← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 45

Sashe 20

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safwan ne kwance sai birgina yake,ko ban fada maku ba zaku gane afuskarshi akwai wani abu da yake damunshi wanda har ya fara cin jikinshi,watau dan ramewa da yayi kadan.

Hajiya ummu salma itama abin ya fara damunta,saboda koda yaushe ta tsareshi don ya fada mata damuwarshi sai dai kawai yace mata sodangi.

Tagumi tayi ta shiga tunani,wai wacece wannan sodangin?Anya akwai ma sodangin nan kuwa?ni dai Allah yasa ba aljana ya gamu da ita ba can wajen yan leke lekenshi na mata.

Mikewa tayi ta fito daga sashenta ta nufi sashen safwan data lura yau kusan kwana biyu kenan bai fita ko ina ba.
Dan kwan kwansa kofar shiga sashenshi tayi,amma taji shiru,haka karo na biyu ma babu wani yunkuri da akayi na bude matan.
Don haka sai tayi tunanin shiga kawai,tana taba kofar sai taga ta bude,ahankali ta sanya kanta cikin dan kayataccen falon da yasha kayan alatu,domin idan ka ganshi kai sai kayi tsammanin falon na mace neh.

Wucewa tayi kai tsaye har zuwa kofar dakinshi,
sunanshi ta kira ahankali.shi kuma jin muryar ummunshi kusa dashi yasa ya takarkara ya mike saboda jikinshi gaba daya yayi mashi nauyi ga rashin karfi.
Budewa kofar yayi tare da danyin murmushi yace,"ummi! Kinji ni shiru hala banzo na duba ki ba?"

Hajiya ummu salma ta kalleshi cikin sigar jin tausayinsa tace,"wai miye ya sameka safwan,don ni fa duk yan kwanakin nan duk na gaza gane kanka,don haka ayau babu inda zan matsa sai ka fada mani cikakkar damuwarka."

Bi tayi ta gefenshi ta shiga cikin dakin,shi kuma yayi tsaye yana kallonta,saboda abinda bai taba gani ba neh,koma minene sai dai shi ya sameta cikin gida.

Kallonshi tayi tana murmushi tace,"kana mamaki neh?hmm ka daina mamaki saboda yau magana nakeso muyi sosai ni da kai."

Safwan shima murmushin yake ya rufe kofar sannan ya koma kusa da ita ya zauna yana cewa,"ummi matsalata dai kin santa, kuma insha Allahu nima komai ya kusa zuwa karshe saboda na tura wadannan body guards din da daddy ya bani suyo mani bincike akanta,sannan kuma abokina tahir ya sha alwashin nemo mani sodangi ta."

Hajiya ummu salma ta zuba mashi ido kawai tana saurarenshi har ya gama,sannan tace,"toh kuma tunda har kasan haka minene na damuwar?"
Numfasawa safwan yayi ya lumshe idanuwanshi ya budesu da kyar yace,"ina fargaba ummi,kuma idan har abinda nake tunani ya faru,toh ni ban san yanda zanyi ba,don dole ne rayuwata taci gaba da zama cikin garari."
Mahaifiyyarshi ta mika hannu ta dafa kafadarshi tace,ka daina damuwa my son,saboda ganinka acikin wannan halin nima zai iya sakani acikin wani yanayi,kuma duk na gane damuwarka akan sodangi,amma kuma miye mahadinka da ita? Kuma a ina kuka hadu?"

Wannan tambayar ba karamin dadinta yaji ba,saboda yana son tunanin rayuwar da sukayi da sodangi,to kuma bare ka tambayeshi labarinta.

Gyarawa yayi yadan kwanta kusa da mahaifiyyarshi ita kuma ta dora hannunta abisa gadon bayanshi tana dan shafawa ahankali tana sauraren labarin da yake bata,bai boye mata komai ba,filla filla har aurenta da yayi,da kuma irin rayuwar da yayi bayan rabuwarsu daya tafi abroad.

