← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 45

Sashe 5

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wurin sha biyun rana dad din ya kirashi awayarshi,da kyar ya samu ya iya daukar wayar saboda gajiyar dake jikinshi,"ina jiranka afalonah."abinda yace mashi kenan shi kuma ya zabura tare da fisgo rigarshi ya zira sannan ya nufi sashen dad din.

A kishingide ya sameshi bisa wata resting chair dinshi yana kallon breaking news a CNN,hankalinshi ya tafi sosai awurin wani labari mai ban al ajabi,don haka sai da aka gama sannan yasa remote ya rage sautin maganar tv din sannan ya juyo ya kalli safwan da yake zaune gefenshi with his confidence yace,"my son safwan,ina ka boya cikin kwanaki ukku?"

Sunkuyar da kanshi yayi yana murmushi yace,"daddy just forget kawai." Kuma don ummi dinshi taja mashi kunne,amma da kai tsaye yayi niyyar fada mashi zaiyi aure, tunda yana da dukiyar da zai iyayi wa kanshi abubuwa da dama ba tare da parents dinshi sun sanya hannu aciki ba.

Murmushi Alhaji salmanu yayi yace," I love you my boy,saboda yanda kake aiwatar da al amurranka ba tare da tsoro ba,shi yasa nake son in doraka bisa wasu harkokina kamar yanda nayiwa dan uwanka yusuf,amma kurucciya ta hana ka tsaya ka fahimci komai."

Dan shiru yayi sannan yaci gaba da cewa," don haka yanzu mi kake ciki akan plain dina na tura ka a broad? You are ready to go ko kuwa?"

Safwan yayi jim bai ba dad dinshi amsa ba,saboda tunanin abubuwa da dama da yake ganin muddun ya tafi,duk zasu iya roshewa,tunda tafiyar zata iya daukarshi shekaru da dama ba tare da ya waiwayi Nigeria ba.

Dagowa yayi ya kalli mahaifinshi da tun dazu shi yayiwa zuru yana kallonshi yace,"I'm sorry dad,saboda irin abinda zakaji daga baki na,domin ni kaina nasan ba haka kaso kaji ba,ina wasu abubuwa da dama da ban ida kammalawa ba,kuma idan na tafi zai zamo nayi failing akansu."

Alhaji salmanu ya zuba mashi ido kawai,saboda babu abinda yake tunani sai wannan abu da danshi ya kafe akanshi ko minene shi? Domin tun kusan waccen shekarar yaso ya tafi ya ida digree dinshi acan amma yaki,kuma kila ba komai ba ne sai harkar mata da ya sanyawa kanshi,don haka girgiza kanshi kawai yayi yace,"inaso ka fada mani abinda ke hana ka tafiya."

Safwan yayi dariya yace,dad kada ka damu about business ne,kuma I promise you next year zan tafi kamar yanda ka bukata.

Babu yanda ya iya,saboda tun farko basu koya mashi bin ra ayinsu ba,sai dai duk abinda yakeso su ma shine abin son su komai rashin kyaun abin da muninshi.

Don haka takarda ya dauko ta agreement yasa hannu sannan yaba safwan shima ya sashi yasa hannun yace,toh wannan shine kashen rigima ta dakai,saboda idan kuma har lokacin yazo kayi mani gardama toh a time din zan dauki kwakkwaran mataki akanka,don wallahi ko kai sai kayi nadamar bata mani lokaci da ka rinkayi.

Safwan fuska a sake sai farin ciki yake, saboda yanda yaci galaba akan mahaifinshi ba tare daya sha wata wahala ba,kamar wancan karon ba.

Kuyi hakuri my fans saboda banyi typing sosai ba saboda rashin caji.

Love you sis😘
08033481518
[4/8, 10:21 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

06

I indicate this love story to my group Hausa Novels & my fans,love you all😘😘

Amsar takardar yayi hankalinshi akwance,domin babu abinda ya dameshi saboda shi kawai so yake yaga ya samu cikar burinshi ta mallakar abinda yake shawa a ajikin yar yarinya wadda bata san ko micece arayuwa ba,watau sodangi.

