Sashe 14
Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Arana ta ukku ne tana kwance tana barci sai kawai molasa taga ta zabura ta tashi tare da kwalawa safwan kira tayi hanyar kofar gida.inda Allah ya taimaki molasa cewa sadah yana nan zaune,domin tun faruwar wannan al amarin, sadah ya daina zuwa ko ina,idan bai zaune wajen sodangi duk yasan bazace mashi komai ba,toh yana zaune kofar gida.
Ganin sodangin waje yasa ya mike da sauri ya nufeta,itama din tana ganinshi ta nufeshi ta rike tana tambayarshi "ina safwan? Kazo muje ka rakani gidah saboda yana can yana jira nah."
Tausayinta ne ya kamashi yasa karfi ya riketa gam,ita kuma sai sambatu take kamar wadda ta zare.girgizata yayi da karfi ya kira sunanta yace,"sodangi! Ki saurareni mana."
Tsayawa tayi cak tana kallonshi saboda tsorata da yayi wajen ihun kiranta,ganin ta saurara sadah yaci gaba da cewa, "dubi yanda kika fito,ko kina tsammanin idan safwan ya ganki ahaka zaiji dadi?"
Kallon kanta tayi taga daga ita sai doguwar riga babu mayafi ajikinta,sai ta kada kanta tace,"a a yaya sadah."sunanshi data kira yasa yaji wani dadi ya kamashi,domin alamace ta hankalinta ya dawo jikinta.
Hamdala yayi yace,"toh muje cikin gida,kinga molasarki can tana kallonki."daga ido tayi ta hango molasa tsaye abakin kofar gidan.
Juyawa tayi suka koma cikin gidan gaba dayansu,sannan sadah yayi dubara ya zaunar da ita bisa yar kujerar tsakar gida ya koma dakinshi ya dauko wannan takardar ta safwan.
Amma kamin ya bata ita sai da yayi mata nasiha mai shiga zuciya,sannan ya mika mata.
Amsa tayi ta fara dubawa,ai bata kai karshe ba ta fashe da sabon kuka saboda komai ne ya dawo mata tsaf acikin kanta.
Molasa ta matsa kusa da ita tana bata hakuri,amma sai da tayi mai isarta sannan ta lafa don kanta.
Kuma tundaga lokacin ta dauki dangana ta sanyawa ranta,saboda molasa ma bata zauna ba wajen samo addu o I wajen malamansu,kullum cikin karantasu take tana tofa mata aruwa tana bata.
aikuwa cikin sati biyu Sodangi ta warware sai dan abinda ba a rasa ba,domin ita kanta ganin yanda dan uwanta ya damu da ita da iyayenta yasa take kauda kanta daga tunane tunane.
Amma kuma mee?ji take jikinta yana canzawa,kullum sai ta kwana da masassarar dare,ga cikinta ya fara gaza daukar ko wanne abinci,dataci sai tayi amai.
Love you sis😘
08033481518
[4/8, 10:27 PM] binta garba: ðŸ’ðŸ’ðŸ’SODANGIðŸ’ðŸ’ðŸ’
Na
Binta garba saleh daudawa
22
I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thank you and love you all😘😘
Masoya na ina godiyya,saboda sakonninku suna samuna ta waya da online,kuma na gode da addu o inku,Allah ya barmu tare.
Please ina mai baku hakuri,saboda na samu mistake wajen rubuta number, instead in sa 21 sai na kara repeating din 20.
ðŸ’ðŸ’ðŸ’ðŸ’
Sannan kuma sodangi ta fara zabin abinda take so da wanda bata so,duk kan wadannan abubuwan da suke faruwa akan idon molasa,don haka sai jikinta yayi sanyi ta fara zargin diyar tata,kuma tana son fadawa ardo amma tanakin tsoron abinda zai biyo baya.
Yau ma tunda safe tashin sodangi tayo waje ta nufi wurin da molasa take wanke wanke ta duka tana ta kakarin amai wanda yasa duk iyayenta suka yo waje tare da dan uwanta suna kallonta.
Ardo ne rai abace yakeyi mata sannu,ita kuma molasa ta sanya mata ruwa tana dauraye mata bakinta,sannan sadah ya kamata ya rakata dakin molasa din.
