← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 45

Sashe 17

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan data fada yasa ya danji sanyi sanyi,don haka ahankali ya sulala ya mayar da kansa bisa cinyarta ya kwanta tare da rufe idanuwanshi,idan ka ganshi alokacin sai kayi tsammanin karamin yaro neh,saboda har wani dan takurewa yayi acinyarta.

Ahankali taci gaba da shafar sumarshi cikin kulawa da jin tausayinshi har suka iso gidah.

🍒🍒🍒🍒

Tafe suke cikin sauri,sodangi tanayi tana duba agogon hannunta ta dubi kawarta surayya tace,"Allah yasa dai mu samu mota da wuri saboda gani nake kamar mun taushe hannu."
Dan karamin galan din dake hannunta ta sake duba taci gaba da cewa,"ni wallahi duk ji nake wannan galan din da molasa ta hadoni dashi kamar in yarda saboda ji naje duk ya kara takurani."

Surayya tayi dariya tace,"wannan kuma neh baki isa ba,tunda bake taba ba,afnan tace ki kai mawa,idan kuma bazaki dauka ba ni ki bani in rike mata."

Murmushi sodangi tayi ta kalli surayya tace,"yi hakuri kawata,kai na abisa wuya."
Suna isowa bakin titi Allah ya taimakesu sai ga wata mota ktsta matsakaiciyyar,kuma suna daga mata hannu ta tsaya saboda akwai space domin sun ajiye wasu abisa hanya.

Basu bata lokaci ba surayya ce agaba ta fara shiga,kuma ta kofar gaba inda duk mazan motar suke azaune.
Surayya na samu ta tsallaka sai sodangi tabi bayanta,aikuwa wurin kokarin tsallakawa dan galan din madarar shanun dake hannunta ya kufce mata ya fada abisa cinyar wani hadadden matashi wanda baimasan abinda akeyi ba saboda idanuwanshi arufe suke,kuma ga head phone makale akunnenshi.

Faduwar dan galan din marfinshi ya bude,nan da nan madarar shanu ta fara zuba abisa cinyarshi.
Cikin salati sodangi tayi maza ta kama galan din,kuma duk cikin lokacin tasa hannu tana kakkabe mashi inda ta bata mashi.
Zabura yayi ya bude idanuwanshi tare da zare headphones din dake jikin kunnenshi yana kallonta,still bata fasa kakkabe mashi madarar ba saboda kusan arude take gashi mai mota ya fara tafiya bata zauna a sit dinta ba,kuma tana gudun kada ya jefar da ita saboda hanyar bata da kyau sosai.
Sameer yasa hannunshi ya buge hannunta yace,"ke baiwar Allah ya isa haka nan,saboda naga kina neman ki wuce gona da iri."
Sodangi bata fahimci abinda yake nufi ba,ta kara mayar da hannunta wurin tana cewa,"don Allah kayi hakuri saboda bada gangan na zuba maka."
Rike hannunta yayi cikin bacin rai yace,"are you mad?kuma idan bakiyi sannun ba sai nayi kararki because for sexual harassment."

Kwalo manyan idanuwanta tayi,😳saboda sai alokacin ta fahimci inda ya nufa da kalamansa,kallonshi tayi up and down tace,"what!!sannan ta kyalkyace da dariyar rainin wayau taci gaba da cewa,look at you malam,miye ke gareka da har kake tunanin kai kara?toh bazan hana ka ba,amma kafin ka tafi kai karar ka sani,kai din nan baka daga cikin samari da zan kallah bare har tunanin wani abu yazo mani,kuma idan kai baka kaini ba toh ni zan kai ka."tana kai aya wurinta ta nufa taje ta zauna,shi kuma ysyi mugun murmushi yace," ke yarinya 👉nasan baki san ni kowanene ba shiyasa,amma kibi ahankali,domin idan bakinki yaci gaba da fadar abinda rankil keso ni kuma zan baki mamaki."

Sodangi ta zaburo zata sake lafta mashi wata bakar maganar surayya tayi maza ta rufe mata baki tace,"yi hakuri malam don Allah,kuskure neh aka samu."
Girgiza kansa yayi ransa kuma abace ya sake nuna ta da dan yatsa amma kuma bai ce komai ba ya koma sit din shi ya zauna yana ta bata rai.

