← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 45

Sashe 3

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da dan tsallenta ta wuceshi tayi hanyar daji,shi kuwa sai da ta bulle duk yana kallonta fuskar nan sai murmushi yake, sannan ya maida hankalinshi ya nufi cikin gida.

Sodangi da kyar ta samu ta cimmah shanunsu,sannan tayi dubarar tsayar dasu tunda wurin akwai danyar ciyawa sosai duk da damina batayi irin kankamar nan ba,ganin sun mayar da hankalinsu wurin ciyawar ita kuma ta samu wani katon dutsi a gindin wata katuwar itaciya ta zauna, time to time takan juya tana dan waige waigen ta wai ko taga safwan,amma shiru.

Can wajen sha biyun rana tana nan zaune tana ta kallon shanunta,domin har ta fitar da ranta da zuwan safwan,kawai sai taji wani lallausan hannu ya rufe mata idanuwa.

Da farko ta dan tsorata,don tana ta magana amma sai taji shiru ba a amsa mata ba,jikinta ne ya fara rawa saboda duk tunaninta sai ya koma ga ko wani mugu neh yazo inda take gashi babu kowa wajen sai ita kadai bare ta sa ran mai ceton ta.

Roko ta farayi muryarta tana rawa,"don Allah wanene,kayi mani magana mana,kada ka cutar dani."

Jin yanda jikinta keyi ne yayi maza ya juyo da ita tare da bude mata idanuwan yana yi mata dariya.

Ganin shine yasa tayi yar ajiyar zuciya ta harareshi tace,wallahi ka tsoratar dani dayawa,domin ji nayi kamar ma mutuwa zanyi don tsoro."

Dariya ta kara bashi don kuwa har yana tafa hannu.hawayene taji sun taram mata acikin idanuwa taji kamar ta fashe da kuka don takaicin dariyar da yake mata,wai dami zataji? Shin tsoron da ya bata ko kuma da dariyar muguntar da yake mata?

Mikewa tayi afusace ta nufeshi shi kuma yana ganin haka sai ya juya ya ruga,haka sukayi ta zagaya wajen da gudu tana kawo mashi duka da sandarta yana kaucewa har sai da ya lura ta gaji sosai sannan ya tsaya.

Da kyar ta iso inda yake,shi kuma ya gumtse dariyar da yakeyi saboda ya fahimci itace take hassala ta,don haka tana isowa itama tsayawar tayi tana share wasu hawaye da suka zobo mata cikin shagwaba irin ta sangartaccin ya'ya.

Kara matsowa yayi gaf da ita yana murmushi yace,"yi hakuri baby tah," daga hannu tayi ta dokeshi cikin shagwaba,caraf yayi ya rike hannun yana dariya,ai kuwa dariyar daya ci gaba dayi yasa ta kara daga gudan hannun zata dokeshi,shima rikeshi yayi,sannan ya zuba mata sexes eye dinshi yana kallonta.cigaba tayi da dan sharben kukanta na shagwaba.

Gaba daya ya jawo duka hannuwanta ta fada jikinshi,bai jira amincewarta ba shi kuma ya maida hannuwa ya rungumeta tsam ajikinshi.

Love you my fans😘
08033481518
[4/8, 10:21 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

04

Narkewa tayi ajikinshi,shi kuma yaci gaba da rarrashinta yana shafar kanta,kuma acikin zuciyarshi wani dadi neh ya kama shi saboda ganin yanda take kwance akirjinshi ba tare data damu ba.
Can acikin kwalwarta taji molasa ta kira sunanta da karfi tace," ke sodangi,asadda takeyi mata kashedi da maza,akul kika yarda wani namiji wanda baki san shi ba ya tabaki koda hannunki ne,saboda yanzun kin haihu ace kinyi abin kunya...........

Ture shi tayi cicin karfinta tana kallonshi kamar wata zakayya zata zazzaga mashi masifa,amma kuma sai ta tafi ahankali tayi kasa da idanuwanta,komi yasa ta fasa oho.

Juyawa tayi ta kama tafiya zata koma wajen shanunta,
Safwan tsaye yayi yana mamakin abinda tayi mashi,ganin ta fara yi mashi nisa yasa yabi bayanta,amma bai tanka mata ba har ya samu ya isketa tunda tafiyar ta ta ahankali takeyinta.

