Sashe 36
Sodangi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sodangi tayi murmushi ta kalleshi,ta fahimci lallai hankalinshi ya tashi sosai,don haka sai ta kama hannunshi suka mike tsaye tare,ta sake jawo gudan hannunshi ta rike cikin nata suka rinka fuskantar juna,ahankali cikin irin muryarta mai sanyi tace,"safwan ka kwantar da hankalinka,kuma ina son kabi komai a sannu,saboda ni kadai sodangi ta safwance,domin babu wani a zuciyata sai kai.........."
Bai bari ta karasa ba ya jawota ya sake rungumeta ajikinshi har ya rasa inda zai sanya ta don jin dadin maganar da ta fada mashi.
Sun jima ahaka,saboda ayanda taji kwata kwata bai da niyyar sakin ta,don haka sai tayi mashi magana can kasa kasa tamkar mai yin rada tace,"safwan dare keyi,baka gudun........
Hannu yasa ya rufe mata baki yace,"kiyi shiru my dear,kada ki datse mani mafarkin dana farayi,yana da dadi,ga wani sanyin dadi yana ratsa mani zuciya."
Dariya tayi a hankali ta zame jikinta daga nashi,saboda ta lura idan ta biye mashi sai su kwana a tsaye.
Kallabinta ta dauka ta daura akanta ta yafa gyalenta ta kama hannunshi suka fita daga dakin,ban kwana yayiwa mutanen gidan sannan ta rakashi har cikin motarshi,saboda anan ma kokarin tsayar da ita ya rinkayi,domin ayanda yakeji sam baya gajiya da ganinta,kuma baya son abinda zai raba su.
Wasu manyan jikkuna ya hadota dasu yace,"tsarabar da yayo mata ce."
Godiyya tayi mashi, sannan kuma da kyar ta samu ya tafi,saboda sai da ya kai wajen karfe goma da rabi na dare.
Washe gari monday,sodangi ta shirya tsaf kamar kullum ta nufi wurin aikinta,aiki sosai ta kamayi, saboda tasan idan har sameer ya shigo bazai barta tayi aiki sosai ba.
Around 2:00pm taji knocking abakin kofarta,ranta ya bata sameer ne don haka sai ta dauko babban gyalenta ta rufe jikinta dashi,saboda tasha alwashin duk wasu abubuwan data san zasu rinka hadata dashi zatayi bakin kokarinta ta kauda su har sai ya fahimci abinda take nufi.
Madadin ta amsa,sai ta mike da kanta taje ta bude mashi kofar gami da kaucewa gefe daya tana murmushi.
Safwan neh agajiye yake kallonta yace,"nayi fushi sarah,saboda kinji ni shiru amma bazakiyi jajena ba kota waya koh?"
Sodangi tana nan cikin murmushin nan nata tace,"sorry my boss,nima aikin ne ya rikeni sosai,saboda kasan tunda muka samu junewa da company su safwan hutu ya kare mana."
Sunan safwan data fada sai da yasa shi yamutsa fuska kamar wanda aka ambaci wani mugun abu agabanshi,ture maganar yayi ya kalleta yace,"sarat yunwa nakeji."
Sodangi tace,"okay ko ka shigo sai asanya akawo maka abincin anan."
"No sarah,sam na gaji da abincin company nan,kizo muje waje muci kinga daga can ma sai in maida ke gida."
Sodangi tayi jim tana nazarin Idan har ta bishi bazata samu matsala awajen aikinta ba,numfasawa tayi ta kalleshi tace,"sameer akwai sauran aikin da ban ida ba,ko kawai ka tafi."
Sameer ya dan daure fuskarshi yace,"okay to nima na fasa cin abincin,amma kuma ki sani cewar babu inda zani,anan office din naki zan zauna kuma babu wani aiki da zan barki kiyi."
Sodangi najin haka tayi murmushi acikin ranta tace watau shima sameer rigima gareshi kamar safwan,kuma tasan tunda yace haka toh komai ma yana iya faruwa atsakaninsu,don haka sai ta tsayar dashi ganin yana kokarin shigewa office din nata tace,"bari in dauko jikkata mu tafi."
Sameer ya tsaya yana wani murmushi afuskarshi,jikkarta ta dauko ta nufeshi suka juya tare suka bar office din.
A bisa hanyarsu ne sameer yayi ta bakin kokarinshi wajen ganin yaja ra ayinta akan soyayyarshi amma sodangi tayi ta fashewa,saboda daya dauko zancen tsananin son da yake mata sai tayi maza ta canza mashi topic har abin ya fara damunshi.
Burki yaja da karfin tsiya ya tsayar da motar cikin bacin rai yana kallonta yace,"sarat na fahimci baki sona,kawai ina bata lokacina neh akanki."
Sodangi ta kalleshi ta girgiza kanta tace,"sameer ai ban ha ince ka ba kuma ban boye maka komai ba,Kai ne idanuwanka suka rufe kake nuna mani ka mance komai."
Sameer ranshi ya kara bace ya kalleta yace," sarah kina ganin wai sonki zai iya saurin rabuwa da zuciya ta ne?ko kadan ki sani har yanzu ina jinki kwance ale ale a zuciyata,don haka sai kiyi hakuri saboda ban fidda rai daga samunki ba."
Sodangi ta dago kai ta kalleshi sai taji gaba daya duk ya bata haushi,sai kawai ta bude motar ta fito,shima fitowar yayi har yana wani huci tare da kiran sunanta.
Ko a mafarki yaji mai irin wannan sunan sai ya motsa,don haka bada bayan da yayi yaji ana kiran sarat ! Sai kawai ya juya da sauri,ai kuwa idanuwanshi suka dira akansu sodangi da sameer.