Tsaf yasa hannu kamar yanda dad dinshi ya bukata,sannan ya mika mashi paper yana dan murmushin samun nasara,shima mahaifin nashi murmushin yake tare da zubawa paper ido yana cewa, amma kafin ka wuce kayi kokari kaga yusuf,saboda akwai wani sakonka daya biyo ta acct dinshi.

Murmushi safwan din yayi,saboda jin wasu kayan tafiyar sun kara shigo masa watau (kudi)godiyya yayiwa dad dinshi tare dayi mashi bankwana,domin yace masa zaiyi wata tafiya da zata dauki tsawon wani lokaci, yana fita wurin dad dinshi ya nufi sashen ummin sa.

🍒🍒🍒

Al amarin sodangi kuwa,kullum cikin tunani take da zaman jiran dawowar safwan,amma shiru kakeji shirwa taje kasuwa,don haka duk sai tabi ta zafge ta rame,ita ba kwanciya tayi ba,amma idan ka kalleta sai kayi tsammanin jinya tayi.

Don haka gaba daya hankalin iyayenta duk yabi ya tashi, dama abinka ga yar lele wajen uwa da uba,kullum cikin tambayarta suke,amma amsar da take basu bata wuce ba komai,kuma tace ita lafiyarta kalau.

Wani lokaci idan suka sanyata agaba suna rarrashi sai abin ya rinka ba sadah mmk,saboda yasan shi kanshi yana son yar uwarshi,amma irin wanda iyayensu keyi mata ba, domin shi yasan duk wazzhala da runtsi bai hanashi karatun arabi da bokonshi,kuma duk ranar da baida wani uzuri yaki zuwa makaranta sai ardo yayi kamar zai dakeshi,amma yana kallo idan har sodangi tace bazata ba toh babu mai takura mata,shi kanshi ya rasa miye dalilin haka?

Yau kamar kullum,gari yana wayewa kowa ya tashi ya dasa hidimarshi,da yake weekend ne don haka sadah ya dauki nono da man shanu ya nufiv katsina,ita kuma sodangi ta fara azamar tafiya wajen kiwo.

Ko yau din ma sai da ardo yaso ya hanata zuwa kiwon amma sodangi ta nace tace tana iya zuwa,ba don sun so ba suka kyaleta,amma ardo ya ja mata kunne akan kada ta dade kuma kada tayi nisa cikin jeji.

Kada shanunta tayi tana tafe tana yan wake wakenta,amma acan kasan zuciyarta tunanin safwan takeyi tare da fidda ran sake ganinshi arayuwarta.

Kamar kullum,bayan ta samu wurin da shanun ta zasuyi kiwo sai ta samu wani gajeren iccen mangwaro ta haye,ta samu reshe mai dan gwabi ta makale ajikinshi tana shan mangwaron.
[4/8, 10:21 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

07

I indicate this love story to my group Hausa Novel &my fans,love you all 😘😘

Ta samu reshe mai dan gwabi ta makale ajikinshi tana ta shan mangwaronta,sai da tasha mai isarta sannan tayi lamo ajikin iccen tana kallon yanda shanunta suke kiwo,wani gyangyadi taji ta farayi mai dadin gaske saboda gajiya,ai kuwa tun tana gyangyadawa har ta fara sakin jikinta,nan da nan kuwa wani barci ci mai nauyi ya debe ta.

Kamar yanda yacewa mahaifanshi zaiyi tafiya kuma zai dan jima kamin ya dawo,kuma duk daga cikinsu babu wanda yayi yunkurin tambayarshi inda zaije ko kuma idan yaje mi zaiyi (freedom) shi yasa yake tsula tsiyarshi.

Don haka shima gari na wayewa ya biyo hanya,amma jirgi ya biyo don ya iso da wuri,kai tsaye guest house din babanshi ya nufa daya kankara acikin garin katsina,kuma gidan yana jimawa ba kowa cikinshi sai dai ma aikatan da aka zuba,kullum cikin gyaranshi suke,shiyasa idan ka shigeshi sai ka rantse akwai mai rayuwa acikinshi.

Don haka ko da ya sauka wanka kawai ya sakeyi yasa kananan kayanshi,yayi kyau matuka,sannan ya dauki mota daga cikin motocin dake rufe a parking space.

