← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 45

Sashe 32

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari sodangi ta tashi cikin yar wal wala,duk da bata san halin da afnan take aciki ba,amma zuciyarta sawai take.
Cikin dan kankanin lokaci ta gama shirin tsaf ta fito,surayya dake ta duminiyya ita har yanzu bata gama shiryawa ba ta daga kai ta kalleta tace,"sodangi wai saurin miye haka kikeyi,har bazaki tsaya kiyi breakfast ba."
Sodangi tayi murmushi tace,"kinga jiya ban zauna aiki ba,don haka nasan aiki na can jibge akan desk dina,shi yasa nakeso inje da wuri don in samu in kammala shi in time."
Surayya tayi dariya tare da yar harararta tace,"kaji agogo sarkin aiki,amma kuma anyi aiki ciki ba komai?"
Sodangi ta kalli surayya akagare tace,"kada ki damu kawata,idan naje office nayi breakfast din." Tana gama fadar haka tayo waje ta nufi dakin mahaifiyyarsu surayya.
Durkusawa tayi har kasa ta gaisheta,sannan ta mike tace mata,"ummah zan wuce wurin aiki."
Itama taso ta tsayar da sodangi,amma data fada mata uzurinta sai ta kyaleta sannan kuma tabi ta da addu a,wannan hali na mahaifiyyar surayya yana burge sodangi,gashi bata raba daya biyu atsakaninta da yayanta,don wani lokacin ma sai tayiwa sodangi abu ba tayi wa surayya ba,shi yasa itama sodangin take tsaye wajen taimaka mata ga duk abinda take bukata tunda su surayya marayu ne,saboda mahaifinsu ya rasu can shekarun baya.

Tunda dan adaidaita ya ajiyeta wurin company su take zafga sauri,don haka babu bata lokaci ta isa office dinta,sai da ta gama gaisawa da na kasa da ita sannan ta kalli office din sameer,alamomin da ta gani neh ta fahimci bai kai ga isowa ba,don haka sai ta shige nata office.
aiki tayi sosai ba kama hannun yaro,ai kuwa nan da nan ta kammala tsohon aikin dake kanta,don shi kanshi aikin yau din taci karfin shi.
Around 12:00 sameer ya karaso ma aikatar,saboda akwai wasu abubuwa da suka kare yayi odarsu,toh ayau ne aka basu tabbacin isowar kayan shi yasa yayi sakko ya nufi filin jirgin don komai ya sauka akan idonshi,don haka agajiye ya dawo,kanshi tsaye office din sodangi ya nufa yayi knowking.
A can kasa yaji amsawarta,don haka sai ya bude kofar ahankali tamkar mai shirin kama wani abu ya shiga.
Hango ta yayi cikin tulin kaya duk tayi wujiga wujiga sai aiki take kamar yar ina da aiki.
Kyalkyacewa da dariya yayi har yana nunata da dan yatsa yana cewa,"wallahi sodangi kin iya over working,dubi duk yanda kika koma kamar mai jin yunwa."
Zuba madhi ido tayi tana kallonshi da mamaki,watau ashe sameer ya iya dariyar mugunta,don Allah jibi yanda har wani tsalle yake don dariya.
Kin tanka mashi tayi har sai da yayi mai isarshi,sannan ta dafe kanta tace,"wallahi sai yanzu na tuna da ban sanyawa cikina komai ba,"wai sai alokacin kuma ya daure fuska zai farayi mata fada,"so kike ciwo ya kamaki neh?kuma sau nawa kikeso na fada maki."
Cikin fushi yayi waje ya tura daya daga cikin ma aikatanshi yaje ya hado masu abinci shi da sodangi.
Cikin dan lokaci kankani sai gashi da manyan ledoji guda biyu yazo ya ajiyesu akan table cikin girmamawa.
Sallamarshi sameer yayi sannan ya umurci sodangi data taso tazo suci abincin saboda shima yunwar yakeji,don taka maimai shima yau bazaice ga abinda yaci ba.
Babu musu ta taso tazo ta zauna,shi kuma ya zazzage ledojin duka ya dingi tura mata agabanta tana ci,sai da ya tabbatar data koshi tayi dam sannan ya fara cin nashi,amma idanuwanshi suna kanta.
Dagowa tayi ta kalleshi suka hada ido sai yayi mata murmushi tare da daga girarshi yace,"yah ina labari,don bai kamata ki mance da alkawarin da kikayi mani ba."
Sodangi tayi kasa da idanuwanta,kuma sai taji gabanta ya fadi,saboda duk da son safwan yayi zarra acikin zuciyarta,amma kuma bata son abinda zai tashi hankalin sameer domin yayi mata halacci a dan zaman da tayi dashi.
Shirun da tayi ne yasa sameer ya tsaya cak da cin abincin ya kura mata ido yace," ke nake sauraro."
Sodangi tayi murmushin karfin hali ta kalli abincin gabanshi tace,"ka gama cin abincin mana,kaga sai muyi maganar da zamuyi."
Sameer yasa hannu ya ture abincin dake gabanshi yace,"idan dai wannan abincin neh zai hana afada mani abinda na kwana ina tunaninshi toh na koshi."
Sodangi ta bata ranta ta juya mashi baya tace,"ni kuma idan har bazaka ci abincin ba,toh babu abinda zakaji daga gareni."
Fushin da sodangi tayi yasa sameer ya matso da abincin ya rinka cin shi ba don dadi ba,hakanan yayi ta cusa shi saboda gaba daya dama tun jiya jikin shi yayi sanyi akan lallai akwai wani abu atsakanin safwan da sodangi kamar yanda ya fara zargi.

