← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 45

Sashe 11

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wuntsile wuntsile ta kama yi don ta kufce amma ta kasa,shi kuma dariya kawai yake yana cewa,"kada ki wahalar da kanki,domin bazan yarda da mu raba shimfida ni dake ba,kuma bazanyi maki abinda baki so ba."

Jin haka yasa ta hakura,wutar dakin ya kashe ya dawo ya rungumata ajikinshi suka kwanta.

Sodangi bata saki jikinta ba har sai da taji saukar numfashin safwan abayanta sannan ta rufe nata idanuwan.

Ana fara kiran sallar asuba safwan ya farka,amma idanuwanshi cike suke da barci,haka nan ya daure ya mike zaune ya kalli sodangi da ita dukkan alama bataji kiran sallar ba.

Kissing dinta yayi a lifts dinta wai ko ta motsa,amma shiru,don haka sai ya sake kissing din amma wannan karon tsayawa yayi yana tsotsar lifts din nata ba tare daya janye nashi bakinba.

Wani yanayi taji acikin barcin mai dadi,kuma duk tunaninta mafarki ne takeyi,don haka sai itama taji taci gaba da kwaikwayon abinda ake mata.

Ahankali ta fara jin abin abayya ne,saboda hankalinta duk ya gama game jikinta,firgigi tayi ta zabura ta mike zaune tare da tureshi ta bude idanuwanta sosai tana kallonshi.

Mikewa yayi ya sauka daga kan gadon yace mata lokacin sallah yayi,ki taso muyi alwallah,kuma atare nakeso muyi.

Yan waige waige tayi,don ta kara tabbataswa kanta,shin mafarkin ne ko kuma abayyane neh?toh amma wanda take tunanin shine yayi mata kamar bai san komai ba.

Haka nan ta tashi sukuku tabi bayanshi,kamin ta isa ya shiga ya rufe kofar,yan mintoci kadan ya dauka ya bude mata yace itama ta shiga idan tana da lalurar da zatayi.

Tare sukayi alwalla, sannan ya nuna mata wani akwati yace,"ta dauko kayan da zatayi sallah aciki."toh tace ta nufeshi,koda ta budeshi abin mamaki ya bata saboda babu komai acikinshi sai after dress da abayoyi kawai ne.

Daya ta dauka ta nufi toilet ta cire na jikinta ta zirata,tunda ta fito yake kallonta har ta zira abayarta ta koma kusa dashi tace,"na kimtsa."

Sai da sukayi raka a tanil fijir sannan suka gaba tar da sallar asuba,sun dade suna lazimi har sai da gari ya fara haske sannan suka tashi,sodangi tayi kasa da kanta ta gaisheshi.

Murmushi yayi yasa hannu ya jawota ajikinshi ya zaunar da ita akan cinyarshi yace,"komai nace maki ki rinkayi mani,zakiyi?"

Daga mashi kai tayi akunyace,saboda ganin yanda ya mayar da ita kamar wata karamar yarinya, don haka da sauri ta amsa mashi,"eh zanyi maka idan har kana so."

Wani murmushin ya sakeyi,duk da dama da wuya kaga safwan yana fushi ko fuskarshi a murtuke,kadaran kadahan.nuna bakinshi yayi da hannu yace,idan zaki gaisheni ba sai kinyi magana ba,nan kawai zaki tsotsa shike nan har mun gaisa tunda ai tare muka kwana kinga nafi kowa sanin yadda muka tashi."

Kunya ce ta kara lullubeta ta rasa yanda zatayi sai tayi saurin yin kasa da idanuwanta tana murmushi.

Kama kanta yayi ya sumbaci bakinta yace,"toh kinga yanda akeyi kuma daga yau haka shine gaisuwarmu koda yaushe."

Tashi tayi da sauri saboda kunya ta ruga ta fita daga dakin.dafe kanshi yayi yace,"wai! ni dai wannan kunya tana cutar dani wllh,amma zanyi bakin kokari na in ga na rabata da ita."

Love you sis😘
08033481518
[4/8, 10:25 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

18

I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all😘😘

Mikewa yayi ya haye bisa gadonshi ya kwanta,saboda har zuwa alokacin akwai sauran barcin jiya acikin idanuwanshi,amma shirun dayaji har yanzu sodangi bata dawo ba yasa ya kasa rufe idonshi sai ma zuru da yayiwa kofar shigo.

