Sashe 44
Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Safwan yayi dif saboda yanda daddy yake ta daureshi da jijiyoyin jikinshi,don gaba daya rasa yanda zaiyi yayi,don sai da daddy din yace,"kai safwan ! Kana jina kuwa?"
Da sauri ya amsa yace,"yes dad ina ji,kuma zanzo din."
Mahaifin safwan ya kashe wayar cikin yin fuska babu wat dariya.
Hajiya ummu salma dake gefe a kagare da son jin yanda sukayi dashi ta kara matsawa kusa da maigidanta tace," ya kukayi dashi ?"
Wani murmushi ya saki yana kallonta yace,"yau safwan zai dawo insha Allahu, saboda babu musu babu gardama,domin idan da yayi daya daga cikinsu to tabbas alamace ta baxaizo ba,don haka sai kisan dubarar da zakiyi domib na nuna mashi kina cikin hali."
Daboda jin dadin danta safwan zai dawo gida yasa takejin sam bata iya rufe bakinta,don haka nan da na ta kira khadija matar yusuf tac fada mata dawowar safwan ayau,don haka tana son ta shiryo mata su afnan da junior tasa driver ya kawo mata su."
A gain kuma ta sake kiran wayar amaryar safwan watau HUMAIRA ta fada mata dawowar safwan ayau,don haka tana son tayi shirin tarbar angonta😜
Kamar yanda ya faru agidan humaira,hakace ta faru agidan sodangi.
Hajiyar dake kai mata ziyara kullum,ayau ma tazo,bayan yan tambayoyi kadan don sanin halin da sodangin take ciki sai tace mata,"yau ne ranar da angonki zai zo gareki,don haka ina son ki kimtsa kanki tare da sanya ma aikata su kara kalailaice maki ko ina na gidan,saboda mijinki abocin tsafta ne da son ado da kamshi."
Gaban sodangi ne ya shiga halbawa da karfi don ji take tamkar zai rabe gida biyu,amma kuma sai daurewa take don batason wannan hajiyar mai daraja da karamci a idonta ta fahimci akai firgita atare da ita.
A yau Hajiyar bata dauki wani dogon lokaci ba ta mike tace,"toh sodangi zan tafi,kuma idan mijinki ya dawo bance kiyi banza dashi ba,nasan baki sanshi ba,amma ki daur ki jure,ibsha Allahu cikin kwana biyu zaku saba ke da shi."
Sodangi cikin jin kunya ta rusuna tace,"insha Allahu Hajiya,zan kasance mai bin umurninki,domin baki da wani bambanci atsakaninki da mahaifana,kuma na gode da duk shawarwarin da kike bani."
A haka suka rabu Hajiyar nan taji dadi kwarai da gaske,kuma ta yaba da tarbiyyar sodangi dari bisa dari,don haka ta shiga sawa sodangi albarka,kuma bata fasa ba har sai da ta shiga motar data kawo ta suka tafi sannan sodangi ta juyo jiki asanyaye ta koma cikin gidan.
Zubewa tayi afalo tana kallon tire din jus da ruwan data kawo wa Hajiya tare da tunanin maganganun data fada mata akan mijinta.
Kawai bata farga ba sai ji tayi ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya,don haka mikewa tayi da gudu ta nufi dakin datake kwana tunda tazo gidan,kuka taci mai isarta har daga karshe wani irin barci ya kwasheta maraddadi.
Safwan kuwa tunda sukayi waya da Mahaifin shi sai ya gaza zaune ya gaza tsaye sai sintiri yake atsakar dakin kamar wanda yayiwa sarki karya.
Gaza jiran Tahir yayi ya farfado kawai ya yanke hukuncin tafiya shi kadai saboda zuciyar shi ta kagara yaga halin da mahaifiyyarshi take aciki.
Duk abinda yake bukata nashi ya dauka ya kuma rubutawa Tahir dan Note ya ajiye mashi inda yasan zaiganta sannan ya fice daga dakin cikin sauri tare dayin addu ar Allah yasa kada ya samu wata matsala afilin jirgi don xuwa Nigeria.
Around five ya isa gidan iyayenshi,duk da gajiyar dake jikinshi,amma azama kawai yake don yaje yaga lafiyar umminshi.
Afalo ya gamu dasu afnan suna ta wasansu,ai kuwa yana ganinta sai wani farin ciki ya kamshi da jin tausayinta,ai kuwa da sauri ya nufeta ya kamata ya rungume ta ajikinshi yana cewa,"I miss you my doter! I miss you!!
