← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 45

Sashe 38

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Afnan tayi tsalle ta rike hannun safwan cikin nuna farin cikinta suka tafi har tanayiwa sodangi bye bye.
Safwan ya kama hannunta suka nufi wani bangaren amma duk dai acikin gidan ne,har suka kai wani daki da yake killace gefe daya.
Knocking yayi sannan ya tura kofar suka shiga,wani babban mutum ne zaune akan kujera mara jiki sosai,yana ganin safwan da afnan ya zare farin glass din dake like da idanauwanshi ya rinka kallon afnan cikin mamaki yace,"Kasan wani abu kuwa?"
Safwan yace,"a ah,sannan ya kama afnan ya zaunar da ita akan cinyarshi suka rinka fuskantar mutumin.
"Kamar ka da yarinyar nan,abin har ya bace,gaskiya sai yanzu na kara yarda da abinda kake cewa." Inji wannan mutumin.
Safwan yayi murmushi yace,"ni sam bani ma ganin kamar da muke kwatankwacin yanda nakejinta acikin zuciyata,don shi yasa ma na gaza hakurin ranar da sodangi zata fada mani da kanta,please docter yi maza kayi aikinka,saboda mammy dinta ta fara maganar tafiyarsu."
Wannan mutumin da safwan ya kira docter kabir yayi maza ya fiddo dan akwatin dayazo dashi duk ya fito da kayan da zaiyi yan aune aunenshi.
Jinin afnan ya diba cikin dubara ta yanda bazata ji zafi ba bare har ta kai gayin kuka.
Kallon safwan yayi yace,"Haji safwan kana iya mayar da ita,ni kuma zanyi kokari kafin ka dawo in samu in kammala gwajin."
Hakan kuwa safwan yayi,amma koda suka koma wajen sodangi sai ya rinka jin kwata kwata bai da kwanciyar hankali,saboda zullumin bai san amsar da docter kabir zai bashi ba,idan har result ya nuna afnan ba diyarsa bace,toh ko ya zaiji?
Zumbur yayi ya mike tsaye sai kuma wata zufa ta karyo mashi duk sai yaji ya rude.
Duk abinda yakeyi akan idanuwan sodangi,don haka sai ta taso ta koma kusa dashi ta zauna tana kallonshi tace,please safwan mi yake faruwaneh? Domin na lura tun dazu kake zufa kamar mai ciwon ciki,kuma nima nace ka mayar damu gida haka nan kayi kamar baka fahimta ta,why !! Ka fada mani mana."
Safwan ya koma ya zauna daga mikewar da yayi ya dafa kafarta cikin murmushin karfin hali yace,"kada ki damu my sweet heart,domin komai yazo karshe,saboda matakin dana dauka shine zai zamo kwaciyar hankalina,tunda ke dama tuni hankalinki akwance yake."
Irin kallon nan tayi mashi na ban fahimci abinda kake nufi ba,sannan kuma taki dauke idanuwanta akanshi,kwata kwata ji yayi idan har taci gaba dayi mashi wannan kallon bazai iyayi mata musu ba,kuma tuni zai iya amayar mata da sirrin zuciyarshi.
Kiran da docter kabir yayi mashi ya tsayar dashi daga abinda zai fadawa sodangi don haka ko wayar bai dauka ba ya nufi hanyar barin falon yana cewa sodangi,"just a minute sodangi,I will be back."
Kafin ace miye haka ta nemeshi bat ta rasa afalon.
Safwan harda gudu ya hada,kuma ko sallama bayyiwa docter kabir ba sai dai ya ganshi kamar daga sama aka tulloshi,amma fara ar da ya gani docter kabir yana yi ne ta kara bashi kwarin gwiwa ya samu ya ida karasawa agaban shi yana cewa,"please kada ka fada mani abinda zai tarwatsa mani zuciya,don Allah ko ba diya ta bace kace mani kawai itace don in samu jin sanyi a zuciyata."
Docter kabir yayi wata irin dariya ya zare glass din fake idonshi ya dafa kafadar safwan yace,"Haji safwan ka kwantar da hankalinka saboda afnan diyarka ce halak malak,kuma babu wanda ya isa ya amsa sunan mahaifinta sai kai kadai sawan."
Wani salati da yayi cicin karfinshi ya suri docter kabir yayi sama dashi yana dariya,shi kuwa docter da abin yazo mashi bazata,saboda bi taba tunanin safwan yana da karfin da zai iya dagashi ba,shima dariyar yake yana cewa,"bi ahankali Haji safwan kada ka kayar dani kasa."
Ajiyeshi yayi fuskar nan tashi kamar gonar auduga yace,"daga yau motar da nake hawa na baka ita kyauta ta zama taka halak malak,kuma zan sa atura maka 2milions,sune goron albishir dinka."
Shi kanshi docter kabir ji yayi ya rude dajin kyautar da safwan yayi mashi ta bazata,duk da dai dama yasan kadan da halin safwan kenan,don haka sai ya shiga zafga godiyya kamar zai durkusa mashi.
Safwan ya dakatar dashi yace,wllh docter ji nake kyautar da nayi maka kamar batayi ba,amma tunda dai kai har kaga tayi shikenan."
Amsar duk takardun da suka zama sune cikakkun shaidarshi ta afnan yarsa ce yayi,sannan ya sallami docter kabir suka rabu cikin farin ciki.

