Sashe 28
Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sodangi ta murguda baki 😠tace,"kada kayi tunanin zan bi wata dokar ka,saboda kai ba komai bane awajena,kuma ada ban saurari samari ba,sai yanzu ne zan fara,don haka idan ka tashi kayi mani duk abinda kaga dama."
Tana fadar haka tayi wuf ta shige cikin gidan,saboda tasan halin safwan yanzun nan anyi ba ita.
Shi kuwa murmushi kawai yayi tunda yasan duk abinda take fada abaki ne kawai.
Juyawa yayi ya nufi motarshi cikin farin ciki da annushuwa,saboda ayanda yake jin kan nashi ayau tamkar wani sabon ango😜 yana shiga motarshi ya zauna ya lalubi wayarshi ya kira umminshi.
Da yake video call ne,nan da nan sai gata ta bayyana,gaisheta yayi cikin fara arshi wadda tana iya cewa rabon da taga yana yin irinta har ta mance.
Murmushi tayi tace,"yaya my son,ina fata kana cikin koshin lafiya?"
Safwan shima murmushin yake yace,"ummi na gano sodangi tah."
"Haba koh inji,shi yasa naga bakinka yaki rufuwa safwan."
Dariya yayi har yana kyakyatawa yace,"ina nan zan kawo maki ita,kuma da kin ganta zakisan danki bai yi zabin tumun dare ba."
Jinjina kanta tayi tana murmushi tace,"okay ina jiranka,amma kuma ya za kai da Humaira yarinyar da Daddy dinka ya baka?"
Dan tsaki yayi ya bata ranshi yace,"ni ai bance ina sonta ba,kuma ummi ki tambayeta kiji koh na tabayi mata wata maganar so?kawai ki fadawa daddy cewar ya nemar mata wani mijin,idan kuma broth Yusuf yana so sai ya kara ta amatsayin ta biyu."
Dafe kanta tayi cikin damuwa tace,wallahi safwan kana sanya mani ciwon kai da yawa,ta ya za a ce kai baka amshi mata ba sai yusuf,toh ina jan kunnenka akan kada ka sake yaji ka."
Safwan yayi murmushi yace,"I'm sorry ummi,kuma duk ranar da kikaga sodangi ciwon kanki zai warke."
Dariya ya bata sosai,sai da ta numfasa tace,"toh bari in fada maka ko yau Humaira sai da tazo gidan nan,baccin dama kusan kullum kafafuwanta suna gidan nan,don haka sai kazo ka warware wannan matsalar da kanka."
"Okay zan zo,amma sai naga anan komai ya ida dai daita sannan.kici gaba da hakuri ummi ko kuma idan kin gaji ki korata gidansu kawai."yana fadar haka yayi maza ya kashe wayar saboda yasan abinda ya fada ba mai yiwuwa bane.
Babban yaro dake gaba yana driving shima farin ciki ya kama shi saboda yaji oganshi yace ya saga farin cikin rayuwarshi.
Ayau haka safwan ya kwana cikin farin ciki da kwanciyar hankali.hakama sodangi, saboda ita duk wata rayuwa da sukayi lojacin tana yarinyarta,itace tayi ta dawo mata tamkar tana kallon majigi,babu yanda surayya batayi ba akan ta fada mata kowanene amma taki ce mata safwan ne saboda surayya ta dade tana yi mata addu ar dawowar safwan ko don saboda afnan.ita kuma sodangi bata so neh saboda abinda yayi mata,kuma Ardo yace idon shi Idon na safwan,idan kuwa yace haka yana nufin bai yafe mashi ba.
A haka tayi ta tunane tunanen ta har barci mai karfi ya kwashe ta.
Washe gari tunda wuri sodangi ta nufi wurin aikinta saboda ayau suna da manyan bakin da suka gayyato domin taya su murna.
7:30 am tana cikin office dinta,domin akwai wasu kayayyaki da suka dinka,kuma sukayi shawarar bayyanar dasu acikin taron domin suyi tallarsu ga ya'yan masu kudi da attajiran garin,saboda kayan ba na masu karamar harka bane.
