← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 45

Sashe 26

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Madadin yanda sodangi ta tsara daga farko,watau ta kwana biyu daura ta koma bichi tayi sauran kwanakinta sai ta fasa tunda afnan tana gida,sai dai bata da wata sakewa da ita ibdai ardo yana nan sai idan bai gida,haka ta cija kwanakinta ta fara shirin komawa kano wajen aikinta.
A yanda molasa tasan halayen sodangi sai taga canji wannan karan,saboda tana fahimtar yanda sodangi take matsawa kanta da yawan tunini,domin wani lokaci da molasa ta fito daga kitchen tayiwa sodangi magana taji shiru bata amsa ba,sai ta waiga ta kalleta,tunanin dai taga tanayi,aikuwa ta matsa mata sai ta fada mata dalilin tunanin,wayancewa tayi tace mata babu komai wai kanta yake mata ciwo.
Hakanan molasa ta kyaleta amma badon ta yarda ba.
Tsarabar nono da madarar shanu suka hada mata harda man shanun sukace ta kaiwa mahaifiyyar surayya,kuma tace suna gaishesu

A wajen tafiyarta ne afnan taso tona masu asiri ta fara kuka wai sai tabi sodangi,da kyar da dubara suka samu ta hakura,ita kuma sodangi tayi hanzarin barin gidan.
Sai da ta biya ta bichi don taga gwaggonta laura,aikuwa tana isa laura ta far mata da fada,"wannan wacce irin rayuwace neh sodangi?"
Sodangi cikin rashin fahimtar dalilin fadan goggonta sai tayi dariya tace,"kai goggo tundaga daura nake ta doki da murnar son ganinki,amma gashi ina dira kin tarbeni da fada ban san hawa ba ban san sauka ba.
Goggo laura ta harareta tace,"ya akayi kikayi tafiya oganki bai sani ba?saboda nan yayi ta zarya kusan kullum sai yazo,kuma ada na fara tunanin turashi daura sai kuma wani tunanin yace mani idan bakije can ba fah.toh shiyasa na kyaleshi sai dai ince har yanzu bakizo ba."

Tana rufe baki taji sautin tsayawar mota sai tayi dariya tace,"shikenan ma gaya nan ya sake dawowa,kuma dama dai dai wannan lokacin ne lokacin zuwanshi,don haka sai ki fita ki gani."

Sodangi tayi dariya tace,"ho goggonah, ko dai sameer ya baki cin hanci ne ban sani ba?"
Itama dariyar take saboda ta gane sodangi yanzu tasan halinta tsaf shi yasa ma har take zolayarta.
A jiye dan trolley din kayanta tayi ta juya zuwa kofar gidan.
Ganin sameer tsaye ajikin motarshi bai sa tayi mamaki tunda dama shi zuciyarta ta aiyano mata,don haka sai taci gaba da takawa ahankali ta nufeshi,tunda ta fito yake kallonta,domin ayanda yakeji acikin zuciyar shi kamar ya tarbeta ya rungumeta ajikinshi saboda ba karamin missing dinta yayi ba.
Face taja mashi,ba yabo ba fallasa har ta isa gabanshi, gaishe shi tayi ya amsa fuskarshi asake,ita kuma yana amsawa taji gaba da kallon gefenshi,kuma bata kara ceawa komai ba.
Zuba mata idanuwanshi yayi yana kallonta,har sai da ya gama karantar tsaf ya gane fushi takeyi dashi,don haka sai yayi murmushi yace,"Sarah fushi kikeyi dani koh?toh I'm sorry I'm very really sorry,saboda wallahi alokacin da kika kirani ko na dauki wayar ban san irin abinda zan fada maki ba,saboda gaba daya raina bace yake akan abinda ya faru,amma tunda har kikaga nazo gareki yanzu ke kanki kinsan na huce,please nima kiyi hakuri."
Dan numfasawa yayi sannan yaci gaba da cewa,"sarah ban san kina da wani matsayi acikin zuciyata ba sai da kikayi wannan tafiyar ta bazata,wanda ni kadai ce nasan halin dana shiga saboda rashin ganinki kusa dani."

