sun amince da suyi kasuwanci damu."

Alhaji yunus ya numfasa yaci gaba da cewa,"sarah ko wani abu ya faru daku neh awajen tafiyar,idan har akwai matsala ai ya kamata kuzo Kuyi mani bayani don mu shawo matsalar dani da ku."

Sodangi tayi dan takaitaccen murmushi tace,"Abba ka kwantar da hankalinks,domin babu abinda zai faru da company ka sai dai alkhairi."

Alhaji yunus yayi wani farin ciki najin dadin maganar da sodangi tayi,don haka sai yace,"ya zama dole in hadama wannan company nawa wata gaggarumar walima don atayamu murnar ci gaban da zamu samu."

Sodangi tayi dan murmushi tace,"godiyya muke yallabai, amma kuma sai tadanyi shiru".
"Umhum ina jinki sarah,ya akayi nrh?" Fadar Alhaji yunus.
Sodangi tayi kasa da murya tace,"yallabai bana jin dadin jikina,shine nake neman alfarma inason inje gida inyi ko sati daya neh don in samu shan magani."

Alhaji yunus yayi shiru kamar mai nazarin wani abu,sai can yace,"No problem sarah,dama nayi shiru neh don in tuna idan akwai wasu ayyuka,amma kada kiji komai Allah ya baki lfy,kuma yau monday sai ki dawo next monday,don haka ranar talata zamuyi celebrate insha Allahun"

Wani farin ciki ne ya kama sodangi,don haka sai tayi mashi godiyya sannan suka ajiye wayar.

Mikewa tayi ta shiga hada yan kayan da zatayi amfani dasu,sannan ta rubutawa surayya dan Note:surayya ina fata kin dawo cikin koshin lafiya,na tafi gida saboda naji duk jikina ban jin dadin shi,amma bazan wuce one week ba insha Allahu."

Ajiye wasikar tayi inda surayya zata gani ta jawo Jikkar kayanta ta fito. Har daki ta samu mahaifiyyar su surayya ta fada mata tafiyar da zatayi.addu a tayi mata sosai sannan kuma tace ta gaida mata mutanen gidansu.

Bayan ta fito daga cikin gidan ta fara tunanin ko ta fara zuwa Daura ta kwana biyu sai ta dawo bichi ta ida sauran kwanakin ta,don haka ta yanke shawarart kai tsaye ta hau motar Daura.

Akofar gida ta sami sadah da afnan suna shan iska saboda maraice yayi sosai, cikin mamaki ta kalleshi tare da dan waigawa dama da haggu tace,"yaya sadah ya naga afnan anan?"

Jin muryar sodangi yasa afnan ta juyo ta ganta,ai kuwa sai dariya ta tashi ta nufeta da gudu,cabata sama tayi tana dariya.
Wurin sadah ta ida isa ta samu kusa da shi ta zauna tana cewa,"na tambaye ka amma baka bani amsa ba."
Sadah yayi dariya yace,ai saboda ardo yana ciki shiyasa naki daga muryarta."
Sodangi ta kara kallon afnan tace,"nima rudewa nayi shiyasa."sannan ta mayar da dubanta ga sadah taci gaba da cewa,"nasan dai kai neh ka dauko ta,yaya sadah baka tsoron ardo yasan tsakaninah da afnan?"
Dan murmushi yayi yace,"wai ai zanso ace kina nan sadda na shigo da ita gidannan,saboda tambayoyin da ardo yayi ta watso mani sai da naji kamar in gudu,amma dana dake sai gashi don kanshi ya kyaleni."

Sodangi tayi tagumi tare da wara manyan idanuwanta ta zubawa sadah ido tace,"toh ina kace mashi ka samota?"
Sadah yadan kanga bakinshi kusa da sodangi ya rada mata, "cewa nayi diyar makwaftan su goggo laura ce,kuma wllh da kyar ya yarda,domin cewa yayi ashe acikin ruga akwai yan gayu haka 😃
Dariya sukayi gaba dayan su sai sadah yaci gaba da cewa,"tun ardo yana kauda kai ga afnan har ta kai idan bai ganta ba sai kiji yana tambaya,kuma kullum aka zauna sai kiji yaba cewa shi gani yake tanayi mashi kama da wata,amma har yanzu ya gaza gane da kowa cece."
Kallonshi sodangi tayi,shi kuma yaci gaba da cewa,"don haka tunda yanzu kin zo sai kin kula sosai,kuma kada kiyi ta jawo afnan ajikin ki har ardo ya kai ga zargin wani abu,ko kuma kamar dayake tunani a ina ya santa kinga sai ya gano ta ajikinki."

Sodangi ta firgita dajin zancen sadah😳 ta kuma kalli afnan tayi sauri ta ajiye ta kasa tace,"tabbas kuwa kasan ardo yana da saurin fahimtar al amurra,amma kuma yaya sadah ni yanzu muna kama da afnan?"

Sadah ya jawo hannun afnan yana kallonta yayi murmushi yace,"duk kusan halittun dake jikin afnan na safwan ne,abu daya ta biyo ki wannan dan point din,sai dai nata sharara yayi akan naki."

Sodangi ta yarda da duk bayanin sadah saboda ita ma tuni take kallon kamannin safwan a fuskar afnan.

Mikewa tayi tace,"yaya sadah na gode kwarai da gaske da irin kulawar da kakeyi mani Allah ya bar mana zumuncin mu."

Dariya yayi yace,"babu komai kanwata,ai ni duk farin cikinki shine nawa."
Tana murmushin jin dadi ta shige cikin gidan su.

Love you sis😘
08033481518
[4/9, 2:28 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

38

I dedicated this love story to my Hausa Novel & fans,thanks and love you all 😘😘
Chapter 25 · 0% Book details