Mamaki ne ya kamashi sosai ya zuba masu ido kawai yana kallonsu,acan kuma kadan zuciyarshi ce take zuga shi,"dama wannan shine aikin da sodangi take zuwa?aiki ko yawo?ji yayi zuciyarshi ta hassala kawai sai ya nufesu kai tsaye.
Har ya isa inda suke basu farga dashi ba sai dai kawai sukaji ance,"what brings you two here?"
Dukkansu juyowa sukayi suna kallonshi,sodangi ta firgita sosai da ganin safwan a wurin nan unexpected,juyawa tayi ta sake kallon erea wurin,taga ashe cike yake da manyan kantina da wurin shan coffee irin na matasa wadanda suka amsa sunansu.
Sameer ne taji daga inda yake yana watsawa safwan shima tambayar kwatankwacin wadda yayi masu,"what are you doing here too?"
Da sauri ta waiga ta kalli safwan taga yayi kucin kucin da rai,kuma babu abinda yake shirin yi sai wulakanci,kai karshe ma yana iya kiran waya yace azo akama sameer ko kuma ya dauki matakin da hannunsa.
Yanda taga sameer ta tabbatar shima adhirye yake ya rama duk abinda akayi mashi,don haka sai ta matsa kusa dashi tace,"sorry sir,kayi hakuri,kuma na gode kwarai da gaske,but you should go."
Sameer da yake kallon kallo da safwan sai yayi maza ya juyo ya kalleta cikin tuhuma da mamaki watau shine ma abin kora.
Da sauri sodangi tayi kasa da idanuwanta,saboda yanda sameer ne yake kallonta taji bata iya jurewa.
Kutawa yayi cikin jin haushi ya juya ya koma wurin motarshi ya shiga,ya jima yana kallonsu ta glass din motar sannan ya figi motar a guje ya bar wajen cikin kunar rai.
Love you sis 😘
08033481518
[4/27, 6:57 PM] binta garba: ðŸ’ðŸ’ðŸ’SODANGIðŸ’ðŸ’ðŸ’
Na
Binta garba saleh daudawa
52
I dedicated this love story to my Hausa Novel group & my fans,thanks and love you all😘😘
Safwan daya bi motar sameer da kallo yayi dan tsaki sannan ya juyo ya kalli sodangi ya harareta fuskarshi a daure yace,"dama sameer yake maido gida idan kuka tashi aiki?"
Sodangi tayi murmushi tadan kauda kanta saboda yanda taga safwan har wani huci yake tace,"bazan ce maka a ah ba,saboda idan kayi la akari da wuri daya muke aiki,kaga dole wata rana ka ganmu tare."
Safwan yace,"Hmm,zaki bar aikin a companing su sai inga ta takamar wurin aikin ku daya."kutawa ya karayi saboda ayau ganin sameer da yayi da sodangi ji yake kamar ya shakeshi sannan yaji ya huce.
Sodangi ce ta datse mashi tunanin da yake tace,"mi kazoyi anan wurin,kuma ina abokan tafiyar ta ka?"
Safwan yayi dariya yace,"shan coffee nazoyi nida girl friend dita."
Kici kici tayi da ranta ta dauki hanya taci gaba da tafiyar ta ba tare data sake kallon inda yake ba,amma a kasan ranta ji take kamar ana tafasa mata zuciya don jin haushin amsar da safwan ya bata.
Safwan yayi wata dariyar jin dadi shima yabi bayanta yanayi mata magana,banza tayi dashi kamar ba da ita yake ba.
Ganin mutanen dake wajen sun fara kallonsu yayi maza ya kamata ya shiga wani tafkeken wajen shan coffee dake kusa dasu.
Kai tsaye ya samu wani table da babu kowa akanshi ya jawo kujerar ya zaunar da ita,sannan shima ya zauna ya zuba mata ido don yaga yanayin da take ciki.
Kauda kanta tayi gefe daya taki kallonshi,murmushi yayi yace,"sorry dodangi! I'm very very sorry please !! Kuma wallahi wasa nake maki,nasan dai munyi appointment da kawarki surayya,kuma koda tazo ban samu abinda nake son ji ba,amma na riga nayi wata shawara da zuciyata,don haka kada ki damu."
Sodangi tayi mamakin abinda yake fada,toh komai zai cewa surayya?gashi kuma yace kada ta damu,don haka sai ta share kawai,kuma sai ta saki ranta tunda taji gaskiyar lamarin.
Safwan yayi murmushi ya jawo hannunta ya rike yana kallonta yace,"please sodangi ina rokon arziki awajenki."
Ji tayi abin yayi mata girma sai taji kunya ta kamata sai tace,"minene wannan abun da har sai ka roke ni shi?"
Safwan ya zama serious akan abinda zai fada mata yace,"so nake gobe ku raka ni unguwa keda afnan."
Sodangi tayi kasa da idanuwanta tana nazari,sannan ta dago ta kalleshi tace,"ka mance gobe working days neh?"
Safwan yace kada kanshi yace,"ina sane sodangi,idan dai har kin amince ni da kaina zanje in daukar maki permission."
Yanda yayi neh ya bata dariya,don haka sai ta amince da bukatarshi.
Farin ciki ya kamashi ya tattara hannuwanta duka ya yi kissing dinsu yace,"na gode kwarai sodangi,Allah ya bar mani ke har mutuwata."
A kasan ranta ta amsa addu arshi,sannan ta mike tsaye tace,"inason in koma gida,don kada suji ni shiru."
Cup din coffee din dake gabanta ya kallah yaga duka dan kadan tasha,don haka ya nuna mata da ido ta koma ta zauna ta kuma shanye coffee din ta.
Haka nan cikin jin kunya ta koma ta zauna kamar yanda ya umurce ta.