Sodangi wata irin kunya ce ta kamata tun sadda sameer ya fara bata hakuri,saboda sai yanzu ta tuna ranar da suka rabu tsateshi safwan yasa akayi,kuma bata san abinda akayi mashi ba.don haka tanajin yayi shiru ta dago kanta ahankali ta kalleshi tace,"ka daina bani hakuri,saboda komai ya faru ta sila ta ce,don haka nima ina mai baka hakuri sameer."

Ba karamin dadi yaji ba,nan da nan fuskarshi ta kara washewa yace,"Na gode sarah ! Thank you very much !!
Itama murmushin takeyi ta kalleshi tare dayi mashi wani kallo wanda shi ya dauka duk na soyayya ne tace,"idan zaka kira ni ka rinka ce mani sodangi saboda duk dangin mu babu mai kirana da saratu,kilama wasu sun mance da asalin sunana."

Rage fara a yayi,tare da kada kanshi yace,ni kuma bana son sunan na sodangi,saboda idan da ina da hali da babu wanda zai kara kiranki dashi."
Dan tsaki ya ja ya kauda kanshi gefe yaci gaba da cewa,"wallahi idan da nasan zuwan mu wannan wurin zan gamu da wannan guy din da tun farko bamuje ba,abin ban haushi da takaici sai idan kinji yanda yake pronouncing din sodangi sai ka rantse kamar tun farko shi ya rada maki sunan ba iyayenki ba."

Dariya sosai sodangi ta kamayi,wai sameer ne ke fada,ko kuwa dai wannan shine kishin da ake cewa.

Tsayawa yayi yana kallonta yace,"watau dariya ma na baki koh? Hmm ya kuta ya canzakan zancen yaci gaba da cewa kije ki dauko kayanki kizo muje saboda nasan duk abinda kike dole ne gobe kije wajen aiki,kuma sannan ga shirye shiryen walima da Abba zai kaddamas."

Tana dariyar ta shige cikin gidan,ban kwana tayiwa laura tare da bata abinda tayi niyya,sannan ta fito daga cikin gidan.
Hada idon da sukayi da sameer sai taji wata dariyar,saboda idan ta tuna wai kamar shi yara maki sunan sai abin ya bata dariya.
Bari yayi sai da suka shiga mota suka fara tafiya ya kalleta yace,"idan har baki daina dariyar nan ba duk abinda nayi mski kada kiyi kuka dani,so you should blem your self."
Wannan furucin da yayi sai yayi mata dai dai dana safwan,wanda karshe ya matseta da karfin tsiya yayi kissing dinta,don haka nan da nan ta natsu harda kara gyara zamanta.

Shi kuma ganin haka yasa ya juyo ya kalleta yayi murmushi ya juya yaci gaba da driving din da yakeyi.

Al amarin safwan kuwa,duk da babban yaro bai san inda sodangi ta sauka ba, amma kullum sai safwan din yasa ya kawo shi sallari sannan babban yaron ya fita yayi ta yawo har sai magriba ta kawo jiki sannan su bar wajen.

Kamar kullum, yau ma tafe suke amma dokokin da safwan yake gindayawa babban yaro sune suka fitgita shi,domin duk AC din da cikin motar amma babban yaro sam bai jinta,don wata irin zufa da yakeyi sai ka rantse ruwa aka kwara mashi.

Safwan ya numfasa cikin takaici yaci gaba da cewa,"yau na fada maka idan har baka gano gidan da ta shiga ba abakin aikinka,kuma kada kayi tsammanin zakaje wani waje adauke ka sabon aiki,Noo duk wata hanya da zaka bi sai na wahalar dakai,don haka dubara ta ragewa mai shiga rijiya."

Wasu hawaye tare da zufa suka hadewa babban yaro duk ya rasa abinda yakeyi mashi dadi,kuma sannan sarai yasan halin uban gidanshi bai magana biyu.

