Sashe 2
Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannu ya zira acikin aljihunshi ya debo kudi,domin shi kanshi bai san ko nawa bane ya mika mata.
Ita kuwa ganinsu sai hankalinta ya tashi saboda duk sakarcin halinta,kwata kwata iyayenta basu nuna mata son kashe kudi ba,don haka sai taja baya tana girgiza kai tace,"ka mayar da abinka,domin idan ardo ya ganni da su zai iya yanka ni."
Shi kuwa safwan sai ya nace wai sai ta karba,ganin haka yasa ta juya da sauri ta nufi cikin kasuwar ta barshi anan.
Duk abinda yake faruwa akan idon driver dinshi,don haka girgiza kai yayi ya dafe kanshi ya fada afili" ya Allah ka shiryar da oga nah,dubarshi don Allah duka shekarunshi badu wuce ishirin da biyu ba,amma yasan darajar mata." Dan tsaki yayi yaci gaba da kallonshi ya kara kada kai da mamakin yanda yaga jikin safwan yana rawa saboda mace.
Love you sis😘
08033481518
[4/8, 10:21 PM] binta garba: ðŸ’ðŸ’ðŸ’SODANGIðŸ’ðŸ’ðŸ’
Na
Binta garba saleh daudawa
02
Hello my fans,ina baku hakuri akan mistake da nayi wajen kiran sodangi na kira sunan ilham ta cikin ZUMUNCI, kun san yau da gobe sai Allah kuma dan adam ajizi ne,dole akwai mantuwa,please ku gafarce ni.
Continue:-
A sanyaye safwan ya dawo wajen driver dinshi yana ta saka abubuwa acikin zuciyarshi,don haka yana isa ya kalleshi fuska ba walwala yace," ina ganin fitowa zakayi ka shiga motar haya ka tafi Abujar ayau fon ka isar da sakon daddy,ni kuma zuwa gobe zan taho."
Driver yayi kasa da kanshi cikin girmamawa yace,"yallabai ko ka mance da irin worning din da Alhaji yayi mani akanka.......?"
Bai karasa ba safwan ya dakatar dashi da hannu,sannan kuma ya bashi umurni duk alokaci daya yace,"fito nace."
Dole driver bai da yanda zaiyi ya fito daga motar,shi kuma safwan din ya shige ya zauna mazaunin driver.
Driver dai bayyi kasa da gwiwa ba yadan leka ta window din motar ya sake cewa Yallabai ko ka mance akwai tafiya da zakayi acikin satin nan,kuma Alhaji yace Akwai wasu abubuwa da dama da zakayi kamin tafiyarka."
Safwan ya dago ido cikin isa da kuma gadara yace,"what do you mean driver?"dan kauda kanshi yayi tare da tsaki sannan yaci gaba da cewa,"kai ma ka koma dan sa ido ko,watau kabi layinsu mummy da daddy da broth koh?" Toh kada ka bari ka bata mani rai wallahi, saboda kai ma ka sani idan har naja maka layi sam bazakaji dadi ba,kuma tafiya da kake fadi,inason idan kaje ka fara sanar da daddy cewa na dagata sai nan da wata daya zuwa biyu.
Driver jin abinda safwan ya fada yasa duk jikinshi yayi sanyi,acikin ranshi yake fada yayin da ya kafawa safwan din ido,"watau yaron nan wannan karon ma ya kara rosawa Alhaji plain ke nan."amma kuma abayyane cewa yayi," ka gafarce ni yallabai, kuma insha Allahu zan isar da sakonka,sai dai kuma yallabai kwana nawa zakayi?"
Takaici ne ya kara kama safwan ya kalli driver yace,kaje kawai,ni dai nasan muddun na gama abinda nakeyi ai dole aganni gida,don haka don Allah kada ka sake damuna," kudi ya mika mashi masu yawa yaci gaba da cewa,"amshi wadannan,idan kuma bazasu ishe ka ba sai kayi mani bayani.
Hannu biyu ya mika ya amshi kudin don baida yanda zaiyi,shi kuwa safwan zamanshi yayi acikin motar har zuwa lokacin da su sodangi suka gama.