Love you sis😘
08033481518
[4/21, 8:53 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

48

I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘

Dariya yaso ya bata,amma ta gumtseta tare da kauda kanta gefe daya tasha mur,saida taga ya gama ta taimaka mashi ta zuba mqshi ruwa ya wanke hannunshi fes sannan ta tura mashi cup din lemu agabanshi ta gyara zamanta ta fara cewa,"nasan ko ba dade ko ba juma dole wannan ranar zatazo,amma inason ka kwantar da hankalinka kuma ka sanya wa ranka cewar ita matan mutum kabarinsa.
Dam sameer yaji acikin zuciyarshi,kuma nan da nan wani zafi ya taso mashi sai ka rantse dakin babu Ac ko fanka,firfita ya fara da wasu takardu da suke agabanshi.
Ita kanta sodangi bata so ganin abinda yakeyi ba,don haka sai tayi shiru har sai da ya dawo cikin hayyacinshi yace,"ya kikayi shiru? Kici gaba kawai."
Sodangi ta numfasa ta kwashe duk rayuwarta da tayi da auren safwan ta fadawa sameer sannan kuma ta fada mashi wannan hoton daya taba gani na afnan diyar ta ce.
Gaba daya wutar lantarkin dake jikin sameer ta dauke mashi saboda har numfashinshi yaji yana shirin daukewa,da kyar ya samu ya dai daita.
Kifa kanshi yayi akan table din dake gabanshi yayi shiru ya fada cikin tunani kala kala.
Kyaleshi sodangi tayi,saboda sam batayi wani yunkurin yi mashi wata magana ba,domin tasan dole ne duk wanda ta fada mawa cewa ta taba aure har ta haifi diya,sai shock ya kamashi.
A hankali ya dago kai ya kalleta,murmushin da yayi mata ne ya daure mata kai,saboda tasa uwaka ubanka zasuyi ita dashi,don haka sai ta bude gaba dayan kunnuwanta👂👂don taji abinda zai ce.
Numfasawa yayi yace,"yanzu abinda na fahimce ki shine,so kike ki koma gidan safwan tunda he's your ex husband?kuma gashi har ya baki baby koh?"
Gaza amsa mashi tambayarshi tayi kawai sai tayi kasa da kanta saboda wani irin kallo da yake bin ta dashi,sun dan dauki dan lokaci wurin tsit babu wanda ya sake yin wata magana,sannan ta dago kanta still dai ita yake kallo kuma bata san abubuwan da yake kiyastawa acikin zuciyarshi ba,don haka sai ta kauda kanta gefe daya tace,"why not bazaka auri fa iza ba,saboda dai ita fa iza duk da ta girmeni amma kaga ai budurwa ce ba kamar ni ba da har.............
Mikewar da yayi da karfi yasa tayi shiru ta bishi da ido,don tsammanin ta tafiya zaiyi,amma sai akasin haka sai wani duka da taji ya kaiwa table din dake gabansu yace,"No sodangi,kada ki sake hada kanki da wannan yarinyar,saboda kwata kwata ba irin tarbiyyarku daya ba."
Juyowa yayi yana kallonta cikin kunar rai yaci gaba da cewa,"fa iza da kike gani yarinya ce mai tsanin son abin duniya da zalunci,saboda idan ba haka bane miye zata hada kai da wadda naki jini arayuwata,kuma baccin tasan banda makiyar data wuce Hajiya maryam,ta kashe mani mahaifiyya,sannan kuma ta mallake mahaifina saboda ayanzu bashi da mai bashi shawara sai ita."