Sodangi da kyar ta samu ta kufce bakinta daga hannun surayya ta tsikara mashi bakin ta cikin rashin kunya tace,"bance ka fasa abinda kayi niyya ba,domin alokacin ne zanfi gane kaiko wanene koma dan wanene."wani dogon tsaki taja ta murguda bakin ta ta kauda kanta gefe daya tana yan harare harare,saboda gaba daya maza haushi suke bata,kuma kallo iri daya take masu na mayaudara amma banda ardonta.

Tafiya motarsu kawai take,amma sameer idan ranshi yayi dubu ya gama baci akan abinda sodangi ta fada mashi,domin idan banda lalura ma da ya za ai ta ganshi a motar gwamnati.

Maida headphones dinshi yayi akunne ,sannan ya zaro bakin tabaronshi ya sakawa idanuwanshi,saboda gani yake kamar duk yan cikin motar shi suke kallo a matsayin mace ta wulakantashi.

Surayya ce ta zunguro sodangi cikin rada tace mata,"wallahi ki kiyaye wajen haye ma wadanda sukafiki karfi, da ya mareki fah?"
Sodangi ta zaro idanuwan ta tace,wai lallai da kinga abinda zanyi,saboda wallahi da sai na rama ko kuma insa wani acikin motar nan ya rama mani."
Surayya tayi dariya,saboda batun yau ba tasan kawarta da irin wannan karfin halin.

Kano line suka isa motarsu tayi parking,nan danan fasinja sukayi ta fita,masu hawan keke napep suna hawa wasu kuma suna gangarawa da kafafuwansu kasa.

Sodangi da surayya suna daga cikin masu hawan keke napep,don haka sai suka tsaya abakin titin suna jiran wadda zata daukesu.

Wata hadaddiyar motace tazo ta gitta ta gabansu,tayi parking daga gefensu kadan.
Sameer ne ya tako daga inda yake tsaye yazo ya gitta ta gaban su sodangi ko kallon inda suke ma baiyi ba,motarnan ya nufa ya bude gidan baya ya shige,shi kuma driver yaja sukayi gaba.

Surayyace ta dafa sodangi tare da nuna mata, kingani koh,kawai muna zaman lafiya kije ki jawo mana fitina,saboda yau wannan guy din idan da ya iya rigima irin taki nasan da yau sai buzun mu."

Sodangi ta kalleta ta tabe baki ta kauda kanta gefe daya tace,"ko jirgi yazo daukarshi ni bazai firgitani ba.
Adai dai lokacin wata keke napep tazo gabansu ta tsaya,ai kuwa sodangi tayi maza ta shige abinta tace mashi sallari bakin ruwa,surayya itama sauri tayi ta fada cikin motar tana cewa,"kawata tafiya zakiyi ki barni don na fada maki gaskiya?"
Sodangi tayi dan murmushi tace,"ni na isa in tafi in barki,don ko na tafi dole neh in dawo saboda kada ummah ta tuhumeni."

🍒🍒🍒🍒

Surayya itace babbar kawar da sodangi tayi tun komawarta secondry har suka gama suna tare,kuma shakuwar da sukayi yasa har iyayensu suna zumunci da junansu.

Surayya yar asalin garin kano ce a unguwar sallari,kuma iyayenta suma ba masu k,udi bane sai dai kuma suna tare da rufin asirin Allah.

Ganin irin kwarewar da sodangi tayi wurin iya dinki ko wanne irineh yasa surayya takeyi Mata sha awar samun babban wuri inda kwarewarta zata bayyana,domin mafi yawan style din da takeyi wa jama a bawai sai taga samful ba,ita da kanta take zanawa sai dai ka zabe wanda kake so.

Yayar surayya ,watau fatima itace lamarin sodangi yake burgeta ,don haka sai ta amshi result dinta na secondary da testimonial din women center da tayi takai mata wani babban company na designer's and fashion.

Sodangi kuwa tayi sa a company suka nemeta interview shi yasa ta taho gidansu surayya ta kwana don tayi sammako tunda safe don kada ta makara.

