← Book details Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 45

Sashe 13

Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin amsar tayi kamar saukar wata aradu abisa kwalwar kanta,don haka sai kawai taji ta gigice ta sake rikeshi tana cewa,"safwan mi nayi maka har zaka yanke mani irin wannan hukuncin?"

Furzar da iskar dake cikin bakinshi yayi yace,"haka ra ayina yake,kuma ke ki godewa Allah dana biyo maki ta wannan hanyar,kuma don inajin tausayinki,amma ayau tsakani na dake the game is over,don haka kina iya tsayawa gari ya waye sai ki nufi gidanku,idan kuma anan gidan zaki zauna gashi nan na bar maki shi har abadan abada."

Shafa idanuwanta tayi sannan tayi addu a,ya Allah kasa duk abubuwan nan da nakeji nake gani su zame mani a mafarki neh.

Safwan ya bushe da dariya saboda addu ar da tayi duk awaje tayi ta,don haka yasa hannu ya damki kafadarta yace,"ba mafarki kike ba,ni safwan nace bana sonki sodangi,kuma na sake ki saki daya,don kada kiyi tunanin zan waiwayo gareki har abadan."

Sandarewa tayi,don gaba daya taji na urorin dake jikinta sun tsaya cak sun daina aiki,domin ko yan hawayen da suke zuba sai da suka tsaya,saboda zuciyarta kadai ke bugawa.

Shigewa yayi cikin motarshi ya bata wuta sosai,can kuma ko mi ya tuna 🤔? Sai ya fito daga motar yazo inda sodangin take ya damki hannunta ya turata acikin motar,sannan shima ya shiga ya bata wuta.

Yana zuwa gaf wurin mai gadin ya tsaya,mai gadi ya fito jiki na rawa ya rusuna yace yallabai tafiyarce ta tashi neh?"

Fuska ba yabo ba fallasa ya amsa mashi,"kamar dai yanda na fada maka,idan kaji zaka iya zama kaci gaba da tsaron gidan da babu kowa toh ga fili ga mai doki nan."

Maigadi ya karayin kasa da kansa yace,aini yallabai ka riga ka gama mani komai a duniya,domin wanda ya dauko albashin shekara biyar ya baka kyauta,ba tare da tunanin komai ba,ai baka da kamarshi arayuwar duniyar nan.don haka ni ina nan ba inda zani zan zauna in tsare maka gidanka har zuwa ranar da zaka dawo."

Safwan ya daka mashi wata irin tsawa da karfinshi yace,"waye ya fada maka cewar zan dawo kauyen nan?dama wani dalili ya kawo ni yanxu kuwa babu dalilin,gida kuma na sodangi ne don haka ita zaka tambaya izinin zama."yana gama fada mashi haka ya figi motar yaguje ya bar wajen.

Maigadi dai bai damu da halin dayaga yallaban nashi ba,shidai sai rafga godiyya yake abinshi.

Gaf da santar da zata kaika har kofar gidan su sodangi suka kai,don haka safwan tsayawa yayi ya sake fito da ita zai shige motarshi tayi wuf ta rikeshi tare da sakala hannuwanta aruwan cikinshi ta rungumeshi ta baya.

Shi kanshi sai da yaji rikon da tayi mashi har acikin zuciyarshi,saboda ko alokacin runtse idanuwanshi yayi,daga bisa ni kuma komi ya tuna oho yasa hannunshi ya fincike nata hannuwan ya shige motarshi yaja ko waiwayenta bayyi ba.

Love you sis 😘
08033481518
[4/8, 10:25 PM] binta garba: 🍒🍒🍒SODANGI🍒🍒🍒

Na

Binta garba saleh daudawa

20

I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks & love you all 😘😘

Bin motar tashi tayi da idanuwanta har ya bulle ta daina hangenshi sai dai kurar daya bado mata.

Wata irin ajiyar zuciya taja tare da zube dukkan gwiwoyinta akasa,sannan kuma wasu hawayene masu zafi hadi da radadi suka gangaro mata.sam sodangi ta rasa gane shin asama take ko akasa ko.

Anan tayi zaune har aka fara kiran sallar farko ba tare data san abinda yake faruwa da ita ba.