Sake sakkowa yayi yabi bayanta,kai tsaye dakinta ya nufa,ai kuwa acan ya sameta ta gyarashi fes duk da babu datti sai da ta shareshi,sannan ta haye bisa nata gadon saboda itama idanuwanta takeji wani iri.

Tsaye yayi a bakin kofar dakin yana kallonta,ita kuma ganinshi sai tasa hannunta ta rufe idanuwanta tana murmushi.

Kada kai yayi shima murmushin yake ya nufeta ya haye bisa gadon tare da rabawa jikinta ya kwanta,jawota yayi ya rungumeta ajikinshi sannan yasa bakinta agefen kunnenta yayi mata yar rada yace,"please ki dai na jin kunyata,saboda ni mijinki ne."

Murmushi tayi ta kara sunnar da kanta ajikinshi,shima murmushin yayi msi dan sauti yaci gaba da cewa,"muyi barci sodangi."

Ganin jiya da suka kwanta babu abinda yayi mata yasa yanzu ma ta kwantar da hankalinta ta lumshe idanuwanta,nan da nan barci yayi awon gaba dasu.

Sai wajen karfe sha biyu na rana suka farka,shima yunwar cikinsu ce ta ishesu har tasa suka farka.

Safwan ne ya riga tashi don haka kai tsaye kitchen ya nufa ya fara tunanin abinda zai girka masu.

Laluba gabanta tayi taji babu kowa sai pilo,shi yasa tayi saurin bude idonta,fitowa tayi ta nufi dakinshi taga baya ciki,sai ta sake fitowa tazo tsakanin dakunan ta tsaya saboda baya san ko ina ba,daga dakinta sai nashi.

Motsi ta rinkaji daga can wani bangare,don haka sai tabi motsin ta rinka tafiya ahankali tare da sanda tana dan lalle kawa har ta gano inda yake.

aikin dataga yanayi ne tayi sauri ta ida isa gareshi ta dubeshi tace," mi yasa baka tasheni ba,domin wannan aikin ni ya kamata inyi shi."

Dariya yayi ya nuna mata bakinshi yace,"baki gaisheni ba,don haka a yanzu babu wata amsa da zan iya baki har sai mun gaisa."

Murmushi tayi tare dajin yar kunya ta mika hannu zata amshi abinda yake fere dankali dashi duk da bata san yanda ake amfani dashi ba,shi kuma sai ya juya mata baya yaki bata.

Duk abinda ta nufa zata taba sai ya amshe ya ajiye gefe,idan ta kalleshi tana son sanin dalili sai ya nuna mata bakinshi.

Rasa yanda zatayi tayi,gashi shi kuma ya zame Mata kurma kuma sam batajin dafin hakan,don haka sai ta fara tunanin yi mashi abinda yakeso.

Yan kame kame ta farayi ga kuma kunya,can ta dake ta nufeshi,shi kuma yana ganin haka ya tsaya da abinda yakeyi ya zuba mata ido,koda ta iso gabanshi sai ta rasa ta yanda zata fara sai ta fara tunanin fasawa,shi kuwa yana ganin haka yayi wuf ya kamata ya jawota jikinshi yayi kissing dinta.

Komawa tayi gefe daya duk ta takura kanta saboda kunya,shi kuma dariya kawai yake mata,sai da yayi mai isarshi sannan ya kalleta har zuwa lokacin fuskarshi fara a kawai yake.

Wayancewa yayi ya kwala maya kira yace,"zo ki gani sodangi,dai dai ya saka dankalin turawan cikin wani dan injin tuliz nan da nan ya mayar dashi piece.

Abin burgeta yayi ta raba jikinshi tana kallo,karshe ya mika mata taci gaba shi kuma ya tsaya ta bayanta yadan rungumota.

A haka yayi ta nuna mata yanda akeyi har aka samu aka soya dankalin da kwai.
Kararrawar gidan ta fara ruri,alamar suna da bako abakin kofa.safwan ne ya rabu da jikin sodangi yace mata,"bari inje in duba."yana fadar haka yayi waje.

