← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 45

Sashe 4

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru tayi har ya gama wayar,ita babu abinda ya burgeta irin abinda taga yana magana dashi, saboda arugarsu mutum daya neh yake da ita,kuma danshi ne daya tafi lagos ya kawo mashi don ya rinka magana dasu.

Bayan ya gama wayar ya kalleta tare da daga girarshi yace,"ya neh?"murmushi tayi tace,"abin maganar neh ya burge ni."

Dariya yayi ya mika mata wayar ta amsa tana dubawa har zuwa lokacin daya mike tsaye yace mata zai tafi,kuma yana ganin gobe bazai zo ba sai dai jibi.

Itama mikewar tayi tare da mika mashi wayar tana cewa,"gashi abin maganarka." Dan murmushi yayi ya kalleta yace," ki dauka na baki ita,kuma ba abin magana ake ce mata ba,phone zaki ce."

Da kyar ta iya cewa phone din,shi kuwa yayi tayi mata dariya har suka isa jikin motarshi sannan ta karamika mashi.

Kada kanshi yayi yace,"da gaske fa nake,ki dauka duka na baki,saboda ina dasu da yawa,kuma idan kina so zan kawowa ardo da molasa suma tasu."

Girgiza kai tayi tace,"ko ka bani ita bazan ita amfani da ita ba,ka barta kawai,kuma kilama idan ardo ya ganta yau sai yayi fushi dashi dani."

Dan murmushi yayi yasa hannu ya amsa yace,"ni kuma safwan bana son ran sodangi nah ya bace,amma ko ba dade ko ba juma kema zakiyi amfani da irinta ko ma wadda tafi ta."

aikuwa wani dadi neh ya kamata tayi murmushi tace,"toh Allah yasa."

Tun daga wannan ranar da safwan ya tafi bai kara dawowa wajen sodangi ba sai da ya kwashi wajen kwana goma babu shi babu labarinshi,ita kuwa sodangi gaba daya ta shiga damuwa saboda rashin ganinshi,kullum idan ka ganta cikin tunani take,gashi ta gaza fadawa kowa bare ta samu saukin abinda takeji.

Molasa ita kanta ta fahimci akwai wani abu atate da yarta,saboda kwata kwata wannan surutun nata duk ya ragu sai dai ta zauna tayi jugum,kuma idan ta tambayeta sai tace mata babu komai.

Ba tayi shawara da kowa ba ta fada daji ta ciccirowa sodangi magunguna saboda molasa irin mutanen nan da basu wasa da lafiyarsu,duk abinda tasan zai amfaneta ajiki ko yayanta nemo abin take kuma ta bashi muhimmanci har sai taga an wadatu dashi.don haka ko yanzu ma magunguna ta samo tare da addu o in tsari wurin malamai don gudun ko aljannu neh suke son shafar mata diya.

Duk abinda aka bata bata musun shanshi,amsa kawai take kuma tayi yanda akace mata,amma kuma duk halin da ake ciki bata fashin zuwa kiwonta,don ko an hanata sai ta nace ta tafi wai duk tunaninta zata gamu da safwan.

🍒🍒🍒

Shi kuwa safwan tunda ya rabu da sodangi kai tsaye abuja ya nufa,saboda daddyn shine da kanshi ya kira shi ta waya,shi yasa bai da yanda zaiyi dole ya amsa kiran.

Lokacin da yayi parking a harabar gidan inda sashen motocinshi su,cikin gidan ya nufa,babu wanda ya samu afalon tunda yasan babu kowa sai umminshi da masu aikinta.

Kai tsaye dakinta ya nufa ya sameta tana sallar magriba,don haka shima toilet dinta ya shiga yayi alwallah ya koma gefenta ya gabatar da tashi magribar sannan yayi addu o inshi ya shafa,zuwa lokacin ita kuma ummin take jiranshi.

Dago idanuwanshi yayi ya kalleta cikin jin nauyi,saboda yasan zuwa wannan lkcn fushi takeyi dashi tunda wurin kwana ukku babu wanda yasan inda yake.

Zuba mashi ido tayi tana kallonshi tace," safwan barka da dawowarka gida." Gaza amsawa yayi,don haka yanajinta taci gaba da cewa," daga ina kake."

