← Book details Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 60

Sashe 9

Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ita kuwa can dakin ta, shiga ta kwaso duk Abin bukatar ta ta mayar dakin da ya kaita ta tsoffin kayanta na gida duka da aka kawo mata ta kwashe ta shirya a waldrop din tareda jera littafan ta gefe guda,
Cikin natsuwa ta ke komai tanajin sanyi a zuciyar ta saida ta kammala ta nemi wasu kayan ta canja wanda ta cire ta shiga bathroom ta wanke harda hijabin ta shanya a ciki, bata kuma jin motsin shiba
Har rana Y'an Uwan inna suka kawo mata kayan garar ta tareda wasu kayan ta suka yimata sallama domin duk yau zasu tafi, ji tayi kamar ta bisu taga su inna Amma ba Abu mai yuwuwa bane dole ta hakuri, bayan tafiyar su ta nemo wayarta tayiwa yaya Aliyu plashing, yako kirata sukasha hirar su yana Kara yimata nasihohi, tace yakaiwa inna sugaisa, yace baya gida Amma zai turo mata kati tasa takira numbar ta, ai kuwa transfer ya mata Dari Biyar ta Kira inna taji muryar ta,
Alhmdulillah batada matsalar komai domin sam ko duriyar shi bataji a gidan sam iya kacin ta gyaran gidan da girkawa cikinta duk Abinda taso ta kuma yi karatun ta wani lokaci har baccin rana takeyi saboda hutu,
Sam bata lura da baya gidan ba domin yaje meeting Abuja saida Husna tazo gidan bayan kwana biyu take cewa yaya yau zai dawo, banga kina shiri ba irin na matan da mijin su yayi tafiya,? "Tace wai baya nan ne?

Kallon ta Husna tayi, wato suna gidan Amma batasan ma baya gariba, shiru kawai tayi domin ta lura tun zuwan ta taga dakin da RAHAMA take taji ba dadi don haka ta kudurce sai ta yi wani Abu akai, duk da RAHAMA akwai duhun kai Amma zataso ace ta fito ta shigo gari yanda zata janyo hankalin Al Ameen ko baiwa Allah, don haka cikin hilata tasa RAHAMA ta d'an saki jiki da ita har ta fahimci wato zaman nasu na I don't care ne,

Ina labarin HAJARA?

Bayan tarewar RAHAMA da sati daya ta dawo gidan, lokacin baba baya gida Aliyu ne zaune gefen inna duna hirar su cikin farin ciki tana yanka Alaiyaho, ta yi sallama hankalin ta kwance, ta nufi hanyar dakin su tana "sannun ku inna yaya barka da rana,
Ai kuwa wani uban tsalle yayi ya shakota tareda bugata da gini ya fara kwance belt din kugun shi,
Ta fasa ihu domin ta bugu, inna tace inka bar yarinyar nan tayi numfashi sai na ci mutuncin ka, ai kuwa ya fisge gyalen ta yafara narkar ta kamar Allah ya aikoshi saida ya mata ligis yana kokarin saka kafa ya take ruwan cikinta baba yayi sallama,
"Subuhanallah haba Aliyu mezangani haka? "Baba wanna yarinyar don ta raina mutane taje yawonta ta dawo ta shigo gida hankali kwance kuma inkyale ta ai wallahi baba kabani izini in karasa ta kowa ya huta,
Assha haba d'an Albarka, bayan ka gama yimin BIYAYYA ina fatan kadace duniya da lahira zaka bata aikin ka, ai Ali duk wanda yace zai iya hadiye gatari sakar mai bota kagani,
Wuce zuwa harkar babanka Allah yama Albarka kaji, Ameen yace ya mayarda belt dinshi ya fice, inna taci gaba da Abinda takeyi baba ma ko gefen ta bai kuma kallo ba ya shige dakinshi,
Iya buguwa ta bugu domin tsawon rayuwar ta ba a taba narkar ta irin haka ba don haka dakyar taja kafar ta tayi dakin su tana jinyar jikinta,

Tareda lumshe idanun ta ta sharce hawaye " please A yabo accept me kazo muyi Aure inbar musu gidan su lokacin ne zasu meme ni, tafada tana Kara ciro wayarta da ta tsage yanzu saboda baduwar da tayi ta fara bude data ta ganshi online a Facebook, jikinta narawa ta tura mai slm,
Lokacin yana hanyar zuwa gidan shi yana kishingide a bayan mota yana duba sakonni, yaga slm din witch yanda yabata sunan domin ya ankare inzai hau goma zaiga sakon ta, dole yau ya bata Abinda takeso don haka yace "hee please Am married so keep your ugly and your disgusting face to your future husband am not interested, ya kashe laptop dinshi tareda jan tsaki, shi duk wata mace mai cusa kai wurin namiji he hate her yafison mace da ba ruwan ta da ko kai waye he want true love a woman who will love him not because he is handsome or rich,

Hajara taji ciwon reply dinshi sosai yanzu kamar ita zai wulakanta yasan ita wacece kuwa? Ai ba son shi takeyi ba kawai taimakon shi zatayi yasamu big girl like her, I hate people who are so proud of their self,