Bai dauki wani lokaci ba ya dawo dauke da kwanan sha na silver tare da cooler ahannunshi,dariya yake yana cewa lallai sodangi ke yar gata ce,wai molasa ce ta bayar akawo mana tun dazu muna ta faman barci.

Barin abinda take ta tarbeshi ta amshi kayan cikin farin ciki,ganin kunun gyada sukayi da lafiyayyen kosai,kuma kunun bai huce ba,don haka safwan ya dauko katon flasks yace ta juyeshi aciki.

Fasa sanya ruwan tea sukayi,sai safwan yasa suka kwaso kayan dazasuyi break fast din ya jata har dinning area ya kuma nuna mata duk yanda zata jerasu akan table din.

Wasa wasa zaman da sodangi tayi da safwan ta koyi abubuwa da dama daga wajenshi,kuma kunyarshi da takeji duk ta ragu sosai saboda duk abinda yakeso shi takeyi mashi har yau kusan watansu ukku da aure.

Shakuwa sosai ta shiga tsakaninsu har ta kai tsakaninsu babu mai iya kwanciya shi kadai,kuma sodangi idan bai rungumeta ba yayi kissing dinta sam bazataji dadin barcin ranar ba,amma duk da wannan shakuwa babu abinda ya shiga tsakaninsu sai tsabar soyayya da yake koya mata.

Alhamdulillahi, yanzu sodangi babu abinda bata iya ba,kan fannin abinci da zuba soyayya da shagwaba,babu abinda za a gaya mata.shi kuwa safwan kullum cikin dauriya yake,saboda gani yake sodangi har yanzu karamar yarinyace,domin ahankali cikin dubara ya binciketa ko period bata fara ba shi yasa take bashi tausayi, aduk sadda ya nemi kusan tar ta.

Yau wata hudu kenan,bayan sodangi duk ta gama ayyukanta ta dora sanwar abinci,sai ta fada toilet don tayi wanka.

Blood ta gani apant dinta ai kuwa sai hankalinta ya tashi ta rasa yanda zatayi,fitowa tayi ta dawo falo ta hada kai da gwiwa tana ta zubar da hawaye.

Safwan yau da wuri yaji yana sha awar dawowa gidansa,don haka bai jira su tahir ba yayi wuf ya baro su ya dauki hanya,saboda idan suka ganshi zai taho sunyi tayi mashi tsiya kenan wai rayuwarshi ta kare acikin kauye.

Shi kanshi yayi mamaki dayaga sodangi bata zo tarbarshi ba,don haka yana yin parking ya nufi cikin gidan da sauri yana kwala mata kira,amma shiru yaji.

Kara tako yayi ya nufi sashenta,bai same ta ba,haka ma bata asashenshi,don haka sai ya nufi falon dake kusa da kitchen.
Anan ya sameta duk tayi wujiga wujiga kamat wadda aka ba kashi,da sauri ya ida isa gabanta ya zauna tare da tallabota yana tambayarta,"mi ya sameki? Mi akayi maki?"babu amsar daya samu daga gareta.

Don haka gaba daya ya rungumeta ajikinshi yana rarrashinta da yake ya san halin shagwabarta don ta yiwu ba wani abin kirki bane yasa ta kuka.

Lema yaji a tafin hannunshi ya dago da sauri ya duba sai yaga blood,kallonta yayi cikin tsokana ya nuna mata hannun yace,"wannan abin kikewa kuka?"

Sharbe fuska tayi zata fasa mashi kuka ga tsoro fal afuskarta tace,"wllh ni banyi komai ba,ganin shi kawai nayi."safwan ya kalleta cikin rashin fahimta yace,"minene bakiyi ba?ai wannan abin ba sai anyi wani abu ba yake zuwa,lokaci ne kawai."

Sodangi ta kara kwabe fuska ta harareshi tace,"ba wani nan,ai Dije ta fada mani cewa,duk wanda yaga jini ajikinshi dan iska neh."

Zaro idanuwa yayi😳 cikin mamakin abinda ta fada yace,"watau kema iskancin kikayi kenan?"sai ya daure fuskarshi ya mike tsaye yana harararta yace,"yau sai kin fada mani yanda akayi har haka ta faru,kuma dawa kikayi iskancin."
Chapter 11 · 0% Book details