Sai alokacin yayi dariya saboda tambayar dayaji yace,ummi don Allah ki daina bata ranki akaina,nifa Namiji neh kuma ba yaro ba,amma kina tambayata daga ina nake."

Dafa kafadarshi tayi tace,haba safwan,ai koda kaji na tambayeka to don na damu da kai neh,kuma bani da wanda yafi ku awurina kai da dan uwanka,toh dammi kai kuma baka son kwanciyar hankali nah?"

Dan murmushi yayi ya langabe kai yace,"yanzu ummi ni mi nayi maki? Saboda duk iyakar sani nah banyi maki laifi ba."

Harararshi tayi tace,ka sani safwan idan har kayiwa daddy dinka laifi toh tamkar ni kayi mashi, ka tafi ka barmu kullum daddy dinka baida wata magana sai taga,ya kira uncle dinka dake katsina yace rabonshi da kai tun ranar da kukaje kai da idi driver,kuma duk wayoyinka idan aka nema switch up,toh don mi hankali na bazai tashi ba?"

Dago idanuwanshi yayi ya kalleta yace,"ummi shima daddy yaki ya gane abinda nake nufi neh." Dan shiru yayi tare da yamutsa fuska shima zai shagwaba sannan yaci gaba da cewa ,"maganar tafiyata a broad ni nace ba yanzu zan tafi ba." Daure fuskarta tayi tace,"saboda mi? Tun yaushe ake tambayarka,amma duk hujjojin da kake kawo wa babu na kamawa,saboda abinda na fahimta ka biyewa abokan banza suna neman su hana ka cigaban rayuwarka koh?sai dai kawai kuyi ta yawon banza na ba gaira ba dalili."

Shiru yayi tunda yasan gaskiya take fada mashi,sai da ta gama sannan ya dago ya kalle ta yace,"kiyi hakuri ummi nah,kuma don Allah ki daina sanya abinda nayi acikin ranki,don bana son ciwo ya kamaki."

Murmushi tayi saboda dama duk sadda zata zauna dashi tanayi mashi nasiha haka yake ce mata,don haka sai tace,"idan har da gaske kakeyi akan abinda ka fada why not ba zakayi abinda mahaifinka keso ba?"

Ganin yanda take ta fada yasa yaji ta bashi tausayi yace,okay! Okay!! Ummi ya isa haka nan,kuma insha Allahu daga yau kin daina fada amma nima sai anyi mani abinda nake so."

Kallonshi tayi anatse tace,minene kake so,har kake ta wahalar da kanka?"
Murmushi yayi ya zuba mata ido don yaga yanda zata amshi maganar yace,"aure nake so kuyi mani."

Zaro idanuwa tayi😳 tace, "what? aure lallai safwan kana da aiki agabanka,domin kasan daddy bazai taba yarda da wannan zancen ba."

Murmushi yayi yace," mi yasa ummi? Watau kun fi gane inje inyi duk abinda naga dama da kuyi mani aure koh?" Jin jina kanshi yayi yaci gaba da cewa,"okay babu komai,duk zanyi abinda kukace but nan gaba don't blame at me."

Mikewa yayi zai tashi ta yi maza ta tsayar dashi cikin tashin hankali tace,wait safwan,yanzu ina zaka?" Ranshi bace ya juyo ya kalleta yace,haba ummi ba nace ki dai na bata ranki ba,kuma ai nace babu inda zani har sai naga daddy."

Yanayin da yayi neh kuma sai ya bata tausayi,don haka sai ta mike ta iskeshi inda yake tsaye tace,"ka kwantar da hankalinka,ni idan daddy din ya dawo zan kwatanta mashi akan maganar auren da kakeso kayi,amma wacece yarinyar da kakeso kuma yar wacece?"

Wani dadi nehya kamashi yace,kai thank you very ummi,idan kikayi mani wannan taimakon ni bazan taba mantawa ba." Don haka zama yayi yai mata bayani komai akan sodangi,babu abinda ya boye mata don hatta da shekarun sodangi sai da ya fada mata.

