← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 45

Sashe 6

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya maganar shi ta bata, aikuwa kyalkyatawa tayi har tana doka sandarta kasa,ga kuma wani dadi da taji wai yanaso tayi rayuwa ajikinshi,to kamar ya yake nufi? Don haka sai ta natsu ta bar dariyar ta kalleshi,wani kalli taga ya kara tsareta dashi,saboda safwan irin idanuwan nan gareshi wanda idan ya kalli mace bazata so ya dauke idanshi ba domin tafiya da imaninta da yakeyi lokaci daya.

Toh abinda yaso ya faru da sodangi kenan,duk da kananan shekarunta.shiru tayi ta dauke idonta daga kallonshi,amma fuskarta murmushi take ta maida kallonta akan shanunsu tana wasa da sandar hannunta.takawa yayi ahamkali ya isa kusa da ita yace"mi yasa kike mani dariya don nace inaso mu rayu tare?" Satar kallinshi tayi ta gefe saboda tana gudun kada ta sake ganin wannan irin kallon da yayi mata dazu tace," mamaki nayi ta yanda zanyi rayuwa ajikinka,"

Bayyi mamakin abinda yaji ya fito daga bakinta ba,saboda dai yarinya ce,kuma gashi bata waye ba tunda bata da ilmin boko,don haka baiji komai ba yace mata,"yanzu dana rungumeki bakiji dadi ba?" Jin maganar da yayi sai taji kunya duk ta kamata,don haka da sauri tasa hannuwanta ta rufe fuskarta tana dariya tace,"banji wani abu ba, amma turarenka kamshinshi shi yayi mani dadi." Shima dariyar yayi yace,"okay thanks,kuma tunda shi kadai yayi maki dadi toh zan sawo maki wanda yafi shi dadi ma,amma ni abu biyu sukayi mani dadi,da yanda na rungumeki sai kuma kamshin turarenki."

Jin zai kawo mata turare irin nasu na yan birni mai kamshin tsiya ta washe baki tace,"ai kuwa na gode,don dama nima na molasa ne nake shafawa." Murmushi yayi tare da zura hannuwanshi a aljihu duka biyun ya kira sunanta cikin wata siga ta yan boko yace," muje wajen mota ta kiga tsarabar da nayo maki."aikuwa cikin doki da murna tayi gaba yana biye da ita tana tayi mashi tambayoyi iri iri,wani ya bata amsa wani kuma yayi mata murmushi.

Love you sis😘
08033481518
[4/8, 10:21 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

08

I indicate this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all 😘😘

Tafiya yake cikin natsuwa,ita kuma sai yan tsalle tsallenta takeyi har suka isa wajen da yayi parking din motar,key yasa ya bude boat din ya daga marfin ita kuma tayi ta maza ta leka tana cewa,"ina tsarabar tawa?" Murmushi yayi ya nuna mata da hannu yace"duk abinda kika gani acikin boat din nan naki ne."

Baya taja cikin mmk da tsoro gami da zaro ido 😳 tace," wa ni?duk ina zan kaisu 🤔kuma yau idan ardo ya samu lbr kila ya yankani."yanda tayi neh ta bashi dariya sosai amma sai ya gintse yace,"waya fada maki ana dukan yar gata? Sam ardo bazai taba dukanki ba tunda kince yana sonki."

Kada kai tayi jikinta asanyaye tace,"na sani ardo yana sona sosai,don ma ina iya ce maka son da yakeyi mani har yafi wanda molasa takeyi mani,amma kuma shi mutum ne mara son wargi domin naira biyar ya hana in amsa awajen wani toh bare wannan tulin kayan haka."

Zuba mata ido yayi yana kallonta,ita kuma sai sheka mashi bayani take har ta gama,ya fahimce ta sosai domin duk afuskarta yaga iyakar gaskiyar abinda take fada.murmushi yayi ya lumshe idanuwanshi ya bude yace,"kada ki damu sodangi,ki bari ni da kaina zan kaiwa hardo kayan ince ya ajiye maki,amma yanzu ina son ki duba kiga abinda kikeso sai ki dauka."