Gidan su yafara zuwa domin ganin momy, tayi mai welcome, tace ina RAHAMA yaushe zaka kawo min ita? "Waye haka?
"What? "Yes momy please who is she? "Your mother, kaji uwarka ce yanzu Abinda zakayi kenan Al Ameen? Yanzu yagano she is talking about that girl, "oh momy ai ni bansan sunan taba and ni nan nace mufara zuwa saboda Am missing you, " yayi kyau kaji, duk namijin Arziki zaiso Aure zaiso mace a karkashin inuwar shi amma kai kasamu gata iya gata kana turewa Iri ne mai kyau muka nema maka Al Ameen karkayi wasa dashi karike damar ka tun bata kubce mska ba zan dauki mummunan matakin da bazaka ji dadin shiba, idan baka warke bane mu koma Asibiti a dora ka akan wasu medication din,
Saboda mundamu da lafiyar ka muka yima Aure Amma saboda ka raina mu shiyasa kake nuna bamu isa ba, bari babanku ya dawo zanfada mai komai shi da kake tsoro kaji Maganar shi,

Ranshi yaji ya baci" yanzu saboda Allah momy akan wannan yarinyar zan gwada lafiyar tawa ya zatayi dani? Ko fa kosawa batayi ba baby Husna ma tafita mature duk da ina mata kallon karama ni gaskiya I can't shear my body with that thing never, daga gani bagidajiya ce sai aikin jakanci sam jikinta kamar injin yanzu zaka bata aiki ta gama ni tsoro ma take bani,
"Yanzu wahalar da Y'ar mutane kakeyi Ashe Al Ameen? "No momy nifa sau daya naganta, a gidan nan nayi tafiyata, ok jeka Al Ameen zaunique u,
Tafada tana shigewar ta daki domin ya mugun bata haushi,
Fitar shi yayi tareda kudurin sai ya wahalar da ita yau saboda tajanyo mai fushin momy,

Da taimakon Husna ta gyare mata dogon gashin ta tareda, busar mata da drayer ta, kuma sata tayi wanka tareda zaunar da ita ta caba mata Ado daidai ba hayaniya tayi mata geling gaban goshinta inda suma ta kwanta, cikin akwatin Auren ta cire mata wata riga doguwa mai guntun hannu ta roba rigar ta hadu karshe jace, ta ciro wani ribbon a jikin rigar ta daure mata jelar dogon gashin kanta dake boye,

Husna kanta ta raina kanta yau domin ganin surar matar yayan nata a bayyane, tasan wannan jikin dole ya firgita namiji mai lafiya don haka har matsuwa take yayan ta ya dawo yagani Abinda ke boye cikin hijabi, ina ga RAHAMA ta waye lallai za ayi mace a nan wurin irin matan nan unique, girar ta lips dinta eyebrow dinta kalar fatar ta mai tsananin laushi da santsi ga tafin hannun ta mai wani irin taushi kamar na jariri, bazakasan hakaba sai hannun ka ya taba inji Husna a zuciyar ta, taji tanason matar yayan nata ta, waye da kyau yanda zata murda, mai kambu,
Dama tasa ta sun shiga kitchen duk da Husna is not good at cooking but she insist domin taga nata kwazon saidai tasha matukar mamakin ganin yanda take girki cikin tsari da kwarewa, anan ma saida ta Kara jinjinawa irin Damin da yayan ta ya kwasa a Kala,

Sallamar shi sukajiyo Husna ta fito domin yaga motar ta a gidan shiyasa ya saita kanshi, ta rugo tareda Rungume shi" Oyoyo my lovely brother, welcome home, " sarkin yawo naje gida banganki ba a she kina, nan? "Yes nazo wurin sister in low dina, Tabe bakin shi yayi yace ok let me fresh up and come, "to kayi sauri we are cooking special dishes for you,
Juyowa yayi tareda bata kallon you are jocking "yaushe kika fara aiki? Kai yaya zaka gani I can work sosai harda girki ka tanbayi momy, naji, yafada ya shige Abinshi ta koma kitchen,
"Yaya ya dawo baki fito ba, wani irin tsoro ke kamata dmtunda taji muryar shi she is happy when he is not Around yanzu kuma yadawo,
Don haka da sauri tafito ta nufi dakin ta ta dakko hijabin ta karami fari tasa akan rigar because she can stand ya ganta a haka gaskiya her chest is showing sosai gasu da girma kunya takeji gaskiya, dariya Husna tayi ganin ta da hijab, "I thought kinje gaida yaya ne Ashe ke hijabi zaki saka? Murmushi kawai tayi ta karasa abinda takeyi,
Pride rice ta hada lafiyayya da kuma pepper chicken dake tashin kamshi tareda coconut juice, a wani kyakkyawan jug tadaiyi ne saboda Husna tasan bazai taba ciba Amma badon tanason ta burgeshi ba, tasan bazata taba burgeshi ba a rayuwa and she don't want to impress him at all tasan yafi karfinta as he said,
Chapter 9 · 0% Book details