Duk acikin wannan dare, molasa ta farka daga barcin data fara,sakamakon wani mummunan mafarki da tayi akan sodangi yasa ta tashi afirgice ta rasa abinda yake mata dadi.

Tashi tayi ta nufi dakin ardo, ta tura kofar dakin ahankali tare dayin sallama.

Cikin yanayin barci ardo ya amsa,da yake mutum ne mara nauyin barci,don haka sai ya tashi zaune har ta iso inda yake ta raba kusa dashi tace,"ardo na gaza komawa barci saboda wani mafarki danayi wadda ya tayar mani da hankali."

Ardo ya tarbi numfashinta da sauri yace,"ina fata dai da kika farka kinyi addu a koh?saboda kusan mafarki duk daga shaidan ne,shi yasa manzon mu ya horemu dayin addu a kamin mu kwanta barci."

Molasa ta numfasa sannan tace,"ardo duk nayi wallahi,amma zuciyata ta kare na rasa abinda yakeyi mani dadi."

Hannu yasa ya rufe mata baki yace,"yi shiru molasa,nace kici gaba da addu a,saboda musulunci ya fada mana ba a son bayyanar da mumunan mafarki."

Dole molasa ta dakata,saboda ji take idan bata fada ba abin zayyi ta damunta ita kadai.

Kasa konawa dakinta tayi,don haka sai tayi kwanciyarta dakin ardo har sai da ta farajin kiran sallar asuba sannan ta fito ta taba kofar sadah,sai da ta tabbatar ya tashi sannan tayi alwallah ta wuce dakinta.

Sadah da ardo kusan tare suka fita zuwa dan karamin masallacin da suka hada da kansu acikin yar rugar.

Sodangi dake zaune cikin tubayar yashi sai kawai ta samu kanta da mikewa tsaye ta hau tafiya ta nufi hanyar gidansu ba umh ba umh umh har ta isa.

Kanta tsaye ta shige cikin gidan, adai dai lokacin molasa ta fito daga inda suke dora sanwa zata koma daki,sai kawai taci karo da sodangi,yanda kasan sakago(robbot) haka take tafiya.

Domin ita kanta molasa don gari ya fara haske da sai tace ko aljana ce,da sauri tabi bayanta har daki ta sameta zaune akan dan bonon molasa.

Molasa ta samu kusa da ita hankali atashe ta zauna gami da dafa kafadarta ta kira sunanta,"sodangi kina lafiya kuwa?miya faru kika taho da duku duku haka,kuma ina mijin naki?"

Babu amsar data samu daga wurin sodangi,illah binta da idanuwa kawai takeyi,hankalin molasa ya kara tashi ta kama sodangi ta girgiza sosai wai don ta dawo hayyacinta amma inaa........
Don haka sai kawai molasa ta samu kanta da fashewa da kuka tana cewa,"shikenan na shiga ukku na lalace sun salwantar mani da hankalin yarinya,oh ni molasa ina zan saka raina."

Fasa kukanta shigowarsu sadah,kuma duk akan kunnensu take wadannan maganganun don haka cikin sauri suka nufi dakinta ardo yana ta faman kiran sunanta.

Ganin sodangi firkai firkai jikinta ko abin rufa babu ga idanuwanta sun kyame sun bushe yasa su duka dukayi turus atsakar dakin.

Sadah neh yayi ta maza ya isa gaban sodangi ya durkusa yana kiran sunanta,"sodangi!!! Miya sameki? Kuma ina safwan din?"

Yanda tayiwa molasa haka tayi mashi shima,don haka afirgice ya juya ya kalli ardo yace,"ardo ko yan fashi duka shigar masu?

Ardo daya sandare abakin kofa,amma dayake namij neh ba farat daya zaka gane haka ba,duk idanuwanshi suna akan sodangi yace,"bamu da tabbas sadah,amma taso muje gidan tunda sodangin ta gaza ce mana komai."

Juyawa sukayi,tare da daukar sandunansu,ita kuma Sodangi sulalawa tayi ta kwanta akan gadon,amma molasa tana lura da wasu hawaye da suka gangaro mata ta gefen ido.