Tsaraba yayi sosai ya cika boat din motarshi ya nufi mazoji,kai tsaye inda sodangi tafi tsayawa tayi kiwonta ya nufa,agefe yayi parking sannan ya ida isa akafa yana takawa ahankali sbd kunyar shuka dake shigar mashi gaba.

Ahankali ya zagaye wajen tsaf amma baiga sodanyi ba,sai dai shanunta dake ta shawagi awajen.

Tsayawa yayi yana mmk tare da tunanin kodai yau ba ita tazo kiwon ba,kuma sai ya tuna ai yau asabar ta fada mashi yayanta sadah katsina yake tafiya tunda babu makaranta,don haka sai yaci gaba da searching dinta.

A hankali yake leka can leka nan har ya iso wajen iccen mangwaron nan ya tsaya game da sarewa,domin har ya fara tunanin juyawa,sai yaji motsi asaman kanshi.da sauri ya daga kai yaga ko minene, sai kawai yaga sodangi makale abinta sai barshi take harda min shari.

Mamaki abin ya bashi matuka yaga ko tunanin fadowa batayi,ai kuwa da gama tunaninshi sai yaga ta rikito gaba daya ta taho babu abinda ya riketa,kuma duk alokacin ta farka,ai kuwa da ta fara tsuwa da neman agaji ga harbe harbe tanayi.nan da nan safwan ya tarbeta ta fado jikinshin,shi kanshi yasan ayau yayi namijin kokari da har ya iya riketa ba tare da sun fadi ba.

Ita kuwa dama tunda taga fadowa zatayi sai ta rufe idanuwanta bakin ne kawai ke neman ceto,don haka jinta da tayi a jikin mutum sai kawai ta kara makalmaleshi,gaba daya kuwa jikin ta rawa yakeyi.

Dariya yayi yasa hannu ya rungumeta sosai ajikinshi har yana rufe idanuwanshi tare da sunsunar gashin kanta,kamshin dayaji tanayi neh mamaki ya kamashi saboda baiyi tsammanin abinda zaiji ba kenan,sumbatar kanta ya karayi tare da ajiyar zuciya wanda shi kanshi bai san dalilin yinta ba.

A hankali sodangi hankalinta ya fara dawowa ajikinta ta fara tunanin a ina take,kamshin turaren jikinshi yayi mata dadi taji kamar tayi ta zama cikin wannan kamshin mai dadin sun suna,sai kuma kwalwarta tace mata toh waye kika makale?

Da sauri ta fara janye jikinta shi kuma jin haka sai ya riketa gam saboda wata duniyar shagala dayaji ya lume cikinta ga wani dadi yana ta ratsa zuciyarshi.karfi ta fara sanya mashi,sunanta ya kira a setin kunnenta yace,"abokin ki neh safwan." Jin sunan da aka ambata yasa tayi saurin kallon fuskarshi,aikuwa ganinshi yasa ta washe fuska sai dariya tace,"lah yaushe kazo? Ka tafi ka barni kullum sai tunaninka nake,jibi yanda na rame."

Ja bayan da ta fara kokarin yi don ta gwada mashi ramar da tayi yasa ya saketa ita kuma ta samu damar matsawa tana cewa jibi.bin ta yayi da idanuwanshi da suka canza yanayi yabi body dinta da kallo,aikuwa idanuwanshi sai kan kirjinta da sukayi dim dim,amma basu ida batsewa ba,wani miyau yaji ya hadiye saboda wani kwadayi daya taso mashi har tsakar kanshi.da sauri ya kauda idonshi saboda wani karatu da zuciyarshi ta farayi mashi.

Ita kuwa haka da yayi sai taji bataji dadi ba,watau bai damu da ita ba kamar yanda ita takejin rashinshi da tayi kamar zata mutu.sumburar bakinta tayi ta nufi sandarta data jingine ta dauka zata wuce abinta.hannunta ya riko da sauri ya jawota kusa dashi yace,"kada kiyi fushi da abokinki,nima nayi missing dinki sosai, kuma rashinki da nayi shi yasa har kikaga na gaza magana saboda yanda najiki ajikina. Da zaki amince da kin dawo jikina kinci gaba da rayuwa ta har abada wadda bazata kare ba."
Chapter 5 · 0% Book details