← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 45

Sashe 41

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gaba daya jikinshi ne ya kama rawa kamar mai jin sanyi.
Dago idanuwanshi yayi da suka yamutse saboda tashin hankalin da yake aciki yace,"ummi nah ki lullube ni,ban lfy,kuma ina ganin mutuwa zanyi."
Wannan furucin da safwan yayi ba karamin tayarwa mutanen dake zaune a falon yayi ba,bama ya umminshi,itama nan da nan jikinta ya fsra rawa tana cewa,"bazaka mutu ba safwan,insha Allahu zaka rayu,amma sai ka sanya hakuri da dangana acikin zuciyarka."
Rumtse idanuwanshi yayi da karfi,watau umminshi ma na nufin yayi hakuri da sodangi kenan,lallai akwai aiki agabana,taya zan rayu ba tare da farin cikina ba?
Zumbur ya zabura ya mike ya nufi hanyar fita daga falon cikin rangaji tare da sarkewar kafafuwa yanda kasan mashayin daya sha yayi tatul.

Hajiya ummu salma mikewa tayi itama tabi dan nata da idanuwa cikin jin tausayinshi tamkar zatayi kuka,aikuwa yana zuwa dai dai kofar da zai fita wani jiri ya debeshi sai gashi akasa yaraf ya zube,sai alokacin mazan dake falon suka zaburo gaba dayansu suka nufeshi,don su Hajiya ummu salma da khadija kuka kawai sukeyi.

Yusuf ne ya ciccibeshi yayi ciki dashi ya dorashi akan gado,shi kuwa safwan sai kokarin tashi yake amma jiri yana mayar dashi akan gadon haka yayi tayi yusuf yana hanashi har ya gaji don kanshi ya hakura ya kwanta tate da mayar da idanuwanshi ya rufe.

Mahaifin safwan da kanshi ya fara laluben number docter kabir,cikin sa a wayar ta shiga ya dauka cikin kankan da kai ya gaida mahaifin safwan din,sannan Alhaji Muhammad yace,"docter kana gari kuwa?"

Docter kabir yayi murmushi yace,"ina gari ranka ya dade,amma ina cikin katsina.
Cikin jin dadin inda docter kabir din yake Alhaji Muhammad yace,"nima ina cikin katsinar,don Allah inason kazo gidana dake lay out ba lafiya."
Yana fadar haka ya kashe wayar ya koma kan safwan da suke tunanin ko suma yayi.
Cikin wasu yan mintoci da basu da yawa docter kabir ya iso,ganinshi yasa duk suka matsa ya fara duba safwan cikin kwarewar aikinshi ya juyo ya fadawa Alhaji Muhammad cewar safwan ba suma yayi ba amma rayuwarshi dai tana cikin hadar don haka sai anyi da gaske wajen kulawa da abinda yake bata mashi rai har ya kai shi ga shiga irin wannan yanayin,domin kara ace suma yayi sai a yayyafa mashi ruwan sanyi da halin daya shiga yanzu.

Gaba daya dakin idanuwansu suka raina fata,sai kallon kallo sukeyiwa junansu,tare da mamakin abinda ya hadassa mashi wannan yansyin cikin dan lokaci kankani.
Drief ya daura mashi don asamu jikinshi ya samu karfi,sannan kuma ya basu shawarar su dan bashi wuri don ya samu hutu,domin bazaiyi mashi allurar barci ba,saboda kada abin yayi mashi yawa.

Shawarar docter kabir suka dauka,don haka gaba daya suka bar sashen suka koma wani bangaren,ita kuwa Hajiya ummu salma tana nan zaune kusa da danta saboda gaba daya hankalinta ya koma gareshi,domin dama tunda taji yace,rayuwarshi bata da amfani tasan lallai akwai abinda yakeji tunda har yayi wannan furucin.
Shafa fuskarshi tayi cikin nunajin tausayin shi ta furta da cewa don Allah safwan kayi hakuri kada ka wahalar da rayuwarka,ni umminka ina sonka kuma daddy dinka ma yana sonka,kuma haka ma yusuf yana tsananin kaunar,idan har ka bari muka rasa ka safwan,ka sani bazamu taba yafe maka ba."
Wannan furucin na umminsa ya darsu acikin zuciyarshi,saboda kwancen kawai yake amma duk abinda akeyi ko ake cewa yanaji acikin kunnenshi,karfin jiki ne kawai baya dashi sai kuma wata irin kuna da zuciyarshi takeyi.
Wasu hawaye neh masu zafi irin na gefen ido suka ziraro mashi,juya kanshi yayi dayan gefen saboda ya fahimci ummun tashi zira mashi idanuwa tayi.
Numfasawa tayi tasa hannunta ta share mashi hawayen tana ci gaba da cewa,"safwan ka tashi kada ka lahanta kanka,kuma nayi maka alkawarin zan tsaya maka tsayin daka inga ka mallaki abinda kakeso,saboda nima inason abinda kakeso kuma dai dai da rana daya ban tabajin kin son sodangi ba a rayuwata, saboda halin da kake aciki ba laifinta bane safwan,ka dauka jarabawa ce daga Allah."
A hankali safwan ya bude idanuwanshi yana kallonta dishi dishi,hannun ta da ta dafashi ya mika hannu ya kama,amma bai iya ce mata komai ba sai kallonta kawai yake,amma acikin zuciyarshi so yake taci gaba dayi mashi zancen sodangi data fara,gashi ji yake bazai iya magana ba daya fada mata abinda yakeso yaji.
Ita kuma ganin har ya bude idanuwanshi sai wani farin ciki ya kamata ta mike da sauri ta nufi wurin kanshi tana tambayarshi ko yana bukatar wani abu,kada mata kai yayi tare dasa hannunshi daya ya dafe kanshi alamun yanayi mashi ciwo.
Da sauri Hajiya ummu salma ta daga wayarta ta kira mahaifinsu safwan tanayi mashi albishir din tashin safwan.
Ba ayi cikakkun minti biyu ba Alhaji Muhammad ya iso dukkanin idanuwanshi zube suke akan safwan ,don haka shima ganin safwan din ido bude sai farin ciki ya kashi,shi yusuf kuwa kasa daurewa yayi har sai da ya dan rungumo dan uwanshi yana dariya.