Tana cikin aikin sameer ya shiga office din nata ya samu kujera ya zauna,dole ne ta bar duk abinda takeyi itama ta zauna ta zuba mashi ido.
Yar harararta yayi yace,jiya bayan na tafi ina kika shiga,saboda nayi ta kiran wayarki amma bakiyi responding ba."
Shiru sodangi tayi ta shiga tunani,tabbas jiya bayan rabuwarta da safwan taga missed call din shi har guda goma sha daya,amma kuma batasan dalilin dayasa bata kira shi ba,sai ma rufe wayar da tayi.
Dago idanuwanta tayi ta kalleshi ta marairaice tace,"I'm sorry sameer,saboda jiya gajiya ce tasa na kwanta da wuri,kuma sadda na farka naga cajin wayata ya kare."
Sameer ya numfasa yace,"toh shikenan is okay, komai ya wuce."hannunta ya jawo ya rike yana wani lumshe mata ido yace,"toh miye labari?"
Sodangi ta zame hannunta tana murmushi ta mike daga inda take zaune ta nufi wata wardrobe dake dauke da manyan yadiddika da take amfani dasu wajen yin dinkuna tana cewa,"sameer ai labari yana wajenku saboda mu mata yan zaman gida ne."
Sameer yayi yar dariya yace,"Toh tunda baki da labarin da zaki bani,ina reply dina?"
Sodangi dai ta san bata samu wata takarda ba,amma zuciyarta tana bata wannan card din da safwan ya tsinta kuma ya tafi dashi,tabbas takardar tana Wurin shi."
Rasa abinda zatace mashi tayi ta nufi yar kwarangar da take hawa idan zata dauko kaya asama ta haye,gashi takalman kafarta high Hill's ne,don haka ashe data hau bata dora kafarta daidai ba sai kawai ta nemi rikitowa,ai kuwa tayi saurin kama wani rool na material tana ganin zai iya riketa.
Gaba daya tayo kasa tana kwarara ihu da neman a gaji wurin wanda zai taimaketa.
Sameer ne ya zabura daga inda yake ya kai mata dauki cikin zafin nama ya tarbota,,aikuwa yanda ya samu ya rikota sai su rool rool din material din suka biyosu,kuma gashi wani irin nauyi tsiya gareshi,don haka bayan ya samu ya tarbeta sai ya kanga bayanshi wadannan rool din duk suka sauka ajikin.
Acan kuma abakin kofar office din, fa iza ce ta biyo bayan sameer,saboda taje nashi office din bata ganshi ba,sai tayi tunanin yana office din sodangi don haka tana bude kofar akan idonta accident din ya faru,kuma da kayan suka gama zuba abisa gadon bayan sameer sai yaki sakinta ya zuba mata idanuwanshi.
Tsoro neh ya kama fa iza,saboda ganin irin mugun kallon so da sameer yake aikawa sodangi.
Da sauri fa iza ta juya cikin mamaki da kutawa,acikin zuciyar ta tace,"lallai wannan yarinyar,sai nayi maganin ta wallahi.
Love you sis😘
08033481518
[4/11, 9:29 PM] binta garba: ðŸ’ðŸ’ðŸ’SODANGIðŸ’ðŸ’ðŸ’
Na
Binta garba saleh daudawa
42
I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘
Sodangi da duk jikinta rawa yake ta kalli sameer tayi mashi sannu,amma shiru yayi mata bai bata amsa ba,sai dai wannan kallon daya tsare ta dashi.
Zame jikinta tayi daga jikinshi ta dan matsa tana daddauke roll roll din tana tayar dasu tsaye.
Numfasawa yayi shima ya fara taya ta,sai da suka mayar dasu tsaf sannan ya kalleta yana murmushi yace,"na dade ina Worning dinki akan ki daina hawa saman nan da kanki,amma baki daina ba,toh yanzun idan da bani cikin office din nan ya zakiyi?"
