← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 45

Sashe 18

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sameer najin abinda Abbanshi yace sai ya mike tsaye yace,"Abba ba yanda za ai muyi tafiya da ita har sai mun gwada kwarewarta tukunna."

Alhaji yunus ya kalli danshi ya jinjina kai yace,"hakan is good,kuma ai kaine sectary sai ka tafi da ita ka gwadata sosai yanda ya kamata."

Wani farin ciki neh ya kama sameer ya kalli sodangi yayi mata irin kallon nan na zaki gane kuranki,gaba yayi ita kuma tabi bayanshi duk jikinta asanyaye.

Wani daki ya nufa da ita yasa key ya bude dakin,suna shiga sodangi ta kalli cikin dakin ta fahimci dakin daga ganinshi kasan an dade ba a bude shi ba saboda kurar data gani ko ina daddan kare.

Juyowa yayi ya kalleta yace,"to Hajiya sarah,sai ashiga a kama aiki,kuma ki tabbatar kin yi mani sample kusan kala goma kuma daban daban koda kuwa zaki kwana anan wurin."

Sadda ya fadi kala goma sai da taji gabanta ya fadi,amma data tuna goggo laura da afnan duk suna can suna jiranta,sai kawai taji wani gwarin gwiwa ya karu azuciyarta ta kalli sameer tayi murmushi tace,"koda kala ishirin kace inyi sam banda sarewa."

Sameer ya kalleta cikin mamaki watau wannan yarinyar bakin ta bazai mutu ba koh? Kada kanshi kawai yayi,saboda shidai yasan ai ya hadata da babban aiki,don haka babu abibda yace mata yayi tafiyarshi ya barta anan.

Sodangi ta shiga cikin dakin tayi tsaye tana kallonshi don taga ta inda zata fara,cire gyalenta tayi ta linke ta saka ajikkarta sannan tafarwa dakin.

Nan da nan cikin dan lokaci kankani ta gyara dakin fes duk ta goge inda ya kamata ta share shi ta sake jera duk kan kekunan dake cikin dakin.

Agogon hannunta ta duba taga har sha biyu saura,gabanta ne ya fadi taga toh yaushe zatayi ta gama aikin nan da aka bata,amma sai tayi wata shawara da zuciyarta ta zaro wayarta ta kira surayya.

Bugun farko surayya ta dauka cikin zalki tace,"yaya sodangi? Har kin gama?Ina fata dai an samu nasara."
Sodangi ta dan numfasa tace,"ina tukunna dai,sai ta kwashe duk abinda ya faru ta fadawa surayya,ai kuwa nan da nan surayya ta tsure saboda tafi sodangi tsoro, don haka sai tace,"don Allah sodangi ki tafi da komai ahankali saboda nasan halinki sarai,kuma komai zakiyi ki rinka tuna muhimmancin dalilin neman aikinki,please kada ki sakeki biyewa zuciyarki."

Sodangi tayi kasa da murya kamar bata son wani yaji abinda zata fada tace,"nasani surayya,kuma insha Allahu zan bi komai ahankali kodan sanin tashin hankalin da nake ciki game da goggo laura,saboda ita kawai yanzu abinda take jira shine,dana samu aiki itama albashi zan rinkayi mata duk wata,kinga kuwa idan ban samu aikin ba akwai rigima kenan."

Surayya ta jinjina kanta kamar tana a gaban sodangi tace,"duk nasan haka sodangi, don haka sai ki bi ahankali,kuma ma bari in hadaki da Anty fatima kiji idan har akwai matsala a company."

Sodangi tace,"ok toh na gode surayya."yan mintuna kadan sodangi taji wayarta tana ringing,don haka sai ta dauka.
Anty fatima bata saurara ba ta hau yiwa sodangi bayani saboda surayya ta fada mata komai tace,"kada ki damu sodangi,wannan company baida wata matsala,don haka ko kwana ya kamaki ki kwana saboda dama akwai masu aiki 24hours,don haka kedai kokarin da zakiyi shine kiyi dinkuna wadanda kikasan zasu gigitasu matuka,kuma kada ki damu da abinda sameer yake nuna maki,domin shima duk yanayi maki haka neh saboda abinda kikayi mashi,amma bayyanannun halayenshi masu kyau ne."