Murnar kawai sukeyi amma duk gaba dayansu basu fahimci safwan bai magana ba,har suka gama murnarsu,sannan Alhaji Muhammad ya dubi karin ruwan dake jikin safwan yaga ko rabi bayyi ba yace,"zuwa dan anjima kadan idan ya kara samun sauki yusuf kuyi magana acire mashi karin ruwan,idan yayi sallolin dake kanshi sai ku bashi koda ruwan tea neh sannan sai asake mayar mashi da drief din."
Yusuf ya dan rusuna yace toh daddy,sannan ya ci gaba da gyarawa safwan kwanciyarshi.shi kuma daddy ya kalli umminsu yace mata," muje koh Hjy tunda dai ya dan autan naki ya farfado,ai kema sai muje ji huta koh."
Hjy ummu salma tayi dariya gami da mikewa tsaye tana kallon safwan tace,"ai sai hamdala,tunda safwan ya tashi,donni wallahi nasa mutuwa zaiyi."
Gaba daya dakin suka dauki dariya suna kallon safwan din,shi kuwa sai raba idanuwa yakeyi tare da tunanin yanda zai samu damar fita daga cikin gidan ba tare da wani ya ganshiba.

Love you😘
08033481518
[5/5, 10:04 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

60

I dedicated this love story to my group Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘

Mahaifiyyar safwan da daddy suka fara fita daga dakin,sannan dan wani lokaci kadan yusuf suma suka tafi da zummar anjima kadan zai sake dawowa wajen safwan din don ya taimaka mashi yayi sallolin dake kanshi.

Fitarsu kenan safwan ya fara tunanin inda wayarshi take,aikuwa ahankali ya laluba aljihun wandonshi ya zarota ya fara neman wayar sodangi,sai alokacin ya iske missing calls dinta ratata,saboda wayar silent take shi yasa bai ji ba.

Dan nazari yayi idan har ya kira sodangi mi zaice mata,tunda halshenshi yayi nauyi sam ji yake bai iya furta wani furuci da bakinshi,don haka sai kawai ya tura mata massege yana cewa,"kada ki damu masoyiyata,gani nan zuwa gareki,babu tsimi babu wata dubara nine mijinki na har abada,sai naxo komai dare."

Murmushin karfin hali yayi ya kuma nemi number tahir,shima ya tura mashi,"duk inda kake maza kazo ka daukeni,please I need your help my Friend. ina gidan daddy dake katsina, kuma ka sani komai dare a kano zamu kwana."

Alokacin da Tahir ya samu sakon safwan sai da hankalinshi ya tashi,saboda duk abinda ake ciki ya sani,don haka shiyasa zuciyarshi ta bashi lallai safwan ya samu matsala awajen iyayen sodangi.
Agogon hannunshi ya duba yaga a round four,kuma gashi a garin Abuja 🤔 koya zaiyi?
Aje duk wani abu dake gabanshi yayi ya dauki past port dinshi ya nufi filin jirgin dake abuja.
Da duhun magriba Tahir ya isa gidan kowa yana ta harabar tafiya masallaci, sam bai bari kowa ya ganshi ba daga cikin gidan don haka ana kabbara sallah ya shige,kai tsaye sashen da safwan yayi mashi kwatance ya nufa.
Safwan na ganin tahir ya fara kokarin tashi zaune saboda jikinshi ya kara samun sauki,wayarshi ya dauko da sauri ya yi dan note ya mikawa Tahir.
Mamaki ya kama tahir ya dai amshi wayar kawai ya duba yaga abinda ya rubuta cewar,"ka dauke ni maza ka rabani da gidan nan,fomin so kawai suke inga na mutu."
Tahir yana karantawa ya zabura cikin sauri ya nufeshi ya kamashi ahankali cikin dubara ya kaishi har wurin motar da zasuyi tafiyar ya sakashi gidan baya,shi kuma ahankali ya sulale ya kwanta.
Chapter 41 · 0% Book details