Murmushi sodangi tayi tace,"shiyasa nake ta kara godewa Allah,don nasan babu abinda zai hana ni jin rauni."
"Ashe kuwa da nayi punishing dinki,tunda har kikayi sakacin jiwa wannan kyakykyawar fatar taki ciwo."jin abinda yace neh yasa ta kalleshi,hada idon da sukayi neh yasa yayi mata murmushi,itama murmushin tayi mashi,sannan ta kauda kanta gefe daya.saboda sodangi tana bakin kokarinta tasa sameer acikin ranta,amma ko kallonta yayi batajin abinda takeji idan tana tare da safwan,shi yasa abin ya fara damunta,saboda iyakar kokarinta shine ta yakice safwan daga rayuwarta amma sai kara shige mata yake kamar wani magnadiso.
Amsakuwar wayar dake cikin office din ita ta farkar da ita daga tunanin data tsunduma,sameer ne ya dauki phone din tare dayin sallama.
Muryar mahaifinshi yaji cikin fada yana cewa,"ina kuka shiga neh wai tun dazu?"inda inda sameer ya fara Alhaji yunus ya datse shi yaci gaba da cewa,"maza ku tahovina jiranku,saboda ga bakin da muka gayyato sun fara isowa."yana gama fadar haka ya kashe wayar ba tare daya jira jin abinda sameer zai ce ba.
Numfasawa sameer yayi ya juyo ya kalli sodangi da tun dazu shi take kallo,kuma ta fahimci da wanda yake waya,don haka sai ta tambayeshi,"abba neh koh?"
Daga mata kai yayi yace,"idan ina tare dake sarat,wallahi mancewa nake da komai nawa na rayuwa."
Kasa tayi da idanuwanta tayi murmushi tace,"yanzu dai mi Abba yace,don kada kasa muyi wani laifin."
Sameer ya mike tsaye yana shafar sumarshi yace,"our guests har sun fara zuwa inji Abba."
Salati sodangi tayi ta mike da sauri ta fara ridar kayan data harhada tana cewa,ba haka mukayi da Abba ba,ya kamata muyi sauri don kada ranshi ya kara bace."
Da sauri suka fita suka nufi inda suka tana da don ajiye bakinsu,aikuwa mamaki ne ya kamasu saboda yanda suka ga wurin kusan cike da jama a sai kai da komowa sevants din su sukeyi.
Daga kan da zatayi sai ta hango safwan acan kan high table inda aka ajiye manyan baki, shi kanshi tunda ta shigo hall din yake kallonta,shi yasa taji ajikinta.
Ganin safwan sai da gabanta ya fadi,saboda bata taba tunanin zai halarci wannan taron ba na karamin kamfani kamar nasu,duk a zatonta ko daga shiyyarshi wasu zasuzo sai dai yayi aiken yaranshi.
Dakewa tayi taci gaba da hidimar ta kamar yanda kamfanin ya tsara mata,saboda ita da sameer sune masu gabatar da duk wani abu na kamfanin.
Shi kuma sameer yana nan kafa da kafa da sodangi,komin su atare sukeyinshi gwanin ban sha awa,amma gasu safwan da fa iza su basuga abib birgiwa ba sai ma haushi da suke basu.
Fa iza ce ta nufi table din da Hajiya maryam take zaune da kawayent,amma daka gansu kasan duk zubin yan duniya ne,saboda babu wata mai shigar mutunci da zaka fidda.
Hajiya maryam tana murmushi ta tari fa iza,saboda bata son magana ta hadata da ita gaban wani don bata son aji sirrinsu,"ya akayi neh fa iza,naga fuskarki baki cikin walwala kamar yanda na saba ganinki?" Fadar Hjy maryam.
Fa iza ta kara yamutsa fuska tace,"kwanaki na kawo maki karar sameer da waccar abokiyar aikin tashi kikace mani babu wani abu atsakaninsu,toh yau na kamasu dumu dumu acikin soyayya ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