Kallonta kawai yayi yaga ta daure fuska sam babu wani fara a atare da ita,gindin iccen ta nufa ta koma kan dutsinta ta zauna,shima gefenta ya samu ya zauna yaci gaba da kallon shanun.

Dan minti biyu suka dauka babu wanda yayi magana sannan ya dan juyo ya kalleta yana murmushi,tare da yar harararta yace,"I'm sorry sodangi👏

Duk da bata san abinda yace ba,amma kalmar tayi mata sanyi acikin ranta,itama harararshi tayi tace,"bana so ne shi yasa,kuma molasa tace idan har na yarda wata rana zan iya haihuwa."

Jin abinda ta fada sai da yasa gabanshi ya fadi yaji kamar ya ruga saboda radhin gaskiya,amma da yake yq goge,sam bai bari ta gane ba sai yace," mi za ayi maki har ki haihu sodangi?"

Dan sumbura baki tayi ta kalleshi tace,molasa cewa tayi idan yarinya na barin maza suna taba mata hannu cewa za ayi yar iska ce kuma a haka har sai ta haihu."

Tsaf ya gane abinda take nufi sai yayi dariya ya zuba mata ido yace," nima yanzu tunda na tabaki na zama dan iska kenan koh?"

Zaro idanuwa tayi tace,"ni dai bance ba,dama molasa ce tace." Daure fuskarshi yayi ya mike tsaye yace toh shikenan tunda dai kin zage ni bari inzo inyi tafiyata don kada ki haihu kice ni neh."

Yana fadar haka ya juya ya fara tafiya yana takaicin yanda sukayi da sodangi.ita kuma zuba mashi ido tayi tana kallonshi,amma zuciyarta tana nadamar abinda ta fada mashi, sannan kuma tana tunanin shike nan ita dashi bazata kara ganinshi ba.

Mikewa tayi tsaye taci gaba da kallonshi,can sai ji tayi ta kwala mashi kira ba tare data sani ba,kin jiyowa yayi,kuma yaci gaba da tafiya,amma kuma kiranshi da tayi yasa yaji wani irin dadi acikin ranshi.

Tafiya ta farayi tana kiranshi,amma baida alamar tsayawa,ai kuwa sai ta fara gudu har ta samu ta iskeshi tasha gabanshi tana hawaye.

Tsayawa yayi kawai yana kallonta,kuma sai yaji ta bashi tausayi,saboda har acikin zuciyarshi yana jin yarinyar,kuma daya isa aure babu abinda zai hana ya aureta amma idan tana da ilmi da wayewa,ahalin yanzu kuwa idan ya aureta gaskiya yaci baya kuma sannan abokanshi zasu iyayi mashi dariya.

Dan daure fuskarshi yayi yace," ki bani hanya in wuce,tunda dai baki son gani na kusa dake." Yana fadar haka ya raba ta gefenta zai wuce,wuf tayi ta rike mashi hannu tace,"don Allah kayi hakuri, kada ka tafi da fushinah."

Dariya yayi yace,mi yasa zaki tsaida ni,ko dai kina so na neh?"Kada kai tayi da sauri tace,wallah bana sonka sai dai ina so ka tsaya muyi labari." Murmushi yayi yace," toh kiyi hakuri tunda baki so na dole neh in tafi in barki sodangi."

Kara rike hannunshi tayi gam tace,nace fa kayi hakuri,kuma ardo ya fada mani duk wanda akace yayi hakuri yaki,toh ya zama shaidan."

Tabbas yasan abinda sodangi ta fada gaskiya neh,kuma mah miye tayi mashi wanda bazai iya hakura ba? Don haka murmushi yayi yace," toh shikenan na hakura sodangi,amma kuma ni da kikace baki sona toh ni ina sonki sodangi ina kaunarki."

Duk da bata da wani cikakken hankalin manya sai na kurucciya,amma kalmar tayi mata dadi har acikin zuciyarta,don haka da sauri ta saki hannunshi taji wata irin kunya ta kamata har bata iya hada ido dashi.

