← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 45

Sashe 33

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sodangi na fita daga wajen aikinta taci karo da yayanta sadah cikin sauri yake tafiyar shi yasa har ya kusa banke ta bai lura ba.
Hannu biyu yasa ya rike kafadunta yana dariya yace,"kanwata na gano inda afnan take,zo muje kada mu bata lokaci mu daukota."
Wani sanyi ne ya ratsa zuciyarta itama sai dariyar take tace,"tana ina yaya sadah? Kuma ya akayi kasan inda take?"
Ci gaba da tafiya sukayi ya fara bata labari yace,"tunda na koma gida idanuwana suna kan ardo,don haka duk wata waya da zaiyi ko kuma bako da zaizo sai nayi mashi labe don inji abinda ya kawo shi.
Don haka yau tunda muka tashi da safe sai na fahimci ana yawan kiranshi ta waya,shi kuma ya gaza zaune ya gaza tsaye sai shiga da fita yakeyi kuma cikin damuwa.
To ahaka nayi ta bin bayanshi har naji,wai afnan sai kuka take,kuma takicin duk abinda aka bata,kuma hadeja ya kaita can wajen wani abokinshi na kurucciyya.

Sodangi ta rike hannunshi tana kuka da kuma dariya,kuka don tausayin yarta sai kuma tana dariya don farin cikin yau zata ga farin cikin idaniyarta.

Sadah babu inda bai sani ba a Hadeja,saboda can wasu lokutta da suka wuce ardo yana zuwa dashi,don haka kai tsaye suka nufi gidan abokin ardo sukayi sallama.
Ana amsawa suka sanya kai cikin gidan,sodangi na gaba sadah yana biye da ita.
Yar tsuwwar dariyar da afnan ta fasa ita ta jawo hankalin duk wanda ke cikin gidan,saboda tunda aka káwo ta babu wanda ya ga farin cikinta sai yau.
Da gudu ta nufesu tana kiran mammy ! Mammy !! Da isarta sodangi tayi sama da ita,sannan ta rungumata ajikinta tana dariya.
Bayan ta sauke ta ne ta nufi sadah shima ta makalkaleshi ya dauketa,aikuwa nan da nan ta fara basu lbr,dama afnan baki abin magana.
Mutanen gidan suka tarbesu cikin farin ciki,dakin mahaifiyyar abokin ardo aka kaisu suka zauna,aka kawo masu ruwa mai sanyi na tulu suka sha,sannan suka gaisa.
Sadah ya gyara zamanshi ya kalli yar dattijuwar nan yace,"dama munzo ne don mu dauki afnan."
Dattijuwar nan tayi murmushi tace,"kai amma ardonku ya kyauta wallahi,saboda yarinyar nan tunda tazo bataci wani abin kirki ba,shi hankalin mu ya tashi kwarai da gaske,saboda kada adalilinmu yunwa ta kamata."
Duk dariya sukayi suka kalli afnan dake makale ajikin sadah,bayan yar tattaunawa kadan sadah yace,"so muke mu juya a yanzu don kada dare yayi mana ahanya."
Dattijuwar nan ta kalli yanayin garin tace,"ai dan samari daren Ma ya riga yayi,amma da atunani nah zaku jira wannan yaron ya dawo sai ku gaisa tunda an kwana biyu baku hadu ba.
Sadah yayi murmushi yace,"idan aka kwana biyu zan dawo,amma yanzu idan har muka tsaya jiranshi wannan kanwar tawa zata iya samun mtsl awajen aikinta."
Toh da haka suka samu suka baro garin Hadeja,saboda gani suke idan har suka tsaya jiran aminin babasu toh zai iya basu matsala ya amshe afnan din ya hanasu tahowa da ita,ko kuma yace sai yayi magana da ardo.

A kano suka kwana,don haka gari yana wayewa suka nufi daura gaba dayansu,kuma sukayi sa ar samun ardo agida.
Molasa tana kitchen suka iso,don haka bakinta abude ta fito tana murnar ganinsu,don ma ba kamar data gansu da afnan.

