← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 45

Sashe 30

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun shigar safwan adakin hutu inda sodangi take sameer yani bayanshi,kuma duk irin maganganun da sukayi da abinda ya faru duk akan idanuwanshi,don haka safwan yana rungume sodangi sameer yayi sauri yaja baya saboda ayanda yakeji idanuwanshi ba zasu jure ganin safwan da sodangi ahaka ba.

Love you sis😘
08033481518
[4/18, 9:46 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

44

I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘

Karar Wayar sodangi ce ta tsayar da safwan ga yunkurin rungumeta,saboda gaba daya ta tureshi ta nufi hand bag dinta dake kan table din farko da shigarka dakin,bude hand bag din tayi ta jawo wayar,ganin sunan yaya sadah akan screen din ne kawai sai taji gabanta ya fadi,don haka wayar tana shirin tsinkewa ta samu ta dauka saboda dadewa da tayi tana ringing din.

Babu sallama bare gaisuwa sadah yana samu sodangi ta dauka yace mata kina ina?
Sodangi adan tsorace tace,"ina wajen aiki,lfiya dai koh?"
Sadah ya numfasa yace,"da sauki sodangi,saboda ayau ardo ya gane sirrin dake rufe na afnan."
Sodangi tayi salati da karfinta wanda har yaja hankalin safwan ya juyo
yana kallonta cikin adan firgice.
Sodangi tace,"ya akayi har kuka bari haka ta faru,kuma yanzu ina afnan din?"
Sadah ya numfasa yace,"muna cikin daki nida molasa muna maganar afnan,ashe ardo ya dawo mu bamu sani ba,kuma acewar shi wai har sallama yayi mana bamu amsa ba,toh daya taho sai yaji duk zancen da mukeyi,kai ardo jiya yayi iyakar wulakancin sa son rai,ni kuma ganin haka sai kawai na daukota na maidota bichi wajen goggo laura na koma ajiyan.
Dan numfawa yayi sannan yaci gaba da cewa,yau tunda safe naga ardo yana shiri sai kawai jikina bai bani ba har ya bar gidan.
Daga baya nima da tunani ya dameni sai kawai na taho bichin,ai ina shiga na iske goggo laura tana ta kuka wai ardo ya dauke afnan yace gidan marayu zai kaita."
Yana kawowa nan sodangi ta fashe da kuka tare da kashe wayar ta jefa jikka,gyalenta ta dauka ta zira takalminta ta dauki jikkar tayi hanyar fita.
Safwan da bai gane abinda ya faru ba ya biyo bayanta da sauri ya riko hannunta yana cewa,"mi yaya sadah din yace maki? Mi ya sami ardo din?"
Juyowa tayi tana kallonshi,kuma sai takejin kamar ta fada mashi ko ya taimaka mata,amma kuma sai ta fasa saboda tana ganin muddun yasan da afnan rabata da ita zaiyi,ita kuma tana ganin ba mai rabata afnan sai Allah,saboda duk kiciniyyar da takeyi duk saboda afnan takeyin shi,domin bata son yar tata tayi maraici ko ta nemi wani abu ta rasa.

Fisge hannunta tayi tayi waje ba tare data kara saurarenshi ba,fita tayi bakin titi sai fama take da yan adaidaita don ta samu akaita tasha,amma abin kamar hadin baki babu mai tsayawa.

Motar safwan ce ta gani agabanta ta tsaya,amma bashi bane aciki sai babban yaronshi,fitowa yayi yazo kusa da ita yadan rusuna ya gaisheta,sannan yaci gaba da cewa,"oga ne yace inzo in kaiki inda zakije."
Ada kin shiga tayi,amma da ta fahimci lokaci sai kara tafiya yake kawai sai ta fada cikin motar shi kuma yaja suka nufi bichi.

A kofar gida suka sami sadah atsaye duk ya hada zufa sai sintiri yace kamar mai exercises, ganin sodangi yasa ya nufeta harda dan gudunshi yace,"duk cikin bichi babu gidan marayun da banje ba,amma banga afnan ba."
Roshewa da kuka sodangi ta sakeyi ta nemi zube mashi yayi maza ya kamata sukayi cikin gidan goggo laura.
Sun jima azaune suna jimamin lamarin,kuma duk daga cikinsu babu mai iyayin maganar kirki sai dai sharben kuka da sodangi da goggo laura sukeyi.

