Sashe 8
Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Subbura dan bakinta tayi ta dan ya mutsa fuska tace,"ni bazan zauna ba,kiwo na zani."sadah yayi dariya yace,toh muje don yau kafana kafarki saboda na ganeki so kike kije kiga safwan."
War tayi da idanuwan ta ta kalleshi,acikin zuciyarta tace,"oh ya akayi ya gane abinda yake acikin zuciyata,tabbas safwan kawai nakeso in gani,domin ayanda nakejinshi bani son ranar da za ace gata ban sanyashi a idanuwana." Don haka murmushi kawai tayi tabi bayan dan uwan nata.
Kamar yanda safwan yayi alkawari haka ta kasance,saboda goman safe a mazoji tayi mashi shida kanin mahaifinshi.
Bayan gaisuwa da kuma ruwa da fura da nono da madarar shanu sabuwar diba da aka jera agabansu safwan sai ardo ya gabatar da kudirinshi akan lamarinsu safwan da sodangi yace,"toh ni bayanin da nakeso inyi maku shine,nan da kwana bakwai nakeso in aurar da sodangi,shi yasa na nemeku inji ko kun shirya?"
Jin maganar kanin mahaifin safwan yayi kamar daga sama,don haka sai ya gyara zamanshi duk da safwan ya riga ya gama tsarashi kamin su zo cewa,so yake ya shige mashi gaba wajen nemqn aurenta ba tare da sanin mahaifanshi ba,tunda ko sunji ba bazasu barshi ba,shi kuma kanin mahaifin nashi da yake ya dade yana kyamar irin dabi u na safwan shi yasa ya amince da shige mashi gaba tare da fatan Allah yasa auren ya zame mashi dalilin shiriya don haka sai yace,"amma ni aganinah ardo kamar sati daya an diba kadan ina ma laifin wata daya."
Ardo yayi murmushi yace,"ai dama ban matsaba,domin sodangi tana da masoya sosai,don dai itace bata sauraronsu,don haka idan har baku shirya ba sai in ba wani,domin asati dayan nan babu fashi ba saba lokaci."
Karaf safwan yayi ya kalli kanin mahaifinshi yace,abba kada ka damu don nima ashirye nake,amma akwai wani hanzari ba gudu ba,tunda sodangi yarinya ce bata ida mallakar hankalinta ba,idan akayi auren zan barta nan kusa daku har zuwa lokacin da zatayi wayau sosai ni kuma alokacin na kammala wasu shirye shiryena sai in dauketa mu wuce."
Ardo ya zuba mashi idanuwa yana kallonshi,sannan yace,"duk ban fahimci nufin ka ba."safwan ya kara gyara zamanshi yayi kasa da muryarshi cikin ladabi yace,"zan ginawa sodangi gida acikin rugar nan mu zauna tare,amma da lokaci yayi sai in dauketa mu wuce tare gidana dake abuja."
Ardo yayi murmushi yace,"na gane kwarai dan samari,ai hakan ma yayi babu matsala,shi kuwa kanin mahaifinshi shiru yayi yana sauraronsu har suka gama,sannan ya dago ya kalli safwan yaga sai wata fara a yake hankalinshi kwance,don haka shima sai ya kwantar da nashi hankalin yasa bakinshi aka ida shirya yanda auren zai kasance."
Har su safwan suka gama tattaunawa amma baiga giccin sodangi ba,don haka sai yaji ya damu,kuma idanuwanshi ita kawai suke kwadayin son gani koda giccinta neh,amma shiru babu ita babu alamarta,haka itama acan sadah yana lura da duk wani motsin da takeyi,tun tanayi da walwala har yaga ta samu wuri ta takure kamar wadda tunani ya matsa mawa.
Murmushi kawai yayi ya kauda kanshi daga kallonta,amma kuma akasan zuciyarshi yana mamakin irin saurin fadawa soyayya da sodangi tayi da wuri,saboda shi azaman yanzu makarabtar da yake zuwa yan mata da yawa sai a pro ching dinshi suke amma babu wadda ya kula,saboda ba abinda ke gabanshi kenan ba.