Ardo ne shima ya fito daga nashi dakin fuskarshi adaure ya dakatar dasu yace,"kada wanda ya wuce mani cikin gida da wannan yarinyar."
Gaba dayansu suka ja tirjiya suka tsaya suna kallonshi,don ita sodangi mah har idanuwanta sun ciko da kwallah cikin yanayin kuka tace,"ardo mi nayi maka da har zaka ki jininah?"
Ardo bai amsa mata ba har sai da ya samu wuri Ya zauna yace,"ina jin dai ai nan gida na neh ko? Toh kuma nace bazan amince da zaman wannan yarinyar agidana ba,ya'yanah guda biyu,kuma su kafai nake so in gani agabana."
Sodangi da tuni kuka ya ci karfinta ta fada cikin karaji,"haba ardo,kada ka zama mai son zuciya mana,kana tunanin idan har ka kori afnan ni zan iya zama agidan nan neh? Har abada wallahi ,saboda yanda kakeson diyanka daka haifa nima haka nakeson afnan,kuma insha Allahu daga yau zan bar maka gidanka..........
Caraf sadah yayi da bakinta ya rufe yana girgiza mata kai yace,"kada ki sake fadar haka,idan kin tafi kina da inda yafi nan ne?"
Kura mata ida yayi don ta bashi amsa,don haka wani gajeren murmushi tayi ta matso hawayen dake cikin idanuwan tace,"idan har afnan bata da wuri ni zaman mi zanyi acikin gidan?komi afnan tayi mani bazan taba rabuwa da ita ba."
Sadah ya harzuka da kalaman sodangi,domin ya fahimci baza tayiwa ardo uziri ba,saboda ai dole ranshi ya bace da abinda ya faru sai ya dakatar da ita,"kada in sakejin kin fadawa ardo irin wannan maganar,kuma daga yau afnan ki mayar da ita wajen mahaifinta tunda kin gano shi ,don shi Allah ya dorawa nauyin rikonta ba ke ba ko iyayenki ba."
Daga inda molasa take arude ta zaburo tacewa sadah,"tasan inda dafwan yake?amma kuma bata taba fada ba?kuma kai ya akayi ka sani?"
Sadah yayi wani murmushin takaici yace,"nima ba itace ta fada mani ba,ganinsu nayi da idanuwana,kuma bakin cikin hakan yasa har yanzu ban tada mata maganar ba saboda hankali na yana kan inga mun gano afnan.

Love you Sis😘
08033481518
[4/24, 8:14 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

49

I dedicated this love story to my Hausa Novel group & my fans,thanks and love you all 😘😘

A ranar dana gansu,raina ya bace matuka,don har rasa irin hukuncin da zan yake mashi nayi, amma duk da abinda ya faru ardo ina mai baka hakuri daka bar mana afnan har zuwa ranar da safwan zai amshi abinshi."
Sodangi ta juyo ta kalleshi tace,"tunda na haifi afnan nake dawainiyya da abina,kuma har zuwa yanzu haka,don haka babu wanda zan ba diyata,don ni kadai na isheta gaba da baya,kuma maganar barin gida,insha Allahu yanxunnan zamu tafi mu barshi.
Tana fadar haka ta mike daga tsugunnen da take,nan da nan itama molasa ta Mike ta nufi dodangi ta rike tace,"haba
Sodangi,ya za ayi ki tafi ki barmu,ko kin mance da mune iyayenki?"
Sodangi ta girgiza kanta tace,"ban mance ba molasa,kuma bazan taba fatar mancewa daku ba,amma kuma kada ki manta da ni na haifi afnan,kuma bata da kamata aduniya don haka dole neh in yi kokarin fita hakkinta da Allah ya dora mani."
Wccewa tayi ta nufi dakin molasa don ta ida hado sauran kayansu dake gidan,tana hawaye tana tattara kayan kuma zuciyarta cike take da bakin cikin abinda ardonta yayi masu ita da yarta,watau ta yanda ya korar mata diya ba tare daya damu da ita halin da zata shiga ba.