Sodangi taji wani sanyi acikin ranta tace,"na gode kwarai Anty Fatima,kuma zanyi bakin kokarina."
Anty fatima tayi murmushi tace,ok toh sodangi, munayi maki fatan alkhairi best of luck."daga nan ta kashe wayar.

Numfasawa sodangi tayi ta kalli roll roll na material da shaddoji da wasu yadiddikan ma bata san sunansu ba saboda bata taba ganinsu ba.

Sai da tayi sallar azahar sannan ta fara aikin,yi kawai take baji ba gani,kamin la asar sameer ya shiga wurin da sodangi take aiki,shi kanshi yanda yaga ta gyara dakin sai da ya burgeshi.ledar dake hannunshi ya ajiye gefe daya ya kalli sodangi yaga aikin yankanta kawai takeyi kuma yanda kasan batasan mutum ya shigo inda take ba.

Sameer yq gyara tsayuwarshi ya zubawa sodangi ido,da yake akwai bakin glass a idonshi shi yasa bata fahimci abinda yakeyi ba.
Shi kuwa gogan ahaka ya samu damar kallonta yanda yakeso,kuma awannan lokacin ne ya fahimci abubuwan dakesa sodangi takeyiwa maza wula,saboda yanda Allah yayi mata fasali da tsari ga kyan jiki,uwa uba kuma ga kyau dan asali.

Tsaayuwar da yayi neh ba tare daya ce komai ba yasa ta fara tsaguwa ta dago kai ta kalleshi,ai kuwa taga ita kadai yake kallo don haka itama sai ta kalli kanta,ganinta tayi daga ita sai matsatstsin riga da siket na atamfa,kjma ga dinkin yayi fitting dinta sosai,kusan da gudu ta isa wurin hand bag dinta ta jawo katon gyalenta ta rufe jikinta dashi.

Murmushi sameer ya taka har kusa da ita sannan ya tsaya tare kuma da tamke fuska yace,"ke baki iya magana bane idan har kinga mutane?kuma inason in fada maki ni bake nake kallo ba da zaki zabura ki rufe jikin ki, domin duk asurar jikinki babu abinda ya burgeni sai style din atamfar jikinki,don haka idan har kin tashi ki dinka da irin style din."

Kada kai sodangi tayi alamar taji abinda yace,"sannan ta juya kan aikinta.
Safwan yasa hannu ya amshi almakashin da take yankan dinkin dashi ya ajiye gefe daya sannan ya jawo ledar daya shigo da ita ya tura mata agabanta yace,"ki daina duk abinda kikeyi kici abinci,saboda mu wannan company masu adalci ne don bamu mayar da ma aikatanmu kamar injina."

Don gudun kada ya bata mata lokaci,kuma dama gashi tun kusan dazu cikinta ya fara kiran ciroma saboda ko break fast batayi ba,don haka bude ledar tayi taga snacks ne da soyayyen naman kaji,sai gwangwanin lemu guda biyu.

Maida hankali tayi sosai ta cinye snacks din nan tare da gwangwanin lemu daya,sai dan naman kajin taci kadan saboda idanuwan sameer ne suka hanata sakewa,amma da babu abinda zaisa bata cinyeshi duka ba.

Murmushi kawai yayi ya juya ya sake fita,sodangi kuma ta mayar da hankalinta taci gaba da dinkunanta.

Kayan da sodangi ta dinka kayane na gani na fada dana maza dana mata,don idan ka kalli kayan sai kayi tsammanin kayan mazan yan kanti ne saboda irin su suit suit din nan ta dinka kala kala,su kuma cikin na matan akwai wadanda idan ka gansu sai kayi tunanin daga sena gal aka jawo su.

Dinkuna dai sunyi yanda ake so kuma ko abirnin hassada abin sai haka,kusan wajen karfe hudu na asuba ta kammalasu gaba daya.