Afnan na ganinshi ta gane shi itama makalkaleshi tayi sosai tana kwaratsin daddy oyoyo oyoyo oyoyo,shima junior rugo wa yayi da gudu yaje ya makalkalshi yana murna ganinshi.
Wannan kwaratsin dasu afnan sukeyi na ganin daddyn su ne ya fargar da umminshi tazabura da sauri ya haye bisa gadonta ta lullube da katon bargonta ta mashashshare tare da juye idanuwanta yanda kasan ta wahala sosai haka ta koma.
Safwan yayi sallama a dakin umminshi yaji shiru sai jikinshi ya karayin sanyi da sauri ya saki hannunsu afnan ya nufi uwar dakinta ya sakeyin sallamar.
Amsawa tayi can kasa kasa kuma da kyar,shi kuma yana shiga kai tsaye bisa gadon ya haye har inda take akwance ya jawo kanta ya for abisa cinysrshi yana hawaye yana cewa,"ummi nah miya sameki,kiyi hakuri ki tashi ga danki ya dawo."
Hajiya ummu salma ta rinka numfashi sama sama ta kalleshi tana kokarin yin murmushi na karfin hali tace,"haba dana ! Ya zaka tafi ka barni cikin tunaninka? Sannan kuma ban san awane irin hali kake aciki ba."
Safwan ya kara tallafar kanta yace,"kiyi hakuri umminah,gani na dawo cikin koshin lafiya,kuma babu abinda ya same ni."
Hannu tasa ta shafi fuskarshi tace,"naji dadi safwan Allah yayi maka albarka,sannan kuma ina rokon wani arziki awajenka safwan ðŸ‘
Safwan cikin sauri ya rike hannuwan datake rokonshi dasu yace,"haba ummi nah ki daina don Allah ki daina rokona,ni danki neh,don haka umurni kawai zaki bani,ni kuma insha Allahu zanyi maki biyayya.
Wani farin ciki neh ya shiga acikin zuciyar ta,amma sai ta dake ta dafe kanta tace,"inason kayi hanzari ka tafi gidanka,saboda amaryarka da aka kawo maka tana nan har yanzu tana zaman jiranka,ka taimakeni kaje ka zauna da ita har karshen rayuwarka.
Wata faduwar gaba ce ta diro mashi yaji kamar ya baje akan gadon saboda yanda yaji ta daki zuciyarshi.
Hadiye miyau yayi da kyar ya kalleta da idanuwanshi masu rauni yace,"insha Allahu ummi zanyi abinda kikace mani."
Ita da kanta tayi mamakin jin abinda danta yace,sannan acikin zuciyarta ta kara godewa Allah da danta yacanza hali ya zama mai biyayya,tashi tayi da kanta ta zauna tana murmushi tace,"Allah yayi maka albarka safwan,ya kuma albarkaci dukkan zuri arka,maza ka tafi safwan, kuma nima daga yau bazaka sake gani nah akwance ba,tunda kayi abinda ya dace da rayuwarka,kuma ka faranta ran iyayenka."
Dafa kafafuwanta yayi yana murmushin karfin hali ba tare dayace mata komai ba ya kama hanyar fita dakin duk jikinshi asanyaye.
Ita kuwa sodangi tunda ta kwanta wannan barcin mai nauyi ya dauketa,itace bata farka ba sai wajen la sar ta farka ta mike da sauri ta duba lokaci,gabanta ne ya fadi data tuna da maganar da sukayi da wannan hajiyar,kuma gashi don karfin hali har wani alkawari tayi mata.
Fita tayi jikinta asanyaye ta nufi wajen yan aikinta ta duba abubuwan da sukayi,yaba masu tayi sannan ta sanya daya daga cikin ma aikatan ta jera abincin da sukayi a dining table,sannan ta koma dakinta don itama ta shirya jikinta kamar yanda tayi alkawari.
Sai yau sodangi ta bude akwatunan data gani adakin amatsayin na lefenta tadan dudduba kayan taga duk kusan dinkakkune,kuma anyi design masu kyau da burgewa.
Wata riga ta dauko ta shadda Yellow anyi mata aikida red zare kuma zubin bubu style,kallabin rigar shima red ne,don haka sai ta samu takalma red axcikin lefen 'yan flats shoe.
Kwalliya tayi yar simple mara hayaniyya afuska sannan ta zira kayan ta koma kan gashin kanta shima ta fesheshi da turaren gashi,sannan tasa ribom ta daureshi waje daya sauran ya sauka akan kafadarta sannan tabi da daurin kallabi irin na wannan