Gaba dayansu suka rankayo,sodangi ce atsakiyarsu,duk da akwai farare tas acikinsu, amma gaba dayansu sodangi ce ke haskasu,saboda da ita kyanta tundaga nesa kake ganinshi ba wai sai ta iso kusa dakai ba.
Don haka suna isowa kusa dashi ya kira sunanta,duk gaba dayansu suka cak tate da kallonshi,dariya tayi tace,"la ashe baka tafi ba?"
Daga mata kai yayi shima yana murmushin yace"ke nake jira don in mayar dake gida."cikin mamaki ta dafa kirjinta tace,"ni,sannan ta kada kanta taci gaba da cewa," kayi tafiyarka kawai,kada mu bata maka lokaci."
Mamaki ne yadan kamashi saboda ganin dazu bata tsaya neman izininshi ba ta shige mashi mota,domin yanzu gashi musamman sbd ita ya tsaya,amma zata ki shiga.
Wani mugun kallo ya sakar mata tare dayin kasa da idanuwanshi,fuskar nan dauke da murmushi yace,"saboda ke na tsaya ke na tsaya sodangi,kuma don na damu dake neh,amma tunda bazaki shiga ba bati inzo in tafi."
Jin yanda ya mayar da ita wata acikin kawayenta yasa taji dadi ya kamata ta dubesu tace,"ku muje ya kaimu gida."aikuwa fadarta keda wuya suka fara rubibin shiga,boat din motar ya bude masu duk suka zuba kayansu,sannan ya bude gidan baya,duk yawansu haka ya cusa su aciki ya rufe,sannan ya bude gidan gaban yace da sodangin ta shiga.dadi taji kwarai da gaske da irin karramawar da yake mata,don haka ta shige motar ta zauna,dan juyawa tayi ta kalli su dije da aka zakirasu kamar sardine, sannan kuma ga wani irin karni da tsami sunayi,ko ita dake mace sai da taji wani iri to ballantana da Namiji kuma dan boko dan kwalisa.
A guje safwan ya rinka jan motar domin sautin da motar keyi duk ya dameshi,don haka saboda irin gudun da ya rinkayi dasu nan da nan sai gasu gaf da rugarsu.
Parking yayi agefe,kafin ya bude ya fita sai da yayi locking din kofar dake kusa da sodangi,don haka alokacin da su dije suke fita ita kuma sai tayi ta kokarin ganin ta bude kofar tunda taga yanda akeyi,duk yana kallonta,dariya kawai yayi ya kauda idonshi har suka fita.
Sodangi juyowa tayi tace " ko nima in biyo ta inda su dije suka biyo neh?" Bai amsa mata ba ya rufe kofar,sannan ya koma sit dinshi ya bude ya shiga yace,"bari dai in bude maki,amma kamin in bude maki inaso muyi magana ni da ke."
Juyawa tayi ta hangi abokan tafiyarya,sai taga duk sunja tinga sun tsaya suna jiranta,dan hankalinta ne ya kwantq ta dago ta kalleshi,shima kallonta yake,kuma haka nan kawai sai taji wani irin abu ya ratsa mata acikin zuciya,don haka sauri tayi ta kauda idonta.
Shi kanshi abinda yaji sai da yayi da gaske ya samu kanshi,dan shirun da sukayi ne yake tunanin kodai ya fara son yarinyar nan ne,saboda wannan yanayin dayaji bai tabajin shi ba don ya kalli mace,sai dai kawai yayi sha awarta.
Kara daga idanuwanshi yayi ya sake kallonta sai kuma yaji gabanshi ya fara bugawa da sauri sauri,lumshe idanuwanshi yayi ya bude ya kira sunanta cikin wani salo da kashe murya yace,"sodangi ina son idan kin amince gobe inzo in kara kawo maki ziyara."
Far tayi da idanuwanta ta kalleshi tace,gobe bazan wuni gida ba,saboda ina zuwa kiwo ni da yaya sada."
Idonshi ya kai akan zara zaran yatsunta,kumbar yatsun sai ka rantse farin jan farce ne ta shafa,saboda yanda suke kyalli gwanin ban sha awa.