Ashe lokacin da safwan yake wannan salatin da karaji sai da sodangi ta jiyo voice din shi amma kuma sam bata fahimci abinda yake cewa ba sai dai amon muryar kawai da takeji,mikewa tayi tsaye ta fara sintiri acikin falon domin gaba daya hankalinta ya tashi matuka saboda rashin sanin abinda yake faruwa da safwan dinta,don haka bude kofar da yayi ya shigo yasa ta nufe shi gaba daya cikin nuna kulawarta take tambayarshi,"mi ya sameka safwan naji kana karaji kai kadai,mi ya faru neh?"
Suna haduwa bai saurari abinda take cewa ba ya rungumeta tare da kadaddabeta gam ajikinshi yana cewa,"thank you so much sodangi,kin biya ni kuma kin gama mani komai arayuwata."
Sam bata fahimci abinda yake cewa ba,kuma dama tun dazu yake tayin wasu abubuwa da yake ta sanya ta tunani,don haka ciro kanta tayi da tsiya daga jikinshi ta tureshi tace,"don mi zakayi tayiani wasu abubuwan da ban ganewa?domin tun dazu nake ta bib kanka akan ka fada mani abinda ya sameka amma har yanzu kaki ce mani komai."
Haka ta karasa maganar cikin nuna mashi ranta ya baci.
Dariya kawai yayi cikin jin tausayin kanshi ya nufi afnan da take ta baza duk abinda ta samu wai ita nan wasa takeyi ya daukota cak ya nufi wurin sodangi suka rinka fuskantar juna yace mata,"don mi zakiyi fushi dani,baccin ni banyi fushi dake ba sodangi?"
[4/28, 10:54 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

55

Kasa yayi da idanuwanshi cikin takaici ya numfasa yaci gaba da cewa,"why you do this to me,mi na rage ki dashi,saboda tsananin son da nake maki har kashe raina zan iyayi,amma abinda na fahimta kamar ni ke haukan banza sam bani bane aganki,domin idan har ba haka bane,toh minene na boye mani afnan baki bayyanar da ita gareni ba har sai da ni na bincika da kaina."

Sodangi shiru tayi tunda safwan ya fara watso mata tambayoyi saboda tasan dai itace bata da gaskiya,duk da itama tana ganin tana da ta ta hujjar data sa ta boye afnan ga mahaifinta,don haka bude baki tayi zatayi magana sai kawai ya dakatar da ita,"babu abinda zaki ce mani daga yanzu in sake yarda dake tunda dai baki sona,kije kawai na hakura da soyayyar da nake maki tunda ke baki amince dani ba."
Yana fadar haka ya juya mata baya amma kuma ya gaza matsawa daga inda yake atsaye.