Murmushi kawai yayi ya kalleta yaga har yanzu kan nata asadde yake,sai ya dubi agogon hannunshi yaga har daya da rabi tayi.

Dagowa yayi ya kalleta yace,"yanzu ina shanunki suke?" Cikin dubara ta daga kanta tana dan dube dube,can tace," gasu can wuri." Shima daga kai yayi ya kallesu yace," okay,dama gani nayi lokacin sallar azahar yayi don kada muje yin sallah su kama gabansu.

Kada kanta tayi tace,"ai bazasu tafi ba har sai idan ni na korasu ko wani ya kore su." Murmushi yayi yace,toh zo muje wajen motata mu dauko kayan da zamuyi amfani dasu,sai mu komo inda zamu rinka hangensu,don kada su gudu yau ardo ya daki wata yarinya.

Dariya tayi tana mamakin abinda yace,can dai ta gaza shiru tace,hai koda duka shanun nan zasu bace ardo bazai taba duka na ba,kuma duk inda sukaje idan lojacin dawowarsu yayi zasu koma gida."

Murmushi yayi tare da yar harararta yace,"lallai ashe dai ke yar gatan ardo ce, saboda nasan dai yanda bafullani yake son shanunshi,amma ardo zai hakura dasu."

Dariya ta rinkayi saboda yanda taga wai yana mamaki,ta sani don dai bai san yanda ardo da molasa da yaya sada suke son ta ba,amma da bayyi tunani ba.

Shi kuma hakan da tace neh ya gane,lallai sodangi yar gata ce awajen iyayenta kamar yanda yake shalele,don shiyasa yake tsula tsiyarshi yanda yake so.

Wurin motar suka isa ya dauko wata katuwar darduma da wani kwali cike da ruwan roba (swan water) sai wata leda duk kayan ci ne akayi take way din su da su chocolate da biscuit da chewing gum da sauransu,sai kuma wata malun malun (babbar riga) itama dauko ta yayi.

Ledar kayan ciye ciyen kawai yaba sodangi ta dauka shi kuma duk ya dauki sauran har suka koma wajen babbar itaciyyar.

Shimfida yayi masu ya dauki ruwa ya koma gefe daya ya fara alwallar,juyowa yayi ya kalleta yace,kema zo kiyi alwallar mana.

Girgiza kanta tayi tace,"sai na koma gida nayi,tunda dama haka nakeyi duk sadda nazo kiwo." Kiranta yayi yai mata alama da kanshi na tazo.

Nufarshi tayi ta tsaya gefenshi,mika mata ruwan yayi, ta kalli ruwan tace,kai safwan wannan kuwa ba almubazzaranci bane,ya za ai inyi alwalla da ruwa mai zaki?"

Dariya yayi sosai har yana kyalkyatawa yace,"waya fada maki yana da zaki?" Mika mata yayi yaci gaba da cewa,"sha kiji."

Amsa tayi ta sha,sai taji shi salaf.Dariya tayi ta kalleshi tace,"laa hai kuwa ashe baida zaki,cai nake zaki gareshi wallah.

Gyarawa tayi tai alwallar kusa dashi, shima duk sai da yaci ta gyara,ahankali yayi ta koya mata har suka gama.

Wannan babbar rigar ya mika mata yace ta lullubata,itama ta tsaya bata san yabda zatayi ba,matsowa yayi ya lulluba mata ita yana dariya har yana dungurar hancinta yanayi mata tsiyar bata iya komai ba.

Tate sukayi sallarsu suka gama,sannan ya dauko snacks din daya sawo ya bude agabanta yace taci.dayake ta fara sakin jiki dashi,hannu tasa ta dan tsinci abinda take iya ci,saboda ba komai ne ta sani ba.

Sai maraice lis sannan safwan yayi bankwanq da sodangi ya koma katsina,ita kuma ta juya ta nufi cikin rugarsu zuciyarta cike da tunanin safwan da irin dabi unshi kyawawa.

Washe gari ma haka akayi,tana wajen kiwon ya sake samunta,wannan ranar tafi sakin jikinta dashi fiye da jiya,sai dai bai dade ba akayi kiranshi ta waya,duk tana jin shi yana wayar yana ba yar da hakuri har yace,gobe zai zo.
Chapter 3 · 0% Book details