Molasa da ardo cikin damuwa suka koma dakin ardo suka zauna,numfasawa yayi yace,"kinsan Allah molasa,idan har yarinyar nan ciki gareta sai na zubar dashi da kaina,saboda banga dalilinshi ba,kuma babu wani amfani da cikin zaiyi mana.
Molasa tayi tagumi cikin damuwa tace,"ardo kada muyi saurin yanke hukunci,mi zaisa bazamu kaita asibiti ba?"
Jin jina kanshi yayi yace,"toh ya zamuyi,ai dole aje asibitin,sai dai kuma idan har akwai cikin bakinku kanin kafarku,don Allah kada ku fadawa kowa,domin ko yanzu garin nan ba tsira mukayi ba sai yan kananan maganganu suke akan auren nan,ni nasan wani abun ma don bai faduwa agabana da cin kashi za a rinkayi mana."
Molasa ta kada kai tace,"haka neh ardo,amma idan muka kauda kan mu ai komai mai wucewa neh."
Ardo yace,"nasan haka molasa,amma ni idan da zaki biye mani da mun matsa gaba,saboda shi mutum ko a ina yake, arzikinshi yana iske shi."
Molasa tayi shiru tana nazarin maganar mijinta,ahankali ta dago kai ta kalleshi tace,"ardo kayi hakuri da abinda zance,saboda shawarar daka kawo ba kinta nayi ba,amma ko zamu bar rugar nan mu bari sai acan gaba ba tare da wani dalili ba,domin yanzu duk wanda yaji mun wuce cewa zaiyi munyi abinda yasha mana kai neh,kuma sannan ayanzu yan rugar nan suna amfanuwa dakai sosai ta fannin ci gaba da rugar ta samu kasan duk adalilinka neh,to shiyasa nake baka hakuri."
Ardo ya jinjina kai yace,"kuma haka neh molasa,wallah kin fadi gaskiya,kuma na gode kwarai da tunasar dani da kikayi,don haka maza ki tashi kije ku kimtsa don ku samu shiga asibitin da wuri."
Bayan sun shirya neh sadah ya rakasu har inda zasu samu motar zuwa karamar asibitin matazu.
Anyiwa sodangi aune aune sosai tundaga fitsari har jini,a inda suka tabbatarwa molasa cewa sodangi tana da shigar karamin ciki na sati biyar, sannan kuma akwai maleria.
Babu abinda ya dami sodangi,saboda ita farin ciki neh kawai takeyi,kuma tana ganin idan har safwan ya dawo ya sameta da cikinshi zai kara sonta matuka,don haka sai kawai ta samu kanta dayin murmushi, ita kuwa molasa abin duniya neh ya dameta tunda taji hukuncin da ardo zai yankewa cikin sodangi.
Ganin farin cikin sodangi afili yasa taji tausayinta tace,"ke kuwa muye abin farin cikin,bayan uban dan ya tafi ya barki da wahala."
Sodangi tayi dariya tace,"molasa wahala kikace fa,ina take?domin ya za ayi samun da ko diya su zama wahala awajen iyayensu?"
Wannan maganar ta sodangi ba karamin gigita molasa tayi ba,don haka sai ta kama hannunta ta samar masu wani waje suka zauna sannan ta numfasa ta kira sunanta tace,"sodangi! Ba ina nufin ya'ya suna zama wahala ga iyayensu,duk inda kikaga haka toh iyayen neh basu ba yaran nasu tarbiyyar data kamata ba,amma ya'ya masu tarbiyya sune wadanda iyayensu suke alfahari dasu kuma sune ya'ya masu albarka."
Sodangi tayi yar dariyarta tace,insha Allahu molasa, abinda zan haifa zai zamo mai albarka kuma duk zamuyi alfahari dashi wata rana."
Molasa ta share zufar data feso mata ta zubawa sodangi idanuwa tana tunanin abubuwa daban daban,saboda yanda taga sodangi ta dauki so da kauna ta dorawa cikin da akace tana dashi.nazari tayi kawai kada ta boye mata komai akan shirin ardo,saboda gaba daya ardo ya tsani safwan da duk abinda ya jibence shi."