Dai dai junction din sallari suka iso zasu gaggara su shiga inda rukunin centocin gidajen suke safwan ya daga ido sukayi ido biyu da babban yaro ta madubin gaban motar yace,"idan ka sauka kuma kaje baka samo gidan ba,toh kada ka sake ka dawo mani,then daga can kayi can."

Gaba daya cikin babban yaro ya murda kuuuuuu kakeji kamar wanda zaiyi tsugunno,ga habar bakin shi sai rawa take,kuma yana son ya kara bashi hakuri amma safwan ya riga yayi worning dinshi,dole ya fita daga motar yana tafe yana waiwaye,domin ranshi ya bashi kallon bankwana yakeyiwa oganshi tunda idan dai har anan sodangi take toh daya gano ta tuni.

Love you sis 😘
08033481518
[4/9, 8:08 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

39

I dedicated this love story to my Hausa Novels & my fans,thank and love you all 😘😘

Zaune yayi acikin motar har kusan gaf da magriba,amma babu alamar dawowar babban yaro,wani takaici ne yaji har acikin zuciyarshi ya rasa abinda yakeyi mashi dadi,ya dago kanshi yana kallon jama ar da suke ta kai da komowa yace acikin ranshi,kada dai ace yanzu ma ya rasa sodangi????

Wani karaji yayi ya fito daga motar yana cewa,it's impossible."bude sit din driver yayi ya zauna yana kokarin rufe motar sai kawai wata mota ta gitta ta gefenshi,sodangi ce kame agaban mota ita da sameer suna ta fesa murmushi,domin daka gansu zaka gane fira sukeyi atsakaninsu.

Wani kululun bakin ciki neh yazo mashi iya wuya,da sauri ya tayar da motarshi yabi bayansu.
Wata kwana ce suka shiga,ada yayi niyyar shigarta sai ya fasa saboda ya fahimci bata da zurfi sosai.
Parking yayi can gefe daya ya taka da kafarsa ya shiga lungun.
Wani wuri ya samu ya dan labe ta yanda zai rinka hangen duk abinda yake faruwa.
A dai dai kofar gidansu surayya sameer yayi parking,sun dan jima acikin motar kamin su fito,wanda har safwan ya kosa ya rinkajin kamar ya fito yaje ya samesu,amma dole ya hakura ba don ranshi yaso ba.

Sodangi ta bude motar ta ziro kafarta ta fito,duk da wajen ya fara duhu,amma safwan yana kallonsu tsaf.
Shima sameer din fitowa yayi duk fuskokinsu dauke dariya,tabbas magana suke amma safwan yaso yaji shin wacce magana ce yake fada mata har take sanyata dariya.

Wasu manyan envelops ne a hannun sameer ya mikawa sodangi yana murmushi yace,"ki rike wadannan envelopes din,saboda suna da matukar muhimmanci awajena,kuma zan kira around nine don ki bani amsar tambayoyin da kika gani."
Murmushi sodangi tayi tace,"babu wata amsa da zan baka da bakina,domin yanda ka bani arubuce haka nima zan maido maka ansarka arubuce."

Dariya kawai sameer yayi yace,"ni kuwa zan baki mamaki,gobe zan fada maki duk abinda yake acikin zuciyata,don haka sai kizo da shirinki.

Sodangi tana dariya ta mika hannunta ta amshi envelopes din tace,"Allah ya kaimu goben."
Tsayawa tayi gefe daya har sai da ya fita da motarshi,sannan ta kalli envelopes din dake hannunta tayi murmushi, sannan ta duka ta dauki trolley dinta ta shige cikin gidansu surayya.

Ashe alokacin da sodangi ta duka jan trolley dinta daga cikin envelopes din guda daya ta sullube mata,kuma daga inda safwan yake ya hangi fadowarta,shiyasa ya fasa yi mata magana har ta shige.
Chapter 26 · 0% Book details