Mika hannu yayi da niyyar kama nata hannun amma sai ya fasa,saboda kada tunda wuri ta zargi wani abu,don haka sai ya kalleta yace,toh zan zo goben,kuma daga wane wuri kukeyin kiwon?"
Nuna mashi tayi da hannu tace," kaga waccar hanyar,to idan kazo tanan zaka bi,amma mota bata shiga,idan kaje sai kayi gabas,to anan zaka same mu da shanun mu."
Murmushi yayi yace,ok toh shikenan sai kin ganni,sannan ya latsa ya bude mata kofar,bai bari ta bude da kanta ba sai ya rabo ta jikinta ya murda kofar.
Gogar da jikinsu yayi sai da taji tsigar jikinta ta tashi,don haka nan da nan ta rufe idonta har sai da ya gama budewa ya janye jikinshi sannan ta bude idonta takalleshi akunya ce tace,"mun gode kwarai."sannan ta fita daga motar taci gaba da cewa," kai kuma Allah ya kiyaye hanya."
Tana fadar haka ta juya ta nufi wurin da kawayenta suke jikanta, tana isa duk suka taso mata da tambayoyi,babu tambayar data amsa sai dai murmushi kawai da takeyi,saboda yanda ta farajin safwan acikin ranta yana burgeta sosai.

03
Shi kuwa daya tayar da motarshi katsina ya koma, wani hotel ya nufa ya kama daki saboda yasan idan ya koma gidan kawunshi fada zaiyi mashi,kuma idan gari ya waye zai iya sanya shi agaba ya mayar dashi gida.
Kusan wunin yau sodangi yinshi tayi akasalance,saboda duk motsin da zatayi muryar safwance take ratsa mata kunnuwa,sannan abubuwan da suka faru atsakaninsu sai su rinka yi mata gizo acikin idanuwanta.
Karshe dai sodangi sai kawai taji ta kagara safiyya tayi don kawai taga ta hadu da safwan.
Don haka gari yana waye wa sodangi tayi kalacinta,sannan tayi wanka ta gyara jikinta harda shafa turaren innarta,sabon takalminta ta dauko ta zira duk molasa tana kallonta,can dai ta gaza daurewa tace,"ke sodangi wai ina zaki neh?"
Sodangi tayi dariya dan dimple din dake gefen kumatunta ya lotsa tace,"kiwo mana molasa." Da yake sunan lakani neh shiyasa itama sodangin take kiranta dashi.
Mamaki neh ya kamata tace"kiwo!! Keda zaki jeji shine kike kwalliya kamar zaki gidan biki?" Sodangi tadan shagwabe fuska kamar zatayi kuka tace,kai molasa,idan nayi kazanta kice mani kazama,amma kuma yau nayi kwalliya kince mani kuma kamar zani gidan biki,toh bari duk in gogeta shikenan koh?"
Molasa tayi murmushi tace," ni bance ki goge ba,kawai dai naga kwalliyar tayi yawa neh shi yasa na tanka mah,ki barshi kawai ysr auta ta."
Dariya sodangi tayi tace,"wai molasa ina ya ya neh ya shiga don tunda na tashi ban ganshi ba?"
Molasa ta nufi daki tana cewa,"tunda safe ardo ya aikeshi katsina yakai manshanu da nono acan madattai,kuma ina ganin shida gida sai yayi yammaci."
Wani dadi ne ya kama sodangi,saboda dama tunda ta tashi take tunanin yanda zasuyi da sada idan ya kyalla ido yaga safwan ayau,don haka hankalinta kwance ta dauki sandarta ta daga muryarta da karfi tace," toh ni dai inna na tafi,sai na dawo."
Molasa tace,"toh auta sai kin dawo,kuma kada kiyi dare don Allah."
"Toh",tace sannan tayi waje,akofar gida taci karo da mahaifinta tayi sauri ta durkusa tace "ardo na shirya zan tafi kiwo."
Fuska dauke da murmushi ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye yace,sodangi Allah ya bada sa a,kuma yau tunda ke kadai ce kada kiyi nisa cikin jejin nan,ki tsaya nan kusa kusa."
Dariya tayi tace"haka ma mosalasa tace mani," ardo yayi dariya yace,"yawwa toh maza ki tafi,saboda naga shanun ahanya kada su ja ki da nisa."