Dafa kafadarta tayi tace,"sodangi zan fada maki wani abu,amma bana son ki tayar da hankalinki,don haka kiyi mani alkawarin zaki kwantar da hankalinki sannan in fada maki."
Sodangi sam bata kawo wa zuciyarta komai ba tacewa molasa,"insha Allahu bazanyi abinda bakiso ba molasatah."
Murmushi molasa tayi ta zauna ahankali ta fadawa sodangi komai,sannan ta dora da cewa,kinga ko a shekarunki sunyi kankanta ace kin fara haihuwa yanzu,kuma idan da ina da iko sodangi,dani zan amsar maki haihuwar nan don ki huta."
Bata ankara ba sai gani tayi sodangi tana shirin tuntserewa tunda azaune take,da sauri tasa hannu ta rikota tana salati,sannan ta rungumeta ajikinta tana kiran sunanta.

Binta garba Saleh daudawa
23
I dedicated this love story to my Hausa Novel group & my fans,thanks and love you all😘😘
Sodangi ta bude idanuwanta ahankali tana kallon molasa tare da langabe kai tace,"molasa ! Ardo yana sona kuwa? Mi yasa zai zamo mai son kanshi ba tare da tunanin ni wacce irin rayuwa zanyi ba...........
Da sauri molasa tasa hannu ta rufe mata baki tace,"ya isa haka nan sodangi,don bana son kiyiwa mahaifinki wata fassara ta daban,kuma akul na karajin furucin wai yana sonki,domin fadi bannar baki neh,saboda son naki shi ya jawo mashi halin da yake ciki a yanzu."
Share mata hawaye tayi taci gaba da cewa," ki daina zubar da hawayenki ya isa haka nan,insha Allahu ni zanyi maki tsaye inga cikinki ya zauna cikin koshin lafiya,amma sai idan kin bi shawarar da zan baki."
Sodangi ta kalli molasa tace,"zan iya molasa!zan iya!!
Molasa ta numfasa tace,kinsan goggonki laura dake bichi?"sodangi ta daga kanta tace,"nasanta molasa,kanwarki ce uwa daya uba daya."
Molasa ta kada kanta tace,"idan kina iyawa can zan turaki wajenta,amma kuma kin san zama da laure sai hakuri,saboda koni da nake yar uwarta idan muka hadu bamu wuce kwana daya zata fara nuna mani miyagun halayenta,don haka idan har zaki iya jurewa sai ki koma wajenta da zama har Allah ya saukeki lfy."
Molasa tayi murmushi tace,"zan iya zama da ita molasa."mamaki ya kama molasa sosai,domin batayi tsammanin zatace haka ba,sai kuma jikinta yayi sanyi,saboda ko ita hakuri take da laura toh ballantana yar cikinta🤔.
Kama sodangi tayi ta mikar da ita tsaye suka nufi inda zasu samu motar da zata mayar dasu gida.
Akofar gida suka samu ardo zaune yana jiransu,don haka sai molasa gaba daya taji ta rude saboda mijinta yanayi mata kwarjini da yawa.suna shiga cikin gidan molasa ta nufi bandaki,ita kuma sodangi ta nufi dakin molasa.
Molasa ta jima abandakin har sai da ardo ya soma magana,sannan ta fito da sauri tana share gumi.
Ardo ya kalleta yayi mata sannu,domin shi duk tunaninshi da lalura ta dawo,wata yar inuwa suka samu suka raba sai ardo yace,"tun dazu na gaza zuwa ko ina molasa,zaman jiranku nakeyi."
Molasa tayi murmushin karfin hali tace,"ardo godewa Allah zamuyi ai,saboda yarinyar na typoid da maleria ne sukayo mata caa."
Murmushi ardo yayi gami da godewa Allah yace,"babu komai idan dai wannan neh sai mu nemar mata magani."
Haka kuwa akayi,ardo ya shiga nemawa sodangi maganin gargajiya,ita kuma molasa idan ya bata taba sodangi sai ta samu wani wuri ta juyeshi,yana barin gidan sai ta tona rami ta ruba ruwan maganin ta rufe.
Haka sukayi tayi har cikin sodangi ya tunkari wata biyar,toh alokacin neh hankalin sodangi da molasa ya fara tashi,domin masana ciki da sun ganta zasu iya cewa tana da ciki.