Wayarshi sadah ya fiddo ya kira molasa,da tuni sodangi ta saya masu ita da ardo,tana dauka yace mata,"ardo ya dawo?"
Molasa tace,"bai dawo ba,amma tun dazu nake nemanshi wayar tashi arufe take."
Kashewa yayi kawai don dama babu abinda yayi niyyar fada mata,saboda tana da hawan jini,yasan muddun taji cewar ardo ya dauke afnan hankalinta sai yayi mugun tashi.

Mikewa yayi ya kalli sodangi yace,"tashi mu shiga garin kano mu bincika gidajen marayu ko acan ya kaita.
Babu musu ta mike,ita kuma laura tabi su da adduar Allah yasa a dace su ganta.
Gaba daya sukace ameen,sannan sukayi waje,ganin har yanzu motar da yaron safwan ya kawota tana nan yasa sodangi tayi hamdala acikin ranta.

Babu inda basu shiga ba agarin kano,sukayi yawo har suka gaji amma basuji duriyar afnan ba har wajen goman dare.
Gidansu surayya sodangi tace ya kaisu,haka kuwa akayi,yana ajiyesu sadah yayi mashi godiyya duk da bai san kowane shi ba.
Mutanen gidan su surayya mutanen kirki ne matuka,saboda ganin yau harda sadah agidansu sai dawainiyya ta karu, ita kuwa surayya abin ba acewa komai saboda kamar tafi kowa farin ciki duk agidan,domin tanajin sadah har acikin ranta haka nan bata san dalili ba,amma bata taba fadawa sodangi ba sai dai itama sodangin tana fahimtar haka duk ranar da sukaje da surrayya daura,amma jin batan afnan sai da duk wanda ke cikin gidan ya girgiza saboda rudewa.

Ayau dai haka sodangi tayi kwanan bakin ciki,saboda ayanda tace,wannan shine abu na biyu da bazata mance arayuwarta ba.
Washe gari,tunda wuri sodangi ta nufi wurin aiki don ta dauki excuses, sannan ta dawo su fada gari suci gaba da neman afnan ita da sadah.

Shigarta office ba dadewa sameer ya shigo ya nufeta fuskarshi ba yabo ba fallasa,wuri ya samu ya zauna tare dazuba mata idanuwa yana kallonta cikin tuhuma yace,"jiya ina kika tafi with out taking permission?"
Sai alokacin ta tuna kuskuren da tayi,don haka sai tayi kasa da idanuwanta tace,"I'm sorry my boss 👏 Wallahi arude na fita daga company nan,saboda wata my relative dita ce ta bace shine muka tafi nemanta."
Dan shiru yayi yana nazarin maganarta sannan ya sake tambayarta da cewa,"ranar da mukaje interview company su safwan,akwai wata magana da yayi yace,"baki fada mani abinda ke tsakaninku ba,kikace mani you just a friend,amma ni abinda na gani jiya a resting room zuciyata ta gaza natsuwa,kuma sai nake kokonton abinda kikace,please ina son ki fitar dani daga duhu."

Sodangi tayi shiru tana sauraronshi,sannan kuma ta rasa shin wacce irin amsa zata bashi,ahankali ta dago ta kalleshi tace,"I will explain you everything, but ba yanzu ba saboda sam bani da kwanciyar hankali,shiyasa ma nazo in dauki permission awajenka."
Sameer ya zuba mata ido kawai yana kallonta,saboda abinda yaso shine sodangi ta fitar dashi daga tunanin daya dameshi,amma kuma tunda har tace mashi haka,watau kenan dai din akwai wata akasa.
Numfasawa yayi yace,"shikenan zaki iya tafiya,amma kuma ki sani duk sadda muka sake haduwa zakiyi mani bayanin tambayar da nayi maki."
Sodangi ta mike tare da jinjina kanta,alamar ta yarda sannan tayi mashi ban kwana ta fita.