Dan matsowa tayi ta sake leka kayan,sannan tasa hannu cikinsu tana daddaga,wani kwalin chocolate idonta yayi arba dashi takai mashi cafka tana dariya tace,"yawwa na samu wannan." Shima dariyar yake ya tufe boat din yana kallonta,tsaye sukayi ajikin motar suka ci gaba da hira ita kuma tana ta aikin cin chocolate din nan har taci kusan rabi.shi kuwa kallonta kawai yake da mmk,saboda yanda tasa zaki agabanta tana taci kamar mai jin yunwa,don haka sai ya tambayeta yace,"sodangi ko kinajin yunwa neh?" War tayi da idanuwanta ta kalleshi tace,"eh amma ba sosai ba." Hannu ya mika ya kama kwalin chocolate din yace," ki daina shan wannan amatsayin maganin yunwa,domin zai iya cutar dake ta hanyar kara maki kiba,kuma gashi ni bana sonta,don nafison mace yar dai dai watau ba ramamma ba kuma ba mai jiki ba kamar yanda kike yanzu.

Duk sadda safwan ya yabeta ko ya yabi wani abinta sai takanji kunya ta kamata,don haka yanzu ma abinda taji kenan shiyasa tayi sauri ta saki kwalin ta rufe fuskarta da hannuwanta tana murmushi.

Murmushin yakeyi shima ya bude sit din kusa da driver ya jawo hannunta ya turata ta zauna,amma bai rufe marfin ba,sannan ya nufi sit dinshi ya bude ya zauna.

Lemu da biscuits ya mika mata yace," kici wannan kilaya rage maki yunwar da kikeji.amsa tayi ta far mashi saboda dama yunwar takeji kuma gashi yau batazo da komai ba shi yasa tun zowarta ta fara da mangwaro.

Daga kanta da zatayi sai ta hango wani can nesa kamar ardonta,saboda duk kayan jikinshi da ya sanya ta sanshi dasu,ba wurinsu ya nufo ba,gittasu yayi,kuma time to time sai ya dago ya kalli inda take fuskarshi babu wata walwala acikinta.

Tsoro taji ya kamata da sauri ta nemi fita daga motar jikinta yana rawa,safwan kuwa duk yana kallonta da canzawar da tayi cikin dan kankanen lokaci, don haka da sauri ya riketa cikin damuwa yake tambayarta," mi ya faru sodangi."

Ture hannunshi tayi ta fita daga motar tana mazurai tate da daga hannunta tana nuna mashi ardon,amma bakinta rawa yake ta gaza furta komai.bin inda take nunawa da hannunta yayi ya hango ardo yana waiwayensu.

Kallonta yayi da sauri yace,"ko ardo neh?" Daga mashi kai tayi dai dai wasu hawaye sun malalo daga idanuwanta,sai lokacin ne ta samu dakyar tace,"ni yau na shiga ukku!!! Kila ardo yau sai ya yanka ni tunda naga yanda yakeyiwa yaran da ake kawo mashi kararsu idan an gansu da wani."

Yanayin da takeyin magana neh yaji duk ta bashi tausayi ya zagayo inda take yace,"kada ki tayar da hankalinki my friend, saboda babu abinda ardo zaiyi maki,ko kin mance kece shalelenshi?"

Dago idanuwan ta tayi cike da hawaye tace,"wallahi ardo sam ba haka yake ba,nidai yau ban san yanda zan kare ba🙆 zabura tayi taci gaba da cewa bari in tafi,don yana iya turo mani baffanah,kuma shi ba tausayi gareshi ba.

Bin bayanta yayi yana kiran sunanta cikin damuwa,sabida ganin irin yanda ta rude yana cewa,sodangi ki jirani mu tafi tare sai inyi mashi bayanin komai. Tsayawa tayi ta juyo saboda tuni tayi mashi nisa tace da karfi"bayanin mi zakayi mashi?"safwan shima ya daga murya yace ,"zan fada mashi cewar,ina sonki."

Duk da tana cikin rashin kwanciyar hankali sai da tayi dan murmushi wanda safwan ya gaza gane ma anarshi,saboda iyakar fuskarta ya tsaya,juyawa tayi taci gaba da tafiya cikin sauri mai kama da gudu.