Hankalin Hajiya ummu salma yayi matukar tashi sosai dajin wai safwan har aure yayi ba tare da sun sani ba,kuma ya saki matar.
Hawaye ta fara zubarwa saboda tashin hankali tace,"safwan dole neh Allah ya kama ka tunda ka dauki alhakin yarinyar mutane da sauran yan mata,kuma yanzu babu abinda ya rage maka sai addu a,saboda ba lallai bane ka samu sodangi free ba tare da aure ba sai dai wani iko na Allah,kuma sannan idan har sodangi tasan kanta da wuya ta kara amince maka akaro na biyu."

Zabura yayi ya mike zaune yana kallonta cikin nadama yace,"don Allah ummi kada kiyi mani baki,domin sodangi tana sona fiye da yanda baki zato,kuma wallahi nima ina sonta,tunda saboda ita yanzu bani iya kallon wata diya mace da sunan so ko sha awa sai ita kadai."

Hj ummu salma ta kalleshi sosai taga iyakar gakiyarshi yake fada mata,don haka sai tace,"toh shikenan, nima kullum addu a nake maka,kuma bazan fasa ba,amma abinda nakeso shine ka tashi ka fita kaci gaba da hidimarka don kada ciwon zuciya ya kama mani kai."
Murmushi kawai yayi ya kauda kanshi,saboda ya fahimci umminshi bata fahimci pain din da yakeji ba,shi yasa kawai ya kyaleta tayi ta fadanta har ta gama ta tafi.

Wayarshi ce tayi ringing,kuma tun dazu yake jiran shigowar kiran saboda aikin da ya bazawa yaranshi.
Babban yaronshi ya gani a screen din wayar da yake video call ne.
Rusunawa yayi yace,"yallabai barka da ranar yau."hannu kawai ya daga mashi ya koma ya kwanta.
Babban yaron ya fara bayaninshi cewar,"yallabai mun gano inda iyayen sodangi suke acan wata rugar fulani dake daura."
Dagowa yayi da sauri ya kalleshi arude yace,"umhm ina jinka,ci gaba kawai."
Yawwa,amma duk iyakar binciken mu bata tare dasu ance ita tana bichi,awata rugar,don haka sai muka bar daura muka nufo bichi din,toh anan din muka samu labarin tayi wata makaranta ta secondry da kuma women center,amma yanzu bata acikin bichi ana tunanin ta kona kano neman aiki."

Zaune ya tashi dirshanyana kallonshi harda kara tallabe wayar ,domin bai son abinda zai kawo mashi wata matsala awannan lokacin.
Don haka yana gama mashi bayanin ya tari numfashinshi yace,"mi ake koyawa a women center din?"
Babban yaro yayi mashi bayanin sana o in mata kala kala,shi kuma sai ya shiga nazari,can yace,"sodangita bazata koyon abinci ba saboda ta iya."🤔tunani yaci gaba dayi ya tuna da saka,itama dan tsaki yayi yace,kai I dont think that."
Babban yaro dake tsaye yana kallonshi yayi dariya yace,"ogah ni dai abinda naga yafi shine,kawai muyi bincike ta ko ina,idan ba a sameta ba nan asameta acan."

Safwan yayi dariyar jin dadi yace,"ok haka za ayi babban yaro, don haka nima gani nan mu hadu a kano kawai."

love you sis😘
08033481518
[4/9, 2:19 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

30

I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘

KANO

Zuwan sodangi a company su sameer komai ya canza masu saboda ci gaban da suke samu,kuma duk adalilinta domin duk abinda ta sanya agabanta sai tayi bakin kokarin ta.

Ganin haka yasa sameer ya sakankance akan lamarinta,domin ko da aiki aka fara lokacin tashi yayi idan har bata ida ba bata zuwa ko ina har sai ta gama,shi yasa baban sameer yake matukar sonta.