A can gefen company ta hango ire iren motocin safwan,kauda kanta tayi taci gaba da tafiyar,horn taji abayanta sannan ya matso kusa da ita yayi parking, cikin girmamawa ya fito daga motar yazo kusa da ita ya rusuna sannan ya gaisheta.
Wani card ya fiddo ya mika mata yace,"dama boss yace,idan kin amince yana son ganinki."
Kallonshi kawai tayi ta sake kallon card din taga yana dauke da full address na hotel din daya sauka,don haka ta kalleshi tace,"ka koma kace mashi ina da abinda zanyi,kuma bazai samu damar gani na ba."
Babban yaro ya firgita dajin amsar da sodangi ta bashi don haka da sauri ya kara kasa da kanshi yace,"sorry madam,don Allah ki taimaka muje saboda kwata kwata bazan iya fada mashi amsar da kika bani ba."
Dariya kawai tayi taci gaba da tafiyarta,ai kuwa cikin sa a ta samu adaidaita ta shige ta barshi nan wurin.

Wunin yau ma haka su sodangi sukayi ta yawo babu wata nasara har ta gaji,wurin la asar suka fara tunanin komawa gida,kuma ayanzu sodangi ta fara tunanin son ganin safwan,saboda sai take ganin kila zai iya taimaka mata.
Kallon yaya sadah tayi tace,"zan koma wajen aikina,amma bazan dade ba zan dawo,don haka kayi gaba sai in sameka agidan su surayya..

Tun anan suka rabu,sodangi ta fiddo dan card din da safwan ya aiko mata dashi taba mai adaidaita,shi kuma ya shiga dubawa yana bin address din har suka isa wani tafkeken hotel wanda duk agarin kano baida na dayanshi.

Reception ta nufa ta fiddo card din ta mika masu,kai tsaye akasa wani ma aikacinsu har ya kaita bakin kofar dakin ya nuna mata sannan ya juya.

Love you sis😘
08033481518
[4/20, 8:01 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

45

I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘

Shi kuwa safwan tunda ya samu sakon sodangi nakin zuwanta hankalinshi ya tashi,saboda shi duk azatonshi sodangi ta yafe mashi laifin dayayi mata,amma dawowar yaronshi sai duk gaba daya yaji jikinshi ya dauki zafi tamkar mai zazzabi,haka yayi kwance jikinshi ya mutu saboda tsananin tunanin daya tsunduma acikinshi.

Ringing din da kofar dakinshi tayi yasa ya dawo daga dogon tunanin daya lula,zubawa kofar ido yayi tare da mamakin kowane ne yazo mashi adai dai wannan lokacin?saboda baiyi appointment da kowa ba.
Ringing ta karayi ya tashi dakyar yana jan jikinshi har zuwa bakin kofar saboda gaba daya jikinshi yayi nauyi,ahankali ya bude kofar idanuwanshi atsaye don ganin kowaneneh,kuma cikin sigar bacin rai.

Sodangi daya gani yasa ya saki fuskarshi tare da washe baki yadan matsa gefe kadan yace,"you're well come my dear."
Sodangi ta yamutsa fuskarta ta kalleshi ranta abace,saboda duk gani take har mtslr afnan da take aciki duk shine sila,don hakasai cewa tayi,"ba sai na shigo ba,domin wasu tambayoyi ne kadai suka kawo ni inyi makasu."
Numfasawa tayi ta zuba mashi duk idanuwanta taci gaba da cewa,"How you tossed me aside,when you let me go,did you feel that you'd regret it for life?"

Dama jikinshi asanyaye yake,amma wannan tambayar da sodangi tayi mashi sai yaji kamar ya zubar da gwiwoyinsa akasa,don ji yayi gaba daya basu iya daukarshi.ga bakinshi yana motsi amma kalmar dazai furta ta gaza fitowa,can dakyar ya iya furta sunanta,"please sodangi ! Sodangi don't...........

Ganin ya gaza iya furta komai tayi murmushin takaicin tace,"Never mind,I should get going."kawai sai ta juya rannan abace,dama kuma fuskarta gaba daya duk akumbure take saboda kukan datasha wajen neman afnan.
Chapter 30 · 0% Book details