Mikewa tayi ta tana dafe da bayanta tare da kugunta sai mammatsasu take,sannan kuma idanuwanta cike suke da barci don har wani donko idanuwanta sukeyi,amma ganin alfijir ya fito,kuma muddun ta kwanta toh bazata samu sallar asuba bah,don haka sai taki kwanciya har saida tayi sallar asuba sannan ta raba jikin wata kujera da table agabanta ta zauna tare da dora kanta bisa.
Duka batayi cikakkin minti biyu ba wani barci mai nauyi yayi awon gaba da ita.
Gari na wayewa,ma aikatan da suka kwana suka fara haramar barin company, su kuma wadanda zasu amshi aiki sai shigowa sukeyi abin gwanin ban sha a wa.
Sameer ne tafe cikin motarshi yanayi yana duba agogon hannunshi saboda bai son takwas tayi mashi sai acikin office dinshi,sodangi ya tuno sai kawai ya samu kanshi dayin murmushi yadan daki gefen sitiyarinshi yace,"nasan duk abinta bazata iyayin set din kaya har kala goma ba cikin wunin jiya,kai koda kwana tayi ma bazata iyaba,saboda yanda nasan mata da less ness."
Murmushi ya sakeyi yaci gaba da cewa,"ta wannan hanyar ma kadai ya isa in kamata tayi feiling."tundaga nesa kamin ya iso bakin kamfanin ya fara horn,toh idan da sabo ma maigadi ya isa ya saba don haka ya tashi da sauri ya bude mashi,shi kuma yana isowa shigewa kawai yayi tare dayin parking wurin dayake ajiye motarshi.

Office dinshi ya nufa,sai da ya shigar da wasu takardu sannan ya sake duba agogonshi yaga 45minute pass nine,numfasawa yayi tare dayin guntun murmushi yace,"duk delay dinta ya isa ace tazo yanzu,idan kuma tayi dubara tazo da wuri har tayi set daya.

Aje duk abinda yakeyi yayi ya nufi dakin da yaba sodangi jiya,dan kasa kunnenshi yayi wai ko yaji motsin keken dinki,amma sai yaji shiru.

Fusata yayi,watau ma bata zo ba,lallai yau zataga karshen rashin mutunchi kenan.
Tura kofar yayi ya shiga with compedance,sai kuma yayi turus,saboda kayan dayagani duk anyi hanging dinsu,wasu kuma an zurawa irin dan butum butmin roba.
Bude baki yayi cikin mamaki ya nufesu yana daddagasu,acikin zuciyarshi ya fada gaskiya kayan nan sunyi kyau,🤔anya kuwa! zan iya cewa yaushe rabon da mu samu kwararre tela haka,sai daisu kware ahannun mu.

Hango sodangi yayi can kwace abinta bisa dogon table din da take yankan dinki duk ta mimmike,sai dan gyalenta data rufe kafafuwanta dashi har zuwa wucewar kugu.

Zuba mata idanuwa yayi,saboda yanda take Barcin daganinta hankalinta akwance yake tamkar tana kwance acikin dakinta.
Kujera ya dauko ya zauna gaf da ita yaci gaba da kallonta saboda yanajin dadin yanayin da yakeji acikin jikinshi idan yana kallonta.fa I za ce ta fado mashi acikin zuciya,shin wai mi yasa bayajin abinda yakeji yanzu idan har suna tare da fa iza?

Motsawa sodangi tayi,kuma duk alokaci daya ta bude idanuwanta,shi kuwa sameer rasa yanda zaiyi yayi,gashi ta riga ta ganshi a gabanta zaune bare ya tadhi,don haka sai ya wayence ya kauda idonshi daga kallonta,kuma ya mayar da glass din ya rufe idanuwanshi dashi.

Mikewa tayi zaune tare da jan gyalenta ta ida rufe jikinta dashi tayi kasa da idanuwanta tace,"morning sir."
"Morning"yace,ya mike tsaye yana dan kame kamen taba kayan data dinka yaci gaba da cewa,"nan kika kwana neh?"Ta sakko daga kan table din tace,"yes sir."jin jina kanshi yayi yace," mi yasa baki sanar da kamfani ba cewar anan zaki kwana?"

Sodangi ta dago kai ta kalleshi taga har zuwa lokacin shafar kayan data dinka yake tace,"sorry sir."

Wani murmushi keta yayi ,acikin zuciyarshi yace,"miye na saurin bada hakuri kuma,kya bari kiga yanda zamu kare."
Chapter 18 · 0% Book details