Jawo akwatin tayi ta fito ta sake durkusawa agabansu tana share hawayenta tace,"ardo da molasa ina rokonku daku yafe mani duk wani laifi da nayi maku."
Da tun lokacin da molasa ta fahimci sodangi tafiya zatayi ta barsu ta fara kuka tare da zargin hukuncin da arfo ya yanke bai yi ba,da sai ya bi abin ahankali ba tare da an bata ran kowa ba.
Share hawayenta tayi ta kalli atdo tace,"don Allah ardo ka yafe mata,kuma kayi hakuri ka barta ta zauna da yarinyarta."
Shi kanshi ardo gaba daya jikinshi yayi sanyi dajin yar shi zata tafi ta barshi amma sai ya dake kawai yace,"bazan karya dokar dana kafa da kaina ba,kuma aini ban kori sodangi ba,diyar safwan na kora tunda ba mu keda hakki akanta ba,kuma abu daya kawai nakeso kiyi mani shine,tunda har safwan ya fara bibiyarki acan din to kiyi kokari ki kawo mani shi agabana don ya fada mani abinda yake nufi da hakan."

Sodangi ta mike tsaye tare da kamo hannun afnan dake zaune akan cinyar sadah tace,"insha Allahu zan fada mashi sakonka."
Shima sadah mikewar yayi ya amshi katon akwatin sodangin suka nufi hanyar fita.
Da gudu molasa ta nufi dakinta tana kuka sosai saboda gaba daya ta gaza daurewa da radadin da zuciyarta take mata,shi kuwa ardo kusan ince mutuwar zaune yayi anan inda yake,saboda bai taba tsammanin sodangi zaya iya tafiya ta barsu ba,kuma sai wasu maganganun da tayi suka rinka dawo mashi acikin zuciya.
Numfasawa yayi ya fada afili,"tabbas nasan sodangi babu yanda za ai ki bar afnan ki zabe mu,saboda jinin tane,kuma afnan bata san kowa ba sai mahaifiyyarta,don haka zanyi bakin kojarina inga safwan ya amshi yarshi don itama sodangin ta huta.

Akan hanyarsu ne sadah yayi ta kwatantawa sodangi cewar,dole ne fah wata rana ta hakura da afnan,tunda mahaifinta yana raye adoron kasa,kuma shike da hakkin riketa ba ita ba,sai dai idan kin san zaki koma gidan safwan din ne,toh wannan sai ince zaki iya ci gaba da rayuwa da ita,amma kuma kin san ardo ba zai yarda da wannan iya shegen ba."

Dago idanuwa sodangi tayi da sauri ta kalleshi har shi kanshi ya fahimci hakan shima ya kalleta cikin mamaki yace,"ya kika kalleni?ko har kun shirya zaki koma gidansa neh?"
Sodangi tayi kada da idanuwanta tare da girgiza kanta tace,"banyi mashi alkawarin zan koma gidansa ba,na dai ce yazo yaga ardo suyi magana."
Dan maida numfashinta tayi tace da murya can kasa,"amma yaya sadah idan ban auri safwan din ba,waye zan aura?"
Daure fuskarshi yayi yace,"SAMEER,sameer zaki aura tunda naga yana sonki sosai,kuma naga dukkan alama ba yanayinsu daya da safwan ba."
Kwabe baki tayi alamar maganar batayi mata dadi ba tayi kamar zatayi kuka,amma kuma batace komai ba,shi kuma duk yana kallonta don haka sai yaci gaba da cewa,"dana koma gida duk zanyiwa ardo bayani akan sameer din saboda na fahimci babu wanda kika fada mawa yana sonki."
Sodangi ta kara bata fuska tace,"nidai ban sanya ka ba,kadai bari kawai kaga yanda zasu kare tsakani Ardon da safwan din,toh baya nan idan ta kama sai suji labarin sameer din."
Dariya kawai yayi ya girgiza kanshi,amma akasan zuciyarshi ya kara tabbarwa kanshi lallai har yanzu sodangi tana son safwan kilama fiye da tana karama.

Kai tsaye ta samu motar da zata kaita kano,sadah ne yayi sauri yace,"amma zaki tsaya ta bichi koh don ki ajiye afnan."
Sodangi ta girgiza kanta tace,"da ita zan wuce,saboda har yanzu ban amince da ardo ba,yana iya kara dauketa."
Sadah ya amince da bayaninta sannan yayi bankwana da ita,saboda afnan dataji ta ajikin sodangi sai tayi barci.
Chapter 33 · 0% Book details