Don haka maida hankalinshi yayi yaci gaba da kiwon shanun har zuwa lokacin dawowarsu gida yayi ya kalleta yace mata ta tashi su tafi.
Sukuku tayi har suka iso gida bata da wata walwala sai dai zurfin tunani data afka.bayan sun hutane ardo ya kebe sadah gefe daya duk yayi mashi Bayanin yanda sukayi dasu safwan,da kuma sati daya daya sanya masu,sadah yaji dadi sosai don bama kamar daya samu labarin yar uwarshi bazatayi nesa dashi ba,don haka sai ya roki ardo da kada ya sanar da sodangi plain din aurar daita ga safwan,amma tasan kawai za ayi mata,kumaya hana sodangin fita sai ranar da za a kaita gidan mijintà .
Love you sis😘
08033481518
[4/8, 10:25 PM] binta garba: ðŸ’ðŸ’ðŸ’SODANGIðŸ’ðŸ’ðŸ’
Na
Binta garba saleh daudawa
12
I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all😘😘
Sadah yayi farin ciki matuka dajin yar uwarshi bazatayi nisa dashi ba,don haka sai ya roki ardo da kada ya sanar da Sodangi cewar za a aurar da ita ga safwan,sannan kuma kamar yadda yake a al adarsu yanason a boye sodangi na tsawon sati daya tunda bikin ba wani lokaci zai dauka ba.haka kuwa akayi,domin tundaga ranar sodangi ta daina zuwa ko ina,ba tare data farga ba abubuwan suka faruwa da ita.
Idan ta tashi tunda safe kamar kullum data fito don ta kada shanunsu zuwa kiwo sai dai taga basu nan,kuma ko ta bi hanya sam bata ganinsu dolenta ta koma gida.kuma idan ta koma gidan idan banda yan jike jike da ake ta banka mata babu abinda akeyi domin ita abin ma har ya fara isarta.
Madarar shanu kuwa maida mata ita akayi tamkar abinci,amma da zuma ake hada mata ita,banda itatuwan magunguna,domin tayi wanka dasu,wasu kuma ayi mata hayaki,wasu kuma a babbar roba ake sanya matasu ta shiga ta zauna.
Ita da kanta sodangi sai da ta gane acikin yan kwanakin nan ta canza sosai domin akoda yaushe cikin canza pant take saboda lema da take damunta.
Shi kuwa safwan suna barin wajen ardo yaje yayi cinikin wata katuwar gona dake kusa dasu,kuma nan take ya basu kudinta,kuma babu wani bata lkc da yayi ya nemi ma aikata nan da nan suka fara gina mashi gidan tare da shawarwarin manya manyan artists da ingenious.don haka acikin kwana biyar har anyi an gama sbd yanda ma aikata suka rinka aikin gina shi ba dare ba rana.
Yau saura kwana biyu kwanakin da ardo ya diba su cika,sodangi tana zaune gefe daya tayi tagumi,domin daga ganinta kasan tana cikin damuwa ta abubuwa da dama,gashi babu wanda ya bata fuska daga cikin dangin mahaifanta bare tayi tambayar abinda yake damunta.
Lumshe ido tayi ta bude tare da furzar da iska ahankali ta kira sunan safwan acikin makoshinta,tunaninshi ta fada dama aikin kenan ba dare ba rana,"ko ina yake yanzu?kuma mi yasa ya tafi ya barni?"wasu hawaye neh taji sun taru acikin idanuwanta,don haka kokari tayi tayi don taga sunki fitowa saboda gudun maganar danginta da suke cewa ba a taba ganin mai hali irinta ba duk acikin danginsu,wai bata da kunya saboda kai tsaye take fiddo al amurranta kamar ba bafullatana ba.
Shigowar sadah yasa ta dawo daga duniyar tunanin data tsunduma ta dago kai ta kalleshi sai zufa yake saboda daga kiwo ya dawo,shima kallonta yake tamkar yau ya taba ganinta,ganin yar ramar da tayi har ta fara bayyana yasa yaji wani tausayinta ya kamashi don haka da sauri ya kauda kanshi ya wuce tare dayin alwallar sallar magriba.