Irin girgicewar data nuba yasa
[4/8, 10:21 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

05

Irin gigicewar da ya gani a fuskarta yasa ya dan sha jinin jikinshi ya zuba mata ido,"No No safwan,wai duka nawa kake da zaka dami kanka akan sai kayi aure?" Abinda kawai yaji ya fara fitowa kenan daga bakinta.

Don haka runtse idanuwanshi yayi yaci gaba da sauraronta," ni wannan zabin naka sam bayyi mani ba saboda kai kanka kasan yarinyar daka kiyasta mani she's not your type, toh miye abin garaje aciki?"

Dan numfasawa tayi sannan taci gaba da cewa," as your age wai duka nawa kake, ko baka ganin dan uwanka ma daya girmeka bayyi aure ba sai kai,toh ban amince ba,kuma idan zakaji shawarata ma kada ka sake ka tunkari dad dinku da wannan maganar,don wallahi zai ture duk wata kauna da yake maka ya ci mutunchinka,karshe ma kuma ya yanke maka hukuncin da bazaka taba tsammani ba."

Tunda ya rufe idanuwanshi bai bude su ba har sai da yaji tayi shiru sannan ya cirasu da kyar ya kalleta,ita kanta jikinta yayi sanyi da irin kallon,amma ganin ya raba ya wuce bai ce komai ba yasa tadan maida numfashinta ta juya cikin dakinta tana mamakin yarinyar da safwan zai aura wai 14yrs.

Hankali tashe safwan ya fada dakinshi,kwanciya yayi rigingine akan gadonshi yana kallon fan din da take juyawa ahankali,sai kuma can kasan zuciyarshi tunani ne fal acikinta,"shin wai sai yaushe neh parent dinshi zasu gane abinda yake nufi,saboda wannan shine Karo na biyu daya kawo masu zancen aure amma suka ki saurarenshi."

Wuf yayi ya mije zaune gami da damkar zanin gadon dake jiki yaci gaba da tunaninshi," ni mutum ne mai tsananin bukatar mace akusa da ni,kuma suna sane amma suka share,tunda sunajin irin aika aikar da nakeyi acikin gari,amma damuwar da suke nunawa kadan ce akan idan nayi masu furucin aure,"

Numfasawa yayi tare da murmushin takaici ya fada afili,"sodangi tabbas ina sonki,kuma zuciyata batajin dadin yin tunanin bata rayuwarki kamar yanda na bata ta wasu 'yan matan,toh miye solution?"

Mikewa kawai yayi ya nufi toilet dinshi,ruwa ya sakarwa kanshi don ya samu saukin tunanin daya ishe shi,ya jima sosai acikin ruwan,sannan daga bisa ni ya fito.

Shiri yayi tsaf acikin kananan kaya,ke mai karatu da kin kalleshi sai ya burgeki,toh ballanta na yan matan da suka mutu kanshi.

Wayarshi ce tayi ruri har ta katse bai ko kalleta ba saboda gyaran gashin kanshi daya dukufa yi,akaro na biyu ne tana farawa yayi dan tsaki ya suri wayar rai bace yace,"alo."

Muryar dayaji ne yasa ya dan saki ranshi saboda kwana biyu yayi missing din mai muryar,ita kuma sai ta fara lankwashe harshe cikin yaudara da kinaya tace,sweet heart wai yaushe zakazo gareni neh,saboda har yanzu gaggan jikina ya kasa amincewa da kowa sai kai,ka taimaki rayuwata because I miss you so much😘."

Murmushi yayi saboda jin abinda tace,shima kanshi yasan yayi missing dinta na kwana biyu,saboda tana daga cikin yan matan da suke dauke mashi hankali har ya fada wata duniya ta daban.

"Kina inah?" Abinda yace mata kenan,wani dan ihu tayi tace," kada kace mani dai kana cikin gari?" Dariya yayi yace,"yes my dear,gani nan zuwa gareki."

Jin abinda yace yasa ta ware ta hau yi mashi bayanin inda zai sameta,akarshe dai club sukayi mahada.

Tunda safwan ya fita bai dawo gida ba sai karfe ukkun dare,shima don dad dinshi yasa mashi dokar indai yana gari toh ya tabbata ya kwana gida,amma da kila dai sai gari ya waye.
Chapter 4 · 0% Book details