Tsaye yayi yana kallonta har sai da ta kai ga bai hangenta kwata kwata,sannan ya juya ya kalli shanunta da ta bari saboda rudewa.murmushi yayi ya saddar da kansa kasa yana wani tunani,toh komi ya tunah??????

Love you sis😘
08033481518
[4/8, 10:22 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

09

I indicate this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all 😘😘

Sodangi tayi ta ta sauri,ga zufa ta hada tayi sharkaf,amma kuma mi?tana isowa kofar gidansu sai ta gaza shiga ta samu wani wuri ta labe,amma duk hankalinta yana kan mai shiga da fita acikin gidansu har sanyin maraice ya fara sakkowa.

Dafa kafadarta da akayi yasa ta juyo afirgice kuma idanuwanta suka karayo waje don tsoro,ganin sadah neh yasa ta mayar da ajiyar zuciya ahankankali harda lumshe idanuwanta,shi kuwa zuba mata ido yayi yana kallonta cikin mmk yace,"mi kikeyi anan wajen?"

Hawaye neh kawai taji ya zubo mata cikin I ina ta fara fada mashi komai, babu abinda ta boye mashi,jin abinda tayi shi kanshi sai da ya tsorata yace,"lallai yau kin ba ardo kunya, sbd duk rugar nan babu wanda yake yabo kamarki,sannan kuma ko tsakanin ni dake kece kullum mai kirki bani ba,don haka sai kisan yanda zakiyi don ni kinga tafiyata.

Da sauri ta cafko hannunshi ta rike ta fara kuka tana cewa,"don Allah kada ka tafi ka barni yayanah,ka taimaka ka kira mani molasa.shi kanshi ta bashi tausai tunda yana sonta don dai kawai yana son ya gwada mata kuskuren da tayi,domin ko kiwon nan da take tafiya inda za a biye mashi baza ta je ba,wannan shine ra ayinshi.

Cisge hannunshi yayi data rike yayi kamar zaiyi tafiyarshi,ta kara wartoshi cikin kuka irin na shagwababbin ya'ya tana cewa"wayyawoo ni molasatah,don Allah ka kira mani ita."

Kama hannunta yayi ya fara tafiya da ita,ada ta fara cijewa,amma ganin yafi karfinta yasa ta hakura dole ta rinka binshi kamar butun butumi sai dai hawaye shar kawai dake fita a idanuwanta.ganin har sun iso kofar gidan basu hadu da ardo ba yasa ta kwace hannunta tayi cikin gidan da gudu,kan ta tsaye dakin molasa ta nufa.

A dai dai lokacin da sadah yake ajiye kayan dayazo dasu ne molasa ta fito daga bandaki,da yake alkunya take mashi bata faye damuwa da al amurransa ba don haka bata tanka mashi ba sai dai shine yayi mata sannu da gida, sannan yaci gaba da cewa ina ardo?

Jim tayi kadan kamin ta bashi amsa,sannan cikin yanayin damuwa ta kalleshi tace," dazu dai ya shigo duk ba yanda yake ba,kuma na tambayeshi amma baice dani komai ba,kuma tunda ya kara fita bai sake dawowa".kamin sadah ya bata amsa ardo ya shigo don haka shiyasa sadah yayi shiru ya nufi ardon ya gaisheshi tare da mika mashi cinikin da yayi na nono da manshanu.

Babu yabo ba fallasa ardo ya amshi kudin tare dayi mashi sannu,sannan ya kalli molasa yace,"ina sodangi?"molasa bata fahimci komai ba tadan waiga hagu da dama tace,"ai bata dawo ba."

Hankalin ardo yadan tashi ya sake maimaitawa yace,"bata dawo ba?toh nima daga can nake kuma bata ba shanun mu." Juyawa yayi zai sake fita sadah yayi sauri ya zubar da gwiwoyin shi kasa ya kira sunan baban nashi da karfi yace,"ardo!!!don Allah ka yafewa sodangi laifinta👏
Chapter 6 · 0% Book details