Ahankali yaja kujerarshi ya sake zaunawa yana kallonta yaci gaba da cewa,"sarat na kwadaitu da tarbiyyarki kuma na amince da dabi unki,please kada ki kini,don wallahi ina tsananin sonki da kaunarki,idan har zaki amince dani ayau ni kuma a gobe zan aure ki.

Love you sis😘
08033481518
[4/24, 4:23 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

49

I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘

Gaba daya sodangi ta fiddo idanuwanta ta zuba mashi tana kallonshi,tare da mamaki fal acikin zuciyarta,domin ita dai bazata ce bata son sameer ba,amma agaskiya tafijin safwan acikin ranta,tana son shi,tana son takonshi da yanda yake tafiyar da ita idan har tana agabanshi.

Numfasawa tayi tare dayin kasa da manyan idanuwanta ta lumshesu ta kara afkawa cikin tunanin ta,can bata ankara ba sai taji ansa hannu an tallabe mata gefen fuskarta yana shafa ahankali.
Ware idanuwanta tayi da sauri ta dago ido ta kalleshi,shi kuwa murmushi yayi mata yace,"mi kike tunani?your husband koh?"
Girgiza kanta tayi,sannan da sauri ta mike tsaye kamar zatayi kuka tace,I'm sorry sameer,kuma please I need your for give ness, saboda bana son anan agaba kace banyi maka dai dai ba,don Allah ka yafe mani.....
Wasu hawayeneh suka da ke makale a idanuwanta suka fara sulalowa,ai kuwa sai ta suri jikkarta da sauri ta nufi hanyar fita daga office din.
Dai dai fitowarta taga alamar wani ya kauce daga bakin kofar,amma da yake hankalinta ba akwace yake ba, sai bata damuba ta wuce da sauri ta na share hawayen dake sauka akan fuskarta.

Ashe tun lokacin da sameer ya shigo companing fa iza take bin bayanshi har zuwa lokacin daya shiga office din sodangi,don haka duka abinda suka tattauna duk akan kunnenta,shiyasa gaba daya jikinta yayi sanyi saboda abinda sameer ya fada akanta,kuma sannan sai yanzu ne tasan asalin kiyayyar dake tsakanin sameer din da matar Abbanshi.
Fitowa tayi daga inda ta labe ta wuce office dinta zuciyarta cike da damuwa tana tunanin abinda zatayi ta wanke kanta awajen sameer.
Chapter 32 · 0% Book details