Bayan yayi sallar isha insa ya dawo gida yayi wanka tare da canza kaya,idan ka ganshi bazaka taba tunanin shine yaje kiwo ba,saboda shima sadah yana daga cikin kyawawan matasan da yan mata ke ribibi a kauyensu da kuma zagayensu.
Dakin molasa ya nufa yayi sallama,duk danginsu dake cike da dakin suka taso mashi bama kamar abokan wasansu,dariya kawai ya rinkayi masu saboda shi Allah bai sa ya iya irin wasan ba,idan da sodangi lami lafiya take da itace mai cashe masu.
Kallo inda take yayi yaga duk ta dukunkune wuri daya, kamar batama san abinda akeyi ba,sunanta ya kira,"sodangi."ta dago ta kalleshi da zurmammin idanuwanta da suka rame yace,"zo muje ki dama mani fura kinji yar kanwata."
Mikewa tayi duk jikinta babu kwari ga rashin cin abinci,saboda madarar shanu kadai take sha amatsayin abincinta,juyawa yayi ita kuma tabi bayanshi har zuwa yar bukkarshi.gefen yar tabarmar dake dakin ta raba ta zauna shi kuma akan katifarshi da yake kwana ya zauna sannan ya zuba mata ido yana kallonta cikin sigar tausayi.
Sodangi ta dago ta kalleshi tace,"yaya sadah ina furar take in dama maka?"murmushi kawai yayi yace,"dama kin san kema babu wata fura da zaki dama mani,saboda bani iya shan damunki sai na molasa tah."sumbura baki ta danyi wai ita taji haushin maganar da yayi tace,"nima ai yau da gobe zan koyi irin na molasar,kuma molasata ce ba taka ba."
Dariya yayi don dama yana sane yace haka,saboda duk ranar dayace mata haka wuni zatayi tana tsegumj shi kuma yayi tayi mata dariya yana kara tunzurita.
Fahimta yayi ta dan saki jikinta sai ya natsu daga tsokanar da yakeyi mata yace,"sodangi kin san ke kadai ce na mallaka amatsayin yar uwata koh?"kada kanta tayi alamar amsawa,don haka shi kuma sai yaci gaba da cewa,"toh inason ki fada mani abinda yake damunki cikin yan kwanakin nan,saboda dai idan har maganar aurece ai ba kanki farau ba,tunda kina sane duk kusan yan matan kauyen nan kusan a haka ake aurar dasu."
Sodangi tayi kwal kwal da idanuwan ta tamkar dama jiran dalili take,nan da nan kuwa sai hawaye shar suka gaggaro abisa kumatun ta,da bude bakinta sai kawai yaji ta ambaci"safwan". Daga nan kuma bata sake cewa komai ba.
Mamaki ne ya kamashi matuka,wai wannan wanne irin so ne sodangi takeyiwa safwan,duk da ya fahimci shima safwan din yana son sodangi, amma kamar na yar uwarshi ya fi yawa,don haka sai ya kara matsawa kusa da ita ya dafa kafadarta yace,"Sodangi mi safwan din yayi maki?"sodangi ta dago manyan idanuwan ta ta kalleshi tace"ya tafi ya barni,gashi innah laure ta fada mani wai aure za ayi mani da kado."
Murmushi yayi tare dasa hannu afuskarta ya share mata hawayen da suka fito yace,"kiyi shiru kanwata, saboda dama ita rayuwa duk haka take,domin ba kullum kake samun yanda kakeso ba,kuma miye a auren kadon?tunda dai ko safwan aka baki ai shima kadon ne,don haka ki kwantar da hankalinki wuri daya,sannan kuma ina baki shawarar duk abinda zaki so kisoshi don Allah kuma sese sese,haka nan ma duk abinda zaki ki shima ki kishi don Allah bada tsanani ba."
Sodangi tayi shiru tana sauraron nasihar da dan uwanta yake mata,kuma da alama duk ta fahimce shi,don haka sai ta sake share hawayenta tace,"toh shikenan yayanah na gode da shawararka,amma inason ka taimakeni da wani abu guda daya?" Sadah ya kalleta sosai yace,"fadi ko minene kanwata zanyi maki idan har bai taka shara a."