Ardo da sadah babu wani bata lokaci da sukayi sai gasu gidan safwan,da yake maigadi yasansu da saurin shi ya fito suka gaisa da ardo,sannan ardo ya tambayeshi ko inah maigidan?"

Maigadi yayiwa ardo bayanin tafiyar safwan,ya kara masu da bayanin cewar ya daiji yallabai din yana cewa ya tafi bazai dawo ba har abada."

Dukkansu gabansu neh ya fadi dammm,saboda babu wanda yayi tunanin jin haka,sadah ne ya kalli ardo yaga jikinshi har rawa yake,watau duk yanda yaso ya taushe tashin hankalin dake ranshi sai da ya bayyana,zare sandar dake hannunshi yayi ya bugi kasa da ita yace,"wallahi kado baka isa ba,har ni zaiyiwa haka?nayi mashi dare shi zaiyi mani rana,idona idonshi wallah,sadah zo muje gida."

Har sun hau hanyar komawa sadah da tunani ya isheshi yace ardo ina zuwa,bai jira amsar ardo ba ya koma gidan safwan,kai tsaye ya shige cikin gidan yana ta yan dube dubenshi har zuwa dakunan su,saboda babu inda aka rufe.

Takardar daya gani asaman gadon sodangi ta dauki hankalinshi ya nufeta ya dauka tare da saurin budeta.

Abinda ya gani rubuce acikinta neh ya kara razanah shi,saboda baro baro safwan ya rubuta ya saki yar uwarshi,tare dayi mata kyautar gidan da abinda yake acikinsa.

Fashewa yayi da kuka,yayi yayi yay mai isarshi,saboda babu komai acikin zuciyarshi face tausayin yar uwarshi,domin yafi kowa sanin yanda sodangi take tsananin son safwan,a rana daya yazo ya karyawa yar uwarshi zuciya,fon haka shima nan take yasha alwashin muddun ya gamu da safwan sai ya ci mutunchinshi koda kuwa zaisa adaureshi ne.

Share hawayen yayi ya zira takardar acikin aljihunshi ya fito,kai tsaye gidan su ya nufa ya samu har zuwa lokacin molasa tana ta matsawa sodangi akan sai tayi magana tayi masu bayanin abinda ya hadata da mijinta har ya gudu ya barta.

Ba barci take ba,amma ta kama idanuwanta ta rufesu tamkar maiyin shi.sadah neh ya raba gefe daya ya zauna duk jikinshi babu kwari ya kalli molasa yace,"ku kyaleta hakanan,domin idan da zata iya magana da tuni tayi,kuma ni ban zargeta baba,saboda halin da safwan ya sakata aciki ba dan karami ba ne."

Ardo dake gefe ya cika yayi faful saboda bacin rai ya kalli sadah yace,"ka gano wani abun hala?"
Sadah ya zaro takardar dake aljihunshi ya mikawa ardo,da sauri ardo ya amsa tare da budeta ya fara karantawa abayyaneh.

Assalamu alaikum.
Ni safwan Alhaji sulaiman, na rubuta wannan takardar domin in baku hakuri akan abinda zakuji,watau na saki diyarku sodangi saki daya badan tayi mani laifin komai ba.
Har gobe ina son sodangi sai dai ina da wani dalilina na dabam wanda bazan iya ci gaba da rayuwa da ita ba.sai dai kuma na bata gidana da abinda ke ciki kyauta,idan ta samu miji tayi aure .
Inayi maku fatan alkhairi tare da cewa sai wata rana.
Naku safwan.

Wurgi ardo yayi da takardar yana ta zafga sababi,"gidanshi na banza,wallahi idona idonshi,domin wallah idan na hadu dashi sai yayi dana sanin abinda ya aikata mana."

Sadah da rarrafe ya dauki takardar da ardo ya wurgas ya mayar da ita aljihunshi yaci gaba da sauraron ardo,kuma dama yasan halinshi idan ranshi ya bace.

Yau kwanan sodangi biyu agidan,kuma har yanzu babu wani cigaban da aka samu,domin ko abinci sai dai molasa ta tayar da ita zaune ta rinka bata, dai dai da sallah itama sai an bata umurni sannan takeyinta.
Chapter 13 · 0% Book details