Kuka neh yaci karfin sodangi saboda hankalinta ba karamin tashi yayi ba da jin irin kalaman da suke fitowa daga bakin safwan,don haka sai ta dauki mayafinta ta juya da gudu ta nufi wani daki da yake jrer da wasu dakunan dake cikin falon,sa arta tana turawa kofar taga ya bude don haka shigewa tayi ta samu wani gado aciki tayi rufda ciki akanshi taci gaba da zubar da hawayen da suke ta ambaliyya a idanuwanta.

Shigarta dakin yasa safwan ya juyo da sauri yabi sawayenta da kallo cikin takaicin abinda tayi mashi.
Kwata kwata ba ayi minta talatin ba da fadan safwan da sodangi su Hajiya ummu salma suka iso tare da mahaifin safwan da yusuf da iyalinshi.
Ganinsu yasa safwan ya ajiye afnan dake hannunshi tun dazu,don ko gajiya baiyi.
Ita kuma afnan yanda kasan ta sansu da gudu ta nufesu tanayi masu oyoyo.
Hajiya ummu salma ce ta tarbeta cikin mamakin ganin yar baby agidan safwan,can kuma sai taji gabanta ya fadi kodai wata ta haifa mashi ita daga cikin yan matanshi na banza suka maido mashi ita,saboda yanda taga kamar ta da danta ma har ta bace,tuna kiran da yayi masu tayi da kuma bukatar son ganinsu cikin sauri saboda yana cikin wani hali da bai iya misalta masu shi ba.

Har Hajiya ummu salma ta zauna tunanin daya addabi zuciyarta kenan,ita kuwa afnan tana kufcewa daga hannun ummin safwan sai ta nufi Alhaji muhammad shima ta kama hannunshi tana dan surutunta.
Zuba mata idanuwa yayi yana kallonta shima cikin mamaki ya kalli safwan yace,"kai zo nan ina ka sami diya? Saboda wannan yarinyar duk yanda akayi baby dinka ce."
Safwan ya zube agabansu yana murmushi yace,"ku bari daddy ku huta sannan zan fada maku dalilin taso daku da nayi ba tare da kun shirya ba."

Alhaji Muhammad ya kalleshi yace,"wane hutu kakeso muyi agidanka gidan gwauro,ai duk kyan gida idan har babu matar aute acikin shi ya zama hoto,don haka maza ka fadi mana dalilin kiran mu da kayi ba tare da bata lokaci ba."
Safwan ya dago ya kalli umminshi saboda yasan babu wanda zai iya dakatar dashi idan ba ita ba,itama kauda kanta tayi alamar ba zatayi supporting dinshi ba ayau.
Safwan ya dafe kanshi ya juya ya kalli yayanshi yusuf da matarshi,suma yi sukayi tamkar basu san yana kallonsu ba,su junior ya kalla shida afnan da suke ta wasansu tamkar dama can sun san junansu.

Murmushi yayi ya kalli mahaifinshi yace,"insha Allahu daga yau komai zai wuce,kuma idan ayau kake son inyi aure ni kuma na amince maka."
Wani farin ciki ne ya bayyana a fuskar Alhaji Muhammad yace,"alhamdulillahi, safwan babu abinda nakeso ayanzu sai don ganin kayi aure ka zama kamilin mutum."
Safwan yayi dariya yace,"daddy tun yaushe na zama kamilin mutum,ai na dade da zama irin yaya yusuf,kuma duk dalilin mammy din afnan."ya nuna afnan dake ta faman goya dan teddy din junior.

Maida idanuwanshi yayi akan ummi din shi yace,"ummi ban boye maki komai ba akan sodangi,kuma ko alokacin dana gano inda sodangi take sai da na fada maki,amma abinda na fahimta daga baya shine,sam ummi bata dauki maganar sodangi da wata muhimmanci ba shiyasa daga baya ma na daina fada maki komai akanta.

A duk binciken da nayi watau shine, alokacin dana bar sodangi ashe na barta da karamin ciki wanda ita kanta bata san dashi ba sai daga baya,gashi ni kuma babu wani address dana bar wa sodangi wanda zata iya nemana ko don irin wannan lalurar.
Chapter 38 · 0% Book details