Love you sis 😘
08033481518
[4/8, 10:28 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

27

I dedicated this love story to my Hausa Novel group & my fans,thanks and love you all😘😘

Monday 7:00 am tayiwa sodangi abakin company,suna da yawa wadanda za ayiwa interview din,don haka itama layi tabi ta shiga cikinsu ta zauna.

Tana nan ahankali suna shiga suna fitowa har layi yazo kanta,mikewa tayi tare dayin addu a acikin bakinta ta shiga office din.

Office din wani dan madaidaicin daki ne dauke da dogon table ma dan tsawo,sai kusan mutane biyarne zagaye dashi,kowanne daga cikinsu da tulin takardu agabansu sai faman yan rubuce rubuce suke.

Shigowar sodangi yasa duk suka dakata suka zuba mata idanuwa,ita kuma sai faman sunkuyar da kai takeyi cikin ladabi ta gaishesu da kalmar turanci.

Dagowar da zatayi ta kallesu sai kawai tayi arba dashi, duk da fuskarshi rufe take da bakin tabarau sai da ta ganeshi,don haka sai tsoro ya kamata saboda kawai sai jikinta ya bata idan har kuwa ya ganeta da kyar zata samu yin nasara awurin interview din nan.

Fara dan nokewa tayi tare da jan gyalenta tana kokarin rufe gefen fuskarta wai don kada ya ganeta.
Dan murmushi yayi acan kasan zuciyarshi saboda ya fahimci abinda takeyi,baccin kuwa tunda ta shigo ya ganeta,saboda yace bazai taba mance abinda tayi mashi ba.

Zare glass din dake idonshi yayi don ya samu hada ido da ita sosai,domin zaiso dalilin haka ma kada ta samu damar lashe jarabawarta.

aikuwa hakan da yayi ya fara tasiri acikin zuciyarta,saboda ta tsorata sosai,don haka sai ta fara rawar haba maganarta ta fara rawa.

Shugaban kamfanin gaba daya dake zaune tsakiyarsu ya fara fahimtar canzawar da sodangi ta farayi,don haka yayi gyaran murya yace mata,"ki natsu sosai,domin ki samu ki cimma gurinki,idan kuma kikasa wasa ke zaki rasa."

Acikin zuciyar sameer yace,"ai nafison ta rasa tunda bata da kunya",don haka sai ya kara tamke fuska ya jeho mata tambaya da cewa,"duk sauran masu neman aiki suna zuwa da sample din da sukayi don aga irin kwarewarsu,amma ke sai na lura da hannu biyu kikazo."

Sodangi tayi sauri ta bude file din dake hannunta ta fiddo wasu zaninnika da tayi jiya da daddare ta mika ma wanda ke kusa da ita.bayan ya gani ya mikawa na kusa dashi har dai takardun suka iso hannun mahaifin sameer saboda shine shugabansu,kallo daya da yayi masu ya yaba kyan zanen,kuma cikin mamaki ya kalleta yace,"kin tabbata ke kikayi wadannan zanen?"

Sodangi ta dan rusuna kanta cikin girmamawa tace,"nice yallabai,kuma ma ina da wasu design din banda wadannan."sameer ya mika hannu da sauri ya amshi takardun a hannun mahaifinshi ya duba,saboda jin ta fara cika baki don kada tayi tsammanin wai kyau sukayi sai yace,"Abba ai atakardu ba yanda za ai mu iya gane kyan dinki,sai idan har mun gansu practically sannan zamu iya yarda da ita tayi su,saboda zata iya samun wani can daban ya zana mata,kaga kenan mu anyaudaremu kenan."

Tabbas maganar da sameer yayi ta ratsa zuciyar mahaifinshi, don haka sai ya mayar da kallonshi kan sodangi yace,"yama sunanki?"sodangi data fara dakewa da kallon da sameer yake mata,sannan kuma kai tsaye ta fahimci abinda yake nufi sai tace,"sunana sarat Abubakar yallabai."

Mahaifin safwan yace,"da kyau sarat,yanzu wacce shaidace ke gareki wadda zatasa mu yarda dake,saboda idan har da gaske ke kikayi zanen nan to lallai dolene muyi tafiyar nan tare dake,domin na hangi ci gaba aciki."
Chapter 17 · 0% Book details