Sameer kuwa ada mutum ne mara walwala da rashin fara a,domin idan da sabo har yarinyar da zai aura ta riga ta saba,kuma koda taji labarin an kai wa sameer assistant da irin yanda ma aikatan wurin suke kodata duk bata damu ba saboda tasan halin mutumin nata.

Akwai wata rana bayan fa iza ta gama aikinta da yake itama duk cikin company take sai tayi tunanin kaiwa sameer ziyara office dinshi.

Shi kuwa sameer yana zaune a office dinshi duk abubuwa sun fara damunshi saboda koda yaushe sai tunanin sodangi ya rinka bijiro mashi acikin zuciya,amma duk yanda ya samu ya tureshi sai kawai yaji ya dawo.

Dan tsaki yayi ya mike ya fito daga office din ya zagaya ta bayan office din don ya shaki fresh air,yana cikin tafiya a hankali sai ya hango sodangi adan gabanshi kadan itama zaunen take ta fiddo photon afnan tana kallo tare dayi mata magana,"afnan I miss you 4 2dys,dan sumbatar photon tayi tayi mata murmushi sannan taci gaba da cewa insha Allah this week din bichi zanyi shi." Maganar dataji abayanta neh yasa ta juyo sai taga sameer da wani karamin ma aikacinsu.
Mikewa tayi tsaye tana murmushi tana kallonshi har ya iso tace,"yallabai kai ma fitowar kayi kasha iskar?"
Wannan murmushin da tayi mashi harda shi yake tsaya mashi acikin rai,don haka shima sai ya samu kanshi dayin murmushin yace,"zowa nayi in tayaki zaman shan iskar."
Koma wa sukayi suka zauna atare,sannan duk sukayi shiru kamar masuyin tunanin wani abu,can dai ya wayance saboda rasa abinda zaice yayi yace,"dazu dana taho na hangeki kina duba pix,ko na masoyin neh? Shiyasa ma kika boyeshi don kada in gani?"

Maganar tashi dariya ta bata,saboda dai ita yanzu bata da wani lokaci na soyayya,abin rufin asiri kawai takeso wanda zata kula da yarta da kuma laura mai kulawa da ita.

Gudun kada yayi zaton itama halinta daya da sauran yan mata sai ta zaro pix din ta mika mashi,amsa yayi har yana saurin kai idanuwanshi sai yaga yar yarinya da shekarunta basu wuce hudu ba.

Dagowa yayi ya kalleta yace,"naga fine girl,ta wacece?sodangi tayi shiru kamar baza tace komai ba sai can tace,"relative di tace kuma ta jini."
Kallon pix din ya sakeyi yace,"babing tana da kyau, kuma daga ganinta tana da wayau sosai."
Sodangi taji dadin yabon yar ta da yayi tace,"na gode da yabonta da kayi."daga nan kusan firar duk sai ta koma akan afnan tana fada mashi irin dabi in yarinyar da dubararta da kuma wayan ta.
Shi kuwa abin sai dariya yake bashi yana sake tambayarta tana bashi labari.
A haka fa iza tazo ta samesu sun shagala sai dariya sukeyi,dominshi har tsayawa yake yana zubawa sodangi idanuwanshi sannan ga smile kasa kasa yanayi mata.

Fa iza tsayawa tayi daga nesa dasu ta gaza isowa saboda bakin ciki,sannan kuma,tsananin mmk ne ya cika mata ciki wai sameer ne ke fira harda Kyakyata dariya abinda bai taba yi mata ba.

Kutawa tayi ta juya ta koma office dinta cike da takaici da bakin cikin abinda ta gani,kuma sai idan tayi magana yace ba haka ba,amma with a time wata rana zata kamashi a hannu.

Wannan week end din sodangi ce har daura wajen iyayenta,bayan sun gaisa neh take ta ba sadah labarin irin ci gaban da take ta samu awurin aikinta,domin har tana ganin zata dauki su goggo laura ta mayar dasu cikin garin kano don ta samu saukin zaryar da takeyi.
Chapter 20 · 0% Book details